KUNCIN ZUCI

The End

by @bintuuu

Kwana biyu da faruwan hakan Ahmad yayi deciding kiran Anty Amnah dan yanda Na'ima ta dage da son zuwan nan yasan sai ya hada da hakan, aikuwa da ya kirata ya tambayeta ko hakan is safe itama tace A'a, nan yaba Na'ima wayan suka gaisa tace mata "Habibtin Mami so kike  ki tsokalowa kanki rashin lafiya ana zaune qalau?" a sanyaye ta amsa da "A'a" sai Anty Amnahn ta cigaba "Kinga ke naki kalan cikin ba mai fitina bane, sai ki nutsu karkiyi stressing kanki da wani tafiye tafiye, first trimester is a risky step daughter, daga nan har ya wuce wata biyar dole zaki kiyaye abubuwa dayawa da zai janyo miki matsala kinji" nan ma ta amsa da "Toh Anty" sannan suka dan tattauna gameda health issues dinta, da haka ta miqawa Ahmad wayan jiki a sanyaye.
Aikuwa kamar su Mamin sun san tana cikin kuncin rashin zuwan sai ga kiran ta ana gobe zasu tafin, bayan Na'iman ta dauka suka gaisa tace mata "Kiyi hakuri ki zauna kinji Habibti, ko bakije nasa celebration din ba ai akwai na Abu in Allah ya kaimu" tace "Toh Mami, zan kira through zoom in gaisa dashi in kun isa" Mami tace "Ba damuwa Habibti, Allah ya sauqeki lafiya" da haka ta bawa Abba dake gefenta suka gaisa sannan sukayi sallama..Haka Na'ima na gani yawancin Familyn suka tafi Toronto babu ita, saidai video call da ta rinqa yi dasu har suka dawo.

Cikinta na da wata biyar aka saka ranar bikin Nafisa sati shida, zuwa sannan cikin yayi wani irin girma kamar me cikin wata bakwai, dan wani irin tsinin ciki Na'ima tayi da yake bawa kowa mamaki, most at time in Ahmad ya dafa saman cikin da hannuwansa yakan ce "Babe ko twins ne acikin nan?" sai ta amsa da "Ba nace muje a duba ba kaqi" nan zeyi murmushi dan yace mata bayason a duba, yana maraba da ko wane irin kyauta Allah zai musu. Ana tafe bikin Nafisa ya fara matsowa lokacin da Na'ima ta shiga cikin wata na shida, a nan ne kuma cikin ya fara mata nauyi sosai har batason fita ko ina in ba dole ba, ana sauran sati biyu bikin Ahmad ya kaita gidan Mamin, da zumbulelen hijab dinta ta fito daga motan bayan Ahmad ya bude mata cab din sai yayi murmushi na ganin yanda taketa kokarin kare cikin da hannunta a cikin hijab din, yace  "Babe, cikin nan fa ko daga mile guda za'a iya hangosa, ki daina kokarin rufewan nan" sai ta kwabe fuska tace "Dan Allah kabari" bai bar murmushin ba yace "Naji nabari, let's go inside" da haka suka nufi gate din gidan, a falo suka tadda Mami kadai da Lantana suna magana, sai da suka gama gaisawan tace da Ahmad Abba yana falonsa tareda su Faruk da Al'ameen sannan ya nufi can, sai ta kalli Na'iman tace "Sannu Habibti, ya jikin" ta amsa da "Alhamdulillah" sai Lantana tace "Bari na kawo miki ruwa, sannu ko" da haka ta nufi kitchen din ta barsu, sai Mamin ta sake cewa "Kina shan maganin can da na aika mikin" ta gyada kai tace "Eh Mami, amma kafar ce har yanzu bata daina kumburin ba kadan kadan" tace "Zai sauqa Habibti, ai da sauqi tunda ba sosai bane, kina dan motsa jikin naki karki rinqa yawan kwanciya" nan ma tace "Toh Mami", bayan tasha ruwan ta miqe a sannu ta nufi dakin Nafisa, tana shiga ta ganta itada Husna suna bubbude dinkunan su, sai tace "Gani nazo, Ina nawa kayan" miqewa Husna tayi tace "Anty Na'ima da alamun sai mun hada miki da sanda fa" Nafisa na murmushi tace "Kinganta ta habaka ko, Allah yasa hudu zata haifo mana" sai Na'ima ta harareta tace "Kayya, kina hanya dai Nafee" nan duk sukayi dariya sannan Na'ima ta zauna a kan gadon suka cigaba da hiran su da ta shafi bikin.
Da bikin ya matso tun ana sauran kwana hudu ta nemi Ahmad ya barta ta koma can da kwana har sai an gama, suna zaune a falonsa lokacin da ta tambayesan, nan yace baisan zancen ba, sai ta kwabe fuska kamar zatayi kuka tace "Ayya zuwa da dawowan zai ta bani wahala" anutse yace "Babe, zamanki acan dinne zaki fi shan wahala, zakiyi ta saka kanki cikin ayyukan da zasu wahalar dake, and beside that...sauran qananun uzurikan ki fa? wa zai maida hankali ya rinqa miki?" tace "Mami zata taimakamin" yana kallonta yace "Itama tanada nata hidiman akanta" sai ta sake cewa "Nafisa" nan kuma yayi murmushi yace "Amaryar?" ta gyada kai, sai ya kamo hannunta yace "Babe, ko bakije anyi hidiman nan dake ba, kowa yasan uzurinki kinji" sai ta gyada kai ahankali tace "I just wanted to be there for her" yana murmushin yace "I know...and she knows too, she sees your efforts even if you're not there" sai ta sake gyada kai tareda kwanciya a jikinsa yayi wrapping hannunsa a bayanta, shiru sukayi a hakan sai kuma cikin sanyinta tace "Kafana daya na ciwo" sai ya danyi dariya yace "You see what i mean?" da haka ya sake ta sannan ya sunkuya yana duba kafar tana kallonsa batace komai ba.

Aikuwa ana gobe daurin auren ta rinqa roqonsa ya barta ta kwanan, nan ma dakyar ya yarda ya kaita da dare, bayan yayi parking ya juyo yana kallonta sai tace "Boo, I'll  be fine" sai ya kamo hannunta yace "Karki kwana cikin jama'a, ki tafi dakin Mami" nan kuma tayi dariya tace "Toh, zan tafi dakinta da wuri in kwanta, sannan zan dauko ruwa na in ajiye a kusa, sannan bazan bi su Nafisa duk inda zasu je ba, sannan..." sai ya katseta da dora yatsansa akan lips dinta yana murmushi, bai bar kallon idanunta ba ya kwantar da muryansa yace  "Sannan, give me my goodnight kiss" sai ya matso ya hade bakinsu guri daya.
Tana shiga falon gidan kuwa ta same shi cike da Family, wasu ma bata taba ganinsu ba, wasu kuma rabonta da su tun lokacin aurenta da Ahmad, su Anty Amnah da Fatima ta fara hangowa a tsakiyar jama'an sai ta qarasa tana sunne kai cike da kunya ta fara gaishesu suna amsawa, wasu na fadin "Amaryar Ahmad ce ko?" nan ma sai ta sunne kai, Anty Amnah tace "Da kinyi zamanki sai goben Na'ima" Fatima tace "Wallahi dai, su Nafisan na can dakinta da jama'a itama" sai ta amsa da Toh sannan ta nufi stairs tana jin nauyin idanunsu akanta, falon Mami ta fara shiga ta sameta itama da nata baqin, nan ta hau mitan zuwan Na'iman itama, bayan sun gaisa sannan ta tafi dakin Nafisan, samu tayi dakin cike da kawayenta, wasu a gado wasu a qasa ana hira, sai Nafisan ta sauqo daga kan gadon ta karaso gurinta tana fadin "Bobo da kin bari sai gobe da safen" tace "Hankalina yaqi kwanciya wallahi, ji nake kamar ina missing abubuwa" sai su Husna dake kan gadon suka fara dariya, tace "Aikuwa anayi babu ke, qaraso ga gurin zama Anty na" sai Nafisan tace "Bari in debo miki abinci sai kiga dinkin naki toh, sai jiya Meerah ta kawo" tace "A'a naqoshi, bari na huta sai in gani" da haka suka matsa mata ta zauna akan gadon ta cire hijabinta aka hau hiran da ita su Lauren na tsokalan ta tayi tulelen ciki. Sai da aka fara bacci a gidan sannan Mami ta shigo dakin Nafisan tana kallon yanda su Na'iman suka duqunqune akan gadon kusan su shida tana tsakiyarsu a kusada Nafisa, sai ta qarasa bakin gadon tana cewa "Sai da jikina ya bani kina nan a matse Habibti, maza tashi muje dakina, bakiga yanda kika danne jikin naki bane" sai Na'ima ta miqe zaune idanunta cike da bacci tace "Bamu matsu ba Mami" tace "A'a tashi, ga gadona can mutum dayace akai" sai Nafisa ta miqe zaunen itama tace "Nima zanje can din Mami" tace "Toh ku taso sai suma su samu sakewa, kun wani dunqule kamar bakusan ciwon kanku ba" da haka ta juya suka miqe tareda bin ta zuwa dakin nata. Ashe da Nafisan ta biyota tanason confiding da aminyar tata ne, sai kuma suka samu matar dake dakin ta koma guest room gurinsu Anty Amnah, nan suka hau gadon suka kwanta sai Nafisan tace "Bobo, inataso kizo din wallahi zuciyata sai tsinkewa take, saida auren yazo kuma nakejin wani iri" sai Na'iman ta kamo hannunta, anutse tace "Babu komai dai Nafee, haka yawancin amaren suke ji in auren yazo, in sha Allah you'll have the best marriage life Nafisa, I'm sure Lamin will be the best husband you could ever imagine" sai Nafisan tayi murmushi tace "Thank you Bobo, I'm glad you're here"  murmushi tayi suka cigaba da hiransu har bacci ya daukesu.
Washegari ya kasance juma'a ranan daurin auren aka tashi da hidima a gidan, zuwa karfe goma 'yan'uwan Na'ima na kano da Adamawa suka iso suma, aiikuwa su Hajiya dasu Jummai sunga karamci gurin iyalan Wadzani, dan Mami taji dadin zuwansu wanda har hakan ya nuna a fuskarta sosai, su Mummy kuwa daman sama sama tazo itada Murja da Ummi, dan Laila bata dawo qasar bama kwata kwata.
Sai da aka taso daga masallaci aka daura auren Nafisa da Lamin akan sadaki million biyar, nan gida ya hau guda sai kuma Nafisa dake zaune a gefen Na'iman ta hau kuka, Na'ima ta dafa ta tana bata hakuri itama jikinta duk yayi sanyi, dakyar suka samu tayi shiru bayan su Anty Amnah sun shigo suma sun lallabata sannan aka ce ga Angon can yazo gaisuwa da kuma ganin Amaryarsa, dan dinner mai rai da lafiya za'a buga zuwa anjima da dare, Na'ima da Husna ne suka riqo Amarya Nafisan dake lullube cikin veil din milk color gown din dake jikinta mai bala'in kyau, tafe suka da agaba while sauran kawayen Nafisan suna biye dasu, sai suka nufi side din su Faruk  da akace musu angon na can tareda abokansa, aikuwa suna shiga suka samesu dayawa a falon ga Angon nan a tsaye yana jiran isowar Amaryarsa, Ahmad dake zaune kusa da Adam ya miqe idonsa na kan Na'ima dake murmushi suka miqa Nafisan gurin Angonta, aikuwa ba kunya Lamin ya riqo hannunta sannan ya zaunar da ita akan kujera kawayen amarya da wasu daga cikin abokan suna daukan moment din a wayoyinsu, sai Ahmad ya kamo hannun matarsa suka dan ja baya daga gurin jama'an, saida hankalin kowa ya tafi kan Amarya da Ango yayin da ya bude fuskarta sannan Ahmad ya duqo ga kunnen Na'ima yace "Babe kinyi kyau" sai tayi murmushi tace "Kaima kayi kyau sosai" yana kallon cikinta yace "Kinci abinci?" ta gyada kai sannan ta maida kallonta gurinsu Nafisa da zuwa sannan Lamin din ya zauna a gefenta tana ta sunne kai.

Sai dare da za'a tafi wajen dinner sannan kafafun Na'ima suka fara ciwo, amma ta danne bata nuna wa kowa ba gudun a hanata zuwa, da akazo tafiya ma sai ta zillewa motan Ahmad data hango yazo tareda Angon zasu dauki Amarya, sai ta shige cikin kawayen Nafisan suka bi wata motan daban aka kaisu while tasan yana nemanta dan har kiranta yayi a waya bata dauka ba, aikuwa tunda ta zauna a seat daya tare dasu Anty Amnah yake kallon gurin, yana zaune tareda dasu Adam da sauran abokan angon a nasu section din amma ba'a seconds talatin bai juyo ya kallosu ba,  Fatima tayi murmushi tace mata "Anty Na'ima kinsa Yaya yanata kallon gurin nan, halan baisan kin taho ba ko" sai Na'ima tadan juya suka hada ido dashi tayi saurin dauke kai, dan saida tazo gurin ta fara dana sani itama jin yanda kafafunta suka qara nauyi, can kuma sai ta hangosa ya miqe ya nufi hanyar fita daga hall din shi kadai, bai jima da fitan ba Abu ya nufo section dinsu yace mata "Anty Na'ima kije Yaya yana kiranki a waje" sai ta amsa sannan ta miqe jiki a sanyaye sai Anty Amnah tace "Habibti ki bisa ku tafi in ya nemi hakan, you look tired" murmushi tayi sannan ta bi bayan Abu suka fita batayi ko sallama da Nafisan ba, tana fitowa ta same shi a tsayen kuwa yana jiranta, sai ya qaraso gareta ya riqo hannunta suka nufi motarsa dake parking space bai ce komai ba amma fuskarsa bayyane take da bacin rai, sai da ya kaita gurin motan sannan taga ya duqa yana duban qafarta, nan ta sha jinin jikinta daya dago yana kallonta, rai a bace yace "Kinga abunda nake gudu ko, I knew it sai kafanki sun kumbura, meyasa bakya jin maganata ne wani lokaci Na'eemah" sai ta fara kokarin yin hawaye tace "Kayi hakuri" bai kulata ba ya bude mata cab din motan sannan ya fara taimaka mata ta shiga da kyar sai ya zagaya ya shige suka bar event centern, har suka isa bai kulata ba sai kallonsa take jefi jefi amma ta kasa masa magana dan ganin yanda ya hade fuska, da suka isa gidan ma sake kama hannunta yayi suka tafi a nutse har suka qarasa cikin falon, nan kuma ya saketa ya nufi kitchen tana kallonsa, bai dade ba ya fito hannunsa riqe da ruwa yana sha, sai ta kwantar da murya tace "Kayi hakuri dan Allah" tsayawa kallonta yayi da farko sannan kuma ya qaraso gareta yace "I knew you weren't okay the moment i saw you, da haka zakiyi ta zama da ciwon kenan?" sai ta girgiza kai ta fara hawaye, nan kuma ya kamota suka zauna a kujera ya miqa mata ruwan ta karba  sannan ya dago kafan yana matsa mata kadan kadan tana kallonsa...Gidan bikin da Na'ima bata sake komawa ba kenan har saida aka kai Nafisa gidanta dake nan cikin Abuja kafin su koma London itada Angonta..

Cikin Na'ima na shiga wata bakwai Ahmad ya fara musu preparing barin qasar zuwa London, dan acewarsa a can zata haihu saboda strong passport na babyn da zasu haifa, A farkon da ya fada mata sai tace "In na haihu a nan din ma duk daya ne ai" ya girgiza kai sannan yace "No Babe ba daya bane, i want an automatic citizenship for this child, visa-free and the rest, I'm a citizen there and i want the baby to be also" shiru tayi sai ya sake cewa "Da Canadian ko U.S passport nake tunani amma kinyi nauyi dayawa Babe, bazaki iya jure zaman jirgin ba, we'll go with the British one kinji" sai ta gyada kai tace "Allah ya kaimu" ya amsa da Amin. A wani yammaci yaje gidan mahaifansa dan sanar dasu batun tafiyan sai ya samu Mamma zaune a falonta ita kadai, sai bayan sun gama gaisawan har sun kama wata hiran sannan ya fada mata, sai tace "Da naga shiru har kun kawo zuwa yanzu sai nayi tsammanin ko bakada niyyan hakan" sai ya girgiza kai yace "Muna jiran a gama bikin Nafisa ne" tace "Hakan yayi, amma bakaga na Canada yafi?, kuma akwai manyan likitocin acan ai" anutse ya amsa da "Farko nan na fara tunani, amma sai naga kamar London zaifi" sai tace "Doctor Lara tananan ai, kamanta ita ta karbi na Fatima a lokacin da zata haifi Hamranta, kuma passport dincan is second to none other than U.S" sai ya danyi jim baice komai ba, nan ta sake cewa "Amma in kaga na British din yafi duk babu matsala" sai yace "A'a sai ayi yanda kikace din, daman Ina tunanin zaman mu a kusada Anty Amnah ne" tace "Eh kanada gaskiya, kuma yanda tayi nauyin nan zata iya taquruwa da zuwa Toronton" "Hakan ma yayi, da idon sani a kusan yafi gaskiya, Allah ya sauqeta lafiya" sai ya amsa da Amin suka cigaba da wani hiran tasa aka kawo masa ruwa. 
Ana gobe zasu tafi Na'ima ta kira su Abbanta na kano da kawunanta na Adamawa ta sanar dasu sannan Ahmad ya kaita gidan su Mami ta musu sallama, nan ta samu Mamin kadai da 'yan mazanta kawai a gidan, sai dare Ahmad ya maidasu gida bayan su Abba sun cika su da addu'o'i, a washegari jirginsu ya daga zuwa England, sauqinta a first class suka tafi sai Na'ima bata taquru ko kadan a tafiyar ba, a gidan Ahmad da ta sani dinnan suka sauqa sannan washegari ya kaita asibitin su Anty Amnah dan a fara dubata tun wuri, aikuwa basu koma gida ba saida takardun EDD'nta.
Sai da lokacin ya wuce da kwana biyu sannan naquda ta tashi mata gadan gadan, sauqinta ma komansu yana shirye Ahmad yayi asibiti da ita a hanzarce...And after a short agonizing labor pain likitocin suka mata duk abunda ya kamata sannan ta haifo yarinyarta kyakkyawa kamar Ahmad, a splitting image na Babanta ba abunda ta baro na Ahmad a fuskarta, haka Anty Amnah ta miqo masa ita kafin akaita dakin jarirai dan ya kalleta, ya tsaya yana kallon yarinyar hawaye na zuwa masa, nan ya hau tambayan lafiyan Na'iman cikin tashin hankali, sai Anty Amnah tace masa ya kwantar da hankalinsa tananan lafiya, few stitches aka mata na dalilin girman yarinyar ya qarata kadan, sai kuma ta jasa suka koma dakin haihuwan tare, Na'ima na kwance akan gadon ta hangosa riqe da yarinyar a hannu ya shigo sai ta qara karfin kukanta tareda miqa masa hannunta ya qaraso da sauri yana riqe hannun shima zuciyarsa na karyewa, nan ya hau mata sannu har da duqawa yayi kissing goshinta likitocin na kallonsu, tare dashi aka miqata dakin hutu sannan Anty Amnah ta karbi jaririyar ta tafi da ita dan a shiryota, sai lokacin Na'ima ta samu baccin gajiya ya dauketa, yana zaune a gefen gadonta bai motsa ba har Antyn ta dawo dakin riqe da yarinyar ahannu, nan ma ta sake miqa masa ita tana murmushi tace "Kaga yarinya kamar Mamma ce ta haifeta, wannan Husna qarama ce" shima yana murmushin yake kallon gudan jinin tasa sannan ahankali yace "She's beautiful" sai ya duqo yafara karanto mata addu'o'i bai bar kallonta ba, saida Anty Amnah ta gama monitoring qarin ruwan da akayiwa Na'iman sannan ta bar dakin da nufin zataje ta dawo bada jimawa ba, haka Ahmad ya rugume babyn ta rinqa bacci a hannunsa har Na'iman ta farka bayan wasu lokuta, aikuwa bude idon da zatayi ta gansu tsaye akanta sai ya duqa ya ajiye babyn a gefenta nan kan gadon sannan yace "Babe, how are you feeling?" ya qarasa maganan tareda kamo hannunta yana kallonta cikin tausayawa, sai ta dan gyada kai tana kallon yarinyar dake baccinta hankali kwance, ganin haka sai ya dauketa ya miqa mata ita, sai ta kuma fara kokarin tashi zaune ya taimaka mata da hannu daya sannan ya sake miqa mata yarinyar ta karba tana kallonta, zama yayi a gefenta shima ya duqo suna kallon yarinyar atare sannan ahankali yace "Isn't she beautiful?" ya kalli Na'iman yana murmushi sai yaga itama ta gyada kai a hankali tana murmushi bata bar kallon yarinyar ba, sai kuma ta juyo ta kallesa sannan anutse tace "Kamar ka ta dauko" nan ma yayi murmushi yace "Harda ke Babe, ki bude kafarta kigani, irin yatsunki ne" sai ta ja towel din tana kallon kafar duk bata daina murmushi ba, sun dauki kusan minti biyar suna kallon gudan jinin tasu sannan Ahmad yayi kissing gefen fuskan Na'ima a hankali yace "Allah ya miki albarka dear, kinyi kokari sosai, Allah yasa ta zamo me tausayinmu" sai Na'ima ta amsa da Amin sannan ya sake cewa "Kisa mata albarka, ki mata naki addu'an kinji" nan ma ta gyada kai tana wasa da hannun yarinyar ta fara karanto mata addu'o'i, sai da ya jira ta gama sannan yace "Me kikeso a kira dashi?" nan kuma ta juyo ta kallesa cikin ido, sannan ahankali ta budi baki tace "Nafisa....inason a kirata da Nafisa" sai yayi murmushi yace "Then sunanta Nafisa, Allah ya raya mana Nafisa cikin albarka".

Bayan awa daya da wasu mintuna Nafisan ta dira asibitin, tun daga corridor na dakunan suka jiyo muryanta tana kiran sunan Na'iman, aikuwa tana shigowa nasu dakin ta buga qara da gudunta ta qarasa bakin gadon tana kallon Na'iman dake riqe da jinjirar har sannan, tana murmushi tace "Har kin iso" tace "Ai da nasan yau zaki haihu ma da ban bisa Leicester'n ba" sai kuma ta duqa ta dauki babyn tana murmushi tace "Ya Allah....yarinyar nan ta hadu, ma shaaaaa Allah, sannu da zuwa kinji" Na'ima na murmushi ta kalli Ahmad dake zaune a gefenta har sannan shima yana kallon Nafisan da murmushi a fuskarsa, sai kuma Nafisan ta kallesa tace "Yaya wallahi kamarku daya sak" bata jira amsarsa ba ta sake kallon Na'iman tace "Husna ta karbe mana 'ya Bobo" sai Na'ima ta danyi dariya tace "Yarta ce daman ai" Lamin ne ya shigo dakin sai Ahmad ya miqe zuwa garesa yace "Tare kuke ashe" yace "Tare muke fa, wai na tsaya gaisawa da wani old friend dina tayi saurin baroni a gurinsa" nan sukayi dariya sai Nafisan tace "Honey, zo kaga yarinya me kama da Yaya" sai ya taho yana leqan jinjirar shima yana murmushi sannan ya gaisa da Na'iman. Saida Anty Amnah ta sake dawowa dakin sannan Na'ima ta gaisa da ita acikin hayyacinta, nan ta bude musu abincin da ta kawo musu sannan ta zubawa Na'iman wanda tayo mata specially dan ita...
Aikuwa a washegarin ranan su Mami, Faruk, Fatima, Husna da Al'ameen suka dira qasar, nan Mami ta fara kula da 'yarta ba sanya, dadin abun kuma Na'iman ta samu kulawan likitocin sosai sai ya zamto har ta dan warware sai hamdala, aranan aka sallamesu suka koma gidan Ahmad, Hajiya ma da farko ta nemi zuwa amma ganin su Mamin na can yasa ta hakura sai sun dawo gida tukun, aikuwa cikin kwanaki takwas suka dawo qasar aka fara shirye shiryen suna, Nafisa batasan sunan ta aka radawa yarinyar ba sai ranar sunan, fadin irin murnan da tayi ma bata lokaci ne, dan har da hawayenta na murna ta rinqa godiya da karamcin da suka mata, nan ma Na'ima ta sake tambayanta nickname din da take ganin za'a sanyawa yarinyar, sai tace "Aidah"..

Aidah nada wata shida a duniya Na'ima ta barta a gurin Mami suka tafi aikin Hajj itada da Ahmad, dan zuwa sannan babu abunda bataci gashi tayi saurin yin wayo sosai,  bayan dawowarsu kuma aka fara mata ginin makaranta da gidan marayun da ta dauki damaran ginawa a kauyensu, da Ahmad ya nemi sanin wanda zata baiwa ragamar makarantan sai tace masa "Sambo, tsohon abokin mahaifinta da yaje har gidan kawu Ayuba ya nemi maida ita makaranta bayan mutuwar mahaifin nata" har su Mami sai da sukayi mamakin ta yanda bata manta alkhairin wannan bawan Allah'n ba,  a wannan lokacin ne Ahmad ya fara gina mata tamqamemen plaza anan cikin Abuja sai kuma bai mata ita kadai ba ya hada da Baby Aidah itama.

A ranar da komai ya kammalu takardun suka iso hannun Na'ima saida tayi hawaye tana dubansu da daddaya, sai mutuwar iyayenta ya dawo mata sabo, wannan abun alkhairi ne da zataso suna raye a tareda ita hakan ya faru, amma Allah ya fita sonsu, haka Ahmad ya shigo falon yana riqe da Aidah da itama ta riqo qaton teddy bear a hannunta, Simba ne biye da ita yana kama teddyn da bakinsa tana babbaka dariya, sai Ahmad ya zauna a kusada Na'iman while Aidah ta cigaba da dan gudunta tana zagaye falon Simba na binta a baya suna wasa, dago kai Na'ima tayi tana kallonsa, sai ya ga idanunta sun danyi ja kadan, nan ya kamo hannunta cikin kwantar da murya yace "Babe, meya faru?" ahankali tace "I'm missing them..My parents" sai ya sarqo hannunsa a kafadanta ya kwanto da ita jikinsa, cikin lallashi yace "In sha Allah, ladan da zai isa garesu sai yafi komai a gurinsu yanzu haka, they're in our prayers and that's what matters kinji" gyada kai tayi sukayi shiru ahaka, sai kuma ta dago tareda juyawa tana ganin yanda Aidah ke gudu har sannan, da sauri tace "Aidah...karki fadi kiji ciw" bata qarasa ba ta fadin kuwa sai Ahmad yayi saurin miqewa ya daukota, amma kafin ya zauna da ita ta sake zillewa ta koma gurin Simba da gudunta tana dariya sai yace "Baby, be careful Okay" sai sannan tace "We duchtt pilayin Daddy" cikin gwarancin turancin ta da ba kowa yake ganewa ba, dan dariya sukayi Na'ima ta girgiza kai sannan Ahmad ya juyo yana kallon takardun yace "Now, let's go put them in a safebox kafin mu qara wasu a hankali" saita dan ware Idanu tace "Bayan wannan din?..this is more than enough" sai yayi murmushi tareda dan duqowa yayi kissing goshinta sannan yace "Naaa... we're just getting started, I want the world for you Na'eemah, because you're the world to me" murmushi mai fadi tayi sannan tace "I love you Ahmad, thank you for everything" nan ma ya sake kissing hannunta sannan yace "No amount of words could describe my love for you Na'eemah" ......

Alhamdulillah, nan na kawo qarshen littafin KUNCIN ZUCI..
Kuskuren da nayi acikinsa, Allah ka yafemin, kuma masu karatu ina neman afuwarku koda na saba muku a bisa rashin sani..Godiya ta musamman ga ahalin group din Kuncin zuci, masu karatu a Arewapen kuma ban manta daku ba, Ina godiya matuqa da irin qwarin gwiwar da kuka bani da comments dinku... I love you Fatima Dahiru, my dear sister that stays with me throughout this journey, Ina godiya sosai, Allah ya bar zumunci.

Please ban yarda wani ko wata su zanja min labarina bada izinina ba, wannan copyright dinane.

Sai kuma mun sake haduwa a next  littafina mai suna MURADIN ZUCI da zai zo muku a cikin shekarar nan ta 2026 in sha Allah, ku dai ku cigaba da kasancewa tareda ni Bintu Musa, domin yanzu tafiyar ta soma, inanan tafe da wani labarin da zai qara taba muku zuqata, with that.. I'd say Bissalam.