RAYUWAR IRFA💕

Chapter 3

by @autarjajirtattu

*RAYUWAR IRFA 💕*
By 

 

*PRINCESS MINAL* (Autar-jajirtattu💅🏼) 

 

 

 

***

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ 

(J.W.A)  

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 

 The noble writer's team🦋

 

 

      Free Book 

 

               Page  

 

5-6 

 

Dedicated this page to my lovely blood sister habiba💞💕 

Inasonki my sister very much kaman nacinyeki nakeji tsabagen so😁 

 

 

Wowww gaskiya dakin khairat ya hadu sosai, daganin kyau da tsaruwar dakin zakusan cewa na auta ce Kuma abbanta da amminta sunasonta sosai Dadi da qarima Kuma yayanta mafi soyuwa aranta, yanasona yana kaunarta sosai da sosai, komai takeso yana mata, sai dai akoi shida izza, Jiji dakai, gashi bayason magana, Inka ganshi yana magana toda ammin sune ko abbansu, sai ita auta, Indai ba atareda suna to bazaka taba tunanin yana magana ba tsabagen shiru-shirun shi. Dakinta ya tsaru iya tsaruwa ankawata shida kantamenen katifa, komai na dakinta pink ne harta penting dakin pink ne saboda shine favorite colour dinta. Uniform dinta tacire tareda sashi acikin laundry, towel ta dauko mai kyan gaske pink colour sannan tanufi cikin bathroom dinta, Wanda ya hadu iya haduwa kaman ba bathroom bane, sai kace wani room. Tadauki akala good 20minute acikin bayin kafun tafito sanyeda rigan wanka pink colour, gashinta Mai kyau irin na Fulani ta wankeshi shima, drawer din kayanta tanufa, doguwar riga ta dauko pink Mai ratsin ja ja, tadauka tareda ajiyeshi asaman bed dinta, tanufi gaban Miro dinta Wanda yake shaqeda kayan kwalliya, mayukan shafawa, tareda turaruka kala-kala, masu kyau da tsada, zama tayi asaman kujeran Dake wajen tareda fara shafa mayuka ajikinta,tana gamawa tafara cancara kwalliya abunta, Dan khairat mayyar kwalliya ce, tana gama kwalliya yanta kuwa tasa ka rigarta tareda dawowa gaban miron ta tafa feshe jikinta da turaruka kala-kala, masu kamshin gaske, Dan inata duka turarukan da take amfani dashi yayanta yake saya matasu, Dan yanaji da ita. Wayanta tadauka tareda dawowa falon inda tabar amminta anan tadawa tasameta, sannu tamata tareda nufan katon kitchen din Dake falon, duk da akwai abinci kala-kala a kan dinning din, dantaga kuloli akan dinning din, amma bata Sha awan cin komai na kan dinning, duk da tasan cewa amminta ne tadafa Dan ita bata barin masu aiki suna mata qirki saide sutemaka mata da wasu abubuwan a kitchen din. Kawai complex take Sha awansha, aiku hakan akayi tana shiga kitchen din Wanda yaji komai nakayan bukata ya hadu iya haduwa kam kaman akasar waje, complex tadiba tareda cikawa da ruwan dumi, tabarshi na tsawan 5miniute Dan yajika mata dakyau, sannan ta zuba Mai sugar tareda Madara Mai uban yawa, bayan tagaba hada tadauki kofin tanufi falo abinta, zama tayi kusada Ammi tanasha suna fira, harta kammala tareda Maida kofin kitchen, tadawo falo, saman cinyan Ammi takwantar dakanta tana bata fuska tace"Ammi wai yaushe Yaya zai dawone nikamNayi missing nashifa, koya yamanta da mune"tafada tana turo Baki, Ammi kam ba abunda takeyi sai shafa kanta, tana murmushi kwata-kwata baraba khairat da korafi, ahankali cikin nutuwa tace"yayaynki yakusa dawowa, Amma dai bazan gaya maki yaushe zai dawoba"aikam tanajin ance yayanta yakusa da wowa Kuma baza agaya mata yausheba tafara dire-dire , tana Kuka wai itasai angaya mata yaushe Yayanta zai dawo, (Niko nace khairat anqirma amma ba asan anqirmaba) Ammi kam shiru tayi tana kallon iKon Allah awajen khairat,jawota tayi jikinta tana lallabata daker tasamu tayi shiru, sannan tace mata abbanta yau zai dawo kilan ma yakusa, shima bataso gaya mataba kawai de tagaya matane danta takwantar da hankalinta, aiko tanaji ance yau abbanta zai dawo tatashi tahau tsallen murna abbanta zai dawo yau, Ammi kam sai murmushi takeyi na shiri ritan khairat, dakyar Ammi tasamu tanitsu sannan suka hau hira kusan minti talatin dazaman su, sukaji Karan motoci allamun Abba ya iso kenan, aikam dagudu khairat tayi waje, dai dai tana fito shikuma Abba yana fitowa daga cikin motansa, Mai kyau da tsada Jami Aine sukaje daukoshi a airport, dogone kyakkawan shuwa arab, fari ne, idanuwan shi kuwa blue eyes keqareshi, gadogon hanji yadai hadu iya haduwa, bazan Karasa suffanta mukushiba saboda nahango Ammi na hararana takishin mijinta atoo, daguda khairat tafada jikin shi tana murnan ganin abbanta, rugumo ta yayi shima yana Mai murnar ganin autar tashi Dan itace auta a 'ya'yan shi, ahaka suka shiga cikin falon yana runqume da ita, da sallama suka shiga cikin falon, Ammi ce ta amsa musu sallamar fiskanta daukeda murmushi Mai kaya tarwa, sannu da dawowa tamai sannan tace khairat tasakeshi yaje yayi wanka, aikam sakinshi tayi ya haura sama Ammi na biyeda shi, dakinshi dayake jikin part din Ammin yashiga, Ammi Dake biye dashi cikin bathroom tashiga domin tahada Mai ruwan wanka, bayan kaman minti biyar tafito, tana murmushi takara gabansa, tace"abban yara nahada maka ruwan wankan, kashiga kayi sai kasauko kasa kaci abinci"tafada tana murmushi, shima Abba murmushi ne akan fuskanshi, shiyasa kullum sonta ke Kara mamaye zuciyarsa saboda kir kinta, uwa uba hankali ga tarbiya da ya isheta, inda umma ne saide tasa yar aiki ta hada Mai ruwan wanka,shinema yagaji yana Yan aikin tunda ita baruwanta suyita shiga part nashi ko ajikinta, ita ala dole batason wahalar da kanta. rungumo Ammi yana murmushi yace"ohh matata shiyasa nake Kara sonki akoda yaushe, gaba daya kinsacemin zuciya da yawo dolema idan danki yadawo in gaya Mai yasaki kimaida min zuciyata"yafada yana dafe saitin zuciyansa, tureshi Ammi tayi tana dariya tace"Kai bakasan ka qirmaba koh, tokafada Mai mana ni inaruwana, nariga nacinye zuciyan saboda karma yaga wata yace yanaso"tafada tana rufe Ido(Niko nace kema Ammi aikin qirman amma kikesama abbansu khairat Ido lol). Dariya Abba yayi yace "Ina naqirma nikam bayan kullum maidani kikeyi karamin yari Taya zansan naqirma"dariya Ammi tayi tace yatashi yaje yayi wanka aikam dakyar tasamu yatashi yashiga bayi.nikam nace su Ammi sun birqeni gaskiya.falon tasauko ta tarda khairat tana kallo Tama canza tashan zuwa mbc 3 domin khairat mayyar katonceZama Ammi tayi aqefenta sukacigaba da kallon tare, can kaman antsikari khairat tace"Ammi Ashe abban ma yakusa dawowa shine Baki gayamin ba, nifa nadauka sai dare"tafada tana batarai, itakam Ammi murmushi kawai takeyi wato ita khairat Indai batayi riqima ba batajin Dadi"to bana gaya mikina, Kuma abban kunne yace Karna gaya maki saboda yanaso yayi surprise naki"shiru tayi kawai Jin abinda Amminta tace suna Nan agun har tsawon minti ashirin saiga aba yasauko sanye da farar jallabiya, yahadukam, kura Mai Ido Ammi tayi tana kallon mijinta, uban yayanta Kuma abin alfaharin ta.niko nace Ammi kardai amanta auta tana wajen lol. dinning yanufa direct, suma mikewa sukayi suka bishi, Ammi ce tayi serving nasu sannan itama tazauna suka fara ci, bakajin komai sai Karan jokala kawai, harsuka gama bawanda yayi magana, suna gamawa Abba yatashi yace bayaje part din umma, sai yadawo Ammi tamai sannan yace khairat ta tashi tarakashi, qirman part din umma dai dai Dana Ammi ne saide ita Ammi nata yafi kayan more rayuwa saboda iyayenta nadashi, su suka saya mata komai nakayan daki saide Abba yakara mata wasu abubuwan, ita Kuma umma abbane yamata komai saboda iyayenta basu dashi, shiyasama take Kara Jin haushin Ammi akoda yaushe, kasan cewan Ammi tafita komai. Zaune suka sameta saman kujera tana kallo abunta ba laifi umma kyakkawa ce, bahaushiya ce umma, amma tanada kyau saide bakin zuciya, da sallama suka shiga, ciki ciki ta amsa musu sallaman kaman ammata dole, gaisheta khairat tayi bata amsaba yima tayi kaman bata jiba, aikam Abba yaji haushin hakan amma baice mata komai ba, ko sannu batacema Abba ba raliya Dake qefensa ne tace m"sannu Abba yaushe ka dawo"murmushi yayi yace "yauwa yar Abba dazu na dawo"Bai karabi takan umma ba shima yace raliya tabiyoshi suje part din Amminsu ya masu tsarabansu itada sauran Yan uwanta, tashi tayi tabishi tana murna raliya sa ar khairat ce amma taqirmi khairat da watanni, shiyasa khairat tazama itace auta, da harara umma tarakasu tanajan tsaki. 

Part din Ammi Yakoma, saman kujera suka zauna jakan kayan daya dawo dashi yace khairat taje ta dauko a dakinshi, aikam dagudu tahaura sama baijimawa sai gashi tadawo da jaka ahannun ta, bashi jakan tayi yabude Dubai abayane aciki masu Kya, sai riga da skert suma masu kyau da sarkan gold da dankuni ne aciki, cirowa yayi yaware nayaran umma yaba raliya harda na Aliya ma da takeda aure danshi inya yitafi yadawo gaba daya yaranshi yake sayoma tsaraba. 

Amsa raliya tayi tana murna haka yadauko na khairat ma yabata itama sai murna takeyi godiya suka hau Mai kaman ba gobe, sai da yace ya isa Sannan sukayi shiru, dama balaifi ita raliya tanada tarbiya Dan kusan awajen Ammi taqirma shiyasa tasamu tarbiya bakaman sauran yayunta ba, harzata tafi Abba yakirata yabata wani laida yace na umma ne amsa tayi sannan takara Mai godiya tareda fita falon. 

Ammi ma da take qefe nata yabata taringa Mai godiya sannan yabata na danta yace ta ajiye Mai tunda yakusa dawowa. 

Umma kam koda raliya takai mata data bude tadiba itama dogayen rigunan ne aciki ta sarka amma bata godeba mitama taringayi tace tasan na Ammi yafi haka itakam raliya dakinta tawuce tanama ummanta addu an shiriya azuciyarta. 

 

 

IRFA pov 

 

Direct daga gidansu gidansu khalisat ta wuce, da sallama tashiga gidan khalisat Dake wanke wanke ne ta amsa mata sallamar, karasawa tayi wajenta tanacewa"Kai Khalisat yanzu Baki gama aikiba tun dazu"dariya khalisat tayi sannan tace"aike IRFA kinriga kinsaba da wahalanne shiyasa kullum kike gama aiki dawuri, nihar mamaki ma nakeyi yanda kike aiki kaman agogo Kuma bakya gajiya"dariya IRFA tayi Wanda yakara mata kyau ga dimples nata dasuka lotsa abin gonin sha'awa, Niko nace dole samarin kauyen wuro Hashimu su takura mata kowa sonta yake kaman ba Yan mata a kauyen, ita kuwa bata kulasu saboda ba soyayya tasa agaba ba, shiyasama sukecewa tanada qirman Kai wai. 

Tace"khalisat kenan badolena ba nasaba"hira dai sukacigaba dayi Irfa nataya khalisat wanke-wanken har suka gama, ta tayata Sharan gida, sannan taje Tama mamanta sallama suka fita waje yawo. 

 

Nima nace bana dasa Aya anan. 

 

Kuyi manage da wannan Banda lafiya kota-kota. 

I need your prayers. 

Luv your all my fan's ❤️💝 

 

*WRITING* 

          By 

*PRINCESS MINAL*