RIGAR KAYA

Chapter 1

by @sadiyaabdulrazak954

*...RIGAR ƘAYA!*



            BY
SADIYA ABDULRAZAK 

MARUBUCIYAR
Dukan Taiki 
Ku yi mana adalci 
Aure A Yau
Sandar dukan uwargida 
Iya ruwa
Zuciyar Mace 
Miji Goma 
Wani Auren
Da Walakin
Wutar ƙaiƙayi 
Matar shige da sauransu
***


 Page 1

  Hausawa suka ce 'Ɗan'uwa rigar ƙaya!' Shin wane son zuciya ne zai saka ɗan'uwanka ya rikiɗa ya zame maka rigar ƙaya? A wannan labarin za ku ji yadda 'yar'uwar tagwaitakar Muhasin ta zama ƙaddararta.

    A zahiri idan ka kalle ta za ka yi zaton ta fi kowace mace kwanciyar hankali da samun hutu, amma da za ta buɗe maka idanunta da suke a lumshe za ka iya ƙaryata hasashenka kai tsaye, saboda damuwar da yi kwance a idanun, ji take kamar ta dakatar da gudun da driver yake shararawa a titin, duk da ta san dole ne ta je inda za ta je ɗin, tsayuwar motar ta yi daidai da tsayuwar numfashinta, domin ta san abin da hakan yake nufi.

"Hajiya mun ƙaraso" Cewar driver bayan ya juyo ya kalle ta, a zaton shi bacci take yi.

Ta buɗe idanunta, ta cikin glass ɗin motar take kallon get ɗin gidan yarin, zuciyarta ta ninka ƙuntata kamar yadda ta saba ji a duk ranar da ta zo, amma ya zame mata dole ta zo ɗin.

Ta fito cikin takunta na mata masu ƙiba, doguwar rigar atamfa ce a jikinta buba, ta yafa mayafi madaidaici, hannunta riƙe da jakarta. Ba ta buƙatar dogon ɓata lokaci kafin ta samu yadda take so, saboda mijinta sananne ne kuma ba yau ta fara zuwa wajen ba, cikin kankanin lokaci aka sada ta da abin da ta zo yi.

 A cikin gidan yarin, dattijuwa ce duƙe tana ta shara duk da tarin gajiyar dake jikinta, amma hutu na mai 'yanci ne, wata ganduroba ta ƙarasa tana ƙwala mata kira daga ɗan nesa da ita "Asabe".

Ta ɗago tana amsawa.

"Ki zo kina da baƙuwa".

Ta san babu wata me zuwa wajenta sai ita, don haka ta ce"Ki faɗa mata ba na buƙatar ganinta".

Sanin matsayin wacce ta zo ɗin da kuma ganin yadda ake girmamata ya sa ma'aikaciyar faɗin "Ki zo ki ganta, sai ki faɗa mata kada ta sake zuwa".

Ba ta yi musu ba ta bi bayanta a dole, ranta yana yi mata zafi.

 Kanta a ƙasa tana kokowa da hawayenta ta ce "Mama ina kwana".

Matar ta yi banza da ita tana kallon wani wajen.

Ta sake cewa "Ki yi haƙuri Mama ina kan haɗa kuɗin ne, in sha Allah za ki fita nan ba da jimawa ba".

Matar ta ce"Muhasin ba na buƙatar taimakonki, na yafe, na yafe ki Muhasin, ina so ki bar ni na dawwama a nan wajen!"

Muryarta ta karye "Allah wadaran haihuwar 'ya'ya irin nawa, da a ce na san irinku zan haifa da na yi ɓarin cikinku tun kafin ku zo duniya, na sadaukar da komai saboda rayuwarku ta inganta, amma ga shi a ƙarshe na wayi gari a gidan yari, ina kwance cikin sauro kina kwance cikin AC, kina cin kalar abincin da kika ga dama, ina cin gabzar da aka tsakurar mini, mene ne ranar haihuwarki Muhasin? Me na yi miki da na cancanci haka daga gare ki? Wannan shi ne ladan haihuwarki da na yi?"

Kukan Muhasin ɗin ya tsananta "Mama ba haka ba ne, wallahi kin tura ni cikin ruwan zafi ne ba na sanyi ba, Jawad kura ne lulluɓe da fatar akuya, sai da na shiga ƙarƙarshin ikonsa ni ma na gane haka, ya hana ni komai Mama, amma ina ta neman hanyar da zan taimake ki, don Allah ki yi haƙuri".

Mama ta yi mata kallon tara saura kwata "Ya hana ki komai amma bai hana ki kwanciyar hankali ba ko? Ai burinki ya cika, ƙin ƙara ƙiba, kin ƙara kyau, don haka ko da na mutu kin samu madogara".

Za ta yi magana ta ɗaga mata hannu "Ba na son jin komai Muhasin, kuma idan ni na haife ki daga yau kar ki sake zuwa wajena, idan ba haka ba ki ƙaddara kina cikin fushin uwa idan har kin san illar shi kenan, ki je ki cigaba da rayuwar hutu, Allah Ya ba ku zaman lafiya".

Daga haka ta tashi ta bar wajen tana share hawaye, Muhasin ta tashi ita ma tana share nata hawayen ta fita daga wajen, har suka ƙarasa gida share hawaye take yi a fakaice, ta yada zango a falo na biyu ta zauna tana bitar kalaman mahaifiyar tata, ta ɗaga kai tana kallon tsaruwar gidan nata, tabbas tana cikin daula, amma kalar wacce sai dai ka ci ka bar ta a wajen, domin kuwa a cikin watanni uku da auren nasu ko naira biyar ba ta haɗa ta da Jawad ba, wanda hakan shi ne ya rusa komai har ya yi sanadin zuwan Mama gidan yari, gabaɗaya da tunanin inda za ta samu miliyan ɗaya take gudanar da rayuwarta tun bayan auren nata, maganar da ake yi har yau babu ko ficika a hannunta.

"Ke kaɗai na aura, kuma ina sauke duk wani hakkinki dake kaina, bayan haka ba zan iya yin komai ba, ba ni da alhakin kula da mahaifiyarki, don haka kar ki saka ran zan yi".

Ta tuna kalaman mijinta a kan mahaifiyarta bayan roƙon shi ya fitar da Mama, kalaman sun yi mata zafi kuma ta yi alƙawarin ba za ta sake yi masa zancen ya taimake ta ba.

Tana son Jawad, son da ba ta fatan rabuwa ta shiga tsakaninsu, shi yasa take bin umarnin shi sau da ƙafa, a ganinta alfarma ya yi mata da ya aure ta, saboda tana tunanin ya wuce ajinta. Wata rayuwa ce wacce take yawan zuwa mata a imagination, ta sha tunani da tsara yadda Jawad zai so ta har ya kasance mijinta, sai ga shi zatonta ya tabbata sai dai a yanzu ta fara zargin ya aure ta ne ba don yana sonta ba, ita kuma soyayyarsa kullum ƙara linkuwa take yi a zuciyarta, ba don ƙarfin soyayya ba da yi wa so biyayya da babu abin da zai raba Muhasin da kasuwancinta, yarinya ce da ta taso da neman na kanta, tun tana ƙarama ba ta raina sana'a, kuma tana matuƙar taimakonta tun tuni, sai ga shi yanzu ta amince da ajiye sana'a saboda auren Jawad, a lokacin ta yi zaton wannan ba kuskure ba ne tun da yana da halin da zai ɗauki duka ɗawainiyarta, tare da zugar Mama da yadda take wasa ta ta amince za ta ajiye sana'a har abada, an riga an yi wannan yarjejeniya a gaban manya kafin aurensu don haka yanzu ta san idan ta ce za ta mayar da bara bana wani ɓalli ne za ta kunce tsakaninta da mijinta.

Amma a hakan ta yi shahadar tunkarar shi da zancen, da daddare tana zaune a falo ya shigo gidan, kamar kullum a bisa ɗabi'arsa kyakkyawar fuskar shi ɗauke da murmushi yana duba fuskar wayar shi, ta fi zaton saƙo yake dubawa wanda ya faranta masa ko kuma hoto, ita ma murmushin ta ƙaƙalo ta yi, sannan ta tashi ta nufe shi domin ta tare shi, Muhasin mace ce mai matuƙar don a zauna lafiya, tana ɗaukar duk wani gyara a zaman aurensu, tun da ya faɗa mata yana son oyoyo shikanan take yi masa har ta saba, kaɗan ta buɗe mata hannu, kamar hankalinsa ba ya wajenta, kuma ta yi masa uzuri tun kafin ya nema, ta har shi a hankalinsa na kan wayar hannunsa ne, ya zauna a kujera tana sauke numfashi, har yanzu tana murmushi ta ce "Da alama ka kwaso gajiya".

Ya jinjina mata kai kafin ya ce "Sosai".

Ya miƙa mata ƙafarsa, ta duƙa ta zare masa takalman da safa, ta ce"Sannu da zuwa".

Ya amsa da yawwa.

Ta tashi ta nufi Fridge ta ɗakko masa lemon da ya fi so tana faɗin "Yau ka yi dare, tun yamma nake zuba idon ganinka".

"E, na je birthay ɗin wani abokina ne".

"Ya yi kyau, a haɗa ruwan wanka?"

"No, na yi a can yanzu".

Maganar ta ɗan ba ta mamaki, sai yanzu ta lura ba kayan da ya fita da su ba ne a jikinsa, amma me zai saka ya yi wanka a can? 'Saboda tun safe yake zaune da kaya ɗaya, ga shi kuma zai shiga taro' Wannan zuciyar Tata mai ƙaunar shi ta yi hanzarin kare shi ta hanyar ɗarsa wannnan uzurin a tunanin Muhasin, kuma ta gamsu.

"Bari na kawo abinci to, a nan ko a dining?"

Hankalinsa na kan waya ya ce"Babu buƙata, thanks".

Ya yunƙura zai tashi waya ƙare a kunnensa da alamun kira ya yi, ta ce "Amm...Zaujee ina so mu yi magana dama".

Ya katse kiran ya ce"Ina ji".

Ta ɗan yi jim kafin ta ce"A kan sana'ata ne, don Allah ka bar ni na cigaba tun da a cikin gida ne, kuma na fi siyarwa online ba zan dinga tara mata ba kamar yadda kake zato in sha Allah".

Ya karyar da kai alamar gajiyawa da maganar "Gaskiya Muhasin kina da naci sosai, Ya subhanallah! Me kika rasa ne da ya zama dole sai kin yi sana'a? Me kike nema ne?"

Kai tsaye ta ce"Kuɗi, kuɗi nake nema, kuɗin da zan kare mutuncin mahaifiyata" Muryarta ta karye.

"Ai sai kina da shi ko? Idan ba ki da shi bai zama dole ba, sana'a kuma ba na so, ba ta zame miki dole ba ko ƙarata za ki yi a kotun ƙoli, tun da na ɗauke dukan nauyi ki da haƙƙoƙinki da ke kaina".

"Na sani ka ɗauke, shi yasa ban sake cewa ka taimaki mahaifiyata ba, hakkina ne na taimake ta, damar da zan taimake ta kawai za ka ba ni".

"Indai sai ta hanyar sana'a ba zan bada ba".

"Amma za ka bar ni na bi dangi da roƙo?"

"Wannan zaɓinki ne, kar ki sake yi min zancen gidan yari, wannan ke ya shafa, gargaɗi na ƙarshe idan ba haka ba zan ba ki mamaki".

"To zan fara fita daga gobe".

Ya yi mata mugun kallo mai ɗauke da harara ya tashi ya bar wajen, ɗaki ya shiga ya rage kayan jikinsa ya yi wanka, ya kwanta ya yi ɗaiɗai a makeken gadonsa ya yi kiran wayar da yake ta so ya yi tun shigowar shi gidan.

 Bai yi nisa da wayar ba Muhasin ɗin ta shigo ɗakin, fuskarta ɗauke da damuwa ta ƙarasa za ta zauna a bakin gadon, ya ɗaga mata hannu yana cewa "Ina waya da Hajiyata ne, ki je ki yi baccinki Please sai da safe".

Ba ta ji daɗin maganar ba amma ta daure ta ce"Dama na ce abinci..."

"Na ƙoshi".

Ta jinjina kai ta fita daga ɗakin.

Ta cikin wayar ta yi dariya ta ce"Sabon suna kuma ka saka min?"

Ya yi yar dariya "Idan ba haka ba ba za ta tafi ba, naci gare ta kamar kaska fa".

"To ai lokacin ne kamata ya yi a ce yanzu da ita za ka yi fira".

"Idan ta iya firar kenan, sannan ni fa ko son ganinta ba na yi".

"Faɗi gaskiya dai amaryar wata biyun?"

"Wallahi da gaske nake, wannan auren kawai na kira shi da auren ƙaddara fa, kamar wanda ya yi cinikin dare, ko sun ganinta ba na yi, tana da kyau amma ban san ƙibarta ta kai haka ba, kin santa kullum a hijjabi to na yi zaton shi yake cikata".

Ta yi dariya "To ai na ga yanzu kun fi son me ƙibar".

Ya taɓe baki "Cire ni a lissafi, me ake da mace me ƙiba ta zama kamar uwar mata, gara yar shawalwala kamar dai ke ɗin nan".

 Daidai nan Muhasin dake tsaye a jikin windon ɗakin ta matsa, saboda Iya nan kunnuwanta za su iya ji, ta yi ɗakinta da sauri ba ta damu da cewar dare ba ne ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, ita fara ce tass mai matsakacin kyau, amma tana da manyan kyau irin wanda kallo ɗaya za ka yi mata ka ce ga kyakkyawa, ko za ka gano kyaun kaɗan ne sai ka tsura mata ido, tana da tsayi kaɗan, sai ƙiba wacce ta san ta gado ce, don duk gidansu suna da ƙiba, kuma mahaifiyarsu suka gado, ko'ina nata a cike yake sosai, ba ta taɓa jin ba ta son surar jikinta ba sai a yau da mijinta ya kushe ta.

Ta koma da baya ta zauna a bakin gado tana tunanin wai shin dole aka yi wa Jawad ya aure ta ne? 

Wannan tunanin ya cushe mata kai kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta ɗauki wayarta ta danna kiran lambar yayarsu, ta yi Sa'a ta ɗauka "Hello Anti Su'ada".

Daga can ɓangaren Su'ada ta ce"Na'am Muhasin ya gidan?"

"Lafiya lau".

Su'ada ta ce"Dama gobe nake son zuwa gidan naki, na samu na haɗa wani abu a cikin kuɗin, sai a haɗa da na hannunki, jiya har mafarkin Mama na yi".

Muhasin ta ce"To sai kin zo ni ma na je ɗazu".

"Tana lafiya?" Ta yi tambayar cike da damuwa 

"Hmm ina lafiya ga wanda yake wannan wajen Anti?"

Kafin ta ba ta amsa ta ce"Anti dama ina so na tambaye ki ne, don Allah mene ne ai anihin yadda aurena ya faru? Kawu ne ya ce a mayar da auren kaina?"

Su'ada ta yi jim kafin ta ce"Mene ne ya kawo wannan tambayar kuma?"

"Kawai ki faɗa min don Allah".

"Mama ce ta roƙe shi ya aure ki fa, an ɓoye miki ne saboda kar ki damu ko kuma ki yi zargin ba ya sonki, kuma ai ba damuwa tun da ga shi kuna zaune lafiya ko?"

Murya ciki-ciki ta ce "Umm haka ne, sai da safe".

Su'ada ta ce"A'a Muhasin mene ne ya faru?"

Ta ƙirƙiro murmushi mai sauti "Babu komai fa kawai yanzu ne tunanin ya zo min".

"To Allah Ya tashe mu lafiya".

Ta ajiye wayar ta shiga tunanin me yasa za a ɓoye mata? Yanzu dama Mama ce ta yi wa Jawad wannan alkhairin amma kuma shi ne shi ya kasa taimakonta duk da yana da iko? Me yasa? Ta ji sam bata son komawa ɗakin nasa, ashe ba ya son mace me ƙiba amma bai taɓa faɗa mata ba? Anya da gaske da babar shi yake waya kuwa? Ta ya zai yi wannan firar da ita? Ta sake kallon jikinta tabbas ita me ƙiba ce, kuma ta san bayan auren ta ƙara ƙiba kamar yadda Mama ta faɗa, tana son mijinta da aurenta don haka za ta fara ɗaukar mataki don rage ƙibar tata, domin samun zaman lafiya a gidan aurenta.


       MAMA

   Da ido take bin matan cikin ɗakin nasu, har mamaki take yi na yadda rabi da kwatan matan suke cikin walwalarsu, sabo ne ko kuma bushewar zuciya? Wata mata da take yawan son janta da fira ta taso ta zo ta zauna a kusa da ita, "Sannu baiwar Allah" Ta yi maganar da murmushi.

Mama ta ɗauke ƙwallarta da sauri"Yawwa sannu".

Matar ta ce"Hajiya na lura kamar kin fi kowa shiga damuwa a ɗakin nan, duk da ke baƙuwa ce kuma ina zargin wannan ne zuwanki na farko, amma ba ki lura da cewar har waɗanda aka kawo bayan ke sun fi ki sakewa ba?"

Mama ta ce"Damuwa ta zama dole, ban ga ranar da zan yi sabon da har zan yi dariya a gidan nan ba, baiwar Allah ban fa gidan yari ne, ta ya ba zan damu ba".

"Mene ne ya kawo ki nan ɗin? Wane laifi kika yi?"

Mama ta yi jim kafin ta ce"Ƙaddara ce ta saka ni cin bashin mutane, na yi wa 'yata kayan kitchen na fita kunya, saboda wanda ta aura mai hali ne, kuma ya ɗauki nauyin kayan ɗaki kin ga bai kamata mu ji kunya a kitchen ba".

Ta nisa kafin ta ce"Matashin mai kuɗi ne, miliyan ɗaya ba komai ba ce a wajen shi, shi yasa na yi zaton Muhasin za ta dinga samu a wajen shi har na biya kuɗin nan ba da jimawa ba, ashe ya shammace mu, ta ce ba ya ba ta komai, kuma dama ya hana ta sana'a, damuwata ita ce yadda na saka 'yata a kunyar dangin miji na san ana ta zunɗenta idan aka ji ina gidan yari saboda bashin kayan kitchen, wannan abun kunya ne, abun yana min ciwo".

Matar ta ce"Sunana Hajiya Habiba, kuma na yi mamakin jin cewar 'yarki kike jiyewa kunya ba kanki ba, ni nan da kika gan ni ba na jin kunyar kaina ballanatana ta wacce 'yata za ta ji, zuwana gidan nan biyu wannan ne na uku, kin san me ya kawo ni wannan karon?"

Mama ta girgiza kai alamar a'a.

"Gidan uwar mijin 'yata na je na yi satar gwal, kuma na ƙi amsa ni na yi, yanzu haka auren 'yar tawa ya mutu, ni ban yi nadama ba sai ke?"

Mama ta ce"Gaskiya Hajiya ba ki kyauta ba".

Ta yi murmushi "A rayuwa kowa ya yi ta kansa kawai, kuma miji goma ai ba uba goma ba ne ko? Za ta samu wani, yanzu ma ina tabbatar miki ita ce za ta fitar da ni daga wajen nan".

"To Allah Ya kyauta" Cewar Mama jiki a mace.

Ta gyara zama ta ce"Kina so ki fita daga nan wajen?"

Mama ta ce"Babu wanda zai so ko kwana ɗaya ya yi a nan wajen".

"To ina da mafitar da zan ba ki wacce a gobe za ki iya barin nan idan kina so, anjima za mu yi magana".



***