Chapter 2
*...RIGAR ƘAYA!*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
Page 2
Da mugun mamaki Mama take kallon Hajiya Habiba, ta girgiza kai da sauri "Baiwar Allah a bar zancen nan ba zan iya ba, nan da kika gan ni 'yar Malam ce ni jikar Malam, sannan mijina marigayi malami ne, son rayuwar ƙarya da arziƙi ne kawai ya zama jarabawata a rayuwa, wanda kuma shi ne ya kawo gidan nan, amma duk da son abun duniyata ban yi zina ba a rayuwar ƙuruciyata ballanatana yanzu da na girmana, yarana uku mata na ja musu abun kunya? Don Allah ki bar zancen nan, ba zai yiwu ba".
"Shikenan, yanzu kin zaɓi ki dawwama a haka a nan gidan?"
Mama ta sauke numfashi "Zan fita in sha Allah! Yarinyar da na zo nan a sanadinta duk cikin 'ya'yana babu me hankalinta, kuma yadda na matse mata lamba na san dole sai ta san yadda ta yi ta samo ta fitar da ni, ba zan yi zina ba".
Kamar saukar guduma ta ji ta jefo mata wata tambayar "Bayan zina akwai maɗugo ko sata za ki iya?"
Mama ta ce"Don Allah Hajiya tashi ki bar wajena, ba na bukatar taimakonki, da na aikata wani cikin wannan gara na tabbata a wajen nan".
Ta haɗe fuska sosai, Hajiyar ta tashi salun-alun ta bar wajen tana faɗin "Saura kwanaki ukuena fita daga wajen nan, idan kika bari na tafi ba ki yanke shawara ba kanki kika cuta".
Mama ta sauke numfashi, a gaskiya tana so ta fita ta samu 'yancinta amma ba ta jin za ta aikata wannan gagga-gaggan laifukan, hawaye ya sakko mata ta furta "Ya Allah Kana gani, a ƙoƙarina na ganin na inganta sunnarka ne abun nan ya faru, Allah Ka fitar da ni don girmanka, Allah Ka tsare ni da aikata baɗala".
MUHASIN
Bacci rabi da rabi ta yi, tana ta tunanin da wa mijinta yake waya? Ta san dama idan ta ce Jawad ba shi da buduruwa ko ma a ce 'yan'mata ta yaudari kanta, ta san yana da son mata, kuma ba abun mamaki ba ne ba dama, saboda samari da suke level ɗinsa dama da yawa ba sa iya tsallake wannan siraɗin, shi yasa ta saka a ranta za ta jure ta kuma yi iya yinta don ganin wata 'yar kwalta ba ta kwace mata miji ba, auren namiji kyakkyawa kuma shahararren ɗan tiktok ɗin da media take damawa da shi, sannan kuma bayan duk haka Jawad mawaƙi ne da duk duniya ya yi suna, kuma ludayinsa yake kan dawo a yanzu, mai farin jinin mata, kuma sam ba shi da wulaƙanci, wanda sai yanzu da ita ta same shi take zargin rashin class ne ma ba rashin wulaƙanci ba.
Da asuba ya tashe ta sallah kamar yadda ya saba, bayan ta idar da sallah ta fita zuwa ɗakin me aikinta ta faɗa mata abin da za ta dafa, ta koma ta kwanta, ba bacci ta koma ba, wayarta ta ɗauka ta kunna data ta shiga tiktok, ta kalli vedios kaɗan kafin ta yi searching sunan Hasina, vedios suka bayyana, ta shiga account ɗin tana kallo, kamar kanta take kallo, kamar ita ce ta cikin vedion, bambancinsu shi ne Hasina ba ta da ƙiba ita a yanzu, sannan gogewar fatarsu ba ɗaya ba ne, ita kam sai glowing take yi, kana ganinta ka san tana cikin saboda tsananin kamar da suke yi da ita, a Airport ta yi vedion cikin shigar riga da wando, ta tsaya tana ta maimaita vedion fuskarta ɗaukw da murmushi, ta yi kyau sosai, Allah ne ya jarabce ta da ƙaunar Hasina komai ta yi burge ta take yi, a ranta tana ayyana burinta ya cika ta samu kalar rayuwar da take so.
"Kina son kanki Hasina" Ta furta a fili sanda ta tuna rayuwarsu ta baya.
Ta tuna watarana da saurayinta Khalid ya kawo mata abaya guda biyu baƙa da maroon, Hasina ta rikice tana zuzuta kyaun abayar, har Muhasin ta yi mamakin yadda aka yi ta san kuɗinta, ganin haka ya sa ta ce ta zaɓi guda ɗaya ta bar mata, ta zaɓi baƙar, amma washegari kawai sai ta yi wanka ta ɗauki maroon ɗin ta saka, ta ce ita ma tana sonta, nunawar da Muhasin ta yi ba zai yiwu ba, ya sa Hasina ɗaukar fushi da ita, za su wuni tare su kwana a waje ɗaya amma ba za ta taɓa yi mata magana ba, ƙarshe sai da ta ba ta abayar duka biyun sannan aka zauna lafiya.
Muhasin ce za ta nemi kuɗinta Hasina tana bacci, amma kuma ita ce ta fi cin kuɗin, ankon ƙawayenta duk ita ce take yi mata, saboda ita ba ta ma da saurayi a lokacin, duk masu cewa suna sonta ta ce ta wuce ajinsu, an haife ta a gidan talaka amma ta tsani auren talaka, tana da buri amma ba ta iya nema ba, Muhasin da take mugun son farincikinta, kafin ta yi wa kanta abu sau ɗaya ta yi wa Hasina sau uku, idan abu guda ɗaya ne da ita za ta iya haƙura ta bar mata muddin ta nuna tana so, za ta iya siya mata atamfar anko ta ba ta kuɗin ɗinki duk da ita ma ta iya ɗinki amma Hasina ta raina ɗinkinta, kuma ta siya mata jaka da takalmi, har ma da mayafi, indai za ta ga ta fito ta yi kyau kuma tana farinciki to ita an biya ta kawai, Muhasin tana sha'awar su dinga yin anko, amma Hasina ta tsani haka, ta ce ƙauyanci ne ita ba za ta dinga haka ba. Muhasin ce ta fara yin babbar waya, Khalid ya siya mata, amma a taƙaice wayar ta zama ta Hasina, saboda wuni take a hannunta, a wayar ta fara kallon tiktok, kuma a cikinta ta fara yin vedios tana posting, yawanci sai da daddare Muhasin take samun damar ɗaukar wayarta, bayan sun gama waya da Khalid sai ta shiga tiktok, ta kalli wanda ya zama kamar ƙaddararta wato vedios ɗin Jawad, ita dai yana burge ta sosai shi kaɗai take yi wa comments a tiktok ɗin, a hankali account ɗin Hasina ya fara ɓunƙasa a tiktok ɗin, musamman ma da Khalid ya siyawa Muhasin iPhone, ranar da Jawad ya yi following ɗin Hasina Muhasin kasa bacci ta yi don murna, sannu-sannu kuma har wataran ya yi mata magana ta DM, ya faɗa mata vedios ɗinta yana burge shi, ta amsa masa da faɗin ita ma yana burge ta, suka fara chatting sosai, har abun ya yi nisa suka yi musanjen lamba suka koma whatsApp, amma duk Hasina ba ta san me ake yi ba, saboda ita ba ta bin Jawad ma, wanda suka fi shi shahara da kuɗi kawai take hari.
Sai da Jawad ya fara kiran Muhasin a waya sannan Hasina ta fahimci ba Khalid ba ne.
"Muhasin wai wa kika samu da kike ƙoƙarin mantawa da Khalid ɗin naki?" Hasina ta tambaye ta tana yamutse fuska, don a ganinta rashin dabara ne zai saka Muhasin ta ƙi Khalid tun da a ganinta ita ba ta da kalar da maza masu kuɗi za su so ta, Khalid ɗin ma Allah ne Ya ba ta, tun da ita ba ta da wayewar da masu kuɗi da kuma samarin zamani za su so ta.
"Wani bawan Allah ne" Muhasin ta ba ta amsa tana murmushi.
Ta taɓe baki "Ai kuwa sai bawan Allah, amma dai idan kika sake kika rabu da Khalid ba za ki samu kamar shi ba, idan kuma so kike ki yi auren da za ki dawwama kina ɗinke-ɗinken nan na zaman basir shikenan".
"Ai miji na gari ne abun fata ba wai mai kuɗi ba".
Hasina ta ce"Ai ba a taɓa zaman lafiya a gidan talaka".
Muhasin ta ba ta amsa da faɗin "Ya Mama da Baba suka kasance kafin rasuwar shi?"
Hasina ta yi tsaki ta kwanta a ranta tana jin 'yar'uwar tata ba za ta gane ba.
Soyayyarsu da Jawad ta fara nisa duk da suna tare da Khalid, wanda ya fara ba ta haushi a yanzu, don son kauce masa ma take yi, shi kuma Allah Ya jarabce shi da ƙaunarta.
Muhasin ba ta taɓa faɗa wa Hasina da Jawad take waya ba, sai ranar da ta gan shi a gidansu, lokacin zuwan shi na uku ne ma, don sauran zuwan da yake yi duk Hasina ba ta gida, shi sam bai gane ba ita ce me yin vedio a tiktok ba, duk da ya yi mamakin nutsuwarta sosai, a yadda yake ganin vedios ɗin ya yi zaton za ta yi rawar kai sosai a zahiri sai ya ga saɓanin haka, sai a zuwan shi na uku ne ranar Hasina ta dawo daga unguwa, ta yi turus tana jin kamar a mafarki, ta kasa ɓoye mamakinta duk da zuciya tana raya mata ba shi ba ne, shi ma haka mamaki ya cika shi, ya shiga ruɗu ganin sun zama su biyu, ya kalli Muhasin ya ce"Hasina dama ku twins ne?"
Kafin ta ba shi amsa Hasina ta ƙaraso tana guntun murmushi ta ce"Ka yi ɓatan kai Muhasin dai ko? E mu twins ne, ita Muhasin ni ce Hasina, Jawad ɗin da na sani ne?"
Ya tattare gira ya ce"Wow! Amma kun rikita ni fa Baby, please da wa nake waya ne?"
Hasina tana ta rangwaɗa ta ce "Da ita kake chart da waya, amma vedios ɗina kake gani".
Ya kalli Muhasin da duk ta kasa nutsuwa da irin kallon da yake yi wa Hasina, ta ce"Umm, ita ce take yin tiktok da wayata, kuma ita ce Hasina, ni Muhasin".
Nan take wani abu ya daki zuciyarsa, daidai sanda Hasina ta shige gida cikin takun yanga, idonsa da zuciyarsa suka bi ta, ya sauke ajiyar zuciya, yana jin tabbas da gaske ita ce, yanzu ya samu abin da yake ta nema, tun ranar da ya fara ganin Muhasin yake ta tunanin ina wannan iyayin nata da rangwaɗa suka tafi? Waɗanda asali su ne suka ja hankalinsa gare ta har ta fara burge shi, don kama dai kamar su ɗaya, amma ya lura hali akwai bambanci, kuma irin wancen halin na Hasina yake so ba na Muhasin ba, yana son mace wayayyiya.
Ya yi wa Muhasin kallon sakanni kafin ya yi huci ya bar wajen, ya shiga motarsa ya tafi, tsoro da rashin nutsuwa sai ya kamata tana tunanin shin ta yi wani abu da yake ba daidai ba ne? Haka ta shiga gida a sanyaye.
Haka ta lalace da tunanin baya har sai da mai aikin ta zo ta faɗa mata ta kammala komai, ta sauke numfashi ya tashi ta yi wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa, ta fito tana ta ƙamshin humra mai daɗi.
Ɗakinsa ta fara leƙawa ta hango shi ya yi ɗaiɗai yana bacci, a ranta ta raya ya raba dare bai yi bacci ba ne, domin sarai ta sani tanaeds chart din dare, ta sha yi masa ƙorafi a kan haka amma sai ya ce mata a lokacin ne yake da time, wani lokacin a farkon dare ma ba shi da lokacinta duk ranar da ya buɗe live a tiktok, sai ya kai sha biyu kafin ya gama, sannan ya fara chatting, kuma ƙiri-ƙiri ya nuna mata ba ta da ikon hana shi.
Ta nufi dining ɗin, naman kai aka dafa za a ci da gurasa, sai dankali da source, da kuma ruwan shayi, Jawad shi yake son cin naman da gurasa, shi yasa ba da rabuwa da ita, yana yawan breakfast da ita, ita kuma ta yi niyyar cin dankalin, amma da ta tuna kalamansa a kan ƙibarta sai ta fasa ci, ta haɗa ruwan shi da madara kaɗan ta sha, ta san biredi yana iya ƙara ƙiba tun da nau'in fulawa ne, don haka ta ƙi ci, ta sha ruwan shayi shi kaɗai ta tashi, duk da ba ta ƙoshi ba amma tana jin za ta daure matuƙar hakan zai saka ta rame, farincikin mijinta shi ne nata, auren celebrity ba abu ba ne mai sauƙi, ta san ta kasance cikin mata masu sa'a shiyasa har Allah ya zaɓe ta a cikin dubban mata ya ba ta Jawad a matsayin miji, don haka ya zama wajibi ta kiyaye abin da yake so da wanda ba ya so.
Tana zaune a falo ya fito, ya yi wanka amma ƙananun kaya ne a jikinsa, kamar dai na shi da shirin fita, ta yi masa murmushi tana gaishe shi, ya ɗaga mata gira ya wuce dining ɗin, ta ƙarasa ita ma, ta zuba masa ya fara ci yana cewa "Kin ci ba ki jira ni ba ne?"
Ta ce"E, ai ruwan shayi ma kawai na sha".
"Me yasa?"
Ta marairaice kafin ta ce"Zaujee, ƙibata kamar ta yi yawa, ina so na ɗan ragu ne, shi yasa yanzu ba komai zan dinga ci ba".
"Good girl! Ashe ke ma kin lura da hakan kenan, wallahi ni ma sam ba na son ƙiba duk da ke taki ba ta yi yawa ba, amma dai da za ki ɗan ragu da na ji daɗi".
"Na san tawan ma ta yi yawa, ba ka so dai ka faɗa ne kawai".
Ya ce "No ba ta yi yawa ba, amma dai da za ki ragu da kyaunki zai ƙara fitowa sosai, like your sis..." Sai kuma ya kasa ƙarasawa, tunawa da kamar bai kamata ya faɗi haka ba, zuciyarsa ta fara raya masa shin ya kamata ma har yanzu a ce Hasina tana burge shi? Me zai yi da ita tun da ga shi ya samu copynta ta zama mallakinsa? Ya sauke numfashi ya cigaba da cin abincinsa.
Muhasin ta ce"Like what?"
"Like a baby sweet sexten".
Ta yi murmushi"Wallahi Zaujee ban san ba ka son ƙiba ba, in sha Allah sai na rame na zama yadda kake so, kamar ya kake so na dawo?"
Ya yi murmushi ya ce"Ki yi ta raguwa kawai, idan an zo daidai inda nake so zan faɗa miki kin ji?"
Ta ce"To in sha Allah".
"Za mu fara shiga ɗakin game tare, za ki iya?"
Ta gyaɗa kai "Zan iya in sha Allah".
Sun ɗan yi fira, kafin ya gama cin abinci ya fita harabar gidan ya zauna da wayarsa, wajen ƙarfe goma Su'ada ta zo gidan, suka gaisa da shi babu yabo babu fallasa, ta shige ciki ya bi ta da harara ƙasa-ƙasa yake faɗin "Kamar gidan ubanta ko kuma tana bi na bashi, gudawa kawai".
Su'ada ta karya a nan ta gama ta kalli Muhasin ta ce"Ashe Hasina ba ta ƙasar, ƙanwar mijina ta ce min an ga vedionta a jirgi".
Muhasin ta ce"Ni ma ɗazu na gansu".
"Hmm to Allah Ya shirye ta, amma Muhasin ba kya jin ya kamatau kira ta mu faɗa mata? Dama wayarki kawai take ɗauka, na tabbata ba za ta rasa kuɗin da ake buƙata don fitar da Mama ba wallahi".
Muhasin ta ce"Idan aka ce miki ta san duka halin da ake ciki kar ki yi mamaki, ba ta yi niyya ba ne, tsaf za ta ƙi taimakawa tun da tana jin haushin Mama a kan auren nan".
Ta sanyaya murya cike da damuwa ta ce"Duk da ita ce ta ce ba za ta aure shi ba, amma kuma tana kishin shi fa".
Su'ada ta ce"Mahaukaciya kenan, za ta aikata, kuma idana haka ɗin ne ai sai dai ta yi ta gama, don na san ko rabuwa kuka yi da Jawad ba zai ko sake kallon Hasina ba".
"Allah Ya kyauta, yanzu ya ake ciki?"
Ta zuge jakarta ta ɗakko kuɗi ta miƙa mata, ga shi nan ki ƙirga, shi ma baban Ihsan ya ba da na shi, yanzu dubu sittin ne".
Muhasin ta ce "Ma sha Allah, Allah Ya taimaka".
Su'ada ta ce"Ke yanzu nawa ce a hannunki?"
Kamar za ta yi kuka ta ce"Wallahi bai ba ni komai ba, ban da ko sisi a hannuna, sam ba ya so ma na yi masa zancen na rasa me Mama ta yi masa".
Ta taɓe baki "Halin ɗan'adam kenan, na ga har wani ɓata rai yake yi kamar ba ya so a zo gidan nashi, kuma dole na zo tun da kina gidan, yanzu ya kike ganin za a yi?"
Muhasin ta ce"Wallahi ni kam kaina ya kulle gabaɗaya Anti, ba ni da wata hanyar samun kuɗi, amma zan dage da addu'a Allah Ya kawo wata mafitar".
"To Allah Ya kawo ta cikin gaggawa, ina tausayin Mama duk da laifinta ne wallahi".
Kafin azhar ta tafi, kuma ba su tsayar da wata mafita ba sai ta addu'a da suka ce za su dage da yi Allah Ya kawo mafitar, da yamma zuciya ta raya mata ta yi wa Hasina magana ko za ta dubi darajar rainon ciki da haihuwa ta fitar da Mama, ta yi mata DM ta tiktok don a yanzu ba ta ma da lambarta saboda yawan canza lamba da take yi, ga shi an ce ba ta ƙasar ma, babu jimawa ta buɗe sallamar kuma ta amsa, amma daga nan ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Ta yi dogon rubutu ta bayyana mata halin da ake ciki, da yadda ake neman miliyan ɗaya domin fitar da Mama, ta dawo mara da amsar ina mijinki? Muhasin ba ta ce komai ba ta kashe data ta ajiye wayar.
Dariya Hasina ta fara yi kafin ta ce"Ai haka za ku yi ta gani, kuma kaɗan ma kika gani, ta nemo wata lamba ta yi kira bugu biyu aka ɗauka suka gaisa sama-sama kafin ta ce"Burinka ya kusa cika fa mutumina, akwai wata hanya da ta buɗe wallahi".
Ta sake kwashewa da dariya ta ce"Mutuniyarka ce take buƙatar one million..."
Ta yi masa bayanin komai, nan take ya gano irin hasashen da take yi masa, sai da ya miƙe tsaye kafin ya furta "Yess, amma dai Hasina kanki yana ja sosai, tabbas wannan ita ce mafita, ki turo min lambarta in sha Allah yau zan fara aikin".
Ta yi dariya "Ba fa wani aiki, ita da take yunwar kuɗin?"
Ya dinga jero mata godiya, ta ajiye wayar tana jin zuciyarta fess, ita a yanzu neman duk hanyar da za ta saka Muhasin a ƙunci kawai take nema, kuma ga shi ta samu mai kyau ma kuwa.
***