Chapter 3
*...RIGAR ƘAYA!*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
Page 3
FIRDAUSI
Cikin ƙaramin gida wata tsohuwa na tsakar gidan tana tsintar wake, rediyo a kusa da ita tana sauraron labaran yamma, wani saurayi ya shigo, sallama ɗauke a bakinsa, kallo ɗaya za ka yi masa ka karanci gayunsa, Kabiru irin samarin nan ne 'yan ƙarya wanda suke iya hana cikinsu don su yi gayu da ƙarya, ta amsa da faɗin Kabiru ka dawo?"
Ya ce"Yes Kaka na ɗan zagayo, ga wannan sai ki taɓa, wannan abun ne na ga an tallan shi sai na yi thinking kamar kina so ko?"
"Dalla idan za ka ba ni ka ba ni, meye kuma tikin?"
Ya ciro shi a ledar ya miƙa mata, ta fito da mutuncin tana cewa Allah Ya alfana.
Ya ce"Ina my favourite sister?"
Kaka ta haddace kalmar sister saboda yadda yake yawan faɗawa ƙanwar tashi, ta faɓe baki "Tana ɗaki kwance, to yunwa da ba ƙanwar uwar kowa ba ce? Ai yau ba ta ci komai ba, da safe koko na yi ta ce ba ta sha, da rana kuma ɗumamen tuwon jiya ne..."
Kafin ta ƙarasa Firdausi ta fito daga ɗakin tana faɗin "To tsakani da Allah brother tuwon da ban ci shi da darajar shi ba, shi ne zan ci bayan ya kwana? Ya yi fa 24hr, haba sai kace a kanmu talauci ya ƙare? Gaskiya Kaka ba kya duba mana wallahi"
Kaka ta jefa mata maficin kusa da ita tana cewa"To me ya hana ubanku ya taso daga ƙabari ya duba muku? 'Yan iskan yara marasa godiyar Allah".
Firdausi ta buga tsalle ta fashe da kukan da babu hawaye, duk da kuwa maficin bai same ta ba, ta shige ɗaki tana rera kuka.
Kabiru ya yi saurin bin ta da ledar hannunsa "Haba mu sister don Allah rikicin tsohuwar nan ya daina ɗaga miki hankali, ungo ga yougurt da balangu na samo miki, daga kasuwa nake".
Ta washe baki tana janyo ledar da faɗin "Allah Ya bar min kai babban yaya".
Ya yi murmushi "Ai tukuna ma, wannan so min taɓi ne cikin romon democraɗiyyar da za ki dinga sharɓa daga gare ni".
Ta yi tsam ta ce"Bro, ko wani sabon aiki ka samu?"
"Muka samu dai, ni da ke za mu yi wannan aikin, kuma za mu cim ma nasara muddin kika ba da haɗin kai, domin wallahi ba ƙananun kuɗi za mu samu ba".
Ta ɓata rai tana kai jarkar yougurt ɗin bakinta, ta kwankwaɗa kafin ta ce"Amma Yaya ni fa na faɗa maka ba zan yi tiktok ba".
Ya ce"Ke stupid! Ba wannan nake nufi ba, shi ma sabon shiri me, wallahi muna zaune sai shugaban ƙasa ya zo har gida nemanki yana sonki".
Ta yi tsaki "Allah Ya kiyaye me zan yi da Tunubu?"
"Ke stupid shugaban ƙasar America ma tsaf zai ce yana sonki".
Ta zabura ta ture naman "Yaya yau dai ba alkhairi a bakinka wallahi, to ba gara ma na auri Tunubun ba?"
Ya yi dariya "Duk ba wannan ba be serious please mu yi magana ta understanding, mu yi magana like a good family sister, akwai wani family planing da nake so mu haɗa ni da ke".
"Don girman Allah ka daina wannan turancin haka, wallahi tsaf sai a mare ka a wani wajen, kamar ya family planing? Aure ne da ni?"
"Ok na masu aure ne? To dai akwai wani shiri da na zauna na yi da zuciyata".
Tana cin naman ta ce"Ina ji, amma don Allah ka yi da Hausa".
"Oh my god! Ni da nake burin ki auri me kuɗi ta ya za ki dinga ƙaunar Hausa? To wallahi da sake".
"Ni dai faɗa min ina ji".
Ya gyara zama "Wallahi Sister zama na yi na yi nazari na ga kina da kyau sosai, idan kika ƙara kyau kaɗan ba wanda ma zai sake yarda a Nigeria aka haife ki, shi yasa na ga idan kika auri talaka zan iya haɗiyar zuciya na mutu, to amma me yasa masu kuɗi ba sa zuwa wajenki? Dalilan suna da yawa, na farko dai kyaun naki ba kya yi masa upgrade, made in da ne, saboda yanzu a fuskar mace bayan ta yi haske ana buƙatar glowing, Wanda za ki ga kamar sun shafa man gyaɗa ban sani ba ko kin sani, na biyu kuma za ki ƙara haske ki zama kamar aljana don kyau, sai ki ɓula hancinki, ta haka ne za a gane ke babban kai ce, sannan kuma uwa-uba ki yi ƙiba, yanzu maza mace me ƙiba suke so, idan kika fashe part of body suka buɗe sai ki ga kin ƙara kyau sosai, sai kuma a samu babbar waya, ga kuma ɗinkuna da za ki dinga yin kin ga wannan aiki ne tuƙuru, saboda haka muna buƙatar kuɗi".
"To a ina za ka samu?"
"I try my best in sha Allah, ko aron kuɗi ne zan yi mu fara mu gani".
Ta ce"Amma Bro kana tunanin ina da kalar da masu kuɗi za su so ni?"
Ya jinjina kai "Yes of course! Da zarar kin rabu da wannan faƙirin yaron shikenan don wallahi dama ba class ɗinki ba ne".
"Ni fa dama saboda na ga tana da kokarin siya min Rufaida ne, shi yasa nake kula shi, amma indai zan samu me siya min ai ba abin da zai hana ni rabuwa da shi".
Suka dinga fira suna tattaunawa a kan yadda abub zai kasance.
Firdausi baƙa ce, black beauty, doguwa siririya, su biyu iyayensu suka haifa ita da yayan nata Kabiru, suka rasu tun suna yara, don tairarsu shekara ɗaya ne, babansu ya rasu da shekara ɗaya ita ma uwar ta rasu, hakan ya sa suka taso a hannun mahaifiyar babansu, tana yin iya yinta wajen kula da tarbiyyarsu duk da an ce goyon Kaka ba a ganin komai daidai, amma shi Kabiru yaro ne ne shegen buri da don rayuwar hutu da ƙarya, kuma haka yake zabga ƙaryar tun yana yaro, a yanzu kuma da ya girma shi ba karatun ba shi ba tsayayyen aiki ba, sai yake neman inda zai fake ya yi kuɗi tashi ɗaya, a cikin ire-iren imagination ɗin da ƙwaƙwalwarsa take yawan yi masa ne ta tsara masa yadda ƙanwarsa za ta zama jarinsa, idan har ya bi wasu matakai.
MUHASIN
Da yunwa sosai Muhasin ta kai dare, saboda ɗan mitsitsin abincin da ta ci da rana, a ƙoƙarinta na ganin ta rage ƙiba, ta fara tunanin ma ta dinga yin azumi kawai, da daddare ma fruit salad kawai ta sha. Suna zaune da Jawad yana cin abinci take ce masa "Zaujee ni me yasa duk da kajin da kake ci ba ka yi ƙiba kamar tawa?"
Ya yi murmushi "Ashe ina tare da Madam sleeming ne, ni kullum sai na shiga game ai, ke ma daga gobe za ki fara, wai ke da ba ki san yadda ƙibarki ta yi yawa ba? Ni fa gaskiya ba na son mace me ƙiba".
Ta marairaice "Amma ai ka san ina da ƙiba, me yasa ka aure ni?"
"Saboda ina sonki kuma dama niyyata idan na ga ƙibar ta wuce gona da iri zan faɗa miki ki rage, to sai ga shi ma kin gani da kanku".
Ta sauke ajiyar zuciya "In sha Allah zan ragu, amma maza da yawa sun son mace me ƙiba, ba ka ga yadda ake neman ƙibar nan ba".
"To daga kanki za a samu macen da take neman rama".
"Allah Ya sa dai zan yi kyau, jikina na ƙiba ne, sai nake ganin zan fi kyau da ƙiba".
"To tun da jikinki zaɓinki yadda za ki kasance ai".
"Zan gwada in sha Allah, gobe zan fara training kuma zan daina cin abincin safe da na dare".
"Allah Ya taimaka".
Bayan ya fita tana kwance wajen sha biyu tana chatting sako ya shigo wayarta da sabuwar lamba, sallama aka yi mata, ta buɗe ta fara shiga duba username babu komai, ta duba dp shi ma babu komai, ta amsa sallamar, tamkar yana jira ya dawo mata da faɗin "Ya kike ya gida ya jin daɗi?"
Ta amsa da "Alhamdulillah"
"Na ji an ce kina neman taimako shi ne na ce bari na ji dalilin da ya sa ba ki tambaye ni ba".
Da ta duba ta cika da mamakin wane mai ƙarfin halin ne wannan, ta ce "Da wa nake magana".
Ya ba ta amsa da faɗin "Mai sonki ne".
Ta duba ba ta ce komai ba, ta saka lambar a true caller ta ga sunan Khalid ya bayyana, dama ta zargi haka, duk da ta yi mamaki, saboda rabon shi da ita tun da aka saka ranar aurenta da ya yi nacinsa ya gama ya rabu da ita, ta je ta yi block ɗin lambar, amma a tsayin wunin shaiɗan bai bar ta ta sarara ba, haka ya dinga bijiro mata da wane ne Khalid da kalar son da yake yi mata, tabbas tana buƙatar kuɗi amma ta san darajar igiyoyin auren da suke kanta don haka ba za ta karɓi kuɗi daga wajen shi ba.
Da daddare ta sake ganin saƙon shi da wata lamba, Khalid ɗin da ta sani dai ba jahili ba ne, don haka ta yi mamakin dalilinsa na aikata haka, ta tura masa saƙo da faɗin "Khalid ka san ni matar aure ce a yanzu, don Allah kar ka sake yi min magana, ka san darajar aure, don Allah kar ka sake yi min magana".
Babu jimawa ya dawo mata da amsa "Muhasin na san darajar aure, kuma ba ƙoƙarin taɓa darajar nake ba, kin sani ai na haƙura da sonki, don da ban haƙura ba ba zan taɓa bari wani ya aure ki ba, ko da ba za ki aure ni ba, Muhasin yanzu matsayin ƙanwata na ba ki, kuma na san halin ɗan iskan mijinki, shi yasa na niyyar ba ki taimako a duk lokacin da kika buƙata, to da yake na sanki da zurfin ciki da kunya ba lallai ki iya tambayata ba shi yasa nake bibiyar halin da kike ciki, har na ji kina neman kudin nan, ko da ba don ke ba ki sani Mama babata ce, zan yi mata komai duk da ba ma tare da ke, don Allah ki ba ni dama, ki ba ni damar da zan zame miki ɗan'uwa, yayanki wanda zai zama kamar garkuwa a gare ki, ni ban ce ki yi fira da ni ba, kawai dai idan kina buƙatar taimako don Allah ki faɗa min, na samu ko da iya matsayin wanda za ki nemi abu a wajensa ne, zan yi alfahari da haka".
Muhasin ta gama sauraron voice ɗin nashi, ta yi shiru tana tunani, zuciyarta sai ta rabu biyu, ɗaya tana faɗa mata Khalid da gaske yake, kuma haka ba komai ba ne tun da ba wata fira za su dinga yi ba, wata zuciyar kuma tana faɗa mata ƙarya yake yi, tsohon saurayinta ne ba lallai ya daina sonta ba, kuma zai iya yin komai saboda ya samu space ɗin da za su samu kulluwar alaƙa a tsakaninsu.
Ta rasa me ya kamata ta yi, tana son kuɗi, ko bacci take yi idan ta farka ta tuna Mama tana can cikin mummunan yanayi sai ta kasa komawa, komai ya tsaya mata cak, kanta ya kulle.
Ya sake turo mata wani sakon ya ce "Idan kin amince zan ba ki kuɗin a duk lokacin da kike buƙata, kawai ki yi min magana".
Ta kashe datar ba tare da ta ce komai ba.
Khalid ya ɗauki duka chatting ɗin ya turawa Hasina ta ji yadda suka yi, tare da faɗin "Kamar ba za ta amince ba".
Hasina ta ce"Za ta amince in sha Allah, ka ba ta lokaci ta yi tunani, idan ta rasa yadda za ta yi da kanta za ta dawo ta ce ka ba ta, idan ta ce ka ba ta ka faɗa min kafin ka ba ta, akwai abin da zan tsara".
Ya ce"Na gode sister sai kin ji ni".
Ba ta ci abincin rana ba, shayi kawai ta haɗa ta sha kaɗan madara ma ba ta ji ba, duk yunwar da take ji haka ta daure, da daddare da ya shigo da tsire ma ƙwaya ɗaya ta ɗauka ta ci, yau ma haka ya ce mata zai yi waya da Hajiya, kuma ya dade yana yi don haka ba ta kwana a ɗakinsa ba, sannan ta fara zarginsa shin aure zai ƙara da yake kula wata buduruwa tun yanzu ko kuma dama can ya saba kula matan? Shin iya soyayya alaƙar ta tsaya ma ko abun ya fi haka? Ta fara tunanin duba wayar shi don ta tabbatar da hasashenta.
***