RIGAR KAYA

Chapter 4

by @sadiyaabdulrazak954

*...RIGAR ƘAYA!*



            BY
SADIYA ABDULRAZAK 



 Page 4


  Saboda ta saka a ranta za ta duba wayar ya sa ta kwana a ɗakinsa, ta kwanta tun kafin ya dawo, ko da ya dawo tana jinsa ya gama komai ya zo ya kwanta, shi kam ba ya tashinta daga bacci don ta ba shi abinci ko wani abun, indai ta yi bacci shikenan, saboda shi ma ba ya so a tashe shi daga bacci. Bai san ba bacci take yi ba sai da ya gama komai, ta yi zaton bacci zai yi sai ta ga ya janyo waya ya fara chatting, yau kwana biyar kenan wani abu bai shiga tsakaninsu ba, kuma ba ya fin kwana biyu, don haka ta yi kewarsa, ta matsa kusa da shi, ya ce "Ba bacci kike yi ba kenan?"

Ta ce"E, kai nake jira".

Ta yi maganar tana shiga cikin jikinsa.

Amma sai ya fara ƙoƙarin matsawa kafin ya ce"Sorry ba ni da sauran condom".

 Ranta ya ɓaci ta ce"Wai don Allah me yasa kake yi min haka ne? Me yasa...".

Ya tari numfashinta "Na gaji da faɗa miki dalili, saboda ba na so ki haihu yanzu, ba mu gama fahimtar juna ba".

"Ni ma ba zan gaji da raunata dalilinka, ai ko ba mu taɓa ganin juna ba aka yi mana aure, zaman aure na wata biyu mu kwana tare mu tashi tare ya ci a ce an fahimci juna indai an yi niyya, mene ne ya rage?"

"Bayan wannan ma ba na so ki haihu da wuri, at least dai a yi shekara ɗaya, kafin nan mun gama cin amarci, don gaskiya ba na son laulayi".

"Duka wannan dai ba hujja ba ce ba, kuma gaskiya ba na jin daɗin yadda kake saka min kariya ina matarka ta sunna, ina raina kaina da jin kamar ban kai mace ba, kuma ina jin ƙasƙanci da tunanin ko kana ƙyamata ne ma".

Ya shafa fuskarta "Ba ƙyama ba ce Muhasin, na ɗan lokaci ne, tsakani da Allah ba na so ki samu ciki yanzu, kin ga kuma idan na ce ki yi planing na cutar da ke ko?"

A raunane ta ce"Shikenan".

Ta sake shigewa jikinsa ta yi lamo, ya ce"Sorry kin yi min girma a jikina fa, kina da nauyi".

Ta ja jikinta gefe ta kwanta, tana ji a ranta dole ma ta rame. 

Ya ɗauki wayarsa ya cigaba da chatting ɗinsa, mata ne kala-kala ya ba wa wannan amsa ya bawa wannan, duk yadda ta so ta hana idonta bacci sai ta kasa, bacci ya ci ƙarfinta, sai da ta farka ta ga ya yi bacci sannan ta ɗauki wayar tasa, ta ɗosana yatsansa a hankali wayar ta buɗe, ta wuce a hankali ta bar ɗakin ta zauna a falon shi.

Ta whatsApp ɗinsa ta fara, gabanta yana faɗuwa, kamar yadda ta yi zato mata ne masu yawa suke chatting da shi, wasu ma babu saving ɗin lambar, ta duba wata lamba da aka yi saving da my Angel, ita ce ta ƙarshe da suka yi chatting, kuma rubutun ƙarshe da ya yi mata shi ya ja hankalin Muhasin har ta duba ta gani, _I will miss You_ haka ya rubuta tare da emoji na kiss, ta shiga ta fara scrolling tana duba chart ɗin, fira suke yi sosai, a cikin firar ta fahimci da alama sun saba haɗuwa, yanzu ma kuma sun yi zancen gobe za su haɗu a wani waje, ta san sunan wajen a bakin Hasina, wajen shan ice cream ne, ta sha jin cewar sun ke tare da Jawad ɗin, kenan wajen zuwan shi ne, amma ita bai taɓa ɗaukarta sun je ba.

Ba ta tsinci wani abun zargi a firar tasu ba, fira ce normal suke yi da ita, amma akwai alamar soyayya a tsakaninsu.

Ta fita, ta shiga lambar da ya yi saving da besty, ta yi scrolling ta dinga duba chart ɗinsu har voice take buɗewa, ba ta yi nisa ba ta fahimci matar aure ce, kuma kau tsaye soyayya suke yi, suna neman mafitar da za ta kashe aurenta don shi ya aure ta, ran Muhasin ya ɓaci sosai, jin yadda yake ta yi mata kalaman soyayya, da ta shiga ta duba hotunan da ta taɓa tura masa ta ganta, siririya ce kuma ba wata kyakkyawa ba, amma kana ganinta ka san tana cikin hutu, ta koma chart din Angle ita ma ta duba hotonta ta ganta siririya, hakan ya ba ta tabbacin lallai mijinta ba ya son mace mai ƙiba, nan take raunatacciyar zuciyarta ta yi wa Jawad uzuri, sannan ta jibga mata laifi, a ganinta ita ce mai ƙiba shi yasa har yake hange wasu matan, ya zama dole ta rame sosai ta zama kamar yadda yake so.

 Ta cigaba da duba chart ɗin mutane, ta shiga na wata da ya yi saving da my sweet, a nan mamaki ya kashe ta, ita kan firar batsa suke yi zalla, har da kalaman da ko ita da take matarsa za ta ji kunyar yi da shi, a nan kam sai da hawaye ya sakko mata, domin a firar ta fahimci ba iya waya suka tsaya ba, sun saba haɗuwa da ita suna aikatawa.

'Da wa nake zaune?' Ta tambayi kanta a zuciyarta hawaye yana sakko mata, ta fara tunanin shin dama ya saba amfani da condom ne wajen yawonsa shiyasa ita ma yake yi mata ko kuwa ita yake ƙyama ba su ba?

Jikinta duk ya yi sanyi, daga nan ta sake duba na mutum biyu nan ma duk ta ga alamar suna haɗuwa, wata lamba da ya yi saving da my fiance ta dauki hankalinta, ta duba ta ga ya saka key a chart ɗin, hakan ya sake ƙarfafa zarginta a kan lambar, ta share hawaye ta tashi ta koma ɗakin, ta ajiye wayar ta kwanta, baccin da ba ta koma ba kenan, kishi da baƙinciki ya cika mata zuciya, tana ta tunanin mafitar da za ta kau da mijinta daga miyagun mata, don ita ta fi ganin laifinsu, gani take su ne suke bin shi saboda ya kasance fitaccen ɗan tiktok.

Washegari da safe ya gama karyawa za ta tashi daga dining ɗin ya ce "Zauna ina zuwa".

Ta koma ta zauna, har yanzu ranta babu daɗi.

Ya yi danne-danne a waya, ya miƙa mata wayar, ta karɓa tana yi masa kallon tambaya, a cikin settings yake wajen saita password.

"Me za a yi?" Ta tambaya da ɗan mamaki

"Ki saka fingerprint ɗinki a kai, yadda za ki samu sauƙin bincika min waya ko?"

Gabanta ya faɗi, ta ji wani abu me kama da kunya ya lulluɓe ta "Zaujee..."

Ya katse ta da faɗin "Ki saka ɗin, ai babu daɗi a ce kullum sai kin jira na yi bacci sannan ki ɗauki hannuna ki saka, abun akwai wahala".

Ta haɗiyi wani yawu ta ce"Ka yi haƙuri, kawai dai na duba ne saboda ina neman wata lamba".

"Lambar wa?"

"Ta Hasina".

"Mene ne haɗina da ita? Ke ma ba ki da ita sai ni?"

Ta sunkuyar da kai.

"Idan za ki duba wayata ban hana ki ba, amma ba ki da ikon tuhuma ta a kan duk wani abu da za ki gani".

Ta miƙa masa wayar, ya ƙi karɓa, sai ma ya taso kusa da ita ya kama hannunta ya saka, ya saita, ya sake ta ya bar wajen yana kiran wata lamba".

Ta sauke numfashi tana tunanin me yake nufi da hakan?

 Ta yi wanka ta kunna data, ta ci karo da saƙon Khalid, sallama ya yi mata da gaisuwa, ta amsa sallamar ba ta ce komai ba, ta cigaba da chatting ɗinta, ta nan suka yanke gobe za su je wajen Mama ita da Su'ada.


     MAMA

  Tafiya take yi kanta ɗaukw da bokiti ta ɗebo ruwa, ba ta san wannan shi ne sahu na nawa da za ta kai ba, bayan uwar sharar da ta yi da wanke-wanke. Tun ranar da suka yi magana da Hajiya Habiba ta ce mata ba ta amince ba, shikenan take fuskantar wannan matsin, kuma daga kallon da Hajiyar take yi mata da dariya ta tabbatar da cewar akwai saka hannunta a wannan gana mata azaba da ake yi, wuni take aiki, sallah da cin abinci ne kawai yake cetonta ta samu hutu,ta yi zuru-zuru, kullum da ciwon kai take wuni, yau kuwa da zazzaɓi ta tashi me zafi, ga ɗibar ruwan da take ta yi, tana dab da kai wa ƙatuwar randar da take tara ruwan, ƙarfinta ya ƙara bakiɗaya, ta zube a ƙasa ita da bokitin tana numfarfashi, wata mara imani cikin gandurobobin ta zo ta fara dukanta tana yi mata masifa da rantsuwar sai ta ƙarasa, sai ta cika randar nan.

Habiba ta ƙaraso ta dakatar da gandurobar, sannan ta ɗaga Mama, hawaye ya sakko mata tana faɗin "Me na yi muku?"

Habiba ta zaunar da ita ta ce"Ba ki yi mana komai ba, kuma zama a cikin wannan azabar ko fita daga ciki wannan zaɓinki ne, a yau idan kika amsa zan fitar da ke".

Mama ta yi mata kallon ke me yasa ba ki fitar da kanki ba?

Kamar ta san mene ne a ranta ta ce"Ni fa ba ɗaurarriya ba ce ba, na shigo nan ne kawai saboda gudanar da aikina, ni agent ce ta wata ƙungiya, wanda ake haɗa mace da namiji ko kuma mace da mace, ko maza, ina zuwa nan saboda na samu masu rangwamen gata irinki na ja ra'ayinta, sai ga shi ma ke kin yi taurin kai, kodayake ba ki gaji da zaman wajen ba ne ina ga".

"In sha Allah ba zan zubar da mutuncina saboda na fita daga wajen nan ba, Gara na zauna wahala ta kashe ni".

Ta tashi ta nufi ɗaki ta kwanta tana rawar sanyin zazzaɓi, su ma ganin ba za ta moru ba ya sa suka ƙyale ta.

Tana cikin wannan halin ne kuma yaranta suka kawo mata ziyara, Su'ada ce ta je gidan Muhasin ɗin sai direba ya kawo su.

Sanda suka ƙaraso kafin su fito daga mota Muhasin ta ce"Ina ga ke ki shiga, ni ba sai na shiga ba"

"Me yasa?" Ta tambaye ta da mamaki.

"Saboda ta ce ba ta son ganina, zuwana na ƙarshe ta ce idan har na sake zuwa wajenta na ƙaddara ina cikin fushin uwa, shi yasa ba zan shiga ba".

Su'ada ta ce"Shikenan, bari na shiga".

Da aka faɗawa Mama an zo ganinta kasa tashi ta yi saboda zafin zazzaɓin da ya yi mata kwaf ɗaya, su ma ma'aikata sai da suka tsorata saboda gudun a zarge su da rashin ba ta kulawa alhalin tana jinya, ma'aikaciyar ta koma wajen Su'ada ta ce"Matar nan ba ta da lafiya, ba lallai ta iya tashi ba".

Su'ada ta zaro ido"Amma shi ne ba za ku faɗa mana ba? To wallahi idan ta mutu ku ne? Tun yaushe take kwance?"

"Ke ki dakata da wannan banzayen kalaman naki, akwai wanda ya wuce ya yi jinya ne? Kuma ba wanda ta faɗawa ba ta da lafiya, saboda munafurcinta".

"Dama kuna saka su aikin wahala ai dole ne su yi rashin lafiya".

 "Uban waye ya ce su yi laifin da har za a kawo su nan ɗin?"

"Ubanki ne!" Cewar Su'ada ta cire mayafinta da shirin yin ɗamara da shi.

Hankalin mutane ya yi kansu aka taru ana sasantawa, Su'ada ta kira wayar Muhasin, tana ɗauka ta ce"To za ki shigo ne ko sau sun kashe mana uwa?"

Muhasin tana jin haka gabanta ya faɗi, ta fito daga motar da sauri ta shiga wajen, da ta ga Mama kuka ta fara yi Su'ada kuma tana ta faɗa da su, ta duƙa a gabanta ta kama hannunta, Mama ta ce"Yanzu Muhasin ba za ku fitar da ni daga wajen nan ba ko? Sai na mutu za a fitar da gawata? Inda ni ce ba zan iya barinku a wajen nan ba, sai na yi duk yadda zan yi na fitar da ku, wannan shi ne halaccin da za ku yi min ko? Na tabbata inda kin so da tuni mijinki ya fitar da ni daga wajen nan".

Ta riƙe hannunta ƙam tana kuka "Za ki fita in sha Allah, zan nema a ko'ina ne Mama, ki yi haƙuri".

Ta fita waje tana ce musu "Za ku ba mu ita mu kai ta asibiti".

Wani cikin ma'aikatan ya ce"A'a, akwai inda za mu ajiye ta a kan mu ba ta kulawa, idan abun ya ƙi ma mu ne za mu fitar da ita asibitin waje".

"Don Allah ku bari akwai asibitin da za mu kai ta, ba ma so ta mutu".

"Haka dokar take, idan ba kwa so ta mutu to ku fitar da ita daga gidan mana tun da dai ba kisan kai ta yi ba".

 Haka suka bar wajen rai babu daɗi, a mota Su'ada take cewa "Kai Allah wadaran talauci, ni kam yau zan siyar da kayan ɗakina na ga me za a ƙara samu".

Muhasin ta yi shiru tana jin kawai ita ce ta ja wa Mama komai.

"Anti Su'ada ni ce silar komai, zuciyata zafi take yi, ku yafe min".

Kamar tana jiranta ta ce"Ƙwarai kuwa ke ce kika ja komai Muhasin, saboda Mama tana ganin mijinki me kuɗi ne wanda kai tsaye ma zai iya cire wannan kuɗin ya fitar da ita, sarai kin sani saboda ke ta shiga wannan halin, kina mace ba za ki iya yin yadda za ki yi ya ba ki kuɗin ba? Haba Muhasin wannan shi ne abin da za ki saka masa da shi?"

Kukanta ya tsananta ta ce"Wallahi ba yadda ban yi ba ya ƙi, sata zan yi masa? In sha Allah zan san yadda zan yi, na fi ki shiga damuwa Anti".

Ta kwantar da kanta a cinyarta, ita kuma ta shiga shafa kanta tana faɗin "Ki yi haƙuri, amma gaskiya mijin nan naki ba shi da kirki sam".

A haka suka ƙarasa gidan, suna shiga suka ga motar Jawad tana nan alamun har lokacin bai fita ba, Su'ada ta ce"Ni ba sai na shiga ba, duk yadda kuka yi da shi sai ki faɗa min ta waya".

Muhasin ta saka direban ya tafi kai ta.

Tana shiga falo ta tarar da Jawad zaune yana vedio, wata waƙar turanci yake waya yana rawa, karo na farko da ya ba ta haushi saboda ganin yana vedio, ta yi masa kallo ɗaya ta shige ɗakinta, zama ta yi tana tunanin mafita.

Ba ta daɗe a zaunen ba Jawad ya shigo ɗakin, fuska ba yabo ba fallasa ya ce"Ya dai? Na ga kin shigo ranki a ɓace".

Ba ta kalle shi ba ta ce"Dama ka yi tsammanin ganin farinciki a fuskar wacce ta dawo daga ziyartar mahaifiyarki a gidan yari?"

Hawaye ya sakko mata ta ce"Mama tana cikin jinya don Allah ka taimake ta Jawad, kana da kuɗin da za ka fitar da ita, me yasa ka ƙi? Ko ba don ni ba, ko don son da ka yi wa Hasi..."

Ya ɗaga mata hannu"Ke ya isa haka dalla! Idan kika sake yi min zancen Hasina sai na faffala miki mari wallahi, ko mahaifiyarku a yanzu ba ni da wani haɗi da ita, ballanta 'yar'uwarki, Allah Ya fitar da ita".

Har zai fita ya juyo ya ce"Na samo condom ɗin idan kina buƙata".

Ya fita ya bar ta da ƙunar rai.

 A can gidan yarin bayan fitar su Muhasin wani ya ɗaga waya ya kira wata lamba yake sanar da abubuwan da suka faru daga zuwan su har tafiyarsu, shi kuma wanda aka sanarwa ɗin kai tsaye ya sanarwa Hasina ta chart, ta yi murmushi ta ɗauki waya ta kira Khalid, ranta fess take ce masa "Kana da dama a daidai wannan lokacin, ina kyautata zaton za ta iya amincewa, ka sake gwadawa".

Ya ce"In sha Allah".