HUKUNCI:1
by @ummyz
*HUKUNCI*
بِسْمِ ٱللّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Dukan rayuwa tana tafiya ne tareda jarabawa dakuma kundin ƙaddara wanda duk wayon bawa bai isa yatsere mataba saboda itaɗin abokiyar halittar ruhice! Daga lokacin data yankewa ruhi, to saidai idan ruhin ya kwanta ne. SOYAYYA! Soyayya tana cikin mafi wahalar jarabawar da duk faɗan da zakayiwa zuciyar bataji tanada wahalar tanƙwaruwa da taurin kai tawanan fanin.
HUKUNCI!
P 1_2
Kyakkyawar matashiyar budurwace a zaune cikin babban falo kuma haɗaɗɗe da kallo ɗaya zakayi mishi kafaɗa cewa lallai mammalakiyar shi tana more rayuwa yadda Yakamata duba da irin tsadaddun furniture dake zube falon cikin yanayin burgewa da ɗaukar hankali babu wani hayaniya mai hawa kai saima sansanyan ƙamshi dake tashi cikeda nutsuwa dabawa ruhi farin ciki.
Karona babu adadi tasake ɗaga wayar dake hanunta tasaka number dataketa faman kira babu adadi amma kiran baya tafiya sam saima line busy da'aketa faman maimaita mata, kyakkyawar fuskarta mai fusgar hankali tasake ɓatawa dama babu wani alamar farin ciki ko kaɗan akanta. ajiyewa wayar tayi ta miƙe tsaye cikin nutsuwa da taurin zuciyar dake neman danne kowane hali take ciki tanufi hanyar Kitchen, lallausar doguwar rigar soft chippom blue black dake jikinta na sauka akan ƙafarta. saidai duk yadda fuskar tata take aɗaure bai hana natural kyawonta bayyana ba saima wani glowing da fatarta keyi,farace sol sol irin hasken nan mai haɗe da yellow yellow.
Kasancewar bawani tazarane daga falon zuwa kitchen ɗin ba yasa tashiga tana tsayawa gaban fridge dake cikin kitchen ɗin tana maida numfashi ahankali sanan tasaka hannu tabuɗe hannun fridge ɗin taduƙa ta janyo wani ƙaramin tukunya dake rufe tawuce gaban gas ta ajiye harta kunna gas ɗin saikuma ta tuna cewar shekaran jiya yaƙare dafe kai tayi cikin yamutsa fuska tana faɗin yah Rabb, tuna cewar da wutar nepa yasada sauri ta kunna electric stove ta ɗauro tukunyar hanunta na ɗaukar rawa saboda sanyin Abincin da kuma yunwar datakeji tana ƙwaƙwular uwar hanjinta,jingina tayi jikin kitchen Island ɗin zuciyarta cunkushe cikeda tunanin menene ya tsayar da HABIB bai dawo gidaba har yanzu saboda yakanyi duk tsiyatakun shi amma baya daɗewa awaje sosai indai dare yayi,tana tsaye har Abincin nata yagama warming sanan tazuba cikin fillet tasaka spoon ta zauna a kitchen ɗin tafaracin jallop rice ɗin da babu wani vaggies aciki tsurar shinkafar ce tsage tsage.
Cin Abincin take cikin sauri sauri saboda warwarewa da uwar hanjinta taji tanayi wata salama na shigarta rabonta da abinnci tunda safe sai yanzu dataji tana neman hallaka kanta, da sauri ta ajiye abincin ta ɗauki cup ta tsiyayi ruwa a sink tafara kwankwaɗa sosai tana shafa maƙoshinta dayake neman shaƙewa sanan takoma wajen abincin hannunta riƙeda cup ɗin ruwan tacigaba dacin Abinci saidai wanan karon aɗan nutse ba kamar farko ba tana daf da gamawa taji horn ɗin mota sosai babu ƙaƙƙautawa Shiru tayi abincin datakeci yana tsaya mata cak a maƙoshi yaƙi wucewa kuma yaƙi yadawo dan haka da sauri tasake shan ruwa sosai sannan ta ture abincin gefe gabanta na tsananta faɗuwa tayi tsaye cikin kitchen ɗin bata motsa ba Saida taji yadda aka buɗo ƙofar falon da ƙarfi sanan tafito tana kame jikinta kanta aƙasa saboda gudun me idanunta zasu gane mata yau kuma.
Saida ta isa tsakiyar falon sanan taɗago Ahankali ta sauke ƙwayar idonta kan agogon dake harbawa ahankali daidai lokacin data nuna ƙarfe 12:45, sanan ta maida idonta inda yafi motsi acikin falon gabanta na faɗuwa lokacin ɗaya kuma ta ɗauke idon nata ƙafafunta na ɗaukar kerma, cikin sauri tafara ƙoƙarin bin hanyar ɗakinta amma ƙafarta na neman hanata kafin taji saukar Muryar shi cikin tsawa mai amo da razanarwa yakira sunanta.
kiran dataji shi har tsakar kanta har batasan lokacin data juyo baki ɗayanta ba tana sake kallonshi idonta waje kai tsaye kallon nata nafaɗawa kan matan dake maƙale jikinshi sunyi mishi wata iriyar naniƙa ɗayar kanunta nakai kawo cikin rigarshi da wuyanta kebuɗe sosai har ana hango gashin dake kwance a kirjinshi ɗayar kuma nata faman shafar fuskarshi da lasar lips ɗinshi.Dukkansu kallo guda zakayi musu ka ɗauke ido saboda sheɗaniyar shigar dake jikinsu marabarsu da babu kaya kaɗan ne.
Janye bakinshi yayi dagana Linda daketa lasarshi ya kalleta cikin ƙaƙarfar muryarshi dake nuna yafara hassala kuma a make yake yace “Dan tsohon ki bazaki zoba, nikike jira nazo kenan?”
Jikinta ƙaramar kerma yaɗauka ta'iso gabanshi hawaye naɗan taruwan mata gefen ido amma tafara ƙoƙarin danne su Ahankali ta gyara tsayuwarta tabuɗe baki cikin siririyar muryarta tace mishi “gani”tana ɗauke idonta daga kallon baɗalar dasuke aikatawa cikin falonta.
Cikin muryarshi dake abuge haɗe da tsawa “yace wuce ki buɗemin ƙofan ɗakina”.
hawayen datake ƙoƙarin dannewa ne suka ɓalle mata cikin rawar murya dawani irin sanyi tace “babu key awajena aika karɓa ranar”.
Wani irin tasowa yayi yana zare hanun Linda dake shafa sumar ƙirjinshi ya ɗauketa da wani bahaggon marin da Saida takife ƙasa tana sakin kuka mai ciwo da ƙona zuciya, cikin hargowa yace “how dare you Ina magana kina bani amsa haka tsaranki neni, kuma ki fitomin da keys ɗina villager girl”.
Baya tafaja daga zaunen datake tana tallafe kumatunta sosai idanunta na ambaliyar hawaye Masu matuƙar zafi da ƙona zuciya bawai saboda marin dayayi mata bane A'a saboda irin maganganun dayake faɗamata kai tsaye zuciyarta sukeyiwa wani irin yanka.
cikeda rashin imani da rufewar ido yaɗaga ƙafa da zumar yatakata Allah ya taimaketa Ruth ta riƙoshi tabaya tana faɗin Please beb leave her alone lokacin mune yanzu ba nataba tayi maganar tana shafa gashin marar shi dake waje linda kuwa ko kallonsu batayi ba saima yamutsa fuska datayi tafara zare mishi kayan jikinshi tana shigewa jikinshi sosai saboda ba ƙaramin tsana tayiwa matar gidan ba sbd fitinnar sonshi da takeyi sabanin Ruth datake faɗin da Habib takeda business ba matar gidan ba
Cikin mutuwar jiki ta lallaɓa tabar falon batare dako waiwayen su tayiba saima ƙoƙarin nemo juriya take ta hanyar share hawayen da sukaƙi bata haɗin kaisu tsayada ɓulɓulowa dasuke daga ƙwayar idonta tashige ɗakin dayake nata tarufo ƙofar tana zubewa a jikin ƙofar tanajin kamar ta haɗiye zuciyarta tamutu tahuta da wanan ƙasƙantaciyar rayuwar datake marar fasali, tarasa yaushe? Tayaya? Tsantsar soyayyar da sukeyiwa juna take rikiɗewa zuwa ƙiyayya duk bayan kowani second na rayuwarsu, tarasa wane haske yakamata ace yana ƙoƙarin shigo cikin rayuwa? har kullum zuciyarta nafaɗa mata cewar wata rana sai labari amma haryau ranar taƙi tazo.
Kukanta ƙaruwa yayi saboda irin nishinsu datake jiyowa tundaga falon har bedroom ɗinta tanajiyo surutu da ihun da Habib keyi cikin kunenta wanda dama idan yana sex baya iya shiru sam,to yanzu kuma abin yahaɗe biyu baya cikin hayyacin shi dakuma yanayin dayake ciki.
Ziciyarta kamar zai tarwatse tatashi tabar bakin ƙofar tana danne bakinta da hannayenta tanufi bathroom tashiga sanan tazare hanunta daga bakinta tana wani irin kuka maiban tausayi ta tsaya gaban sink ta tara hannayenta ruwana sauka ciki,cikeda ƙoƙarin ƙarfafa kai tafara ɗauraye fuskarta da ruwan tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta amma takasa Mussaman data ɗago ta kalli mirror taga yadda yatsun hannunshi suka fito raɗau kan farar fatarta kamar anyi zane ne. Jingina tayida jikin sink ɗin tasaka hannu tarufe fuska taci gabada kukan tanajin nauyin da zuciyarta yayi yanayin ƙasa,tadaɗe wajen kafin tacire kayanta tayi wanka da Alwollah tafito ɗaure da towel fuskarta ta kumbura sosai saboda kukan datayi hancinta yayi pink.
Tsaye tayi tsakiyar ɗakin Saida ta tabbatar batajin kowane motsinsu sanan ta isa gaban kayanta ta janyo silk gown sky pink tasanya tana zare towel ɗin dake ɗaure jikinta tasaka hular net akanta sanan takoma toilet din ta ajiye towel ɗin tafito cikin tafiyarta marar gaggawa tasaka hijjab ɗin sallarta dahar kullum bata rabuwa da ƙamshi tun dacenma ta matsa inda take gabantarda ibadunta ta kabbara sallah saboda zuciyarta ta'ida daidaita wanda kobata faba faɗa mataba tasan albarkacin ruƙoda ibada dakuma fawwalawa Allah komai ne yasa yanayin datake ciki bai shafi lafiyar kanta ba haryau take cikin hankalinta amma masifar datake fuskanta da yanzu depression yanemi haukata ta.
Saida ta tabbatar 12:30 tabuga sanan tafito daga ɗakin cikin sanɗa a ɗaɗɗare saboda mugun ƙishin ruwa datakeji,wani irin Gwauron numfashi tasauke ganin babu kowa cikin falon sai haske dake tartar kamar allurarka yafaɗi kaduƙa ka ɗauki abunka.wutar tafara kakkashewa sanan tanufi hanyar kitchen saboda takaso wutar can kumata ɗauko ruwan.
Saboda hankalinta nakan shiga kitchen ɗin dakuma haske data kashe yasa bata kulada mutum kwance a gefen kujera ba tuntuɓe datayida ƙafarshi yasa tafaɗa kanshi shima cikin gigin baccin dayake ya riƙeta gam ya sarƙafo hannayen shi kan ƙugunta yana kiran sunanta ahankali.
Wani irin faɗuwa gabanta yayi tafara ƙoƙarin fita ajikinshi saboda jin jikinshi datayi babu kaya amma yasake mannota jikinshi sosai yana neman kamo bakinta, cikin dasashiyar muryarta ta kira sunan shi tana ƙoƙarin tashi at the same time.
Da ƙyal yabuɗe idon yana ganin fuskarta kaɗan ta hasken kitchen dake hasko falon kaɗan yabuɗe bakin yana ɗago kanta sosai yakira sunanta cikin taushin murya sosai.
Da sauri tayi gefe da kanta amma yasake kai hannu yajuyo da fuskar ta yanata ƙoƙarin buɗe idanunshi kanta da kyau.
Ɗan karfin daya rage mata tasa ta tureshi da ƙarfin dan tasan ƙarshenta yace zai mata wani abun yana cikin janaba da najasar karuwan shi. Ita kuma tadaɗe dayiwa kanta alƙawarin tagama yadda yafaɗa mata yana cikin yanayin janabar dana itace sanadin taba.
Wucewa tayi kitchen ɗin tana haki saboda kokowar tureshi datayi amma abinda tagani yasa tayi turus takasa aiwatar da abinda tajeyi saboda ganin Linda tsaye cikin cikin kitchen ɗin hannunta riƙeda waya tana danne danne tana blushing gabanta ta kunna kettle ga dukkan alamu tana jiranya tafasa ne, jikinta kuma ɗaure d towel ɗin habib.Wani sabon takaicine taji yakama mata zuciya ba kaɗan ba saboda ganin yadda tayi kane kane da kitchen ɗin kamar irin tana cikin gidanta ɗin nan kokuma irin tana cikin gidan ubanta Wallahi jitayi kamar tajeta ɗauki kettle ɗinta kwara mata ruwan zafin ajiki uban kowama yahuta.
Shiga datayi kitchen ɗin shine ya ankarar da Linda amma kallo guda tayi mata ta watsar taci gabada da danna wayarta bayan taja dogon tsaki tadire ko kallon banza batayi mataba balle na kirki.
Baƙar zuciyarta data daɗe da mutuwa a kirjinta ce taji tana motsawa acikin kirjinta idanunta na neman rufewa tabuɗe baki da ƙyal tace mata “excuse me”.
Wata shegen dariya Linda tayi ta tsiyaya ruwan a cup sbd sun tafara ta zagayeta tafita tadaga kitchen ɗin tana faɗin nonsense.
Tun bata ida fita daga kitchen ɗinta ba tayi wani wawan tsalle ta cafko bayan towel ɗin jikinta har kerma yake tajuyo da ita,itama a tsiwace tajuyo saidai tun kafin tabuɗe baki tayi magana ta ɗauketa da wani bahaggon mari tana damƙar Wing ɗin kanta cikin ɓacin rai tace zakiga aikin nonsense kuwa dan ubanki,shegiya ƙazamiya mai fitsari a tsaye zaki banbance tsakanin nidake wane mara hankali baƙar karuwa.
Itama zafin marin daya shigeta dakuma zafin kama mata gashi datayi yasa tana juyowa ta kwara mata ruwan dake hannunta Suna tururi sosai saitin fuskarta kai tsaye.
Assalamu alaikum jama'ar Arziƙi ayi haƙuri, hausawa nacewa idan kiɗa ta canja wai rawama canjawa take gamudai acikin Hukunci! Menene ma'anar Hukunci kuma meyasa yazama Hukuncin? Waza'a Hukunta? Duk sai acikin labarin zamu warware