RIGAR KAYA

Chapter 5

by @sadiyaabdulrazak954

*...RIGAR ƘAYA!*



            BY
SADIYA ABDULRAZAK 



 Page 5


  Haka Muhasin ta yi sati ɗayan cikin zulumi, a cikin satin kamar Jawad ya sani ya hana ta fita ko'ina, ita kuma Su'ada kullum sai ta je gidan yari, amma ba a taɓa bari ta ga Mama ba, sai dai a kore ta, saboda faɗan da ta yi da wannan ma'aikaciyar, sannan sun raina ta saboda ba su ga an kawo ta a babbar mota ba, ba su ganta da sutura mai tsada ba, amma a haka kullum sai ta je ɗin.

Cikin satin kullum sai sun yi fira da Khalid, har kiranta yake yi a waya, kuka haka take ɗagawa ta saurari surutunsa wanda ita da kanta ta san bai kamata ba, tun da labari yake ba ta a kan yadda yake sonta, da halin da ya shiga bayan ta auri wani ba shi ba, tare da jaddada mata ba zai taɓa daina sonta ba har abada, dole take kula shi saboda sanin taimakon da zai yi mata nan da wasu kwanaki, da satin ya cika sai Khalid ya ce bai koma gida ba, saboda 'yan gidan nasu ma ba sa nan sun bar ƙasar, sai nan da sati biyu za su dawo.

Zuciyarta ta yi rauni ta ce"Amma Khalid kenan kwata-kwata ba ka fita daga ɗakin hotel ɗin? Ko sallah ba ka fita? Me yasa ba zan ci darajar son da ka ce kana yi min ba ka fita ko wajen me POS ne ka tura min kuɗin?"

Bai yi zaton za ta yi masa wannan ƙorafin ba, ya ɗan daburce ya ce"Amm...ai...kin ga su eriyar babu masallaci a kusa da su shiyasa, kuma da kike maganar masu POS kin manta kuɗin da yawa? Yes ba wani kuɗi ne mai yawa a wajena ba kin sani, amma a wajen talakawa yana da yawa, ina nufin saboda yanayin tsaro ba zan iya zuwa shagon me POS da one million ba wai ya tura miki, sai ki ga wani ya biyo ni da sauransu, ki ƙara haƙuri zuwa sati biyun ina komawa gida zan tura miki in sha Allah my Baby".

"To" Kawai ta ce da ƙyar.

"Baby" 

"Na'am" Ta amsa duk da ba ta so a ce wanda ba mijinta yana kiranta da sunan ba, amma nema take yi a wajensa dole ta amsa.

"Ba damuwa ko?"

"Damuwa kam akwai ta, tun da ban san halin da mahaifiyata take ciki ba, Anti Su'ada idan ta je ba a barinta ta shiga, ni kuma Jawad ya hana ni fita" Ta ƙarasa maganar da raunin murya

Ya sauke ajiyar zuciya "Baby, idan har kin matsu da kuɗin nan me zai hana kawai ki zo ki karɓa? Mintina ƙalilan ya ci kin zo kin karɓa fa, ba wanda ya ji ballanta ya gani, amma a ce Mama tana wanna halin kuma kina da hanyar fitar da ita kin kasa? Haba Baby ki yi tunani fa".

"To zan duba na gani".

 Washegari da ta tambayi Jawad Allah Ya taimake ta ya yarda ta je duba Mama, kuka ta dinga yi ganin halin da take ciki, domin kuwa malaria ce ta rafke Mama sosai, kuma ulcer ta tasar mata kamar za ta mutu, da ƙyar take magana, kuma wannan karon ba ta yi mata fadan da ta saba yi ba, sai kalaman kwantar da hankali da masu kama da wasiyya, ta kama hannunta ta ce"Muhasin mijinki ba shi da laifi, yanzu na gane kuskurena na cusa masa ke alhalin ba ke yake so ba, ni a ganina ke da 'yar'uwarki duk ɗaya zai kalle ku, na tabbata da Hasina yake aure zai iya taimakona, ban ga laifinki ba, mijinki ne ki yi masa biyayya, amma ko bayan raina idan Hasina ta dawo gida ku faɗa mata na mutu ina fushi da ita, tana tare da fushina a duk inda take, sannan ko bayan raina na haramta muku yin zumunci da ita, Hasina 'yar'uwarki ce, amma tun kuna ƙananu na lura ta zame miki rigar ƙaya, to ban amince ki saka wannan rigar ba, gara ki zauna tsirara, Allah zai dubi farar zuciyarki ya suturta ki, ina sonku ke da Su'ada, ina saka muku albarka, ina yi muku fatan alkhairi".

Kukan Muhasin ya tsananta ta ce"Ba za ki mutu ba Mama, za ki bar wajen nan in sha Allah, wallahi ba ni da ko ficika, ba a son raina nake ganinki a haka ba, ba ku da kwanciyar hankali, kuma ki janye kalamanki a kan Hasina don Allah, Allah zai shirye ta, hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar, tamu ce, ba ta da kowa sai mu, sai dai mu dinga yi mata addu'a".

"A'a Muhasin, Hasina ta nuna tana da wanda suka fi mu, don haka dole mu ma mu nuna mata ba ita kaɗai gare mu ba, idan 'ya'ya ne ina da ke da Su'ada, idan 'yar'uwa ce kina da Su'ada, don haka ki cire ta a lissafin danginki".

Ta ɗan jima suna tattaunawa kafin ta tashi ta tafi, ba ta bi direba ba ta ce masa ya tafi akwai inda za ta je na sirri, ya bi umarnin ta, amma nan take tana fita ya kira Jawad a waya ya sanar masa, ya kuwa cika da mamakin inda za ta je, don haka ya ce direban ya bi bayanta cikin dabara ya ga inda za ta je.

A titin ta tsaya ta kira lambar Khalid lokacin yana office cikin aiki, ya ɗauka suka gaisa, ta ce"Khalid...". Sai kuma ta kasa ƙarasawa

Ya ce"Baby ya aka yi? Akwai matsala?"

"E, daga wajen Mama nake, jikinta ya matsa, ina tsoron ta mutu?"

"Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ya kenan?"

"Ina ga ka faɗa min inda kake zan zo yanzun nan".

Ya ɗan daburce kafin ya ce"Yanzun nan? Ok, to bari na tura miki address wajen".

Ya katse kiran ya kira Hasina tana ɗauka ya ce"Muhasin fa ta amince, yanzu ta kira ni ta ce za ta zo, ga shi ni ina wajen aiki kuma".

Ta ce"E yanzu ake faɗa min ta je, kuma ta sallami direbanta, duk da bai tafi ba yana son bin bayanta ne ina ga".

Ya ce"Yanzu mene ne abun yi?"

Da muryarta mai cike da tsiwa ta ce"Kamar ya? Har neman abun yi kake yi? Tashi za ka yi ka je hotel mafi kusa ka kama ɗaki, ka san ba za mu bari wannan damar ta wuce mu ba ai ko?"

"Ok bari na je to".

"Khalid idan ka yi sake ka yi mana asarar wannan lokacin shikenan, duka burikanmu ne a kan Muhasin, kuma wannan tsani ne muka samu, burinmu shi ne mu yi tarayya wajen kashe aurenta ka samu biyan buƙatarka na aurenta ni ma na samu biyan buƙatata na auren mijinta, don haka dole ka daga kafin a zo gaɓar da zan karɓi ragamar komai, ka tashi ka tafi, ka tabbata kun yi hoto Please".


Ya tashi yana harhaɗa takardun gabansa yake cewa"In sha Allah! Na fi ki son cikar burin nan, amma ina so mu bi komai a hankali ne, saboda ina buƙatar samun cikakkiyar soyayyarta bayan mutuwar aurenta, ba na so ko kaɗan na ba da ƙafar da za ta gane plan ɗina ne".

"Idan har kana bin matakaina komai zai zo mana da sauƙi, wani Alhaji ne ya riƙe ni a nan, amma na kusa dawowa in sha Allah, ina dawowa bomb zai tashi da auren nan, don Allah ka yi komai cikin tsari".

Ya fita ya shiga motarsa suna yin sallama, ya turawa Muhasin gajeren saƙo da sunan hotel ɗin kusa da su, sannan ya doshi gida da gudu, don kuɗin ya cire su daga banki suna gida a ajiye tun tuni, ya ɗauka ya doshi hotel ɗin yana fatan ba ta ƙarasa ba tun da akwai tazara a tsakanin wajen da gidan yari, ji yake babu daɗi a ransa, tunawa da cewar direba yana bin bayan Muhasin, zai so a ce ta samu saɓani da mijinta irin wanda zai kai su ga rabuwa, amma kuma ba ya son ganinta a tashin hankali, don haka ya yanke zai gyara abun, ba yanzu komai zai faru ba.

 Ya shiga ya kama ɗaki, ya tsaya ta window yana kallon farfajiyar wajen, babu jimawa ta kira shi a waya ta ce ta ƙaraso.

"Ki shigo ciki".

"Na zata ba sai na shigo ba, sai ka fito kawai ka ba ni, ina cikin adaidaitasahu ma".

Ya ce"No, ki shigo ɗin zai fi Baby, kuma ki kama ɗaki da kanki, bayan kin shigo sai na same ki a ɗakin naki ko kuma ki shigo ɗakin nawa".

"Amma me yasa?"

"Idan kin shigo za ki ji".

"Ba ni da ko sisi fa, mai adaidaitasahun ma ban sallame shi ba".

"Oh my god! Turo min account details ɗin naki yanzu, sai ki yi masa transfer ko?"

Ta tura masa, ya saka mata, ta sallami mai adaidaitasahu, ta shiga ciki gabata yana faɗuwa, wannan shi ne karo na farko da ta shiga hotel a rayuwarta, kuma tana fatan ya zama na ƙarshe indai ba tare da mijinta ba. 

Da sauran kuɗi ta kama ɗaki, ta wuce tana kalle-kallen neman ɗakin, a ƙofar ɗakin ta tsaya ta kira shi "Room..."

Ta bayanta ta ji muryar shi "009".

Ta juyo ta gan shi tsaye yana murmushi hannunsa riƙe da jakar kuɗin, ita ma ta ƙirƙiri murmushin ta yi, ya ce"Mu shiga ko?"

A tsorace take, ta ce"Tun da ga kuɗin ka ba ni na wuce kawai".

Ya narke murya da idanu"Kina tunanin tarin kewarki da na yi zai sa na iya hakan? Please Muhasin i love you, mu shiga ki ji don Allah".

"Na ji me? A'a Khalid ba mu yi haka da kai ba fa".

"Na sani, kuma ni ma ban san zan kasa control ɗin kaina ba, gaiswa kawai za mu yi, sannan akwai maganar da nake so na faɗa miki, don Allah mu shiga".

Idanunta suka yi raurau kamar ruwan hawaye za su zubo, ya ce"Ba abin da kike zato ba ne, ni ne Khalid me sonki, me son zuciyarki ba jikinki ba, a baya ma ban so jikinki ba ballantana yanzu da kike matar aure? Ba ki yarda da ni ba ashe?"

Ba ta ce komai ba, ta yi ta maza ta shiga ɗakin ya bi bayanta.

Daidai lokacin da direban Jawad ya kira shi yake faɗa masa ta shiga hotel, lokacin yana tare da wata shi ma a ɗakin wani hotel ɗin, ya ji wani abu kamar kibiya ya soke shi, ya tashi da sauri yana zame jikinsa daga nata.

      FIRDAUSI 

   A cikin satin da suka shirya wannan plan ɗin, Kabiru ya siyowa Firdausi mai da sabulu na bleeching, ta fara amfani da su, sannan ya siyo zumar ƙiba da sabaya ta fara sha, sai lallaɓata yake yi yana nuna mata ribar da za su ci idan ta samu me kuɗi, cikin wata ɗaya ta fara yin haske tana yin kyau, haka ƙibar ma ta fara murmurewa, ita kanta sha'awar kanta take, Kabiru kuwa kullum cikin wasa ta yake yi, ya fara aro iPhone ɗin abokinsa yana yi mata hotuna yana ɗorawa a status, abokin nasa da ake aron wayarsa ne ya fara cewa yana sonta, saboda yadda yake kallon hotunanta bayan ya dawo masa da wayar, nan take Kabiru ya amince, a plan ɗinsa wannan abokin nasa sam ba ya cikin jerin wanda Firdausi za ta yi soyayya da su, amma zai iya zama wani tsani, za a yi maleji da shi kafin a samu na ainahin.

Shi ya haɗa su ya kai shi har gida, kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka fara soyayya, duk da Kabiru ya faɗa mata za ta kula shi ne kafin ta samu wani, Kabiru da kan shi ya zaunar da abokin nasa yake ce masa "Yusuf ka ga dai ba yabon kai ba Firdausi kyakkyawa ce, ina ƙaunarta sosai, komai ni ne nake yi mata, amma dayake samun nawa ka san dai yadda abun yake to ina so na dinga yi mata sutura wallahi babu dama, idan ka lura kayanta duk yawanci tsumma ne, kayan sallarta take sakawa idan ka zo zance, to ɗazu take faɗa min sun ƙare, yanzu kunyar ka zo ka ganta da tsohon kaya take, tun da ka ga dai ba za ta yi ta saka wanda ka santa da su ba, shi yasa ma jiya da ka zo fa ta ce ba ta da lafiya, wallahi ƙalau take kunya ce saboda babu suturar arziƙi".

Yusuf ya yi shiru yana mamaki kafin ya ce"Ban da abun Firdausi ni ai yayanta ne, kuma ita nake so ba kayanta ba ko?"

Kabiru ya ce"Haka ne amma ka san dai da kunya ai, ni zan ba ka shawara a matsayina na abokinka, ita wannan ƙanwar tawa gaskiya tana da buri da don gayu kuma, indai ba ka so ta dinga kula wani kuna tare to dole sai ka dage da kyautata mata, sai ka buɗe bakin aljihu, don wallahi maza da yawa suna sonta Allah ne Ya ba ka sa'a, idan kuwa ba ka sakar mata kuɗi ba ta samu wanda ya sakar mata to wallahi sai dai ka ji ana yi".

Yusuf ya ce"Haba KB kar ka yi min haka, ai na san za ka tsaya min, ina son yarinyar nan sosai wallahi, in sha Allah zan matse lamba, yanzu ba ni shawara me ya kamata na yi mata?"

Kabiru ya ce"Ai yanzu tun da buƙatar ɗinkuna take, to su za ka yi mata iya ƙarfinka, sannan kuma idan so samu ne ka bar mata wayar hannunka ko kuma ka siya mata wata iPhone ɗin ita ma, tun da eleven ce ba wata babba ba".

Yusuf ya juya wayar ya ce"To ita ɗin ka san kuɗinta kuwa? Amma dai zan duba na gani, ɗinki kuma zan yi mata in sha Allah ko kala uku ne".

"Gara dai ka motsa don ina jiye maka wani ya zo riga ka, mata yanzu sai kana sakar musu kuɗi, soyayya ba ta talaka ba ce, shi yasa ka ga ni ban da buduruwa, sai na yi kuɗi tukunna".

"In sha Allah zan dage, na gode da ka ankarar da ni, ai ba zan yi saken rasa Firdausi ba, don wallahi dami na tsinta a kale, kalar manyan mutane ce".

Suka yi dariya duka, Kabiru yana ayyana sai ya yi masa ƙarƙaf sannan zai raba shi da ƙanwar shi, ya tafi gida yana farinciki.