GANIN IDO

Dandano

by @mamuhgee

*GANIN IDO*

Mamuhgee

2026

Kaddara ko sauyin lamari zasu Kira guguwan mafi girman Al’amarin daya rufesu na wanzuwan abinda zasu iya Kira da tamkar haramtacce???🔥

A nata bangaren kaddara ce da fitina tareda tsautsayi Mafi girma sbd samun kanta a tsakiyar aminiyarta da mahaifiyar aminiyar da Wanda basu taba hada komai da tsantsar soyayyarsa,kaunarsa da tsantsan tattalinsa🔥

Tayaya zata fuskanci kaddarar datake a cikin ahalinda bata taba tsammanin saninsu ba bare samun kanta a cikinsu🔥

Tayaya zata fuskancin rayuwa a inda take kallan tata duniyar daban da tasu,

Hukunci ne daya sauka akan Wanda baisan me tasu duniyar ta kunsa ba bare iya kasancewa a cikinta,

Hukunci ne daya tsayar da duniyarsu da Wainda take cikinta sbd babu ta yanda lamarin zai shiga Kansu bare kwakwalsu da bazata bar duniyarsu daidaituwaba,

Uwa ce

Mata ce

Ya ce

Uba ne duka suke zagaye da alaqar data tabbata Wadda babu Wanda ya shirya mata bare su Wainda kaddadarar ta fada kansu🔥🔥

Shi guguwa ne da babu kowane sauki a cikinsa bayan na iyayensa da familynsa dan haka baisan wata rayuwar ba bayan tasu iya su kadai rak dan haka babu wata Sauran Idon nutsuwa daya rage a rayuwarsa dazai iya kallan wata alaqar bayan ta matarsa da babu kowace mace a duniya a idonsa data kaita🔥

Mata uku ne rak a rayuwarsa da sune wainda duniyarsa kowa ya sani,MAHAIFIYARSA,MATARSA sai ‘YARSA,

Bayansu babu kowane shafi ko babin daya rage na rayuwarsa da wata macen take ciki ko a tarihinsa ansan da hakan🔥🔥

Wannan babin shine nata shafin kaddarar bayyanarta tsundum a tsakiyar shafi da babin da aka rufe ruf da kauna da soyayyar datake tin auren yarinta har zuwa yanzu da girma yafara zuwa🔥

Shi SHUGABA ne mai tsananin kwarjini da kuma kauna me karfi daga ahalinsa🔥

Shi ‘DA ne mai tsananin biyayya da Sanyi ga iyayensa da duk girman matsayin dayake dashi a Idon duniya bai hanasa kwantar da Kai da yi musu biyayya hakama shekaru da tsantsar gogewansa a duniyarsa ta mulkan navy’s bai hanasa kwantar iyayen nasa da Kai ba sbd a duniya Su kadai ne ke iya tsayawa gabansa batareda kwarjinsa da matsayinsa sun saka jikinsu kamewaba🔥

Hakama shi MIJI ne da matarsa kusan tafi ko wace mace Saar samunsa a matsayin miji kuma abokin rayuwar da duniya takewa kallan duk Wanda yake a familynsa me saa da nasara a rayuwa🔥

Sannan shi uba ne da ‘yarsa take alfahari da Jin a duniya babu kamarta kasancewanta jininsa ba sirki hakama ake mata kallan ‘ya mai saa,

Bai hada komai da kowa da ahalinsa,iyayensa ba da kuma qaninsa da yake tankar shine uba a garesa,

Sune alfaharinsa,sune bugun gabansa Hakama sune iya Wainda suke da shamaki Akan aikinsa da

Matsayinsa daya bawa rayuwarsa gabaki daya,

Rayuwarsa a daban take,

a kebe take,

a natse take,

a tsare take,

A sirrance take sbd da yawa sunansa ne ya karade duniyarsa batareda ganinsa ba sedai hotonsa sbd ya zabi rayuwan kwanciyan hankali da nutsuwa tareda Siri ga ahalinsa sbd yanda duniya ke kallansu a Masu saa🔥

Al’adar mahaifiyarsa ta haramta masa abubuwa da yawa na gudanar da rayuwa ciki hadda rayuwar data wuce daga shi sai matarsa da yarsa sai kuma mahaifinsa…..

A bangare daya addini da al’adar mahaifinsa sun halasta masa hakan harma fiyeda hakan Wanda kuma mahaifinsa shi duniya ta sani da FORMER NAVY ADMIRAL HAKEEM JEERAH,tsayayyen tsohon sojan ruwa dayake kaifi daya Akan ko muamalar waje data iyali,tsayayye kuma jajirtacce da zafinsa yake bayyane kuma yake tamkar uba ga kowane babba dayake fada a ji sbd dattakonsa,

ADMl Hakeem jeerah babba ne dayake da tsananin Girma a fannin Addini,siyasa,bangaren Armies da kuma bangaren tycoons ta kowane bangare shi babba ne da ake Bawa girmansa da kuma kasancewansa mahaifi ga FLEET ADMIRAL of the navy gabaki daya na qasar qetare Wanda shine sunansa yake sake fiddo Dana matsayi da darajar ahalinsa…….

Wace guguwance zata feso iska a rayuwar Ahalin JEERAH da zata saka tsayayyun tsoffin sojojin ruwa dagowa,

Yaya amintakar yan mata biyu zata Ginu bayan sanin alaqar dayake kaman a boye,

A bangare Daya mahaifine

A bangare dayan kuma mahaifin Aminiya ne….

Tayaya zasu fara fuskantar guguwan sauyin kaddarar dazai bullowa rayuwarsu da alaqoqi da dama?🔥🔥

Tayaya zasu iya rayuwa a tsakiyar kaddarar da basu taba tunaniba bare tsammata?🔥

Tayaya zasu kalli juna tareda girmammiyar alaqar data sauya suna daga amintaka da amana zuwa sabon yanayi.🔥🔥🔥

#MAMUH

#A RAHEEM JEERAH

#JEERAHs

#FLEET ADM JEERAH

#BESTLOVE

#AGE GAP

#HOTLOVE

#FRIENDSHIP

#FAMILY SAGA

#BEST LOVE STORY

#GODFATHER

#MAN OF PRINCIPLES

GANIN IDO 2026

Kada ku Bari a baku labari sbd salon na daban ne

GANIN IDO

1k

Vip 5k

0022419171 Accessbank Maryam sani gummi