PAGE 3
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
PAGE 3
Gefen su Oga Jud kuwa. Misalin ƙarfe biyar na yamma. 5:30pm, Zaune suke a bakin swimming pool na katafaren Gidan na su. Wasu laptop ce a gabansu suna aiki da ita, wasu lissafin kuɗi suke domin kassafawa kamar yanda suka saba.
Wayar Oga Jud da tayi ringing ce ya ɗaga tare da kara ta a kunnensa yace.
"Alaji ka karɓi kayan ka?"
Daga can ɓangaren mutumin ya ce.
"Na karɓa. But where is the money?"
Karan sigarin da ke hannunshi ya wani zuƙa da ƙarfi sannan ya yi wurgi da ita ya furxar yana mai jinjina kai.
"Kuɗi namu ne Alaji. Kai kasan ba sa daga cikin jadawalin aikin da ka bamu, abin da ka nema ka samu, komai an yi shi yanda ka ce babu kuskure a ciki..."
Daga can ɓangaren Alajin ya katse shi da faɗin.
"Yes! Aiki ya yi kyau. But dole ku bani nawa kason daga ciki because nasan cewa manyan kuɗi ne kuka karɓa..."
Yanzu kam ƙara gyara tsayuwar sa ya yi da kyau ya ɓata fuska tamkar yana a gabansa ya ce.
"Alaji! Listen very well...Bana tsallake iyakar mutum, haka zalika bana son nima a tsallaka iyaka ta. Ina da rules ɗina, Aikin da ka bamu ya kambala ba tare da an samu kuskure ba. Ka aiko mana da cikon kuɗinmu, ka manta da kuɗin da mu ka karɓo domin babu naka a ciki, idan kuma ka ce za ka kawo mini wasa...tabbas zan kashe ka,zan shafe tarihin ka ka zamto tamkar ba'a yi ka ba. Na rantse da Allah kasan zan aikata..."
Cikin tashin hankali Alajin ya ce.
" Kwantar da hankalinka..eh..Ahm! daman wasa nake maka. Zuwa an jima In Sha Allahu zan tura maka cikon kuɗ..."
Kashe wayar ya yi kai tsaye ba tare da ya jira ya sauke maganar tasa ba.
Waigawa ya yi ya kalli Daniel (Bado) dake ta faman lissafi ya ce.
"Daniel...ka ajiye kassafa kuɗin nan ka bari an jima idan ya ƙarasa ciko mana kuɗin aikin sai a haɗa a turawa kowa nasa. Idan kuma yace zai kawo mana wasa ku bi duhun dare ku sheƙe min shi har lahira."
Jinjina kai Daniel ya yi yace.
"OK Oga."
Wata takarda Bash (Ashu) ya fito da ita daga cikin wani file ya ce.
"Wannan shi ne aikinmu na gaba, Habib (Tiger) ka karɓa Ka shirya bayanai sannan ka turawa kowa.."
Nan suka zauna suna ci gaba da duba abubuwan da ke gaban su.
Yayin da Jak ke can kwance a ɗaki tun baccin da ya kwanta bayan sun dawo daga operation ɗin bai farka ba sai yanxu. a hankali ya shiga motsawa jin gabaɗaya yanda gaɓoɓin jikinsa suka saki yana mai jin tamkar ba za su sake moruwa ba.
Daƙyar ya iya juyawa daga position ɗinda yake tare da saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa jin yanda yake wani irin tsananin sara masa tamkar zai tsage ya rabe gida biyu.
"Abbah!!!"
Wannan itace kalmar da ta fara zuwa a masarrafar tunaninsa yana mai jin yanda muryarta ke ratsa dodon kunnen sa cikin wani irin taratsi tamkar yanzu ne abun yake faruwa.
Wata irin zabura ya yi ya miƙe zaune yana mai jin duniyar na juyawa da shi ƙwaƙwalwarsa kuma na daɗa hautsinawa.
A hankali hotunan abubuwan da suka faru a daren jiya suka shiga dawo masa bit by bit tun daga farko har ƙarshe.
Wani irin tsalle yaji zuciyarsa ta yi wanda a lokaci ɗaya ya ji wani irin tashin hankali ya mamaye masa zuciya.
Cikin zafin nama ya diro daga kan gadon da yake kwancen direct ya fito parlour yana rarrabo idon inda zai gansu. Ganin ba kowa a nan yasa ya fita waje da sauri tamkar zai kifa domin tashin hankalin da yake ciki a yanxu yama zarta misali, tuni ya nemi gajiya da wata kasalar da yake ji ya rasa.
Yana zuwa gaban Oga Jud ya wani turasa da ƙarfi sai da ya faɗa cikin swimming pool ɗin ba tare da ya shirya ba.
Ganin hakan yasa duk su ka miƙe a tare cike da mamaki suna kallonsa.
Cikin mamakin shima Oga Jud ya fito daga ruwan yana mai ƙure fuskarsa da kallo ya ce.
"lafiyarka kuwa?"
A fusa ce ya ce.
"Miyasa kuka cutar da wannan yarinyar??"
Cike da mamaki Oga Jud ya kalle shi domin shi har ya ma manta da wannan zancen ya ce.
"Wace yarinya??"
Idonsa a buɗe ya ce.
"Kasan yarinyar da nake nufi Oga Jud, don't pretend. Wannan yarinyar ta gidan Alhaji Mas'ood Galadima."
Jinjina kai Oga Jud ya yi sannan ya ce.
"Ohh! Wai operation ɗinmu na jiya kake magana a kai? To miye abun da ya dameka da wannan? Babu abin da tayi mana kawai dai tana cikin aikin da Alaji ya bamu yace ita fyaɗa za'a yi mata..."
Cikin wani irin tsananin ɓacin rai yana mai yi masa wani mugun kallon ya ce.
"And Why me? Why me Oga Jud??"
Hannu Oga Jud ɗin ya ɗaga masa ya ce.
"Hey! Point of correction. Ba suna na Oga Jud ba, sunana OGA BADRU kamar yanda ka sani. Kafi kowa sanin cewa sunayen da muke amfani da su a lokacin da za'a fita aiki Saƙaƙƙun sunaye ne da muke ƙirƙirarsu a lokacin da zamu fita aiki, kuma daga zaran mun dawo shikenan sun zama expired domin gujewa matsala. Kada ka sake kirana da Oga Jud...Kai da duk wanda ke wurin nan ma, kowa ka kira shi da sunansa... "
Wata irin shaƙa Jak ɗin ya kaiwa kwalarsa a fusa ce yana faɗin.
" Ba ka bani amsa ta ba. Tambayarka nake Why me? Duk cikin yaranka ba ka ga wanda za ka saka ba sai ni? Miye ya haɗani da ita da har za ka sanya na aikata mata haka? Abin da ya kai ni daban kuma abin da ya kai ku daban. Why did you involve me?"
Da ƙarfi Oga Badru ya saka hannayensa ya ture Jak ɗin sannan ya ce.
" Because naga cewar kana son ɗaukar fansar mahaifin ka ne. Kada ka manta mahaifin ta shi ne ya kashe maka mahaifi, hakan yasa naga cancanta ka ƙuntata musu sosai kamar yanda kai ma ka ƙuntata...sanin irin halin ka ne yasa na saka su Bash suka haɗa maka ƙwayoyi masu saka matsananciyar sha'awa a lemu da kuma canja tunani,wanda ba don fyaɗen kaɗai nayi maka hakan ba, hatta wurin kashe mahaifin na ta nasan cewa kana iya kofsawa. Kuma sai ga shi,ban yi kuskuren hasashe ba, duk da wannan shirin da na yi maka sai da ka kofsa ɗin Azaan. And ni na yi komai ne domin ka samu cikar burin ka na ɗaukar fansa a wannan daren..."
Wani irin girgiza kai ya shiga yi yana mai jin wani iri a ransa ya ce.
" Na yi nadamar sanin ka a rayuwata Oga Badru! Na yi matuƙar baƙin cikin haɗuwa da kai....Cutar da rayuwar mace musamman irin wannan zunubi ne, idan har wannan shi ne taimakon, to Allah ya tsinewa taimakon naka...."
Hannayensa ya saka ya dafe kansa, sannan ya shafo tundaga saman goshin sa har zuwa bayan ƙeyarsa yana mai jinjina kai sai kuma ya sake ɗagowa ya kalle shi cike da hauka ya ce.
"Kana gani fa...Hatta mahaifin na ta kasa kashe sa na yi, duba da yanda iyalinshi suke kuka, suka dogara da shi. shin idan na kashe shi a gaban su how are they going to feel? Ni ɗin ba kamar shi ba ne, ni ba zan iya kisan kai ba...Na bar shi...na barshi da Allah, shi ne wanda zai yi mana sakayya a gobe ƙiyama...but! Ya zama dole na na koma wurin wannan yarinyar,... "
A tare suka waigo suka kalle shi lokaci ɗaya jin wata irin yasassar maganar da hankali ma ba zai ɗauka ba.
Wata irin damƙa Oga Badru ya kai wa hannun Jak ɗin a ruɗe ya ce.
"AZAAN...Are you out of your senses? Noo! Ina ga ka fara hauka ne Azaan."
Wani kallon ya yi wa Oga Badrun ya ce.
"And nobody will stop me!"
Cikin wasu irin kalamai masu nuna alamar gargadi Oga Badru ya ce.
"I'm warning you Azaan! A very big sound warning! Lallai ka karɓi kuɗin ka kawai ka kama gabanka. Idan ka kuskura ka amince da wannan gurguwar shawarar da tunaninka ke baka, to fa kana cikin hatsari, domin daga lokacin da ka nuna kan ka gare su, daga lokacin tarihin ka zai shafe har abada."
Jinjina kai ya yi bakin gaskiyarsa ya ce.
" ban san mi ya kamata na yi ba, amma kuma ya zama dole na je naga halin da yarinyar mutane take ciki. Idan har wani abu ya same ta, har abada ba zan yafewa kai na ba..."
A tare su ka miƙe suka sha gaban shi kowanen su da fuskar shanu tamkar za su rufe shi da duka.
Girgiza kai Oga Badru ya sake yi a karo na barkatai sannan ya kalli Azaan ɗin ya ce.
" Ba za ka aikata hakan ba Azaan! Ni ba zan taɓa bari ba..."
Shi ma da wata irin wuta a kalamansa ya ce.
"Ba bu wanda ya isa ya dakatar dani daga cikin ku."
Wani irin karyar da wuya Oga Badru ya yi tare da yi masa wani kallon yace.
"Shekaru goma sha takwas na kwashe ina wannan harakar, daidai da rana ɗaya ban taɓa kuskure wa ba. Babu kuma wanda ya taɓa kawo min matsala, a kanka kuma ba za'a fara ba Azaan. Kada kace za ka yi wasa da rayuwarka..."
Ratsa tsakaninsu Daniel da Bash ya yi kai tsaye ya wuce.
Cikin wani irin mamaki Oga Badru ya shiga kwala masa kira amma sam ko alamar juyowa bai yi ba. Abu kamar wasa sai ga shi sun gan shi ya shiga gidan ya fito ya figi mota da ƙarfi.
" Prince...Kada ka ɗaga ƙafa, just Shoot him. We have no choice."
Oga Badrun ya faɗa yana mai kallon inda Prince ɗin yake tsaye.
******
Ya Muhammad kuwa, a hankali ya shiga maida numfashi jin cewa tana raye ba ta mutu ba. Kawai dai har yanzu likitocin sun kasa shawo kan ta ne har yasa su Mubarak ruɗewa domin da ta ja wani irin numfashi sun za ta ta mutun ne kamar yanda Dr. Anil ya faɗa.
Yana nan a tsaye jingine jikin ƙofa Yaya Amina ta zo da waya a hannunta a hankali ta kara ta zuwa kunnensa wanda shi sam bai ji zuwan na ta ba, sai saukar maganar Mukarram da ya ji tana karaɗe masa dodon kunnensa.
Daga can ɓangaren Mukarram ɗin ne ya ce.
"KATEH! (Ma'ana yaya) Miyasa ba za ka yi magana da ni ba? Na fa riga na ji komai da ya faru tun ɗazu. Idan ka buɗe bakin ka, kai ko Mubarak ku ka yi mini bayanin gaskiyar abin da yake faruwa, shi ne zai sa hankalina ya kwanta. Amma gujewa magana da ni da kuke yi shi ke sa ina ƙara jin karaya. Dan Allah ka faɗa mini miye ya faru? "
Jinjina kai Yaa Muhammad ɗin ya yi tamkar yana gabansa a rauna ne ya ce.
" Abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi Mukarram. Na rasa ta yanda zan fara yi maka bayanin ne. But duka su ukun suna cikin mawuyacin hali..."
Nan ya yi masa bayanin komai yanda ya faru sannan daga can ɓangaren Mukarram ɗin ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya sannan a hankali ya ce.
" Ba komai. Allah yana sane damu Kateh,muna roƙon ya bamu ikon cinye wannan jarabawar ya sanya mana haƙuri da dangana ga duk wani abin da zai riskemu. A tsaurara bincike sosai. Muna kan hanya zamu je Airport In Sha Allah. Sai mun iso."
Janye wayar ya yi tare da kallon Yaa Amina wacce ke ta sharɓar hawaye ya ce.
" Thank you."
A hankali ta jinjina kanta ta ce.
" I'm sorry! Shi ne ya kira da kansa yace na baka..."
"Ba komai Amina."
Muryar Mubarak ya ji a bayansa a hankali yana faɗin.
"Daddy Ridwan ya zo yana ƙasa, Baba Salisu shi ma yana ɗakin Abbah tun ɗazu."
✍️ OUM-AMEER ✍️