PAGE 4
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
PAGE 4
Da sauri Oga Badru ya ɗagawa Prince ɗin hannu ganin yanda Azaan ɗin ke ta faman danna horn but gate ɗin yaƙi ya buɗe,jinjina kai ya yi tare da kallon Prince ɗin ya ce.
"Wait! Wait prince"
Dakatawa ya yi suka zuba ido suna kallon Azaan da mamakin abin da ya hana shi tafiya.
Muryar Aroun (James) suka ji yana faɗin.
"Na rufe gate ɗin ta yanda ba zai iya fita ba."
Cikin farin ciki Oga Badru ya ce.
"Thank you so much Aroun. Haƙiƙa Aikin ka yana kyau. Tamkar kar ka koma ƙasar ka haka nake ji domin kana da matuƙar basira da kaifin tunani."
Daga haka ya taka ya isa har bakin gate ɗin inda ya tarar da Azaan ɗin still yana ta danna horn ɗin ba tare da ya sare ba.
Ganin Oga Badrun a gaban motar ne yasa ya fito daga ciki yana wani irin ɓata rai ya ce.
" Ka buɗe mini ƙofa na fita!!!"
Jinjina kai ya yi yana mai kallon fuskar Azaan ɗin ya ce.
"I will, but ina da wata 'ƴar magana wacce daga ita na baka damar yin duk abin da ranka yake so.."
A hankali ya taka ya shiga zagaye shi yana taku a hankali ya ce.
"Kana ta iƙirarin cewa kai sai ka je Kaga halin da yarinyar take ciki. Shin kana da masaniyar cewa idan kaje kuka yi ido biyu da ahlinta ba za su ƙyale ka ba? Yarinyar yanxu haka duk da ban sani ba, ina da tabbacin cewa tana gadon asibiti. Saboda haka, ba za ka ganta ba. Abu na biyu kuma mai matuƙar muhimmanci shi ne...Shin idan kai ka shirya salwantar da rayuwar ka to ita mahaifiyar ka fa? Kada fa ka manta sai da ta gargaɗe ka. Yanzu kuma da ka tsallake sharaɗinta ka karya alƙawarin da ka ɗaukar mata da umarninta ya ya kenan tsakaninku zai kasance? Duk ka bi ka wani ɗaga hankalin ka wai kai ka yi fyaɗe. To me..wannan ɗin is common, domin na yi yafi dubu kuma babu abin da ya faru. Da fyaɗen da kashin kai da ka yi niyyar yi wanne ne yafi zunubi?"
Da ƙarfi ya runtse idanunsa, yana mai jin yanda kalaman mahaifiyar tasa ke dawo masa tamkar yanzu ne take yi masa gargaɗin.
" Ban amince da ka nemi wata fansa ba! Tun da har hukuncin ya zo a haka, to ina roƙon ka alfarma don Allah mu barwa Allah. Na rasa mahaifin ka, ba zan iya jure rasa ka ba, idan wani abu ya sameka tabbas zan kasance a baƙin ciki da dana sani fiye da wanda nayi a baya da kuma wanda nake ciki a yanzu. Saboda haka, Ka bar wannan maganar ta wuce har abada. Idan kuma kaje bayan idona ka aikata wani abun to lallai kaje ka nemi wata uwar ba ni ba..."
Wani irin mugun duka ne ya kaiwa glass ɗin motar wanda duk ƙarfinsa sai da ya fashe ya tarwatse. Sosai hannunsa ya shiga zubar da jini, duk da haka ba wannan ɗin ya ke ji ba. Shi wannan wace iriyar mummunar ƙaddara ce? Ta ina zai fara?
A raunane ya sake ɗago ido ya kalli Oga Badru, murya a karye ya ce.
" And duk da cewa kasan na faɗa maka wannan kuma shi ne ka yaudare ni? Kasa na aikata mummunan kuskure, kuskuren da ba zai taɓa gyaruwa ba. Zan iya faɗawa mahaifiyata cewa na kashe Alhaji Mas'ood ta yafe min, but yiwa wannan yarinyar fyaɗe..."
Cikin ɗaga murya oga Badru ya ce.
" Common Azaan ka daina yin kamar babu ruwan ka a cikin wannan lamarin! We plan everything together, yes! Da Kai muka shirya komai, and kai ne da bakinka ka faɗamin cewa kana son kashe wanda ya kashe maka mahaifin ka. But abin mamaki yanzu kuma kana ƙala mini laifin ni kaɗai kamar janyo ka nayi don dole.."
Juyawa ya yi kawai ya koma ciki tare da barin motar nan bakin gate ɗin.
Jikin ƙofar ɗakin ya jingina tare da lumshe idanunsa tsawon lokaci yana ta tunani barkatai na neman mafita.
Ya jima yana saƙawa yana warwarewa, wanda daga ƙarshe ya wuce toilet ya yi wanka sannan ya ɗoro alwala ya fito ya shiga jera salloli.
*******
Gidan Alhaji Mas'ood kuwa.
Zaune Alhaji Mas'ood ɗin yake an rataya masa bandage a wuyan sa wanda ya tallafe masa hannun sa da suka harbe shi. Jingine yake jikin kujerar sosai tare da lumshe idanunsa waɗanda suka yi masa nauyi sosai akan rashin wadataccen baccin da baya samu a 'yan kwanakin nan. Muhammad ne zaune a kusa da shi, sai kuma Mubarak, Baba Salisu da Alhaji Ridwan zaune a mabanbanta wurare, yayin da Mukarram ke tsaye kamar yanda jami'an da suka yi sallama su ka shigo kai tsaye a tsakiyar parlourn suka tsaya su ma.
Jerin jami'ai kala uku ne suka haɗa hannu wurin aikin bincike akan wannan abun da ya faru a gidan babban Attajirin ɗan kasuwa Alhaji Mas'ood Galadima, abunda ake kira Joint Task Force. Wanda investigation ne da ya haɗa da police force sashen CID unit,sai hukumar DSS, da kuma Elite Cyber Forensics Unit. Wanda National investigator Coordinator (DCP) Hadi Balarabe Shi ne wanda yake jagorantarsu.
Mukarram shi ne wanda ya fara magana da cewa.
"Wai DCP miye yake faruwa ne? Yau sati ɗaya da faruwar abun nan amma har yanzu babu wani bayani."
Jinjina kai DCP ya yi sannan ya ce
"Wannan gaskiya ne Doctor Mukarram. Ahmm! Haƙiƙa mun gudanar da cikakken bincike na tsawon sati ɗaya, wanda mun yi aiki tuƙuru ba dare ba rana. Mun duba dukkan kyamarori, bayanan Na'urar ORION-9,motsin shiga da fitar mutane, har da bayanan Wayoyi da antenna na wannan yankin...."
Ɗan wawwara ido ya yi yana kallon su kamar yanda duk suka zuba ido suna kallonsa, sannan yaci gaba da cewa.
" But unfortunately....with all the hard work, abunda muka fuskanta a wannan lamarin ba sata ce ta yau da kullum ba kamar yanda aka saba. Waɗanda suka yi wannan ta'adin masu matuƙar basira ne sosai, domin sun yi aiki da ilmi, tsari da kuma fasahar zamani. Sun yaudari tsarin tsaro ba tare da sun bar kowace irin alama da za'a iya kama su ba. Sun yi amfani da gurɓataccen tsarin lokaci, signal Masking da kuma pre recorded feeds. Sam ba su bar kowace irin alama ba, kamar sawu, zanen yatsa, fuska ko DNA da za'a iya bin diddiginsu da shi..."
DCP ɗin ya ƙarasa maganar tare da ɗora wasu takardu akan centre table ɗin da ke gabansa na shaidar bayanan da ya gama bayarwa a yanzu.
Ɗaya daga cikin jami'an Cyber Forensics Unit ne ya jinjina kansa ya ce.
" Ko a matakin binciken Digital da muka gudanar, an goge hanyoyin data, an karya hanyar bin IP, wanda sun yi amfani da na'urorin da ba sa barin alama komai ƙanƙantar ta. To a wannan gaɓar gaskiya, bamu da wata shaida da za ta kaimu koda ga mu mutum ɗaya ne a yanzu dai, sorry to say....."
Cikin zafin rai Mukarram ya ce.
"To yanzu mi kuke nufi kenan DCP? Kuna nufin kenan waɗanda suka aikata mana hakan shi kenan sun ci bulus kenan? DCP ka kuwa san halin da Anaam ɗinmu take ciki?"
Tasowa Muhammad ya yi yazo ya dafa Mukarram ɗin camly ya ce.
"Ya isa Mukarram! Ka bari abi komai a san..."
Cikin wani irin raɗaɗi da zafi ya kalli yayan nasa ya ce.
"Kateh kana fa jin maganar banzar shirmen da suke faɗa! Wanda ya yi wa Anaam ɗin haka za'a ce wai ba'a san yanda za'a yi a kama shi ba? Ni nan da zan gansa seconds sun yi yawa na kashe shi..."
Cikin kalaman Ladabtarwa Baba Salisu ya kalle sa ya ce.
"Mukarram ya kamata ka nutsu. Duk abinda kwanciyar hankali bai bayar ba tashin hankali ba zai bayar da shi ba. Ka yi haƙuri ka sassauta."
Miƙewa Alhaji Ridwan ya yi ya kalli DCP ya ce.
"Let's go outside Please."
A tare suka fice Alhaji Ridwan ɗin yana gaba, su kuma jami'an suna bayan sa.
A wata rumfar shaƙatawa ya ja su suka zauna akan tsararrun kujerun da ke wurin.
Jinjina kai Alhaji Ridwan ya yi yana mai kallon DCPn ya ce.
"Ina baka haƙuri DCP... Haƙiƙa suna cikin jimami da tashin hankali shiyasa ka ji Mukarram ya yi magana haka. Amma ni ma a gareni gaskiya wannan maganar ba magana ba ce ku ce wai babu ta yanda za'a yi a gano waɗannan sheɗanun mutanen."
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya jinjina kai ya ce.
" Magana ta gaskiya ranka ya daɗe a yanzu dai, babu wani bayani. But za mu ci gaba da bincike in sha Allah. Ko a ma'aikatan gidan har yanzu bamu samu wata makama ba."
Hannu ya bashi alamar godiya yace.
" Shi ke nan DCP. Mun gode sosai. Allah ubangiji yasa mu dace, Allah ya bayyanasu ko su waye ya tona musu asiri."
Miƙewa su ka yi DCPn yana mai faɗin.
" Amin Yah Allahu. Mun barku lafiya."
Cikin parlourn ya koma bayan sun wuce ya zauna cikin nutsuwa ya fara musu magana musamman Mukarram wanda ya fahimci cewar yafi kowa ɗaukar zafi.
" Dan Allah abin da nake so da ku dangane da wannan abun da ya faru....komai fa da kuke gani muƙaddari ne daga Allah. Duk abinda Allah ya ƙaddaro cewa zai sami bawansa to babu wanda ya isa ya hana. Mu ɗauki wannan abun da ya faru a matsayin ƙaddara. Idan muka ce zamu ci gaba da hakan to har abada zamu ci gaba da ƙuntata a zuwan kowace rana. An rasa rai kuma aka haƙura aka ci gaba da rayuwa ballantana wannan ɗin, mu yi haƙuri,mu maida hankali wurin ceto rayuwarta, su kuma Allah ya tona asirinsu...."
Miƙewa Mukarram ya ƙara yi yana mai kallon Mubarak ya ce.
" Mubarak mi ma kace wannan ɗan daban ya faɗawa Alhaji??"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
" Yauwa...cewa ya yi wai su ɗin 'ƴan aike ne right? kuma duniya ta lalace yasan irin abokan hulɗar da zai riƙa mu'amala da su ko?"
Wani irin tafa hannu zai yi yana wani jinjina kai cikin ɗaga murya ya ce.
" To na ma gane kowaye ya aikata mana wannan abun! Alhaji Gimba ne...Yes! Alhaji Gimba... "
" Mukarram ya Isa!!!"
Cewar Yaa Muhammad yana mai yi masa wani kallon da ke nuni da cewa kamar ya fara zaucewa.
Kallon Yayan nasa ya yi yana jinjina kai ya ce.
" Shin wai Kateh mamaki ka ke Ko kuma tantama? Alhaji Gimba kowa yasan cewa shi ne wanda yake takun saƙa da Alaji tsawon lokaci...and bai fi 3month ba da yazo yace a ba wa ɗansa Faris auren Anaam aka ce a'a. To ka gayamin idan ba shi bane waye?? Waye nace ya turo su?"
Ido kowa ya zuba yana kallon sa wanda Abbah ne kaɗai wanda idanunsa suke a rufe har yanzu tamkar baya jin abin da yake faruwa.
Ganin yanda Mukarram ɗin ya juya a fusace yasa Muhammad da Alhaji Ridwan suka shiga ƙwalla masa kira amma sam bai waigo ya kalle su ba.
A zafafe yaje yaja motar kai tsaye ya nufi gidan Alhaji Gimba ransa na masa wani irin tafarfasa.
✍️ OUM-AMEER ✍️