DUHUN DARE

PAGE 11

by @oumameer2671

D U H U N   D A R E

A 2026   N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

      OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

PAGE 11

***

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzartq shiga wannan link.💃💃💃

 Anam kuwa, kwana ta yi tana abu ɗaya, wato kuka. Gabaɗaya ta susuce ta fice daga hayyacinta. Wannan abun da Rabi'a ta nuna mata ya tayar da hankalinta. She thought cewa daga ita sai familyn ta ne kaɗai suka san wannan abun, she thought a yanzu komai ya wuce domin sirrinta a rufe yake. Ashe labarin ta da abinda ya faru da ita har hotunan ta suna can suna yawo a kafafen sada zumunta. Wanda ya santa da ma wanda bai san ta ba a yanzu kowa ya ji abinda yake faruwa da ita. Wannan wace iriyar ƙaddara ce? Ina ma ace mutuwa ta yi! Da yanzu ta manta da wannan baƙin cikin da take ciki.

Abubuwan da ta kwana tunani kenan a ranta tana mai darzar kuka tamfar wacce saƙon mutuwar ta ya risketa. Gabaɗaya mutanen gidan kusan kwana suka yi ana aikin rarrashinta da ƙyar suka samu ta ɗan sassauta. a haka suka kwana tare da Na'imatu har garin Allah ya waye ba tare da sun runtsa idanun su ba.

Bayan ta kambala sallar Asuba ne ma ta ɗauko alƙur'ani ta fara karantawa. Ganin hakan yasa Na'imatu ta samu wuri ta ɗan kifa kanta sai gashi bacci ya kwashe ta nan take wanda koda ta farka ta ga Anaam ɗin itama ta ɗan kifa kan ta gefen gadon Ammien daga nan bacci ya kwashe ta.

Ta shi Na'imatu ta yi taje ta yi brush tare da wanko fuskar ta ta fito, jin motsin ta yasa Anaam ɗin buɗe idanunta waɗanda suka kumbura sosai tsabar yanda tasha kuka ta kalle ta kawai ba tare da tace mata komai ba.

Murmushi Na'imatun ta sakar mata sannan ta ce.

"Kin farka kenan?"

Ɗauke idon ta tayi tare da jinjina kanta kawai alamar eh ba tare da yi mata magana ba.

"Please you need to Eat something, Gabaɗaya daren Jiya ba ki saka komai a cikin ki ba..."

Da sauri ta girgiza kanta alamar a'a.

"You must eat something Gaskiya. Bari na fita na samo mik..."

Ɗagowa ta yi ta kalle ta muryar nan can ƙasa sosai ta ce.

"Aunty Na'imatu ki fahimce ni please! bana son cin komai a yanzu. Idan na ƙara hutawa zan fito na ci abincin."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Shi ke nan."

Daga haka taje ta ɗora zani akan sleeping gown ɗinta ta saka hijab ta ɗinta ta fita waje.

Gabaɗaya gidan tsit yake tamkar ba kowa a ciki. A dining area ta tarar da Nene tana shirya table domin breakfast ta kalle ta.

"Nene ina kwana..."

Cike da girmamawa Nene ta kalle ta da fara'a ta ce.

"Ina Kwana Na'imatu. Ya jikin Anaam?"

"Jiki Alhamdulillah! Ammie fa?"

"Ta fito amma tun ɗazu ta koma..."

"Abbah ya fita ne?"

Girgiza kai Nene ta yi ta ce.

"A'a. Mubarak ne dai na ga ya fito da shirin sa yace mini ya tafi Abuja..."

Jinjina kai ta yi tare da juyawa ta nufi Sashen Abbah tana faɗin.

"OK...please ki haɗawa Anaam breakfast a single tray, zan zo na karɓa."

"Ok."

Wayar ta dake hannunta ta ɗaga ta kira Mubarak,ringin ɗaya zuwa na biyu ya yi picking.

"Yaa Mubarak tafiya ba sanarwa?"

Murmushi ya yi ta daga can ɓangaren tamkar yana a gabanta ya ce.

"please I'm sorry. Ni ma ban san da tafiyar ba sai yau da asuba. Kaya aka sauke kuma Yaa Naseer kin san Nusaiba ba ta da lafiya shi kuma Yaa Muhammad baya ƙasar..."

"Ok, Allah sarki Yaa Mubarak. Ba damuwa Allah ya tsare hanya yasa a dawo lafiya."

"Amin. Ya Anaam take? Koda na fito na haɗu da Ammie ta ce daga ɗakinku take ta dubo duk kun yi bacci...na ce Alhamdulillah! Mutuniyar ta ɗan sassauta..."

Girgiza kai ta yi da ɗan murmushi ta ce.

"Yaa Mubarak Anaam ba ta samu bacci ba ko kaɗan. Rabi'atou ba ƙaramin kofsawa ta yi ba..."

"Ki bar Rabi'atou kawai, Sam ba ta da wayau ko kaɗan. Allah ya kyauta yasa mu dace. Allah ya bata hakuri da dangana."

"Amin Yaa Mubarak, bye..ka gaishe da su Yaa Amina."

********

Ammie.

Ta fito daga wanka kenan ta zauna tana shiryawa ta ji wayar ta tayi ringing.

Agogon da ke manne da bangon ɗakin Abbahn ta fara kallo taga ƙarfe bakwai da minti uku sannan ta miƙa hannu ta ɗauko wayar ta duba.

Sunan Hajiya Salamatu ta gani yayi appearing gaban screenv ɗin wayar wanda sai da ta jira ta gama ringin kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta kamo numbern ta kira ta back, cikin seconds ta yi picking tare da fashewa da kuka daga can ɓangaren ta ce.

"Hajiya Nasmah!"

Cikin tashin hankali Ammie ta miƙe tsaye jin yanda ta fashe da kuka ta ce.

"Subhanallah! Hajiya Salamatu lafiya?"

"Ba lafiya Hajiya Nasmah...Wai yanzu Gimba har yana iya kallon idona ya ce wai idan ina son saki zai bani akan zai yi aure..."

Cike da mamaki Ammie ta ce.

"Aure? Shi Alhaji Gimban ne zai yi aure?"

"Aure wai zai yi. Wulakanci a kwanakin nan sai abin da ya manta, daga ni har Faris ɗin ba wanda ya ragawa. Gabaɗaya ya gigice ya ƙarasa birkicewa tamkar burgaggen kan famfo....wallahy ko wannan abun da ya same ku Hajiya Nasmah na so na zo kamar me amma ƙememe ya ce ba zani ba. Na rasa miye abin da yake damunsa a 'ƴan kwanakin nan..."

Girgiza kai Ammie ta yi ta ce.

"Ba komai Hajiya Salamatu, na gaji me ki. Sannan dangane da auren sa don Allah ni dai ina baki shawara ki daina koke-koken nan ki daina ɗaga hankalin ki..."

"To Hajiya Nasmah ya zan yi? Kin fi kowa sanin waye Alhaji Gimba da irin zaman haƙurin da nake da shi. A haka ma haƙuri nake ina ga ya auro mini yarinya ƙarama Hajiya Nasmah?".

"Haka ne, to amma ke kanki gashi yanzu kin faɗi cewa zaman haƙuri kike, saboda haka ki yi haƙuri ki kauda kan ki ki ɗauki komai ba komai ba. I know cewa abun da ciwo sosai, but ki yi haƙuri ki kwantar da hankalin ki. Aure dai yarinya ba akan ki za ta zauna ba, musamman idan ma ba a gida ɗaya zai ajiye ku ba, hakan sai ya fi miki sauƙi wanda sai ma kin manta da cewa wai yana da wata matar bayan ke. Idan kina damuwa shi zai sa ya yi ta yi miki abubuwan ɓacin rai, amma idan kika nuna mai cewa aurensa bai dameki ba kina murna kina komai wallahy sanyi zai yi. Saboda haka ki yi ta ibada kina gayawa Allah sannan ki yawaita yin sadaka domin tana maganin masifa."

"Hmm! Ni fa ko? Wallahy gani nake kamar wasu Aljanu ne suka shafe sa Hajiya Nasmah...ki duba wai lokaci ɗaya ya ce ya katse duk wata alaƙar sa da Alhaji Galadima da kuma Alhaji Ridwan...."

"Ba komai Hajiya Salamatu, Allah yasa mu dace, Allah ya baki haƙuri."

"Amin amin, na gode sosai."

"Ba komai sai an jima..."

Tana tsinke kiran ta kalli Alhaji Galadima dake zaune da wani littafi a hannun sa ta ce.

"Hajiya Salamatu ce, wai Gimba Aure zai ƙara sai tujara yake mata. Daman kuma ku ne ke ɗan tsawatar masa kuna faɗa masa gaskiya, to kuma yanzu yace ya yanke alaƙa da ku...."

Murmushi ne ya suɓuce wa Abbah yana girgiza kai ya ce.

"Ba komai, Allah ya kyauta ya basu zaman lafiya. Tashi ki ƙara dubomin Anaam na san yanzu ta isa farkawa."

Ɗan kwalin ta ta ɗauka ta ɗaura sannan ta feffesa turare ya nufi ƙofa tana faɗin.

"Kasan fa kwana ta yi zaune tana kuka da wuya yanzu idan ta isa farkawa."

A hanya suka ci karo da Na'ima ta kalle ta ta ce.

"Na'imatu..."

Ɗan rusunawa ta yi kaɗan tana murmushi ta ce.

"Na'am Ammie....ina kwana?"

"Lafiya lau, ya gajiya Na'ima? Ina Anaam ɗin?"

"Lafiya lau Ammie ba wata gajiya, Anaam na can na baro ta..."

"Ai na zo ɗazu na tarar kuna bacci a zazzaune..."

"Wallahy fa. Nima bacci ne ya sace ni, koda na farka sai na ganta itama ta ɗan gincira, shi ne na lallaɓa na shiga toilet tana jin motsina na san ta farka, nayi nayi ta ci wani abu tace min a'a, kin san halinta..."

Jinjina kai Ammie ta yi tace.

"Okay...bari na lallaɓota ko Allah zai sa ta fito...zama a ɗakin ma ita kaɗai wani abu ne wanda zai iya saka ta tunani negatively..."

"To Ammie...bara na gaishe da Abbah."

A dining area ta tarar da Nene ta kambala komai fitowarsu kawai take jira. Tana ganin Hajiya Nasmah ta ƙara ɗan rusunawa alamar girmamawa ta ce.

"Hajiya sannu da fitowa..."

"Sannu da aiki Nene...yau gidan ya yi shiru an barku ku kaɗai..."

"To ya za'a yi! Allah dai ya bamu ikon cinye jarabawar da duk ta zo gabanmu yasa mu cika da kyau da imani."

"Amin Nene...Ahm kina ji na? Yau ma please the house should be quite....kada a bar kowa ya shigo please...idan kuma ya zama dole to kowaye ya jira a waje sai a sanar da ni..."

Jinjina kai Nene ta yi tana faɗin.

"Okay...in sha Allah."

******

Anaam kuwa, tana ganin fitar Na'ima ta mayar da kanta ta kwantar jikin gefen gadon ta lumshe idanun ta a hankali ta ji komai ya shiga dawo mata kamar yanda ta saba ji.

Daren ranar, abin da ya faru tsakaninta da Jak, da kuma labarin da Rabi'a ta ba ta sun kasa fita daga ƙwaƙwalwarta. Gabaɗaya ta ji duniyar ma ta ishe ta, ina ma ace mutuwa ta yi da ta huta da wannan baƙin cikin da abin kunyar.

A rufe idonta suke amma kuma kuka take, tun tana yi a hankali har ta fara da ƙarfi tana wani irin girgiza kanta wanda daga ƙarshe ta miƙe ta janyo towel ta ɗaura ta shige toilet ta sakarwa kanta shower tare da saka sponge tana wani irin darza jikinta da ƙarfi tamkar za ta saɓule fatar jikin nata tsabar yanda take ji.

Jikinta da Jak ya taɓa ji idan abun ya zo mata ji take da tana da iko da ta canja fatar jikinta gabaɗaya, domin ba ta san shi ɗin kowane irin mutum ba ne. Ba ta san daga ina ya fito ba, musulmi ne ko arne ba ta sani ba.

Towel ta sake janyowa ta ɗaura taje jikin mirror ta tsaya tana mai ɗaga hannayenta ta kalla sai kuma ta dawo shafa jikinta da fuskar ta still tana kallon mirrorn tana wani irin kuka mai ban tausayi.

Babu abin da take ji da hangowa a fuskar ta fa ce wai Ita ɗin yanzu fa kowa ya gama sanin abin da ya faru da ita. Colleague ɗinta a school both islamiyya and boko, mutanen anguwa, mutanen gari dama duniya baki ɗaya, everyone knows what happened to her....

Wani irin duka ta kaiwa Mirror ɗin a karon farko wanda duk ƙarfinsa sai da ya tarwatse, sannan ta sake bugawa a karo na biyu, sai kuma ta buga kanta sai ga shi tayo baya tana tangaɗi tana neman zubewa.

Ƙarar fashewar Mirror ɗin ya yi daidai da shigowar Ammien ta ta cikin ɗakin wanda a gigice ta ƙara so cikin ɗakin ta buɗe toilet ɗin ta shiga.

A yanda ta ga gaɓoɓin hannayenta da kuma fuskar ta yanda Jini ya ɓata ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba.

Da gudu ta je ta rungumota jikinta a gigice tana faɗin.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Haba Anaam dan Allah! Miye ya yi zafi haka?..."

Daƙyar ta iya buɗe idonta tsabar azaba ta kalli Ammien ta ta da wasu irin hawaye masu matuƙar zafi da ɗaci ta ce.

"Ammie rayuwa ta ta zo ƙarshe....my life has become miserable and useless...i can't show my face to world Ammie...idan na fita kowa zai riƙa kallo na ana nuna ni...duniya ta gama jin abin da ya faru dani to miye ya rage mini Ammie??"

Wani irin ƙanƙameta Ammien ta yi ta fashe da wani irin kuka tana girgiza kai tana faɗin.

" Noo....Anaam! This is not the end of the world...please nock senses in to your brain. No need for you ki riƙa wannan abun, sam bai kamata ba. Rayuwar nan fa gabaɗayanta jarabawa ce sai mun jajirce zamu iya zama masu nasara a cikin ta..."

Girgiza kai ta fara a hankali tana mai lumshe idanu tana kallon fuskar mahaifiyar ta ta murya a ƙasa sosai tana faɗin.

" I fail Ammie.....I couldn't make it any more...Ina fata watarana za ku yafe mini...Ab...Abbanah..."

Ganin yanda numfashinta ya tsaya lokaci ɗaya ta ƙarasa zubewa a jikinta yasa Ammie buga wata irin gigitacciyar ƙara ta shiga jijjigata tana ambatar sunanta.

Shima Abbah a gigice suka faɗo Toilet ɗin tare da Na'imatu kowa na rige-rigen ƙarasowa inda suke.

"Lafiya Hajiya Nasmah? Miye ya kawo wannan jini haka a jikinta? Waye ya yi mata haka?"

Ganin tayi shiru bata amsa ba sai wani irin uban kuka da take risgawa yasa Abbah ya kalli Na'imatu a ruɗe ya ce.

"Na'imatu please je ki faɗawa Anasi cewa ya kawo mota da saur...."

Girgiza kai Ammie ta yi tare da runtse idanun ta sosai ta katse shi da faɗin.

"Alhaji sai dai fa haƙuri!!! Domin Anaam ta riga ta amsa kiran mahaliccinta...."

✍️ OUM-AMEER ✍️