DUHUN DARE

PAGE 14

by @oumameer2671

U H U N D A R E*

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

PAGE 14

***

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Gidan Alhaji Gimba.

  Yau kwana biyar cif da kawo masa amaryarsa Maimuna wacce bai haɗa ta da kowa ba. Hajiya Salamatu babu yanda ba ta yi da shi ba akan ya kai ta gidan ta daban amma ya ce shi sam ba zai iya raba kan matansa ba,wuri ɗaya yake so su zauna, idan kuma ba za ta iya zama ba za ta iya tafiya. Wannan kalmar da yake yawan faɗa mata a yanzu na cewa idan taga ba za ta iya ba za ta iya tafiya ba ƙaramin ciwo take yi mata ba a zuciya,sam wani lokacin idan rigimarsa ta motsa abun da yake a yanzu yana matuƙar ba ta mamaki. Yanzu ba Hajiya Nasmah kaɗai ya hana ta alaƙa da ita ba har matar Alhaji Ridwan Hajiya Farida yace ya raba su da ita baya son ta ƙara mu'amala da ita.

Hatta danginta sai da ya yi faɗa musu tamkar wani mai motsin ƙwaƙwalwa.

Tun da ya yi auren ita ce wacce ke dafa musu abinci kamar yanda ya sharɗanta mata, domin tasan cewa baya cin abincin masu aiki sai na ta, hakan yasa ya ce ko yanzu ita ce za ta riƙa girka musu abinci har sai girki ya dawo hannun Maimunar tukun sannan za su riƙa canja wa.

Yau ma da wuri ta kambala haɗa abincin breakfast domin tun daren jiya ya sanar mata cewa ta tashi da wuri ta haɗa musu abincin kari domin suna da fita unguwa.

Mai aikinta na kambala shirya table ɗin suka fito hannun su maƙale cikin na juna suka zauna. Mai aikin na cikin serving na su Faris ya fito shima a gaggauce cikin shirin sa na fita Office ya zauna yana mai kallon Daddyn nasa ya ce.

"Daddy good morning?"

Kallon sa kurum ya yi sannan ya waiga ya kalli Maimunar yanda take wani yatsine fuska ya ce.

"Faris ita Maimunar ba za ka gaishe ta ba ne?"

Banza ya yi masa tamkar bai ji abinda yace ba ya wani haɗe girar sama da ƙasa yana mai ci gaba da haɗa Tea ɗinsa.

Taɓe baki ta yi sannan ta wani Hararesa ta ce.

"Ni daman bana maraba da gaisuwarsa domin ni sam ban ma ga dacewar zuwa ya zauna gani ga shi a kusa da kusa ba, domin shi ɗin dai ba muharram ɗina ba ne, kuma kamar a bisa ƙa'ida ya wuce shigowa cikin gida."

Within seconds ya ɗago ya ƙare mata kallo wanda shi ne karo na farko tun kawo ta gidan sannan ya mayar da kansa daga baya ya ci gaba da abin da yake.

Ajiye cup ɗin hannun sa ya yi yana mai jinjina kai alamar ya gamsu da zancenta ya ce.

" Eh kuma fa. Gaskiya zancen ki akwai gaskiya a ciki Maimunice, domin shaiɗan tsab zai iya haɗa tsakaninku....kai! Faris..."

Tamkar ba shi da yake maganar ba haka ya yi masa domin ko kaɗan bai nuna alamar cewa ya ji zancen da Daddyn nasa yake ba. Ransa ya kai ƙololuwa wurin ɓaci kawai dai yana danne zuciyar sa don cika umarnin mahaifiyarsa.

Ganin ya yi masa banza yasa Alhaji Gimba rai a ɓace ya ɗaga murya yana ƙwala kiran Hajiya Salamatu.

Cike da mamaki ta fito tana faɗin.

"Alhaji lafiya?"

Wata irin zabura ya yi ya miƙe tsaye yana ta wani tada jijiyar wuya yana bala'i yace.

"Ina fa lafiya tun da ɗanki bai da mutunci...."

"Ɗa na? Ɗa na ko dai ɗanmu?"

"Ah to, tun da ya nuna ba shi da tarbiyya ba shi da bin na gaba da shi ai dole na kira shi da ɗan ki..."

Jinjina kai ta yi tare da sakin wani guntun murmushi mai ciwo ta ce.

"To na ji! Ɗa na ne na ɗauka miye ya faru?"

"Miye ma bai faru ba! Ya zo ya zauna ƙaton banza da shi yaƙi ya yi aure, ni na yi aure ne yana neman ya hana mana zaman lafiya ya hanawa Maimunice sakewa ita da gidan auren ta. To wallahy tallahy ba zai yiyu ba..."

A hankali ta saukar da idanun ta akan Faris ɗin wanda har yanzu yake zaune hankalin sa kwance yana auna Wainar ƙwai da soyayyen Irish a bakinsa ta ce.

" Faris miye abin da yake faruwa?"

Tissue paper ya ɗauka ya goge bakinsa tas sannan ya miƙe ya ɗauki briefcase ɗinsa ya kalle ta a hankali ya ce.

"Ki tambayi mijin ki ga shi nan tsaye a gabanki."

Daga haka ya kama hanyarsa ya fice daga gidan baki ɗaya. Wani irin kama haɓa Maimuna ta yi tana jinjina kai ta ce.

"Cabɗi jam! Yanzu Alhaji daman ashe duk daɗin bakin da kake mini ashe baka isa da gidanka ba?"

"In ji ubanwaye ya faɗa miki haka?"

"Ga shi kuwa na gani a fili. Ɗan ka ma ka kasa iko da shi ina ga matar gidan..."

Cike da ɓacin rai ya shiga gyara hannun babbar rigarsa wacce tasha karin guga sai walwali take yana ci gaba da bambanmi ya kalli Hajiya Salamatu ya ce.

"Yanzu kuwa zan nuna miki na isa da gidana Maimuna...Hajiya Salamatu ina so ki ji da kyau, daga yau kada Faris ya ƙara shigowa cikin gidan nan wannan shi ne hukunci na. Don ba zan yarda ƙato da shi ya riƙa shigowa cikin gidan nan a duk sanda yaso ba  alhali ga iyalina a ciki tana son ta wataya, akwai ɗakuna birjik a waje ko kuma ya koma wannan mansion ɗin na baya, idan kuma ya gaji da gantalin ya samo mata shike nan kowa ya huta."

Cike da mamaki ta kalle shi ta ce.

" Faris ɗin ne zai daina shiga ɗakin sa saboda Maimuna?"

" Eh, haka na ce..."

"To ta tsaya ɓangarenta mana, ai ba dole sai ta fito nan ba, komai take so tana da shi a ciki..."

Ƙugu Maimunar ta kama tana wani ɗaga haɓa ta ce.

"Cab! Ai wallahy ni da gidan mijina babu wanda ya isa ya hana ni zama a duk inda na so, wallahy ba'a isa ba..."

Ganin hakan yasa ya ƙara matsowa gaban Hajiya Salamatun ya wani kafe ta da ido yace.

"Salamatu! Shin nan ɗin gidan waye?"

Amsa ta bashi da cewa.

"Gidan ka ne Alhaji Gimba..."

"To daga yau wannan ita ce doka ta, kuma billahilazy idan yace zai karya wannan dokar to daga ke har shi sai ran ku ya yi masifar ɓaci..."

Juyawa ta yi ta koma ciki akan tsabar baƙin ciki ba ta ko tsaya sauraren ƙarshen maganar tasa ba ta wuce ciki tana mai fashewa da kukan baƙin ciki.

Wayar ta ta ɗauko tashi ga kiran Faris amma har ta yi ringing kusan sau uku bai ɗaga ba. Hakan yasa ta ajiye wayar ta koma bakin gado ta zauna taci gaba da kuka.

******

Gidan Alhaji Mas'ood.

Da dare bayan sun dawo sallar isha ne Mubarak yasa aka tara masa rankatakaf ma'aikatan gidan domin sanar da su halin da ake ciki.

Tun da ya fara musu bayani gabaɗaya hankalinsu ya tashi musamman Junayd da yake jin tamkar zai sako fitsari tsabar kiɗimewa.

Babu tunanin da yake a ransa sai na yanzu da aka dakatar da shi ta ina zai fara kenan? Wannan gidan Allah ne gatansa shi ne gatansa yanzu kuma da aka sallame su ya yi ina kenan?

"Junayd na ga gabaɗaya hankalinka baya tare da ni...haƙuri za ku yi, daman haka zama ya gada. Shiyasa a rayuwa yafi cancanta mu zauna da kowa lafiya, mu riƙe amana sannan mu yi ƙoƙarin zama mutanen kirki. Allah yasa mu dace. In Sha Allahu yanzu cikin daren nan zan turowa kowa kuɗinda mai gida yace a baku, but Adam da Yunus za su gaba da zama a matsayin security ɗin su su ci gaba da tsare gidan in sha Allah."

Jiki a sanyaye Adam ya buɗe baki ya ce.

" Mun gode mai gida Mubarak, Allah ya ci gaba da tsare ku a inda kuke. Allah ya bawa Anaam lafiya yasa hakan shi ne mafi alheri."

"Amin ya Allah Adam. Mun gode sosai da wannan kyakkyawar addu'ar, kai ma ina maka fatan hakan."

Daga nan kowa ya hau yi musu godiya da addu'a musamman da suka ji irin kuɗinda za a ba su domin su samu su ja jari da su.

Bayan Mubarak ɗin ya koma ciki ne Alhajin na su ya kalle shi ya ce.

" Mubarak akwai wanda ba shi da gidan kan shi daga cikin ma'aikatan nan da samu sallama?"

Jinjina kai Mubarak ya yi yana mai kallon Abban na su ya ce.

"cikin su mutum huɗu ne basu da gida wanda shi ma kasan dalilin filin da aka siya ne kace ya yi daji da yawa a dawo gari a saye, to tun a lokacin ne kuma bamu ƙara maganar ko da Yaa Muhammad ba."

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Haka ne, to yanzu cikin daren nan a shirya yanda za'a samar musu gida, kodai a siya ko kuma a gina musu, kada ka bari a bar su haka dan Allah..."

"In Sha Allahu za'a yi musu abin da ya dace."

Ɗakin Ammie kuwa, zaune suke suna ci gaba da haɗa tarkacen abin da suke so tsakanin Ammie, Na'imatu da kuma Sa'adah ɗiyar Mama Hanne da ta zo.

A hankali suke tattauna fira wanda sai san ba'a rasa ba suke ganin murmushin Anaam wacce ke can ƙarshen Gado riƙe da kofin Tea a hannun ta tana sha.

Ganin ba ta da niyyar cewa komai ba yasa Na'imatu ta kalle ta ta ce.

"Madam are you happy? Ina nufin...kema kina ɗoki da jin tafiyar nan da zamu yi a ranki kamar ni kuwa? Ni dai I'm so excited..."

Jinjina kai ta yi fuskar nan ba yabo ba fallasa ta kalli Ammie sai kuma ta kalle su ita da Sa'adah ta ce.

"Bana ce ba Yaa Na'ima. Ya danganta da yanda can ɗin ya karɓe ni..."

Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.

"to Allah yasa hakan ya kasance alheri amin."

Kallon Ammie Sa'adah ta yi ta ce.

"Ammie gidan shiru, kamar ba tashi zaku yi gobe ba, na yi mamaki, domin gidan nan ya saba cika da jama'a idan wani dalili ya taso ko bikin sallah ko juma'a ko neman wani taimako  amma ace yau shiru."

Jinjina kai Ammien ta yi ta ce.

"Babu wanda yasan da wannan tashin da zamu yi Sa'adah, ko dangi ba kowa aka sanarwa ba, domin yanzu al'amarin duniyar sai addu'a."

"Wallahy haka ne fa Ammie, Allah ya ci gaba da tsare ku a duk inda kuke."

"Amin Sa'adah..."

"To amma dai za ku dawo aurena??"

Kusan a tare Na'ima da Anaam suka zubo ido suka kalle ta. Daman ko a school ba ta da wani zance sai na aure yanzu kam tun da aka saka date babu sauran wani zaman lafiya wanda idan ba auren aka yi ba to ba za ta taɓa bari su shaƙi iska mai daɗi ba.

Wani frame ne mai zanen red heart a ciki an rubuta Anaam wanda wata ƙawarta Zainab ce ta aiko mata da shi Na'ima ta ɗago ta nuna mata ta ce.

"Kina da buƙatar wannan?"

Kallo ɗaya ta yi wa frame ɗin sai kuma ta kauda idonta a hankali ta girgiza kai alamar a'a.

Sam ba ta buƙatar wani abu da zai tuna mata da rayuwar da tayi a baya, hakan yana sa ta jin wani iri a ranta.

Haka suka kwana suna fira har gari ya waye, bayan sun yi sallah suka yi wanka suka shirya suka fito sai Abuja.

*******

Maheer.

A gaggauce Maami ta ɗauko abincin da su Abdallah suka kawo ta nufi ɗakin da yake kwance ana jinyar sa.

Tana shiga ta tsaya turus ganin ba Maheer ɗin ba alamar sa. Ga drip ɗinda aka saka masa nan ya cire ya yi hanging meaning cewa da gaske ya bar asibitin.

Daman tasan za'a rina, domin tun safe taga take-taken sa na son ya samfe kamar yanda ya saba.

Ya tsani asibiti a rayuwarsa, Sam baya ma son ganin ta ko son jin yaji an ambace ta, tun da ya rasa mahaifinsa shikenan ya ɗauki tsanar duniya ya ɗorawa asibiti.

Wayarta ta ɗauko ta kira shi sai gashi nan take ya ɗauka ya ce.

"Maami kada ki damu na ji sauƙi. Yanxu haka ina wurin aiki har na saki boat biyar. Thank you so much."

Murmushi tayi tamkar yana a gaban ta tace.

"To abinci fa?"

"A gidan su Naana (cewa da grandma ɗinsa mahaifiyar Maamin tasa) na yi wanka na ci abinci daga can na wuto nan ɗin.

" OK to..Allah ya taimaka ya ƙara maka lafiya mai amfani."

"Amin Maami na, na gode."

        ✍️  OUM-AMEER ✍️