DUHUN DARE

PAGE 23

by @oumameer2671

D U H U N  D A R E

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

PAGE 23

Duk bayanin da take kora musu yana tsaye jikin ƙofar parlourn tun ɗazu yana saurare. Ya rasa dalilin da yasa yake jin a ransa ya cewa ya tsani duk wanda ke neman ya ɓata mata rai. And imagine ace wai iyayenta da kan su amma ba za su iya bata farin cikin da take so ba. Hakan yasa kenan Alhaji Mas'ood ba kawai mutanen waje ba. Hatta iyalansa baya iya basu farin cikin da ya dace da su.

Ganin yanda take ta kuka sai ya ji ransa ya sosu sosai. Hakan yasa ya yi hanyar kitchen ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa da glass cup ya zo kai tsaye ya tsaya a gefen kujerar da take zaune ya tsiyaya ya miƙa mata.

Lokaci ɗaya Yaa Nameer ɗin da Aunty Dina suka ɗago kai suka kalle shi kamar yanda Anaam ɗin ta yi.

"I just wanted to help..."

Ya ambata ba tare da ya janye hannun sa daga miƙa mata ruwan ba.

Jinjina kai Aunty Dina ta yi tace.

"Kada ki damu Anaam, he's my brother...."

Anaam na jin hakan sai ta karɓi ruwan ta kurɓa sau biyu sai ta ajiye a ƙasa.

Cikin sigar lallashi Nameer ya ce.

"Ki yi haƙuri Anaam, idan su Gwaggo (cewa da Ammie) suka gano cewa bakya cikin gidan kuma basu san inda kika je ba, za su shiga tashin hankali..."

Girgiza kai ta yi still da ruwan hawaye a idanunta ta ce.

"Ya Nameer ni fa ba zan koma gidan ba, and idan ka ce zaka sanar musu wallhy zan gudu daga nan...."

"Please allow her to stay, and don't tell her parent Kamar Yanda ta roƙeka..."

"But Maheer za su shiga damuwa, and idan suka gano cewa tana gidan nan daga daga miye za su ɗauke ni?"

"Farin cikin ta da kwanciyar hankalinta is the top priority Oga Nameer....and idan har hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa komai mai sauƙi ne. Basa so hankalin su ya tashi suka kawo mutanen da ba ta so a gidan?..."

Agogon hannunsa ya kalla sannan ya sake kallon su yana jinjina kansa ya ce.

" Getting to 12am now...please ku barta ta huta tukun."

Miƙewa Dina tayi ta ja hannun Anaam ɗin ba tare da kowa ya sake cewa komai ba suka haura sama ta buɗe mata wani ɗaki suka shiga. Komai a tsabtace yake gwanin sha'awa, wardrobe dake gefe ta buɗe ta ɗauko bedsheet ta shimfiɗa akan gadon sannan ta fita ta ɗauko mata sababbin sleeping dress ta bata ta ce idan tana so ta shiga ta yi wanka.

Toilet ɗin ta shige ta yo alwala ta fito ta gabatar da sallar Isha sannan ta sauya kayan jikinta ta haura gadon ta kwanta ta yi lamo tana nazarin kalaman Maheer. Ta ya za'a yi ace mutumin da ya ga hawayenta lokaci guda ya iya fahimtar damuwar ta amma ace su Abbah su kasa hakan?

Tabbas da ace sun damu da farin cikin ta da basu kawo Faris da Rabi'a ba a cikin gidan nan ba. Ita yaushe tace musu tana da buƙatar wata wacce za ta ɗebe mata kewar Na'ima?

Ta jima a gadon idan ta juya nan ta juya nan abin duniya duk ya ishe ta. Ta ɗauka cewa dawowa nan ɗin da suka yi zai sa ta manta da bayan ta sannan ta gina sabuwar rayuwa, but ta ya ya za'a ce su Ammie su ne suke gayyota mata sabuwar matsalar har cikin gida? Komai sai su ce haƙuri haƙuri, but a rayuwar nan akwai gaɓar da idan kace za ka yi haƙuri to tabbas shi ne zai yi ajalinka.

Maheer kuwa, ya jima a rumfar shan iskan gidan yana ta nazari da al'ajabin wannan al'amari. Ko a mafarki aka ce mi shi zai ganta gidan mutanen da ya sani tabbas zai Ƙaryata. But sai gashi unfortunately ba zato ba tsammani ya tsince ta tsaye a gaban shi, sai dai a yanayin da ya same ta ya yi matuƙar baƙanta masa zuciya.

Why is she in pain always? Last ganin da ya yi mata bata cikin yanayi mai daɗi and again yau ma ga shi cikin yanayin damuwa da ƙunci ya risketa. Idan har zai so mutuwar sa to zai ƙaunaci ganin kukanta. Har cikin ƙahon zuciyar sa yake jin kukanta idan tana yin sa wanda hakan ya samo asali ne tun a daren da suka shiga gidan su. Idan tana kuka yana jin sa har cikin kansa. A irin wannan yanayin da take ciki taya ya zai iya confronting ɗin ta da wani zancen neman yafiya? Hakan ba zai faru ba a yanxu, but tun da har Allah yasa a nan take,he will wait for the right time ɗinda ya kamata ya yi magana da ita. But a yanzu kam tana buƙatar space.

********

Hajiya Nasmah ce tsaye a jikin wardrobe ɗin Alhaji Galadima tana jera masa kayan wankin sa da aka kambala wankewa da gogewa.

Sai da ta kambala gyara su tsab sannan ta rufe ta waigo ta kalli inda yake zaune a gefen gadonsa yana duba waya da 'ƴar damuwa ta ce.

"Alhaji kana ganin zaman Faris a gidan nan ba zai ƙara janyo wata wutar matsalar ba tsakanin ka da Alhaji Gimba? Ka fa san halin sa sarai ƙaramin abu sai ya mayar da shi babba. Gabaɗaya hankali na ya kasa kwanciya..."

Ajiye wayar ya yi a gefe ya kalle ta na ɗan lokaci sannan ya jinjina kai ya ce.

" To ai naga Faris ba yaro ba ne. Don ya zo gidan nan ya zauna bai zama wani laifi ba..."

"Duk da haka Alhaji...sau nawa kana yi wa iyalinsa abun arziki amma daga baya ya dawo ya na ganin laifin ka?"

"Na kira Ridwan duk da cewa baya ƙasar mun tattauna, shi ma yace na bar sa ya zauna a nan ɗin tunda ya nema, kada kuma ya wuce inda za'a dawo daga baya ana dana sani..."

Cikin rashin ga suwa da bayanin sa ta girgiza kai ta ce.

"Ni dai duk da haka ina gudun abin da zai je ya dawo..."

A hankali wayar ta ta shiga ɓurarin neman agaji sanadiyyar kiranta da akayi.

Hannu ta miƙa ta ɗauko wayar daga kan ƙaramin glass table dake gefe ta amsa kiran tare da ɗora ta a gefen kunnen ta ta ce.

" Nene lafiya kuwa?"

Hankalin Nenen a tashe daga can ɓangaren ta ce.

"Hajiya ba lafiya! Maryam ba ta dawo gidan nan ba. Na ɗauka tana gidan Amina,amma na kira tace ta dawo, kuma na binciki Anas ya ce ya dawo da ita gidan nan shi bai san inda ta je ba..."

A ruɗe Ammie ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye kike cewa Nene? Anaam ɗin ce ba'a san a ina take ba?"

Kashe wayar ta yi ta ci gaba da kallon Alhajin wanda shi ma lokaci ɗaya ya zabura ya miƙe yana faɗin.

"Tun ɗazu fa nace miki ina neman ta kika ce ta je raka matar Madu..."

"Wallahy Alhaji ni dai na san su Amina taje rakawa gida..."

Bai tanka ta ba har suka fito harabar gidan inda suka tarar da su Nene har da Rabi'a sun tsatstsaya cirko-cirko suna jimami.

Wani kallon Alhaji Mas'ood ya jefawa Anasi ya ce.

"Anas Ina Maryam?"

Hankalinsa a kwance ya ce.

"Alhaji ni ne wanda na kai su gidan Yallaɓai Madu, bayan mun ajiye su kuma muka dawo sai naga sun bar kayansu a motar shi ne naje na kai musu amma ni ban san inda take ba."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mun shiga ukunmu shi ke nan an sace Anaam tana can tana ganin wahala..."

Cewar Rabi'a tana mai ɗora hannu a kai ta rusa ihu kamar da gaske.

Wata uwar tsawar tsawar ce Abbah ya doka mata domin kalaman ta ba ƙaramin ƙara ɓata masa rai suka yi ba ya ce.

"Ke wace irin shashasha ce? Waye ya faɗa miki cewa sace ta akayi?"

"Mahaukaciya ce ai! Wawiya kawai! Fatan sharrin da fatan a sace ta kike ko? To sharrin da kike kira mata a kan ki zai ƙare..."

Da sauri Ammie ta riƙo hannun Mukarram ɗin ganin yanda ya wani yi kan Rabi'ar yana shirin kai mata duka ta ce.

"Mukarram please ka saurara mana dan Allah!"

Wayar shi ya ciro ya koma gefe yana ta kiran waya wanda gabaɗayansu ba su san ko da waye yake yin waya ba.

Su ma dai a nan suka ci gaba da kiran wayar su Amina da sauran dangin su dake nan Abujar amma ko'ina suka kira sai ace ba ta je ba har gidan Nameer wanda ƙiri-ƙiri ya ce bata gidan amma ba don ransa ya so ba.

Ganin yanda Hajiya Nasmah ke ta rusa uban kuka yasa Alhaji Mas'ood ya tako ya matso inda take tsaye a sanyaye ya ce.

"In Sha Allahu a duk inda take tana cikin amincin Ubangiji..."

"Amma Alhaji ina Anaam za ta tafi cikin daren nan? Kana ganin lafiya ƙalau za'a neme ta a rasa haka kawai?"

Ganin suka yi Mukarram ya je da kanshi ya buɗe gate sai ga jami'an tsaro sun shigo cikin gidan mota guda.

Gefen da Faris ke tsaye ana jajen dashi tun ɗazu ya nuna musu kai tsaye ya ce.

"Arrest him! Kuma kar ku saurara masa har sai ya faɗa muku inda ya kai ta..."

"Mukarram...miye haka? Miye haka na ce?....officer please wait..."

Cewar Alhaji Mas'ood yana mai nufar inda Faris ɗin yake, ganin da gaske neman suke su kama shi kamar yanda Mukarram ya umurce su.

Shi ma Mukarram ɗin matsawa ya yi yana faɗin.

"Alaji ka bar su su tafi da shi domin ko tantama babu shi ne wanda ya ɗauke ta. Tun da Anaam take ba taɓa tunanin barin gida ba, amma yana shigowa gidan nan gashi an neme ta an rasa..."

Girgiza kai Alhaji Mas'ood ya yi ya ce.

"Wannan ba hujja ba ce kace shi ne ya ɗauke ta..."

"Kada ka ce za ka yarda da wannan mai fuska biyun Alaji! Dole za'a kama shi kuma dole sai ya fito da ita."

Cike da zallar mamaki Faris ya kalli Mukarram wanda ke ta ɗaga jijiyoyin wuya yana bala'i ya ce.

"Kai ka tabbatar cewa ni ne na sace ta?"

Mukarram ɗin na yi masa wani kallo ya ce.

"I'm 100% sure! Kai ne ka sace ta saboda an hanaka ita a karo na biyu."

Wani murmushin gefen baki Faris ɗin ya yi sannan ya girgiza kansa yace.

"Daman kai kullum a ruɗe kake. Baka taɓa bari ayi abu cikin nutsuwa sai kasan yanda ka yi ka kawo rikicin..."

"Abin da za ka ce kenan? Na ce abin da za ka ce kenan? To bari na nuna maka ƙarshen ruɗewa..."

Mukarram ɗin ya faɗa yana mai kama kwalar rigar sa.

Rikici sosai ya ɓarke a tsakanin su inda jami'an tsaron da ya kira suka tattara suka wuce ofishin su da su.

Har gari ya waye babu mutum ɗaya da ya samu bacci a gidan, gabaɗaya hankalin kowa a tashe yake har su Muhammad dake can wurin hulɗar kasuwancin su, musamman wannan rikicin da Mukarram ya sake jangalo musu na ɗora laifin ɓatan Anaam akan Faris, tabbas idan Alhaji Gimba ya ji to ba lafiya kuma.

Gari na fara yin haske Alhaji Mas'ood ya shirya ya tafi wurin su Faris ɗin domin ya samu ya shawo kan matsalar kafin ta girmama. Sannan kuma ya saka binciken neman Anaam kamar yanda suka tsara da Hajiya Nasmah.

******

Gefen Anaam kuwa ta jima tana baccin wanda ta koma bayan ta kambala sallar Asuba, sai da kusan ƙarfe goma da rabi ta fito Sanye da kayan baccin da ta kwana da su daren jiya. Tana leƙowa suka yi ido biyu da Maheer wanda ke zaune a dinning area da abinci kari a gaban sa, sai Aunty Dina dake gefensa.

Saurin ɗauke kanta tayi kamar yanda shi ma ya yi bayan sun haɗa idon a ba za ta.

Murmushi Dina ta yi tana kallonta ta ce.

"Anaam...kin fito?"

Ƙarasowa ta yi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun ta ce.

"Uhm! Ina kwana Aunty Dina?"

"Lafiya lau Anaam...fuskar dai kam, yanayin ta ya nuna rashin bacci mai daɗi. Please ki kwantar da hankalin ki kinji ko, in sha Allahu komai zai yi daidai."

Tun da ta zauna bai sake ɗago ido ya kalle ta ba, but yana ganin ta haɗa Tea ta zuba ruwan da yake flask ta ɗaga cup ɗin zuwa bakinta ya yi saurin tura mata wanda yake gaban sa yace.

" Wannan yana da zafi sosai...zai iya ƙona miki bakin ki, but za ki iya shan wannan."

Lokaci ɗaya suka kalle shi ita da Aunty Dina. Ganin hakan yasa ya miƙe yana faɗin.

"Ni zan tafi. Na gode sosai."

Miƙewa Aunty Dina ɗin ta yi ta biyo shi tana faɗin.

"Driver yana jiran ka sai ya sauke ka a Airport ɗin."

"Na gode sosai, amma sai naje hotel ɗin da na sauka na ɗauki kayana daga nan sai na wuce."

Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.

"Ba damuwa Maheer,mun gode sosai da ziyara, Allah ya bar zumunci."

Har ya buɗe motar zai shiga sai kuma ya juyo ya kalleta ya ce.

"Aunty Dina...dan Allah ina neman wata alfarma."

"Faɗi kanka tsaye."

Ta faɗa tana mai jinjina masa kanta.

"Dan Allah kada ki ce wa yarinyar komai dangane da ni...ahm! Ina nufin kada ki bata labari na..."

Cikin rashin fahimta ta ce.

"Miyasa haka? Amma ai na faɗa mata cewa kai ɗin ƙanina ne."

"Eh, mu bar shi a haka."

"Mi yasa?"

"Ina jiran lokacin da ya dace ne."

Kafaɗa ta ɗaga alamar ba damuwa ta ce.

"Okay! Allah ya nuna mana da alheri."

"Amin. And again...dan Allah idan ba ta so ta koma gidansu kada ku takura ta..."

"Maheer ni ɗin fa kawai matar ɗan uwanta ce. Ban isa na shiga tsakanin hukuncin da suka yanke ba..."

Tamkar wanda zai fashe da kuka ya ƙara saukar da muryarsa ya ce.

"Za ki iya mana...ciwon mace fa akace na mace ne. Dan Allah ki yi min alƙawarin wannan Aunty Dina. Ba laifi ba ne idan kuka sanar da iyayenta cewa tana nan domin hankalin su ya kwanta, amma idan bata so ta koma don Allah ku barta ta yi zaman ta a nan ɗin...ki duba halin da ta shiga tun daren jiya, ko baccin kirki bata samu ta yi ba. Ya kamata ace an kula da ita yanda ya kamata..."

Shiru ta yi na ɗan lokaci tana digesting maganganun nasa tare da ƙura masa ido na tsawon lokaci, sannan daga ƙarshe ta jinjina masa kanta tana murmushi ta ce.

"Shi ke nan Maheer...in sha Allahu I will try my best."

"Na gode da fahimta. Sai an jima."

"Allah ya tsare yasa a sauka lafiya."

       ✍️  OUM-AMEER  ✍️