DUHUN DARE

PAGE 25

by @oumameer2671

D U H U N  D A R E

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

PAGE 25

Sai da ya kambala sauraren shawarwarin kowa sannan ya buɗe baki a hankali cikin rashin hayaniya kamar ko yaushe ya nisa ya ce.

"Duk na ji maganganun ku...musamman kai Madu da kace farin cikin ta yana gaba da komai. Yes! Farin cikin Maryam a gareni yana gaba da komai, and ku shaida ne ina yin duk abin da ya kamata domin naga ta samu farin cikin da take buƙata. Har baro garina na yi...garin da shi ne tushena shi ne asali na, amma haka na haƙura na baro don kawai ta samu farin ciki. Saboda haka a wannan gaɓar...ba zan kori Rabi'atu daga gidan nan ba wai don kawai ita bata son zamanta..."

"Amma Alaji..."

Saurin ɗaga masa hannu ya yi alamar ya dakata ya ce.

"Ya isa Mukarram! Kun gama naku, Saboda haka ya kamata ku saurare ni. Idan har nuna son kai shi ne ɗabi'arku da rashin ɗaukar zumunci da muhimmanci ni bana daga cikin ku. Alhaji Salisu da ni uwa ɗaya uba ɗaya muke idan kun manta in tuna muku, yaran sa da ku ni duk ɗaya kuke a wurina babu bambanci. Faris zai iya barin gidannan ko shi idan yaso amma ba don wai ni na kore sa ba, haka ma Rabi'atu matuƙar ba ita ta so tafiya ba har abada ba zan ce ta tafi ba. Da suke zaune a gidan ai ba a kanta suke ba. Yanda muke ƙoƙari muna gudun ɓacin ran ta ya kamata ace itama tana dubawa. Idan abubuwan da suke faruwa a rayuwarmu basa wucewa ai da an shiga uku. Saboda haka Rabi'atu ba za ta bar gidan nan ba saboda ita, idan ta gama ta dawo gidan, idan ta gama taci gaba da zamanta a gidan Nameer babu wanda zai hana ta..."

"Alhaji ya kamata fa a duba wannan lamarin..."

Cewar Hajiya Nasmah, domin sam ba ta yi tunanin irin wannan hukunci daga gare shi ba. Ko a lokacin da su Muhammad ɗin suka so ta dawo wurin su Alhajin ƙin amincewa ya yi, amma yau kai tsaye yake faɗa da bakin sa cewa a bar ta ta yi ta zama a gidan Nameer.

Ƙara kwantar da murya Mubarak ya yi ya ce.

"Alaji ni ma dai ban ga abin nan ya yi making sense ba. Don Allah..."

Hanya fitar parlourn ya nuna musu yana faɗin.

"Please za ku iya bani wuri, ina da buƙatar na huta please."

A hankali suka miƙe suka sulale ɗaya bayan ɗaya suka bar shi daga shi sai Hajiya. Itama tana buɗe bakinta ya ce ta bashi wuri baya son maganar kowa a halin yanzu.

******

Alhaji Gimba.

Gidan su dake Life Camp ya wuce da shi direct. Tun a harabar gidan da suka fito mota ya fara balbale shi da masifa tamkar zai kifa masa mari yana faɗin.

"Ni za ka kawo wa iskancin banza iskancin wofi! Gabaɗaya Ka gama zubar mini da mutunci na a gaban maƙiyana. Wace irin lalacewa ce ace ka rasa inda za ka je ka zauna sai gidan Mas'ood? Mas'ood da baya so na baya ƙauna ta..."

"Alaji ya kamata fa..."

"Wallahy tallahy idan baka rufa min baki ba sai in zabga maka tafi ka ji na faɗa maka ba! Uwar taka ma sai ta zo nan kafin na yanke hukuncin da naga ya cancanta. Shi ke nan ka baromin kasuwancina ka dawo gidan maƙiyi na ka zauna saboda kawai baka san ciwon kan ka ba ko? To wallahy tallahy ba zan yarda ba, kuma sai na ɗauki mataki ka ji na gaya maka..."

Hannu ya saka a aljihu ya ciro wayarsa da ake ta kira tun ɗazu wanda bai san ma daga ina kiran yake ba.

Har ya kai wayar kunnen sa bai san waye mai kiran nasa ba. Jin muryar Mace yasa ya bar gun Alhajin ya matsa can nesa da shi ya ce.

" Wa ke magana?"

Sautin murmushin ta ya jiyo daga can ɓangaren ta ce.

"Uhm! Rabi'atu ce ta gidan Abbah."

Cikin rashin fahimta ya ce.

"Wane Abbahn kenan?"

"Ta gidan Alhaji Mas'ood wacce na kawo maka breakfast ranar da safe. Daman na ce bari na kira na ji halin da kake ciki an ce an wanke ka baka da laifi a ɓatan Anaam. Allah yasa kana lafiya?"

Jinjina kansa ya yi tamkar yana a gaban ta ya ce.

"I'm fine....Thank you."

Daga haka ya katse kiran ya waiga ya kalli mahaifin nasa wanda shi ma ɗin shi yake kallo tun ɗazu.

"Waye ya kira ka?"

Wani kallon mamaki Faris ya yi masa ba tare da ya ce komai ba.

"Waye ya kira ka na ce?"

"A friend."

Abin da ya furta kenan sannan ya kama hanya ya shige gidan direct ya shige ɗakinsa.

Har ya shige ciki Alhaji Gimba bai daina kallon sa ba sannan daga ƙarshe ya yi ƙwafa ya fito da wayarsa ya kira Hajiya Salamatu baiwar Allah wacce hankalin ta ke can a tashe,tana ɗagawa ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba ya ce.

"Ki zo Abuja Salamatu domin ba lafiya...asirin ki ya tonu daga ke har ɗan na ki..."

Hankalinta a tashe ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Alhaji wannan wace iriyar magana ce haka?"

"Ba kin tura shi gidan maƙiyina ba don kawai kuga na tozarta? To wallahy ta Allah ba taku ba. Shi ne har da kukan munafurci kina faɗin baki san a ina yake ba, to wallahy sai na ɗauki mataki kin ji na faɗa miki."

Maimuna dake laɓe tun ɗazu bayan ta ji sun yanke wayar ne ta ciro wayar ta ta kira shi tamkar za ta fashe tsabar yanda take ciki tana batsewa. Yana ɗagawa ta ce.

" Alhaji yau ni ce na dawo banza a wurin ka?"

Cikin hargagi ya ce.

" Eh ɗin! Eh Maimuna tun da haka kika ce!....kinga...Dan Allah ni ki barni na ji da abin da ya dame ni dan Allah. Kin cika naci kin cika matsala. Da ki ka ga ban ɗauki kiran ki ba ai sai ki saurara ki ji. Mts!"

Tamkar wacce ta samu matsalar ƙwaƙwalwa haka ta zare wayar daga kunnenta jin cewa kamar ya katse kiran da gaske. Tana dubawa kuwa ta ga da gaske ya tsinke kiran, hakan yasa ta faɗa kan kujera ta fashe da wani irin mugun kuka tana faɗin.

" Na shiga ukuna ni Maimuna? Tun yanzu? Kwana ɗaya gabaɗaya? Yaushe ma aka yi daren balle dare ya waye? Wallahy ba zan yarda ba. Na rantse da Allah ba zan yarda ba.."

Daga haka ta miƙe ta zari mayafinta ta bar gidan.

******

Jiki a sanyaye Mubarak ya shigo ɗakin Hajiyar ta su yana mai samun wuri ya zauna akan kujera ya ce.

"Ammie Anaam taƙi ta saurare ni....infact taƙi ta saurari kowa har Yaa Muhammad. Wai ashe duk laifin kowa take gani Ammie? Fushi take da kowa. Kuma ya zamuyi tunda mai gida ya yanke hukunci mu miye namu a ciki?"

Cikin nuna rashin jin dadinta ta ce.

"Yaushe ta ce za ta dawo gidan Mubarak?"

Girgiza kai ya yi ya ce.

"Ta ce fa matuƙar Rabi za ta ci gaba da zama a gidan nan to ita ba za ta dawo ba."

"Oh ni Nasmah! Wannan wace irin rayuwa ce? Ga Alhaji Shi ma ya tsaurara, hatta gidan Nameer ɗin ya ƙi amincewa na je."

Miƙewa ya yi yana faɗin.

"To ai ko can ɗin da take zaune ba damuwa ba ne. A ƙyale ta taci gaba da zamanta har Allah ya kawo mana ƙarshen abin."

"Dole kam haka za'a yi Mubarak. Allan yasa mu dace amin."

Yana fita ta ciro wayar ta ta kira Dinaratu, bayan sun gaisa Hajiya Nasmah ta ce.

"Dinaratu Anaam ɗin fa?"

Kallon gefen da Anaam ke zaune ta yi wacce ke rungume da Ashnan tana bata abinci ta ce.

"She's here Ammie...Anaam. Ga Ammie..."

Ta ƙarashe maganar tana miƙawa Anaam ɗin wayar. Anaam kuwa, tana jin cewa wai Ammie ce sai ta sauke Ashnan ta miƙe kawai ta bar parlourn kai tsaye ta shige ɗaki.

A sanyaye Dinaratu ta ce.

"Ammie ki yi hak'uri...ta tashi ta bar wurin, haka ta yi wa Mubarak ɗazu da ya zo,but In sha Allahu a hankali za ta sauko kuma ai kun sani."

Cikin nuna rashin jin daɗi ta ce.

"Hmm! To shi ke nan Dina, na gode sosai. Ki gaishe da su Arif."

"Tau za su ji in sha Allahu. Sai da safe."

******

Tun da Hajiya Salamatu ta iso Alhaji Gimba bai sarara ba, cin mutunci sai abin da ya manta, tamkar wani mahaukaci haka ya dawo wanda hatta Faris a wannan karon sai da ya jikin sa ya yi sanyi.

Da kukanta da hawayenta ta hau rantse-rantse akan ita bata san cewa Faris na gidan alhaji Mas'ood ba amma firr yaƙi yarda ya ce Ƙarya take ta san komai.

Bayan kusan kwana biyu da shafe bai ƙara shiga sabgar su ba, sai da ya ji ransa ya ɗan ƙara sanyaya sannan ya kira su a parlour cike da rashin arziki ya kalle ta ya ce.

"Salamatu!"

"Na'am"

Ta amsa tana mai kallon inda yake tsaye.

"Salamatu idan har na isa dake a duniyar nan. Babu ke babu ƙara hulɗa da iyalin Mas'ood, ko ta Waya wannan ban amince ba. Yanzu dan Allah daɗin ki ne ace wai an laƙaba masa satar Maryam harda tozar ta shi su sa a rufe shi police station tsabar wulaƙanci?"

Girgixa kai ta yi ta ce.

" Wallhy Alhaji ni ma kam sun yi matuƙar bani mamaki da har suka iya sa a rufe Faris akan ɓatan Anaam..."

"To ai ke ake faɗawa Salamatu? Idan za ki yi hankali sai ki yi. Maƙiyinka har abada komai za ka yi masa Maƙiyinka ne domin har abada ba zai so ka ba....saboda haka dole zan ɗaukar masa mataki."

"To Alhaji. Allah ubangiji ya kyauta yasa kuma mu dace..."

Duk faɗan da suke Faris na gefe yana chart da Rabi'atu wacce ta nace da kiransa ba dare ba rana tare da turo masa messages wanda tun bai kawo komai a ransa ba har ya ɗan fara jin interest a kanta.

******

Tun da ya koma duk bayan kwana biyu haka sai ya kira Aunty Dina domin kawai su gaisa. Ko sau ɗaya bai taɓa attempting tambayar ta Anaam ɗin ba, tun da ya tafi duk kiran da yake mata maganar Anaam ɗin ba sake shiga tsakanin su ba sai yau da dawo gida misalin sha biyu saura na dare ya kira ta.

Cike da mamaki ta ɗauka ta ce.

"Allah yasa lafiya Maheer?"

Jinjina kai ya yi yana mai ƙara lowering voice ɗin Tvn da yake kallo ya ce.

"Lafiya ƙalau Aunty Dina...."

Daga haka sai kuma ya yi shiru,ya yin da ta nutsu sosai ita kuma tana jira ta ji mi zai ce.

"Ko zan iya magana da ita please?"

Cikin rashin fahimta ta ce.

"Wa ke nan?"

"Baƙuwar gidan ki. Ina so in ji ya ya take..."

"Ohh! Wai Maryam ka ke nufi?"

"Yeah!"

"Okay. Lemmi check on her Idan ba ta riga ta yi bacci ba."

Daman tana ɗakin Arifa da Ashnan ne ya kira ta. A hankali ta fito ɗakin ta zo bakin ɗakin Anaam ɗin ta tsaya, ta jima tsaye a bakin ƙofar tana tunanin yanda za ta yi convincing Anaam ɗin akan ta karɓi wayar domin tasan ƙaramin aikinta ne taƙi karɓar wayar. And shi kuma he's still on the phone bai yanke ba.

Bayan ta gama addu'ar Allah yasa bacci take ta tura ɗakin ta shiga, zaune ta cim mata da System ɗin Aunty Dinar a gaban tana kallon Film ta ce.

"You still awake?"

Murmushi ta yi tare da tsayar da film ɗin tana jinjina kan ta ta ce.

"Ina ɗan rage daren ne Aunty Dina..."

"Uhm"

Ta faɗa tana mai zaunawa a kusa da ita tana facing ɗin ta kai tsaye ta ce.

"Maheer yana so ya miki magana Anaam...hope ba a takura jindaɗin ki ba?"

Agogon system ɗinda ke gaban ta ta kalla taga dare ya yi ta ce.

"Aunty Dina yanzu?"

"Uhm! Yanzu ya kira, kin san yanayin aikinsa ba koda yaushe yake da time ba. Ga shi ma bai kashe ba..."

Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora wayar a gefen kunnenta.

Lumshe ido ta yi sannan ta buɗe a hankali ta ce.

"Halo..."

Jin bai amsa ba, yasa ta ɗan janye wayar kaɗan ta duba don ta tabbatar shin yana kan Layin ko kuma ya yanke kiran, but ga mamakin ta call ɗin nan har yanzu.

Sake mayarwa ta yi ta ce.

"Halo...."

Muryarsa ta ji a hankali yana faɗin.

"How are you?"

✍️ OUM-AMEER ✍️