1
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
* NA*
NANA BMB
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
YA ALLAH YADDA NAFARA BOOK DIN NAN A SA AH KASA NA GAMA SHI LAFIYA, KABANI IKON RUBUTA ALKHAIRI, KURA KUREN DAKE CIKI KUMA ALLAH KA KABANI IKON GYARA WA.
BANYI NOVEL DINA DON CIN ZARAFIN WANI BAH KO WATA, KIRKIRAR RAN LABARI NE NAYI NE DOMIN JAN HANKALIN MU MATA.
Idan kisan bazakiyi comment bah kada ki fara karanta min novel, saboda kada nayi removing naki kiji haushi don babu dadi, banyarda wani ya juya min book dina a yadda nayi shiba Allah ya baku ikon kiyaye wa,yadda nake kokari akan na faranta muku kuma ya kamata ku na karfafa min gwiwa yimuku typing kullum, Allah yasa zamu amfana da juna baki daya na gode. 🥰
Episode one
KANO
Prime College ga haduwa ga tsari gashi ta tara 'ya'yan wane da wane, karfe 4:00pm aka bude gate din makarantar dalibai suka soma fitowa mata da maza, wasu samari ne su biyu suke sauko wa daga steps fuskan su dauke da murmushi suna fira, na site din dama shine kawai yake magana aminin nashi sedai murmushi dayake tayi har beauty point dinsa yana lotsa wa hakan ke kara bayyana asalin amazing pretty face dinsa, he's handsome guy, and good looking, fari ne sosai har yana yellow kalan skin dinsa, gashi yadda yawa suman sa gyara yanayin sa ya bayyana kamar ba indiye, shi kuma aminin nashi ba fari bane chocolate ne masha Allah kyawu kam shima dole baze wuce sawun farko bah, asalin hausa fulani ne tubar kallah, wanda be sani bane ze iya cewa ga ba indiye ga dan sudan kuma, ( to bari dai kada na cika ku da surutu )koda suka fito daga bakin school din wasu luntsu ma luntsu man motoci ne guda uku ta tsakiyan itace har wani walwalin sheki take na daukar ido se bakaken motocin da suka sata a tsakiya bodyguards ne suka zagaye motan sunyi kikam a tsaye da bakaken kaya suna dan taba hira har suka karasa gurin motocin, daya daga cikin guards dinne ya bude farar motar farin saurayin ya shiga baya ya zauna yana kallon aminin nashi ganin baida niyar shigowa ne yasa shi cewa.
" Farid shigo mana mu tafi"
Murmushi yama sa gami da girgiza masa Kai yace." Ba tare zamu tafi ba Omar yau na hutashe kah baseka kaini gida ba kaga driver na yazo da wuri yau yana jirana" sunkuyar da kansa yayi yana murmushi sosai damuwa ta bayyana a face din sa na rashin binsa da aminin nashi zeyi, beji ba dadi, kada masa kai yayi gamida da cewa." Ok Allah ya tsare hanya" shima Farid smile din ya maida masa yace." A sauka lpy" ya matsa ya rufe masa motan, suka tafi yanata yi masa bye bye duk da baya ganin me Omar din ke masa saboda tinted, harseda suka bacewa ganin sa tukunna yaje ya shiga nashi motan suka tafi yanata smile abinsa sosai yakejin aminin nashi har jinin jiki,
Yana zaune ya kwantar da kansa kan kujeran motan, idanun sa a lumshe suke wakar Maher Zain ce kawai take tashi cikin motan me taken. { Number one for me } koda suka isa dankare ren gidan nasu dake GRA yana a haka Horn din da sukayi ne guards din yasashi bude idanun sa gami da mikewa zaune don yasan sun iso gida, wangame men gate din aka bude musu suka kunna kai ciki, kai tsaye parking space suka nufa sukayi parking cikin azama suka zo suka bude masa kofar motan nashi ya fito slowly kamar wanda baya son taka kasa sunyi masa kikam a tsaye suna kallon sa harya isa kofan daze sadashi da cikin gidan ya danna security din kofan ya shiga cikin main parlour din tsarar re dashi yasha kayan alatu, kai tsaye ya nufi siririyan hanyar daze sada shi da stairs din daze hau, yana tafe kamar bayaso harya gama haura wa saman daga bakin kofan yay knocking daga cikin dakin ne aka bashi damar shiga, da sallamar sa ya murda handle din ya shiga, wata beautiful din matace ta amsa masa sallamar fuskan ta dauke da kaya taccen murmushi tana zaune kan daya daga cikin kujerun parlour din kallo daya zaka mata kaga tsatsan kamar da takeyi da Omar, shima face din sa dauke da murmushin ya karasa kusa da ita ya zauna, cikin farin ciki ta shafi gefen fuskan nasa tana cewa.
" My son se yanzu ka dawo?"
Dan ya mutse fuska yay yace." Lesson din nan yake ja mana time haka kullum a gajiya nake dawowa gida yanzu"
" Ayya sorry my sweetheart kaga kun kusa kare karatun kune dole ku dage da karatu" kafadun sa tadan soma mamma tsa masa tana cewa." Sorry kajee my son kaje kayi wanka kaci abinci ka huta kuma abinka" ayan da takeyi maganar ne tamkar irin taba rarrun 'yan yayen nan 😀 hakan ne yasa shi shima tura nashi bakin gaba yace.
" Haba Ammi wai har se a yaushe zaki dena abun yara ne? Saboda halin nan naki duka wani occasion da muke hallarta ake raina ni, maza suyi ta binki haba Ammi, keba yarinya ba kuma kiyita bani kunya idan nace mahaifiya tace ma ke dariya akeyi min ba a yadda"
Tunda ya fara maganar ta soma pouting din small mouth dinta gami da kwabe fuska harya gama saba binsa tukunna ta dauke hannuwa ta dake saman shoulder dinsa ta kauda kanta gefe alamun tayi fushi ta cukule dan bakin ta, marai rai ce fuska yay ya kamo hannun nata ta fisge abinta gami da harde su a kirjin ta tana me kara cin magani, sassauta voice din sa yay gamida da cewa. " Yanzu saboda na fadi gaskiya kike fushi dani, to am sorry ok" juyo wa tayi tana hararar sa tace." Sweetheart saboda mutane sun rainani kaima yanzun ka Raina ni koh kalla yadda kake min magana harda min shouting, saboda wani banzan dalili naka" kura mata idanu yay cike da mamaki yace." Ammi Yanzu maganar tawa ce banza, duka ranar da kika fita se an biyoki, haka idan tare muka fita se an biyo mu, duka mazan dake kawo miki hari bakya damuwa kenan?"
Taba bakin ta tayi tace." To seme don sun biyo ni, ko a jikina badai sena saurari mutum bah dai koh ze shigo min rayuwa, ko kuwa ka taba ganin nataba sauraren daya daga cikin su, so bari ma kaji son, duka mazan duniya babu wanda zan iya aure inba wanda zuciya ta ke gunsa ba, shikadai ne zan iya rayuwar aure dashi yanzu"
Wani irin kallo yake mata me cike da mamaki, cikin takaici yace." Yanzu Ammi daddy ko shekara baiyi da rasuwa ba kike maganar yin aure har da cemin wanda zuciyan ki take gunsa, shi daddy da waca zuciyan kike tare dashi dah? Ay dama tunda daddy ya rasu banga kinshiga irin damuwan dani na shigaba" shiru yadan yi yana thinking kafin yay ajiyan zuciya yace " Allah sarki daddy sai Yanzu na gane dalilin dayasa koda kun samu sabani shine yake lallaba ki koda kece kika masa laifi, ashe yasan bada zuciya daya kike zaune dashi.... Tasssss! Ta dauke shi da mari cikin matukar mamaki kuwa ya dago yana kallon ta idanun ta yay shabe shabe da hawaye cikin fushi take cewa.
" Idan bada zuciya daya nake zaune da mahaifin kaba taya zan haifeka namaka tarbiyya me kyau? To bari kaji in gaya maka saboda dole nake zaune da mahaifin ka kan dole! Don banida yadda zanyi ne iyaye na kawai nakewa biyayya, kuma dukda hakan kataba ganin Daddyn ka yabani umarni naki bi ko kuwa ka taba ina ganin ina daga masa murya sauda kafa ina bin mahaifin ka domin samun aljanna ta kuma Alhmdlh mun rabu dashi lafiya sedai Addu'ah dazamu yita binshi ta ita har zuwa lokacin da tamu zata riskemu, then haramun ne don nace zanyi aure yanzu ko kuwa kafiso na zauna kaita kallo na kullum, shekaru na 36 tsufa nayi dayin aure kodan kaga nice na haife ka ka girma yanzu"
Saboda tsananin mamaki kallon ta kawai yakeyi harta kare maganar ta, fararen idanun sa tuni suka kada sukayi zajur heartbeat dinsa na kara speed sosai idonsa tab da kwallah yace." Saboda dole kike zaune da daddy na ashe nima kan dole kike tare dani ba sona kikeyi bah, Allah sarki daddy ka mutu ka huta dama nima Allah ze dauka raina yanzun don abinda nake fuskan ta yanzun ya zarta tunani na, ban taba tsamma nin wan nan maganar daga bakin kiba Ammi why don daddy baya raye zaki canza haka meyasa zakiyi masa haka?"
Yana karashe maganar hawaye na sauko wa kan cute face dinsa, kallon sa kawai take duk jikin ta yay sanyi ganin dan lelen nata na hawaye, shima ita yake kallo tana nata hawayen wani irin kululu ya hadiye gamida mikewa tsaye yana cewa " fine Ammi kije kiyi rayuwar ki da wanda zuciyan ki take hannun sa" kai tsaye ya fice yana me banko kofar da karfi, sauka yayi abinsa yana yin nashi upstairs din ya shige har master bedroom dinsa ya fada kan makeken bed dinsa ya lumshe idanun sa hawaye masu zafi na fito wa a cikin su, ya juma a haka kafin ya tashi ya sawa kofan nashi key ya canza kayan sa zuwa towel ya wuce bathroom ya sakar ma kanshi ruwa koya danji saukin sara masan da kansa keyi ga yunwa na kwakular sa.....✍️