Chapter 7
Shiru yayi sosai yana nazari bayan fitar zannur,yaji komai ma na duniyan ya dena masa dadi miqewa yayi ya shiga dakin shi bed side drawer ya bude ya dauko daya daga cikin alqur'anin da yake dakin ya shimfida prayer mat ya zauna budewa yayi ya fara karatun with his melodious voice bayan dan wani lokaci ya fara jin 80% na damuwar da yake ciki yana yayewa, yayi karatun for more than one hour sannan yayi folding prayer mat din ya aje ya maida qur'anin shima ma'ajiyar sa sai a lokacin ya samu relief fita yayi zuwa kitchen ya hada hot chocolate ya fito parlour system din sa ya dauka saboda akwai wasu mails da zai tura yana sipping hot chocolate din shi yana aiki.....................
Sooraj Abdulhakeem ni cikakken dan jigawa ne kazaure local government aiki ne ya kawo ni zaman Abuja nida mata ta na ganki ne ranar da kika tsaya siyan kaza Idan zaki iya tunawa sai a lokacin JAY ta daga Ido ta kalli Sooraj dake jiran Jin me zata ce Sai da ya fadi haka ma ta gane shi a hankali tayi nodding kanta alamar ta tuna sannan ya cigaba da maganar da yake naso ko number ki ne na karba amma sai naga ba mutuncin ki bane na tsaida ki a hanya shiyasa na biyo bayan motar ki har naga gidan ku kiyi haquri Jaiyana ba danyi bincike akan ki saboda ni tsakani da Allah auren ki nake sonyi idan har kin amince da farko ma kasa cewa komai tayi sai kuma tayi ajiyar zuciya sannan tace nagode sosai amma don Allah ina son ka dan bani lokaci nayi tunani akai tohm shikenan zan dawo nan da sati daya sai naji hukuncin da kika yanke nodding kanta kawai tayi har ya fice daga parlour jiki a sanyaye ta koma cikin gida...............................
Yayi nisa cikin tunanin da yake yi Muneerah ta zauna gefen shi ta dafa shoulder dinshi juyowa yayi ya kalleta tace fuskar ka ta nuna kana cikin damuwa ka daure ka fada mun meke damunka ko nima zan samu nutsuwa a zuciya ta,a jiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleta yace sweetheart HAYDAR yana cikin damuwa wanda hakan ne yasa kika ga nima na shiga damuwa,sau dayawa zan zaunar da HAYDAR nace mashi ya nemi maganin sihiri amma sai ya mayar da ni sakarai wanda bai san abunda yake yi ba yace shi babu wanda zai yi masa sihiri tun ina dagewa har na gaji na haqura amma kuma kwana biyun nan na kasa daurewa kin sani ban dauki HAYDAR matsayin aboki ba na dauke shi ne a matsayin dan uwa,duk lokacin da na ganshi cikin matsala bana Jin dadi,ajiyar zuciya ta sauke sanin babu abinda ke dagawa zannur hankali kamar yaga damuwa a kan fuskar HAYDAR ka kwantar da hankali ka komai zai wuce kamar bai faru ba ka sani kowa da kalar nasa jarrabawar a duniya amma baka yi amfani da shawarar da na bada ba kenan A'a nayi masa magana jibi asabar zamuje Abuja in shaa Allah yawwa Allah yasa bakin wahalar sa kenan yace Ameen Toh yanxu dai ka saki ranka ka dena damuwa don Allah murmushi yayi mata sannan ya janyo ta jikin shi ya rungume a hankali yake mata magana thank you so much sweetheart for always being there for me,i really appreciate your constant support martanin murmushin ta mayar masa bata dai ce masa komai ba Allah ya sani ita dai bata son ganin koda digon damuwa ne akan fuskar shi.........................
Jaiyana ce zaune a kan Italian carpet din dake malale a parlour dad ta tankwashe kafarta suna magana kana gani kasan magana ce mai muhimmanci suke yi from the way she's listening to each and every single word he's telling her attentively,cikin kwantar da murya yace you are not getting any younger JAY and duk wani achievements na rayuwa kin samu me kika nema kika rasa,duk da na yadda da tarbiyar da muka baki amma kullum cikin zulumi nake kwana,kuma nasan haka ne daga bangaren mahaifiyar ki saboda babu wasu iyaye na kwarai a duniyar nan da xasu so ace yau ga diyar su nan zaune a gida babu aure,but one thing i want you to put at the back of your mind is marriage is a lifetime journey don't rush things because you might regret doing so at the end,kiyi addu'a ki nemi zabin ubangiji kar kibi zabin zuciyar ki, a cikin alqur'ani suratul baqarah aya ta dari biyu da sha shida (216) Allah madaukakin sarki yana cewa وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا۟ شَيْـًٔا وَهُوَ خَيْرٌۭ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا۟ شَيْـًٔا وَهُوَ شَرٌّۭ لَّكُمْ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
Transliteration
Wa 'asā an takrahū shai'an wa huwa khairun lakum wa 'asā an tuhibbū shai'an wa huwa sharrun lakum wa Allāhu ya'lamu wa antum lā ta'lamūn
A hankali ta dora kanta a kan qafafunshi dake kan carpet din while shi kuma yana zaune akan kujera ajiyar zuciya ta sauke tace in shaa Allah dad zanyi duk yanda kace and I'll pray istikharah too yawwa that's my girl Allah ya albarkaci rayuwar ki ameen tace sannan tace thank you so much dad for always being the amazing father you are and thank you for all you've done to us may Allah reward you with jannatul firdaus wani hawaye ne ya silalo daga idon ta ya sauka kan kuncinta bata damu da ta goge ba saboda tasan ko ta goge wani ne zai qara sakkowa shiru parlour ya dauka babu wanda ya qara cewa komai,they are all lost in their thoughts......................
Kamar yadda safiyyah ta fada ma momma zata je gidan Hamma khaleel bayan ta tashi daga bacci ta shirya cikin wata rantsatsiyar atamfa dinkin riga three quarter da skirt dan kwali ta daura style din zara buhari sannan ta yafa gyalen ta ta dauki makullin mota ta fita zuwa gidan Hamma khaleel,ta tarar baya gida sai lateefah matar shi da ta fito daga kitchen bayan taji anyi sallama turus ta tsaya bayan ganin safiyyah da tayi tsaye a kofar parlour qarasa fitowa tayi cikin parlour da murmushi akan fuskar ta tace lallai Yau za'a yi ruwa har da qanqara yau kece a gidan mu safiyyah ita dariya tayi tace kai Addah lateefah sharri zaki yi man ina zuwa fah hmmmm ai shi kenan bari na kawo maki ruwa kafin na qarasa abinci Tohm Addah kitchen ta koma ta dauko ruwa da lemo sai snacks ta dora kan tray ta fito ta aje ma safiyyah dai dai nan me aikin ta ta fito riqe da ilham da ke ta kuka miqa ma lateefah tayi sannan ta gaishe da safiyyah da tayi kamar ba da ita ake ba,karban ilham tayi daga hannun lateefah tana lallashin ta tace kuma fah na dade ban zo gidan nan ba Addah don rabona da gidan nan tun ranar sunan ilham lateefah tace kuma ilham dai jibi zata yi shekara daya ciff a duniya,ai baki da kirki wallahi Allah dai ya shirya Ki ameen tace tana dariya hira suka yi sosai har lateefah ta gama girki ta zuba masu suka ci har yamma tana gidan bayan la'asar Hamma khaleel ya dawo sun gaisa yake tambayar ta mijin ta tace bai dawo daga wurin aiki ba,biyar da rabi ya tafi dauko su sultan da sultana daga school,sai bayan maghrib tayi shirin komawa gida turarukan wuta ta bata na jiki da kuma na gida masu qamshi godiya tayi mata sannan ta raka ta har mota tana tsaye har ta fita daga compound din gidan sannan ta koma cikin gida..........................
Tun bayan da ya dawo gidan daga wurin JAY Laylah ke ta masa fitsara bai kula ta ba da taga yaqi ce mata komai sai ta dawo gaban shi ta tsaya tace ai dama baka da bakin magana Sooraj baka da wani abu da zaka fada man na yadda da kai ban san cewa kai mayaudari bane wallahi kuma ka cuceni Allah ya isa tsakani na da kai,sai da ta tsorata bayan ya daga idanun shi ya kalleta da rinannun idan shi da yayi ja kamar Wuta saboda bacin rai,ki bace man daga gani malama kafin nayi maki abinda zamu zo muna da na sani,ai tun kafin ma ya rufe bakin shi ta yi hanyar dakin ta saboda yayi mugun bata tsoro,dafe kan shi yayi da ya masa nauyi saboda ciwon da yake masa,bawai saboda yana tsoranta ya kyaleta ba yasan dai shi ke qoqarin yi mata laifi kuma duk abinda take yi tana yi ne saboda tana son shi,shiyasa yake mata uzuri amma ta fara qure haqurin shi kuma zai dau mataki akanta............................
Bayan dan wani lokaci ta kalli dad taga alamun bacci yake ji sai tace dad zan je na kwanta Tohm shikenan good night and don't forget to pray in shaa Allah dad bye i love you,bata jira jin me zai ce ba ta fita daga parlour a bakin qofa suka hadu da mom ita kuma zata shigo parlour da yankakkun fruit a bowl ta daura kan tray Sai da safe tayi mata sannan ta wuce part din su, a parlour ta samu hajiya mama da ayaanah suna kallon cartoon,zama tayi a daya daga kujerun parlour ita ma sai kuma kamar an tsikareta tace ma ayaanah ta tashi suje ayi wanka ta kwarata dare yayi Sai da safe tayi ma hajiya mama da har ta fara gyangyadi amsawa tayi sannan ta miqe itama ta kashe kayan kallon ta wuce dakin ta,bayan ta yi ma ayaanah wanka ta saka mata sleeping dress ta kwantar dakin ita,komawa tayi itama tayi wanka ta shirya sannan ta janyo laptop din ta dun duba mails din da aka turo mata,ta danyi replying wasu kiran sadeeq ya shigo wayar ta picking call din tayi ta kara wayar a kunnen ta daga daya bangaren sadeeq yace good evening JAY mayar masa da gaisuwan tayi ita ma sadeeq ne yace you know what JAY yau Abbah ya kira ni yace man sunyi magana da uncles dina sunce kiyi ma dad magana ya saka date xasu zo nema man auren ki I'm so happy wallahi sosai taji gabanta ya fadi amma sai ta daure tayi murmushin qarfin hali tace zan yi ma dad magan in shaa Allah but I'm really sorry sadeeq ina wani aikin ne yanxu ka kira ni in ba damuwa sai muyi magana gobe ko yace ok ba matsala good night my love,bata iya ce masa komai ba tayi ending call din,sosai tayi qoqarin cire damuwa daga ranta tayi focusing kan abinda take yi amma ta kasa kashe system din tayi ta kwanta amma sai me bacci ya qauracewa idonta,tafi awa daya a kwance amma ta kasa yin bacci miqewa kawai tayi ta shiga bathroom ta daura al'wala ta fito ta shimfida prayer mat ta fara sallah bayan dogon lokaci ta daga hannayen ta sama tana addu'a sosai ta da de tana addu'a da kuma neman zabi ta dade a zaune har aka fara kiran sallah,tashi tayi ta yin raka'atanil fijr,bayan ta idar tana ta zaune tana jiran a shiga sallah aka bude kofar dakin ta dad ne ya shigo ganin ta tashi yasa bai ce komai ba ya wuce dakin mom,yana shiga itama ya tarar tana toilet tana al'wala,dakin hajiya mama ya shiga ya tarar da ita a kan prayer mat tana sallah juyawa yayi ya fita masallaci kuma dama hakan al'adar sa ce idan har yana gari kafin ya tafi sallah sai ya tabbatar duk sun tashi sannan ya tafi masallaci.................................
Hafsat na dira Nigeria daga airport ta wuce gidan Laylah ta same ta zaune a daki tayi ta gumi tayi nisa cikin tunani tace amma wallahi kin bani mamaki da zaki zauna kina sa ma kanki damuwa akan namiji baza ki gane bane hafsa ina cikin tashin hankali wallahi akan namiji zaki kashe kanki Toh wallahi tun wuri ki dawo hankalin ki jiya ma fa Sai da na bi shi wallahi fa da ya fita nasan wurin yarinyar yaje,Toh yanxu kafin ki dawo kan shi ita yarinyar zaki fara yima kashedi Idan tayi ma kanta gata ta kyale maki miji idan kuma bata ji ba duk abinda aka mata ita ta so,yanxu ya za'ayi musan address din ita yarinyar ai zan gane gidan da yaje toh saka mayafi mu tafi........................
Kwance take a kan kujera tayi pillow da qafar mom a parlour kasancewar yau Saturday bata fita aiki suna magana akan Sooraj da yazo jiya,ta bata labarin yadda suka yi da shi gaskiya yayi hankali da bai tsaida ke akan hanya ba ya nemi gidan ku yaxo wannan ma kadai ya isa musan cewa yana da hankali amma ba hakan bane zai sa a bashi dama ya kamata ace kin san waye shi kuma kinji eh zaki iya rayuwa dashi,bata rufe bakinta ba aka bude qofar parlour with force tun daga sama har qarasa JAY ta bisu da kallo sannan ta dauke kai shigowa suka yi har tsakiyar parlour suka ja suka tsaya daga JAY har mom babu wanda ya ce masu ko ci kan ku da suka gama kalle-kallen da suke suka ce gargadi muka zo yi ma ko ma wacece take qoqarin shiga gona ta toh wallahi miji na yafi qarfin auren ta yanxu mun xo ne cikin kwanciyar hankali muka xo amma idan tayi taurin kai wallahi next xuwan mu bazai mata dadi ba idan kunne yaji toh jiki ya tsira Sooraj don ni kadai aka halicce shi bai isa ba ya auro wata da sunan inyi kishi da ita ba sai a lokacin JAY ta qara daga ido ta kalli mai maganar jin sunan da ta ambata har suka gama haukansu don ita gani take kamar basu da hankali don mai hankali ba zaiyi abinda suka yi ba qala babu wanda yace masu daga ita har mom jan hannunta hafsa tayi sannan tace shawara ya rage ga mai shiga rijiya suka fita,hajiya mama ce ta qaraso cikin parlour wanda tun lokacin da aka banko qofar ta fito tayi tsaye tana kallon su tama kasa ce masu komai ganin JAY sai gaggaba dariya take kamar mahaukaciya yasa ta tsuke fuska tace ke kuma dariyar uban me kike qara fashewa tayi da dariya sannan tace wallahi hajiya mama wannnan daga gani dai daga psychiatric hospital suka gudu don ba dai masu hankali bane wannan zama tayi akan daya daga kujerun parlour tace ke kuma a ina kika san mijinta da har take zuwa tana ma mutane tijara har gida mom ce ta bama hajiya mama labarin komai nan ta fara fada tace toh wallahi kar ma ku yadda ummaru yaji wannan maganar don wannan sam ba mijin aure bane ina dalili wannan figaggiyar matar tashi ma baza ta bari kiyi zaman lpia ba ko anyi auren shikenan hajiya yanda kika ce haka za'a yi nima dama naji gaba daya kuma ya fice man a rai kallon JAY da har lokacin tana kan cinyar ta tayi tace kinga JAY idan ya qara dawowa kawai ki ce masa yayi haquri Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi,Tohm shikenan mom in shaa Allah yawwa hankali na ma yafi kwanciya da hakan kar daga baya azo ana da an sani amma kunga yanxu bakin mu alekum babu wanda yaji babu wanda ya gani juyawa tayi ta kalli JAY sai kuma tace kee Lpia naga kamar idon ki ya kumbura yawwa hajiya wata qila ke ta fada maki tun daxu na tambaye ta amma sai tace man wai bata yi bacci da wuri bane jiya,A'a kinga tashi muje daki na muyi magana tashi suka yi suka tafi dakin hajiya mama mom kuma ta wuce bangaren dad,bayan sun zauna gefen gado hajiya mama tace kinga fada man damuwar ki kinji dora kanta tayi akan kafadar hajiya mama tace ba na taba baki labarin wani sadeeq ba a wurin aikin mu ehh naji wanda ya taba zuwa ya gaishe da ni ko eh shi jiya da daddare ya kira ni wai Abban shi yace na sanar da dad ya saka masu rana zasu zo neman aure na amma ni ina ganin kamar naci amanar shi kenan idan na amincewa auren wani namijin tana kaiwa nan kawai ta fashe da kuka bata ce mata komai ba tana patting bayan ta har tayi kuka mai isar ta sai sa taga ta dena kukan sannan tace wannan ne dalilin da yasa jiya bakiyi bacci ba kenan ta gyada mata kai ta tausasa harshen tace da muryar lallashi tace kiyi haquri hakan ba komai bane fa ce jararrabawa ki amshi qaddarar ki da hannu bibbiyu wata qila dama ubangiji ya rubuta babu aure a tsakanin shiyasa ma duk abinda ya faru a baya ya faru ki cigaba da addu'a duk da nasan kina yi amma ki qara kinji in shaa Allah komai zai wuce kamar bai faru just believe that this is your fate and accept it with good faith Allah yayi maki albarka bayan nasihan hajiya mama ta dan ji nutsuwa a zuciyar ta sosai suka shiga hirar duniya ta ma manta da wata damuwa a haka mom ta dawo ta same su suna ta dariya kuma taji dadin ganin babu damuwa a fuskar JAY dama tasan idan har hajiya mama na nan toh bata da damuwa don wani lokacin ma sai sun gama abin su take sani................................
Kamar yadda suka tsara da zannur ranar Saturday zasu je Abuja hakan ne ya kasance don qarfe sha biyu na rana suka bar gida tare da driver din HAYDAR wanda shine zai kai su airport din,tafiyar minti arba'in da biyar ne ya kawo su cikin airport din kasancewar basu samu hold up sosai a kan hanya ba driver din na ajiye su ya musu Allah ya kiyaye ya koma cikin airport din suka shiga suka zauna a waiting lounge saboda jirgin su sai qarfe daya da rabi zai tashi sun fito da wuri gudun kar su samu hold up a hanya zaman su ba dadewa suka tashi suka wuce masallacin dake cikin airport din don lokacin sallah yayi bayan sun dawo ne suka wuce wurin check in kasancewar basu da kaya yasa basu bata lokaci ba suka karbi boarding pass din su suka wuce departure gate sukayi boarding plane,bayan duk wasu formalities suka zauna cikin jirgin suna jiran take up,suna zaune har aka fara sanarwa jirgi zai tashi kowa ya daura seatbelt din sa.......................
Bayan su laylah sun koma gida ita da hafsa suka tarar da Sooraj zaune yana latsa wayar sa yi yayi Kamar baiji shigowar su ba ya cigaba da abinda yake hafsa na ganin shi tayi ma Laylah sai anjima tayi wucewar ta yana nan yanda yake bai ko daga Ido ya kalleta ba har ta qaraso inda yake ta riqe qugu tana masifa bai ce mata qala ba har ta gama duk tijarar da hafsa ta ce tayi masa tayi shiru don kanta ganin yaqi tanka mata sai da ya tabbatar ta gama sannan ya kalleta da kyau yace wallahi kwanan nan zaki sha mamaki na a gidan nan Laylah sannan idan har shawarar qawaye zaki na dauka to zakiyi da kin sani a lokacin da bashi da amfani don haka idan kina da hankali tun lokaci bai qure maki ba kiyi ma kanki fada ki gyara shawara ce nake baki a matsayi na wanda yake son cigaban ki bai qara kallon ta ba ya wuce dakin shi............................
Yau ma dai kamar sauran kwana kin da suka wuce tun bayan zuwan ta gidan su maganganun momma ke maimai ta kansu cikin kwakwalwarta sosai take shiga cikin tashin hankali Idan ta tuna zaunawa tayi tace kai da sake gaskiya dole nayi wani abu zuciyar ta tace mata toh ya zakiyi da shema'u dayan ta bata amsa da ki kyaleta har kiyi accomplishing mission din ki sosai taji hankalin ta ya kwanta da wannan shawara ta zuciyar ta ta jinjina kai cikin yadda da kanta.......................