2
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
* NA*
NANA BMB
Episode two
Ita kuwa Ammi din tashi yana fita tsoro ya shige ta ganin yanayin da dan lelen nata ya shiga yasa ta karawa kukan ta sauti tana cewa.
" Haba sweetheart meyasa zaka min wani irin fahimta? Taya yanzu zaka fahimce ni? Niba cin zarafin mahaifin ka nayiba, Ya Allah ka kawo min mafita my son fushi yake dani" Takasa zaune ta kasa tsaye,
Daurewa yay kawai ya gama bukatun sa a bayin ya fito daure da towel zara zaran gashin dake jikin sa sun kwanta sunyi luf saboda ruwan da sukaji karamin towel ne hannun sa yana tsane ruwan dake diga a suman sa ransa babu dadi haka ya zura jallabiya abinsa yayi sallah tukunna ya gama shafa ya kwanta zuciyan sa a cunkushe,
Ganin bata da wata mafita ne yasa ta sauko ta nufi ban garen nashi sedai kofan nashi gam tajishi a rufe, cikin wani kalar yanayi kamar zatai kuka tace." My son please ka budewa Ammin ka kofa kaji, bazan iya jurar barin ka cikin damuwa ba haka, ka fito kaci abinci kada ciwo ya kamaka please!" Tun tana buga kogan slowly har tasaka karfi tana dukan tana kiran sa amma shiru ko motsin sa bataji ma ta kusa rabin awa a tsaye harta zame tai zaman dirshan gaban kofan jin takaicin ya mata yawa ne yasata sake fara yin wani kukan don ita a nata ganin wan nan kamar a dakeka a hanaka kuka ne, daga tayi zancen masoyin ta🤷,
Yana kwance haryanzu idanun sa a rufe suke kuka ma ko wani irine baya kaunar sa bare na mahaifiyar tashi dayake jin sa har cikin bargon sa, yasan dole baze iya share taba haka ya mike yaje ya bude kofan, ya tsugunno dai dai saitin ta yana kallon ta, ya rigada yasan halittar Ammin tashi ce a haka abin kuka baya mata wahala ahaka ya taso ya sami wan nan halin nata, yana cikin tunanin ne yaji ta riko hannayen sa tana cewa.
" Sam ni ban fadi maganar nan don na tozarta mahaifin kaba kawai bazaka fahimce ni bane, bazan kara maka irin wan nan maganar ba, kada nakarajin kalmar bana kaunar ka a bakin ka sam bakayi min adalci ba kasake furtata banason na karaji, yadda nake kaunar ka koni banason kaina duniya baki daya ta shaida hakan!"
" Enough of the tears! Please" hannu yasa yana share mata hawaye, se tura baki gaba take kamar wata yarinya wan nan halin nata ta rigada ta saba babu yadda ya iya da ita shine ya temaka mata ta mike tsaye yace." Bari na shirya to na fito" kutsa kai tayi cikin dakin ta dauko masa kayan daze saka, tana kara gyara masa wardrobe din harya gama shiri tukunna suka fito har zuwa dining dan gatan abinci me rai da lapiya ta zuba masa tana feeding din sa yana kallon ta don shi har yanzu mamakin ta be sake shiba, seda ya koshi tukunna ya mike suka zauna a parlour yana shaida mata a gobe yanada baki a company murmushi tayi tana cewa.
" A ah! Sweetheart fah an girma yanzun harka ma soma sabawa da business na Daddy ka" soman sa yadan shafa shima yana murmushi yace." To ya zanyi tun ina karami nauyi ya hau kaina dole na dage rainani mutanen daddy keyi se an zauna lissafi da tsari sunga nima kwallo ne suke kiyaya ta!" Ya karashe maganar yana dariya itama dariyar tayi tace." Allah dai ya tsare min kai sweetheart ya karemin kai daga magauta ni tsoro na daya shine tafiya ta kama ka zuwa wata kasar kai kadai yanzu babu Daddy ka yadda zamanin nan ya kara lalace wa mata nata kawo maka hari haka kawai kaje su lalato maka tarbiyya, nidai anya kuwa ba auren wuri zan maka ba kuwa shine kawai hankali nah ze kwanta duka inda zaka kuna tare hakan yafi a mutum ce" sosai Omar yake mata dariya harta kare maganar ta kana yace.
" Yanzu Ammi ko shekara 20 ban cika ba kike min maganar aure, gaskiya kinada abin dariya, nida mata yanzu ina! Ki tausaya min haka kawai a hadani da jigila kwata kwata soyayya bata burgeni ba komi cikin ta se wahala, ko sauraren matan ma inayi ne gasu nan a skull din mu kala kala ko kallo basu isheni bah" wani irin murmushi tasaki har Chicks dinta na lobawa tace." Sweetheart nawa kaidai kawai kayi Addu'ah kada Allah ya jarabce ka da irin soyayyar danayi, don zaka wahala, kuma sannu sannu dai se in time din ka beyi bane"
" Kai haba koda wasa ma kada ki hada life dita da irin wahalan lal son nan bazanyi shiba har abada Ammi ke kadai ce farin cikin rayuwa ta" wata shewa tayi gami da cewa tom ay shikenan Allah kaimu lokaci dai.
ASALIN LABARIN
Garin shanono gidan malam bala, matarsa daya juhainah 'ya'yan su uku Haseen shine na farko se ta biyu Hashmat se autar su kuma Zainab yana da rufin asirin sa gidan sa kuma rayuwa ake me cike da tarin tarbiyya da girmama juna, autar su Zainab itace Allah ya yota da kyawu naban mamaki gata fara sol Masha Allah duk da namijin daze dora idanun sa kan Zainab seta burge shi har matan ma duba da irin halayyen ta daya gama bi mata jiki shagwabab biyace sosai Zainab abin kuka baya mata wahala ko bacci take haka zata tura baki gaba saboda shagwaba, a time din da takai shekaru 14 ne maza aka soma yi mata tururu wa kowa yana so, ita kuwa kaf garin nan babu wanda take kauna se wani yaro me shago a layin su me suna Omar bashida burin da ya wuce ya auri Zainab haka itama hakan take a boye suke soyayya su sosai suke jin bazasu iya rayuwa idan ba juna bah, seda akayi bikin yayar ta Hashmat kowa ya fahimta irin soyayyar tasu saboda komai tare sukeyi anko ma sukayi kaya kala daya 'yan gayan seda bayan biki ne Zainab taje gidan yayar tata anan shanono din suke fira abinsu anan take tambayar ta tace.
" Zeetah dama soyayya kukeyi keda Omar da duka a tunanin mu shakuwa ce kukayi kawai" wani lallau san murmushi Zainab tayi gami da cewa." Yaya Hashmat shine ay wanda zan aura shi kadai nakeso" wata irin harara Hashmat ta watsa mata gami da cewa." Lallai ashe zeetah bayan rashin wayan ki harda rashin hankali ashe yake damun ki! Yanzu wan nan yaron Omar zaki aura duka dunbin masoyan ki dake bibiyar ki suke neman auren ki ido rufe ki rasa kuma wanda zuciyan ki zata aukawa se Omar, gaskiya kin yaudari kanki zeetah har kin soma bani tausayi, tun wuri ma gara kisan batun ki kisawa zuciyan ki salama ki zabi daya cikin maneman auren ki, tunkan lokaci yayi don kinsan kina kan hanya gara ki zaba inba haka ba baba ya aura miki wanda yake so, in banda rashin wayan kima zeetah wazewa Omar aure yanzu yana ma karatun sa"
Tuni Zainab ta fara kuka harda birgima tana " wlh! Yaya Hashmat baki sona baki kaunata tunda har kike min wan nan fatan kuma in Sha ALLAH shi zan aura, abinda ba yanzu zamuyi auren ba nida shi se mun gama karatu, babu wanda ya isa ya rabamu duk duniyar nan se Allah, zuciyan mu a tare take tafiya nida shi bazamu iya rayuwa ba juna ba" sosai Hashmat ta sau baki tana kallon rashin hankali karara gurin Zainab seda taci kukan ta ta koshi tukunna ta bar gidan sam taki saurarar yayar tata tanata rarrashin ta taki kulata haka ta tafi gida tanata kuka, tunda ga wan nan rana duka wani mahaluki dayace yana sonta rashin ta ido take masa ta koreshi ko kadan babu me ganin kofar tunkarar ta, ita a nata tunanin idan tayi haka babu yadda za ay a mata aure haka suka cigaba da soyayyar su harta zaga gari har zance yake zuwa Omar har gida kasance war mahaifiyar Omar kawar maman su Zainab din ce kuma layin su daya kusan can nema Omar din ya taso shiyasa bashida shamaki a cikin gidan nasu Zainab can dakin matar yayan ta suke zama suyita fira abinsu, haka zalika tanada kawa lubabatu kusan abokiyar rigimar tace a nan layin nasu take itama mahaifin ta dan sanda ne wata rana kamar yadda suka saba fada ya harke a tsakanin su akai kaca kaca aka denawa juna magana, sedai 'yar aiken kawaye aka komayi wa juna na magan ganu, tsautsayi yasa lubabatu ta zagi Omar din ta kawayen ta sukazo suka gaya mata harda kari kuwa, takanas Zainab taje har gida gurin lubabatu tasame ta sam barka tana zance a kwar gida tai mata tass gaban saurayin ta tonan silili iri iri bawan da Zainab bata mata ba harda su fitsarin kwance 😂 tsaf ta kunya ta ta luba kam harda hawayen bakin ciki taji daci hakan yasa taci nata alwashin na wulakan ta Omar din data mata wan nan tozarcin akan sa,
A washe gari kuwa luba tasami Omar a shago ta inda tashiga bata nan take fitaba sam Omar be iya haya niya ba ko kadan kuma baya sonta sosai ransa ya baci saboda irin zagin da take wa Zainab din tashi yayi maganar duniya kuma tabar masa cikin shago taki tana ta masa ihu a ka, a zuciye yay wacakali da ita daga cikin shagon haka yasata soma kururuwa tana birgima harda yayyaga rigar ta ita alan dole sharri zata masa tanamai ihun kwarto sosai hankalin jama a ya dawo kansu tanata masha sharri kiri kiri yanaji yana gani wai taje siyayya ne yasoma mata a dumbule da kirji 😂 don yaganta me garun jiki, nan danan kuwa jita jita yasoma yawo wasu suce sun yarda wasu kuma suce basu yarda ba, sam malama zeetah batasan meke faruwa ba sedai kawayen ta 'yan kunzugulu sukaje har daki suka sanar da ita kasa magana ma tayi saboda takaici sedai hawaye,
To a washe gari sun dawo daga makarantar dare Zainab ta kama luba a cikin lungu ta dafe ta yaga duka yakushi cizo ta fisge mata hijab da dan kwali ta yage mata riga duk girma irin na luba sega Zainab 'yar mitsili tai mata kaca kaca ta fashe mata baki nan danan ta kumbure mata fuska dama seda suka shigo lungu tukunna, kawayen luba zasu shigar mata na Zainab sukai tsallen albarka suka hanasu sun zagaye su zuga Zainab kawai suke a takaice dai seda ta kusan sumar da luba tukunna sukai tafiyan su suka barta bayan ta warning din ta kan Omar dinta, kusan da rarrfe luba ta karasa gida da lalube a duhu dare yayi sedai hasken farin wata kawai, koda ta karasa gida mahaifin ta yay arba da luba ranshi yay matukar baci yakwa ce bazata sabuba, washe gari da wuri akazo har gida jami ay suka iza keyar Zainab suka tafi da ita ba karamin tashi hankalin iyayen ta yay ba mussam man maman su juhainah se kuka Zainab nacen police station, Omar besan wainar da ake toyawa ba yana can makaran ta har batun dukan da tayima luba akan shi be saniba, seda wajan yamma likis ya dawo ko gida be biya ba ya wuce gidan saboda tsegun ta masa din da aka soma tas matar yayan Zainab din ta gaya masa komai hankalin sa a matukar tashe ya nufi police station din, besan sanda yaji hawayen ba shima ganin zeetah dinsa dayay a guard room taci kuka ta koshi ga yayan nata Haseen yanata fama da 'yan sandan sunki saura rar sa sunce se ogan nasu yazo tukunna, shi mahaifin nasu ma yayi fushi yaki zuwa Saboda abinda sukace masa ta aikata, magiyan shima Omar ya fara akan a fito da ita shi a kulle shi ya yarda ba laifin ta bane duk hukunci da za ayi shi ayi wa, suna cikin wan nan hali sega mahaifin na luba tujara kuwa Omar yagan ta yace 'yar sa nacen asibiti, dakyar suka shawo kanshi yasa aka fito da Zainab din bisa sharadin a washe gari zasu dawo a karashe case din ahakan ma yace darajar tsohon ta taci ya fito da ita, tun a hanya yayan ta Haseen yake zazza ga musu nashi fadan har suka kai gida hakuri Omar yay ta bashi na kada su dake Zainab din kamar yay kuka hakuri yay ta bawa iyayen nata har tausayin shi ya kamasu, haka ya tafi yana mejin dama ya dauke ta su tafi don kada su taba masa lafiyan mata,
WASHE GARI...✍️