🧑‍🍼 RABO...❣️

3

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

* NA* 

       NANA BMB

Episode three 

Tunda farar safiya Zainab ta tafi gidan su Omar din ta jirashi ya shirya suka tafi police station din acan yayan ta Haseen ya samesu aka kare maganar har gida seda sukaje suka bawa luba hakuri kura ta lafa, bayan wasu kwanaki ne Omar ya gayyaci Zainab din bikin yayar abokin sa da akeyi a gidan shaharar ren dan siyasa inuwa mu'az shanono kowa yasan da zaman sa saboda temako dayake mutumin kirki ne sosai family hause ne yake zaune shida iyalan sa 'ya'yan sa biyar Eshan shine dansa na fari se me bi masa Eshaal  se kuma kanin su me bi mata Esmaeel me bi masa kuma itace Emaan se auta Eira, Esmaeel aminin Omar ne sosai suke amin taka a yanzun bikin Eshaal ne za yi ya bashi katin gayyata, Eshan shine ya gaji mahaifin sa a siyasa tun tasowar sa ya zamana komai dashi mahaifin su keyi don shima siyasa din ita ya saka a gaba yanason mikami Sosai, mahaifiyar sa batada burin daya wuce yayi aure amma sam yakiya ko 'yan matan ma baya shiga shirgin su duk nacin su kuwa har aka gaji ma aka saka masa ido don yace shi bega irin macen dayake soba har a wan nan lokaci, wan nan kenan!

      Ranar da za a fara shagali Omar yaje har gida ya tafi da Zainab gurin biki tayi matukar kyau shigan datayi duk da bawani makeup tayi ba amma in aka kalle ta se an kuma kallo, sosai take shan kallo a gurin duk inda suka gitta idanu ke binsu gashi ta likewa Omar din taki zama saboda batasan kowa ba kishi ne sosai ya kama Omar yawa Esmaeel magana shi kuma ya kaita gurin kannen sa Emaan da Eira inda suke zaune itama ta zauna sam taki sakin jikin ta a gurin su sedai ido kawai da take binsu da shi sunci uban ado abinda takeso Zainab shiyasa suka burge ta, ana cikin shagali motocin inuwa mu'az suka sawo kai cikin gidan can gurin parking suka nufa ay da gudu su Emaan sukai gunsu suna murna, tashin su kenan Zainab taga wani saurayi yayo inda take zaune dama ya juma yana kallon ta ganin hakan ne yasata kwasa da gudu itama tayi inda su Eira suka nufa tana waigen mutumin sam batasan ta isoba sedai kawai taji ta daki abu hakan ne yasata karasa yin tintube ta fada kanshi gaba daya kam ta rintse idanun ta tana Addu'ah a zuciyan ta jin wani irin ni'im taccen kamshi dake ziyar tar hancin tane yasata dagowa da sauri suka hada idanu da Eshan atake zuciyan sa tayi wani irin harbawa kallon ta kawai yake cike da al ajabin yanayin daya tsince kansa a ciki tura baki tayi gaba kamar shine ya mata laifin ta sunkuyar da kanta sim sim sim taje ta rabe bayan su Emaan kamar muna fika se dariya suke mata mahaifin su yana gefe yana kallon ta yanata murmushi shima, goga kuwa daskare wa yay a tsaye sam ya kasa dauke mayun idanun sa akan ta haushi ne kawai taji ya kamata Zainab saboda irin kallon da yake mata kamar bakin maye, suna gama welcoming dinsu su Emaan aka koma gurin shagali su kuma sukai cikin gida abin mamaki ko ruwa Eshan ya kasa sha yakasa zaune ma yayo waje don sake ganin Zainab wanda yakejin wani bakon lamari a tare da ita me girma, can ya hange ta cikin su Emaan tayi tsumu tsumu yanata ansar gaisuwa har abin ya isheshi sam besan abinda ze dauke masa hankali yadena kallon ta idan aka saka kida ya mata tasoma rawa daga zaune Abin ta se ta lura ana kallon ta ne zata nutsu tafara cin magani ana tura baki zaman aikin kallon ta kawai yake Eshan duk matan dake feleke a gaban sa batasu yake ba wani irin nishadi yakeji da farin ciki mussam man dayaga sun shiga fili suna cashe wa ta cire kunya abinta sam kasa jurewa yayi Zainab seji tayi yasoma mata ruwan kudi ta dago taji wani irin faduwan gaba dataga irin kallon da yake mata, 'yan gidan su kuwa mamaki ne ya matukar kamasu saboda abinda yay yanzu betaba yin koda makaman cinsa ba, to wan nan ne yasa aka soma tsegumi kuma, har aka tashi taro Eshan bewa Zainab magana ba sedai kallo yana gani time din da suka tafi da Omar, tunda ga wan nan ranar Eshan bashida wani aiki se mafarkin ta da masa gizo lokaci daya ya fada a kaunar zeetah haryay nisa gashi be kuma sakata a idanun saba, tunda ta bangaren Omar din yayi yayi da ita tazo a karashe bikin da ita tayi kememe tace bazata kuma zuwa ba saboda sam batason kara ganin Eshan cuz irin kallon da yake mata har tsoro ma yake bata, kasa hakuri yayi Eshan din wata rana yake tambayar Esmaeel wacece Zainab din, sosai ya gama karantar yayan nashi dama yana murmushi yace.

    " Yaya Zainab ay budurwar Omar ce amini na ita ze aura soyayya suke abinsu" 

   Sosai haushi ya kamshi dajin zancen kanin nashi harda watsa masa uwar harara yana cewa." Wan nan dan yaron dana gansu tare kake nufi ze aure ta?" Dariya ce taso kwace wa Esmaeel ganin yadda yayan nasa ya dinke fuska." Yaya soyayya fa sukeyi!" Wani dogon tsaki yaja Eshan yana cewa." Wasan yara dai duka wan nan yaran ne zasu san wata soyayya, ay yaudarar kansa ma zeyi wlh yace ita ze aura tariga ta masa nisa kuma ay" gajiya Esmaeel yay da tambayoyi da yayan nasa ke masa akan ta yace." Wai to Yaya sonta kakeyi ne?" Beji wani shakkar komai ba ya bashi amsa." Karewar so ma auren ta zanyi gaba daya" cikin fargaba Esmaeel yace." Amma yaya kasan yadda takeson Omar kuwa?" 

    " To seme! Ahakan zan aure ta, ko kana ganin anan gaba bazata iya sona ba?" Girgiza masa kai yay gami da cewa." Bana tunanin haka gaskiya, donni ganau ne ba jiyau ba akan lamarin ta da Omar" cikin fushi Eshan yace." Esmaeel banason maganar wani Omar ni kawai kasa ido kayi kallo nasu wasa ne" ya fice abinsa Esmaeel kawai ya bisa da kallon tausayi su duka ukun se suka bashi tausayi sam beyi farin ciki ba da yayan shi ya auka son wadda yake da yakinin bazata kauna ceshiba.

    Bayan maganar su da 'yan kwanaki mahaifin su Zainab ya kirata cikin manema auren ta akwai wanda ta tsayar ne, ta shaida masa a ah ita iya Omar din ta kawai takeso, murmushi kawai ya mata yana me cewa." Yanzu Auta kina ganin Omar aure zeyi yanzu? Kofa secondary be kare ba" cikin sanyin jiki tace." Ay dama baba ba yanzu zamuyi auren ba se mun gama karatu" dariya kawai yamata yace." Kai auta yarinta na dawai niya dake, aini bese kin gama karatu ba zan aurar dake kina cika shekara 15 zan aurar dake ko baki ga yayar kiba itama bata gama kara tunba se sauka datayi a islamiyya, saboda haka kema kinga saukar ki nata kara towa da kin yi se maganar aure kuma don haka tun wuri kada lokaci ya kure miki ki tsaida mijin aure idan kin kiya kuma na aura miki zabi na" ganin mahaifin nata da gaske yakeyi yasa ta mikewa ta tafi tanata sharbar kuka ta shiga dakin umman tata ta gaya mata kome ke faruwa, murmushi kawai tayi tace." To zeetah seki maida hankali ki fitar da mijin cikin masu neman ki dama ay shirme ne kukeyi taya Omar ze aureki wanda ko sana a baya da ita se jiran shago" cikin kuka tace." Wlh ummah nayar da zan zauna dashi haka semu zauna a dakina kina yin girki damu" dariya kawai tayi mata tana Addu'ah Allah ya yaye mata wan nan hali nata, nan sukai drama dinsu ta wuce batare da Omar ya sani ba don bata fada masaba suka cigaba da soyayyar su, batun Eshan kuwa indai kaga fara ah fuskan sa to tunanin Zainab yake kullum idan zata school seya tsaya a hanya domin ya ganta takanas yake zuwa donya ganta kawai kuma be taba mata magana ba kaf mutan gidan nasu yanzu sun san da zaman Zainab a zuciyan sa, ita kuwa batasan yanai ba sabgar gaban ta kawai take don harga Allah tama manta dashi, haka suka cigaba da rayuwa harta shiga aji uku a secondary, time din kuma ta cike shekara sha biyar kyawu da diri malam na kara bayyanar mata, a lokacin ne baban nasu ke tambayar ta wata tsayar cikin maneman nata, kai tsaye ta shaida masa babu kowa ita Omar kawai take so, shima batare da shakkar komai bah ya shaida mata cewar ay ya bada ita don haka ta shirya aurar da ita zeyi, Ya ilahi!! Zeetah tashiga tashin hankali ba kadan ba tana barza uban kuka kamar tabab ba ta isa shagon Omar tanasar dashi halin da ake ciki, nan danan yaji duniyar na juwa masa shima se hawayen ko rarrashin ta ya kasayi seda yay ta Addu'ah a zuciyan sa tukunna ya iya saita nutsuwar sa ya bata hakuri akan ta bari susan waye aka bata se susan yadda zasuyi dashi, ay tana komawa gida ta shige dakin baban nasu tana tambayar sa waye wanda ya zaba mata, sosai ta bashi dariya yarinyar da tabar gaban shi tanata rusa ihu kamar wadda aka wa rasuwa dukdan saboda ya bada ita shine kuma yanzu zata zo masa da wan nan zancen ya rigada ya san ba maganar ta bace wan nan dama, gimtse dariyar yay ya shaida mata ta bari idan yazo tadi ta ganshi, 

    Haka sukayi hakuri tadai sanar dashi koma waye yana zuwa zata zo ta kirashi su hadu suyi masa cin mutum ci daze sa yafasa auren nata, har aka tsaida lokacin biki basu saniba ta daiga ita kullum da irin gyaran da akeyi mata hakan yasa tsoro ya kamata tana kuka taje har shago take gaya masa kodai an kusa bikin ne ba a gaya musu ba, gashi yaki zuwa wanda aka batan, daurewa kawai Omar yay ya rarrashe ta dukda tashin hankali dayake ciki don tuni ya fara sarewa a lamarin, a lokacin kuma Allah ya kawo Eshan, shima kuma maganar biki ce ta kawoshi zasuyi, saida baban nasu ya kaishi dakin sa tukunna yaje yawa Zainab din magana cewar angon ta na jiranta a dakin sa ya wuce masallaci abinsa, jikin Zainab har bari yake ta zura hijab ko takalmi babu ta nufi shagon Omar ta shaida masa yau Allah ya kawo mara mutum cin nan yata ho suje suyi masa tass in ta kama harda duka ya dake shima don ya fasa auren ta 😂 taketa rattafa masa zance, shima jiki na bari ya rufe shago suka tafi Omar ya tanaji cin mutum ci kala kala dazeyi masa dama sauri suke kamar saci da baka ko sallama basuyi ba suka afka dakin tun abakin kofar dakin dama Omar ya rike mata hannu, hakan ne yasa ta soma kiciniyar kwace hannun ta don kada bakon yagani yace mata 'yar iska, sam bata kula da waye zaune gaban su, Omar kuwa mutuwar tsaye yayi ganin yayan aminin nashi dayay cikin muryan kuka yace.

    " Yaya! Kaine dama zaka auri Zainab, kaine zaka aure min farin cikin rayuwa ta" 

  Ay tanajin furucin Omar din tai azamar dagowa suka hada idanu hakan yasa ta kurma wani ihu gamida dafe kirji tamkar taga masifa cikin rudu tace." Wai kaine dama wanda baba ya bani?" Tuni hawaye ya fara sunturi a fuskan Omar jikin sa ya matukar yin sanyi be taba tsamma nin ganin yayan aminin shiba yana matukar jin nauyin Esmaeel baze iya cin zarafin yayan saba, batare da bata lokaci ba yay waje ay da gudu itama Zainab ta bishi, Eshan dai yana zaune kallon su kawai yake tana isa zaure sukai kicibus da yayan ta Haseen yana watsa mata wani irin kallo dan yaga fitar Omar yanzun cikin tsawa yace.

  " Gidan uwar wa zaki! Ba bako kikayi bah? shine zaki fito kibi Omar saboda baki da hankali bikin ki saura sati biyu kinki dena shashan ci!" 

   " Nashiga ukuna na lalace!! Wai yanzun Yaya Haseen aure zakuyi min dagaske so kuke ku rabani da Omar dina, don Allah yaya Haseen kada kuyi mana haka" tana cikin magiyan ne taji saukar maruka a fuskan ta batabi takan wanda ya mare taba ta zube anan ta fara tumami tana kuka tsawar da baban su ya daka mata ne yasata mikewa ba shiri ya kama kunnen ta yamata gargadi me kyau gamida murde kunnen, duk da haka batayi shiru ba takoma dakin baban nata, kome sukeyi yanajin su harta shigo ta tsugunna a gaban sa kanta yana kasa tanata kuka me ban tausayi ganin baida niyyar ce mata kala ne tace.

  " Don Allah ina neman agaji a gare ka kate maki rayuwa ta da zuciya ta kada ka aure ni, ni bana sonka bana kaunar ka ko ganin ka bason yi, ka hakura da wan nan auren cutar dani zakayi, indai kana sona to kada ka aure ni Don Allah!" 

  Tana maganar tana jan ajiyan zuciya saboda kuka ido kawai ya zuba mata duk da kalaman ta sun sosa masa zuciya  baiji digon santa ya ragu a zuciyan sa ba sema linkuwa daya keyi, cikin sanyin voice dinsa me dadin sauraro ya ambaci suna ta.

  " Zainab" 

  Sosai taji faduwan gaba jin muryan sa datayi, " Shin Zainab meyasa bakya son ganina? Na taba yi miki wani abu ne?" Cikin tsiwa ta dago tasoma ce masa." Duk wanda ze rabani da Omar dina to makiyi na ne shi na har abada ma kuwa don haka ni ko ganin ka banason yi" mamaki ne ya kama sa ganin lamarin nata da gaske take yi yasashi yin ajiyan zuciya yace.

   " Yanzu idan na fasa auren ki bakya tunanin irin fushin da iyayen ki zasuyi dake? Kuma hakan zesa ki fuskan ci fushin ubangiji, mezesa bazakiyi musu biyayya ba ku rabu lpy, itafa rayuwar nan ba komai ne da mutun yaso yake samuba zata yiwo wanda kika kwalla fa ran akansa ba alheri bane a gareki, meyasa bazaki dauki kaddara ba, san nan ni da me Omar yafini dabaki kauna ta haka? Duk wata soyayya dayake miki ni idan na aure ki zan miki soyayyar da zata mantar dake wani Omar" 

  Jin wan nan furucin nashi datai na karshe ne yasa dariya kwace mata tana darawa tana hawaye bakin ciki biyu ga dariya, dariya tata ce yasa  Eshan sakin baki yana kallon baiwar kyau a gurin nan malam seyaga ashe shi ba komai ya ganiba, seda tagama dariya tukunna tace." Kaine ka faramin irin wan nan tatsuniya ta zan manta da Omar dina shiyasa ka bani dariya, sam bakason matsayin sa a gareni ba koh?" Saurin katse ta yayi da cewa." Shikenan yanzu dai aure ne bakya so Koh" cikin sauri ta daga masa kai tana sharar kwallah,

   " Good! To yanzu abinda nakeso dake, kinga biki saura 2weeks kuma iyayen ki sun gama shirin biki idan aka fasa zaki ja musu asara ransu kuma ze baci ga duka dole nasan zasu dakeki, ki kalli ma yadda kikasa sukawa face din nan taki kamar ni suke mari haka nakeji, saboda hakan ki bari ayi auren daga baya se musan abinyi ki dawo gidan, a lokacin babu mejin haushin ki don kin dawo gida, amma yanzu ina fasawa auren naki kinsan wani ma zuwa zeyi ayi auren dashi bakuma ze dawo dake gida ba kinga gara ni kenan" 

   Shiru kawai Zainab tayi tana tunani wanda ga mamakin sa kuwa se gani yayi tana murmushi zama tayi a gaban nashi tana kara matso shi tana cewa." Amma naji dadin shawarar kan nan, kuma yanzu na yarda kana sona tunda zaka temakeni, amma kayi min alkawari zaka maidoni gidan?" Murmushi yake yana kara kokarin danne dariyar sa Tabbas ya yarda kam yanzu Zainab bata da wayau rashin wayan ma nata har yay yawa, kallon ta yay dakyau san nan yace." In Sha ALLAH meze hana na kawoki gida indai kika bada hadin kai abu ya tafi yadda akeso" 

   " Wlh zanyi kome nene indai zan dawo na auri Omar dina zanyi komeye kace" 

   Wan nan karon kasa rike dariyar sa yayi seda yadan dara tukunna yace." To yanzu dai kada ki nuna bakisan auren nan kada su baba su cigaba da dukan ki banason hakan kalli yadda suka mayar miki da fuska" yana maganar yana kokarin kai hannu ze shafi kumatu ta dayay ja na marin da tasha, saurin kautar da fuskan ta tayi tana pouting din bakin ta, maida hannun sa yay yana shafar suman kansa yana sakin wani killer smile yace." Dama zuwa nayi akan maganar bikin abubuwan da kike bukata zaki sanar dani" 

  " Cikin shagwaba tace." Babu abinda nake bukata ni burina kawai shine ayi auren na dawo gidan mu" 

   Yana mikewa ya aje mata kudade masu yawa har suka so bata tsoro, tace, duk wan nan kudin na meye?" 

   " Naki ne na hidimar biki" 

" Toni waca irin hidima zanyi wai? Ni banason kudin ka ka tafi da abinka" 

  Tsugunno wa yay saitin ta yace." Ok bakya jin magana ko! Kin manta plans dinmu ne ko gidan ne bakyason dawowa?" 

  Da hanzarin ta ta kwashe kudin harda godiya shikuwa yana kunshe dariya ya tafi ko rakiya yasan beze samu ba shiyasa ma yawa su Ummah sallama kawai ya tafi zuciyan sa kal da farin ciki ✍️