4
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode four
A ranar seda Zainab ta gayawa Omar duk yadda sukayi yana gida ta sameshi a kwance ba lpy, abu nata matsawa har an kawo mata lefen ta wanda kana gani kasan na masu dashi ne zainabu nata shan gyara ita dai kallon su kawai take har aka fara shagali zuwa ranar daurin aure dun bin al ummah ta shaida, ana fara bikin dama Omar yabar garin yay kuka harya gode Allah hakan ne yasa hankali zainabu tashi bataga Omar din taba gashi ana shirin kaita gun miji kuka ihu an shashi, ba a sanin ma ta balle ta tafi neman Omar sedai aka mota kamar tabab ba ta koma dakyar Hashmat ta rarrashe ta, tai shiru ganin yayan ta na shirin casata Omar kuwa yasha kira yana kan shama, haka aka gama biki duk da suna fuskan tar kalu bale daga dangin su Eshan din sunada ji dakai sosai ga sharia gamida raini don sunga sun fisu, Esmaeel ne kawai yashiga cikin su akaita kujiba kujiba kasance war sun saba dama ta dalilin Omar, sam beyi mamaki ba na rashin ganin Omar din dayay yasan za a rina haka dama yana kuma kara tausayin yayan nashi don zama da wanda baya son ka ai se dole, tunanin Omar din kawai yake yanajin babu dadi rabashi da akai da masoyiyar sa, da nasihohi da fada gami da jan ido aka saka zeetah a mota akai gidan su Eshan da ita suma nashi iyayen suka mata nasu nasihohi gami da zaga gidan da ita family su ganta, tayi kuka Zainab kamar hawayen ta ze kare duka 'yan uwan nata sun tafi don gujewa wulakan cinsu se Hashmat kawai data zauna don debe mata kewa zasu kwana tare, a washe gari kuma ango ya tafi da amaryar sa kano inda yake karatu Sosai Hashmat ke tausar zuciyan Zainab tana nunar mata yadda auren yake, haka yasa zuciyan ta kara karaya,
Gidan su ya tsaru matuka kayan more rayuwa yaji wanda zainab duka basa gaban kaman tana kan kaya haka takeji koda wasa ta kasa dena tunanin Omar din ta tana tunanin yanzu yana ina ko me yakeyi, ganin bashi da niyyar maida ta gidane yasa ta sawoshi a gaba tana tambayar sa yaushe ne ze maida ta gida ne itafa bazata iya zama dashi ba, cikin zumudin sa yana murmushi mugun ta yace.
" Meze hana idan kinason zuwa zaki idan kin bada hadin kai, but bana tunanin ma zaki iya" da saurin ta tace." Wlh zan iya indai zan koma gida" seda ya kare mata kallon da ako yaushe yake mata shi yana sa zuciyan ta na tsinkewa, sauke ajiyan zuciya yayi Gami Da cewa." Hanya daya ce kawai dazaki gida shine idan kin haihu" cikin firgice ta dafe kirjin ta dayake tsananin buga wa tace." Nashiga ukuna yanzu nice zan haihu!"
" Kwarai kuwa itace kadai mafita dazaki gida batare da kananun magan ganun komai bah" kan zeetah a kasa tana hawaye jin abinda ya girme ta cikin muryan kuka tace dashi." Ni tsoron haihuwa nakeji, idan na haihu mutuwa zanyi!!" Ta karashe maganar tana kokarin hadiye kukan dake shirin kwace mata saboda dawowa kusa da itan da Eshan yay hartana jin fitar numfashin sa sosai ya shiga lallabata." Waya gaya miki haka? Mu iyayen mu da suka haife mu mutuwa sukayi? Kema ba mutuwa zakiyi ba sema kiga dan baby dinki me kyau, ko bakyason kiga danki naki na kanki kiyi yacca kike so da kayan ki?"
Shiru Zainab tayi don tana magana kuka zata saka gaba daya ta gama karaya da wan nan lamarin nashi mussam man dataji yasoma lashe mata neck da gefen face din ta tsoro sosai ya kamata tana tunanin kodai maye ne mussam man irin kallon da yake mata sosai zuciyan ta ke raya mata maye Allah ya hadata dashi 😂 ni kuwa nace akwai sauran maita a gaba kuwa, lallaba ta yay tayi yana mata dadin baki harta aminta, a wan nan dare suka raya shi Eshan ba tausayi a lamarin sa sam baya duba kan kantar Zainab baje mata aiki yay iya aiki, ita kuwa tayi nadama ba 'yar kadan ba da dana sani harda cizon yatsa dama Zainab ga raki, tasha kyautut tuka babu iyaka har tasoma masa kallon almu bazzari gashi dagashi har kyau tar tashi ba kaunar sasu a idon ta take ba ita dai Allah Allah take tabar wan nan gidan tunda ta dan dano masa kuma Zainab ta shige uku a haka suka cigaba da rayuwa baya ko raga mata don yana mata dadin bakin ay ta kusa samun ciki kukan ta da kiran sunan Omar har seda yama saba dajin su a cikin kunnen sa har tama saba idan yazo mata da bukatar sa batajin tsoro suna cikin wan nan zaman Allah ya bada ciki amma sam yaki gaya mata don baya son ya dena hutawa da matar sa gashi cikin bame laulayi bane sosai sam bata gane ba mara wayan seda cikin ya soma fitowa tukunna ya girma ta gane da kanta hakan yasa ta dau zafi dashi sosai na rashin gaya mata din da yayi yanata more mata jiki, sosai ta birkice mishi ta dole ya hakura da ita, ganin be iya jurar wan nan ba ya kuma suburbuda mata karya kan cewa indai basa tarawa cikin zube wa zeyi ko kuma ta haife shi babu rai ko ba lafiya irin hakane da an haife da seya koma don haka tayi hakuri ta jure waccar wahalan ma bare dan wan nan yasa ta kuma zaman haihuwa ta biyu,
Zainab sarkin marasa wayau tuni ta amince masa ana buga harka harta shiga watan haihuwa Eshan ya kasa hakuri ya raga mata seda yaga dai zama dakyar tashi dakyar irin wahalan da takeyi 'yar karama da ita, hakan yasa tausayin ta kamashi, time din da akazo haihuwa kuwa ansha kwakwazo har seda Eshan ya mata kuka Omar yasha kira tana cewa.
" Omar idan nasame ka nasha wahala saboda kai inata cin azaba kazo ka temaki rayuwa ta zan mutu!!"
Da haka dai ta santalo san talelen danta Masha Allah kyau kamar ta tashi ya maye, farin ciki gurin Eshan ya rasa inda ze tsoma rayuwar sa zainab ta bashi mamaki haifa masa da datayi dukda kan kantar shekarun ta bata gaza ba, sosai kimar ta da darajar ta suka karu gurin sa da kuma iyayen sa ba karamin farin ciki da godiya ga Allah sukayi ba gami da mamaki na haihuwar ta, garin shanono fa nan ma ya dauka da surutu zeetah daga aure se haihuwa dama tanason auren gul mane irin nata, time din da Omar ya samu labari yay matukar bakin ciki da kuka mara iyaka ya kuma gama tabbatar da zainab ta masa nisa, dama abinda suka tsara ne shida ita koda anyi auren kada ta zauna ta fito suyi auren su yanzu kuma yaji zance yasha ban bam, iyayen zainab sunyi farin ciki suma da mamakin haihuwa ta mussam man mahaifiyar ta ita da tasan wacece 'yar ta gurin raki da tsoro, hakan yasa ta jinjina wa 'yar tata gami da sa mata albarka haka yayar ta Hashmat,
Zainab tafi kowa farin ciki zatabar wan nan gidan daya zame mata tamkar kurkuku, farin ciki duka ya mantar da ita wahalan data sha saboda zata gida taga Omar dinta, dama duk Sanda Esmaeel ya kawo musu ziyara haka zata tasa shi gaba ta ringa tambayar sa Omar din ta sosai abin yake bashi mamaki yacca take maganar Omar a gaban yayan nashi kuma bata kobi takan ta ma, dama da Esmaeel din ne kawai suka saba koda zuwa sukayi mutan gidan nasu daga gaisuwa shikenan sesu Emaan nema suka saba shima sama sama don bata shiga sabgar su ganin yadda suke da dagawa, Saboda hakan ne yasa 'yan uwansa suke ce mata me girman kai, mussam man Eshaal datake aure anan kano din itama basa jituwa da zainab ko kadan don batada kirki duk sanda tazo gidan nasu Zainab a takure take harta tafi,
Koda suka tafi shanono gidan su yay birki da ita ace warsa se bayan suna tukunna zata gidan nasu kome yace bata masa musu fatan ta dai be wuce su rabu lpy bah, Baby boy din ta na ganin gata don duk wanda ze ganshi seya shiga ran mutum Sosai kowa na rubibin dauka itama taita mamakin wai itace ta haife da haka har ake rubibin dauka, ba karamin sake jiki tayi bah ganin mutan gidan nasu itama suna zuwa ganin ta, kamar yadda ta roke shi alfarmar yasaka wa yaron ta sunan masoyin ta, ranar suna da yaci sunan nashi kuwa Omar farouk, duka ya mata haka ne saboda ya sanyaya mata ta nan gurin tana bashi tausayi sosai ganin taki hakura da Omar har yanzu har fargaba yake don yasan ya hada wa kansa rigima akwai kura, ita kuwa farin ciki isar ta yayi sunan Omar din daya sawa dan ta harda masa godiya dashi albarka kamar babar shi 😂, tun daga nan take kiran Omar din nata da sweetheart tana matukar kaunar sa matuka kamar zata lashe masa...🤪, Koda aka tafi da ita gida wanka baki kamar ze yage zuwan ta da kwana biyu ne taji Omar shiru be zoba ta fake ido tai waje kai tsaye ta wuce har gidan su Omar, sam barka kuwa ta samesu dukansu a tsakar gida shida iyayen nasa da kan warsa fadimatu,
Duka tsayawa sukayi suna kallon ta ita kuwa masoyin nata take kallo tana farin ciki, cikin sake masa murmushi ta karasa gunsa ta zauna kusa da shi tana gaishe su, cikin mamaki umman tashi tace." Zainab lafiya nagan ki haka ko takal mi babu ina dan kika barsa, murmushin ta ta kara fadada wa tace." Sweetheart dina yana gida ummah ta goye shi nima fitowa nayi ba a sani ba" suduka suka dauki sallal lami tana me kara tambayar ta, " To meya fito dake yanzu ba a saniba?" Kallon Omar tayi daya kafeta da idanun sa tace." Dama gurin Omar dina nazo fa najishi shiru tunda na dawo bai zoba guna, shine nazo inji lafiya yake kuwa?" Bil hakki zainab take maganar ta harda shan kunun ta nakin zuwan da yay, Abban nasu ne dake gefe zaune yana watsa wa kaji hatsi yace." To in banda abinki zainabu me Omar ze miki yanzu harda zezo gunki, ai sedai kawai ku gaisa yanzu a duk sanda kuka gamu"
Batasan sanda tasaki kuka ba Zainab tana cewa." Shikenan yanzun daga yin wan nan kaddarar ren auren zaku rabani da masoyi na, duk da nadawo dinma bazaku barmu a tare bah saboda shifa na dawo kuma ba komawa zan ba" cikin sallal lami maman tasu ke cewa." Yanzu nan Zainab kinyi aure har kin haihu amma kinki yin hankali, shin yaushe shirmen nan naki ze kare ne? Kinki cire Omaru a ranki har kina maganar kashe auren ki, to wlh bazata sabuba bada muba za ayi wan nan aikin na rashin kan gado, ahir dinki kada na kumajin ma kince bazaki koma dakin mijin kiba, daga zuwa gida wanka kuma saboda shirme irin naki, kawo yanzu ya kamata ki cire Omaru a rayuwar ki haka, ki tsaida zuciyan ki guri daya kiyi rayuwar auren ki cikin salama"
Cikin tashin hankali Zainab take cewa " Wlh mama bazan iya hakura da shiba shi kadai ne farin ciki na na riga nagama zama a gidan yaya shima ya sani babu ruwana dashi yanzu, ni gurin Omar dina na dawo" tana kuka tana maganar kamar tababba, tom maman su ganin abinna Zainab da gaske take yasa ta tura fadima ta kira umman ta, cikin kukan ne ta kalli Omar din tana cewa." Wai shin bazaka min magana ba tunda na zauna kallo na kawai kake kaki kulani ko yanzu ka dena so nane? Kayi min magana don Allah, sam bakason irin wahalan dana shaba akan ka duk dan na dawo gare amma shine zaka min shiru haka! Kace min wani abu don Allah konaji sanyi" haryanzu kallon ta kawai Omar yake hawaye na shirin sauko masa ganin ya mata shirun ne yasata kamo masa hannu ta rike, a time din kuma umman tata ta shigo kamar ze fashe da kuka Omar ya kwace hannun sa ya tafi dakin sa hawaye masu zafi na sauko masa ko kalma daya besan meze iya furta mata ba a yadda yakejin zuciyan sa Tabbas a kalaman ta duka ya fahimta ta yadda Eshan yabida zainab din tashi, salatai kawai umman keyi tana cewa.
" Yau naga ta kaina ni shin ke waca iri ce Zainab Allah ya yoki ne? Yanzu waya baki izinin fitowa waje, ay nazaci kinyi hankali Zainab ashe ba haka bane!" Duka furucin da tayi seda maman nasu ta gaya wa umman don ta kwakwafe ta akan ta zauna gidan auren ta, kasa magana tayi don takaici batasan sanda taje ta rufe zainab da duka ba baiwar Allah, da kyar aka kwace ta suka tafi gida tanata kuka, haka shima Omar ke nashi kukan a daki don duk yanajin komai jiyake kamar yaje ya dauke ta su gudu gaba daya su tafi inda baza a kara ganin suba, ai suna komawa gida umman tasa aka kira abban su ta gaya masa duka abinda Zainab din tayi, ranshi yay matukar baci ya kuwa ce baza tayi zaman wankan ba, tayi a dakin ta tunda batada hankali, takanas ya tura Haseen yaje ya kira wo masa Eshan suka taho tare, sedai a yadda yaga zainab dinne ta matukar bashi tausayi yasan duka shine silar faruwar komai suna shiga ta ganshi kuwa tayo kanshi cikin matsanan cin kuka tana cewa.
" Yawwa Yaya ka fada musu gaskiya kosa yadda dani, sunce sena koma gidan ka bayan ba haka mukayi dakai ba! Kayi musu bayanin ni bazan kara komawa gida...pauuu!! Taji Abban nasu ya kuma sauke mata mari yana cema Eshan din." Sedai kayi ta hakuri da zainabu takiyin hankali a yau din nan zaka dauke ta ku tafi tunda batta mutumci!" Cikin marairai ce fuska yace." Don Allah baba kayi hakuri ka batta ta gama wankan nine nayi mata alkawarin zuwan ta gidan ba laifin ta bane" ko kadan yaki sauraren sa ya dage seya dauke matar sa sun tafi, da kyar ya shawo kansa yace su bari se gobe yazo su tafi gidan, Zainab kallon sa kawai take cike da mamaki tana kuka, haka ya tafi jikin sa a mugun sabule tausayin ta na kara kamashi se a yanzu ne yake nadamar biye mata din dayay akan zuwan ta gida....✍️