🧑‍🍼 RABO...❣️

5

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode five 

Zainab tayi kuka har hawayen ta sun kare seda dare umman nasu ta sata a gaba tanai mata nasihohi masu ratsa zuciya akan tabi mijin ta sauda kafa domin samun aljannar ta karta bari so ya rufe mata idanu ta cuci rayuwar ta don haka ta nutsu ta kama kanta, cikin kukan ne ta fadawa umman duka yadda sukayi Eshan din, cikeda mamaki Ummah tace." Ai dama biye miki kawai yake domin, kema in banda yau darar kanki da kike taya Eshan ze sakeki akan Omar? Laifin sane ma daya biye miki tun farko, ke kuma dayake sakarai ce se kika aminta, to bari kiji zaman aure keda Eshan Yanzu kuka fara shi don haka kicire Omar a tsarin rayuwar ki yanzu kisan kuma me kikeyi" 

   Cikin kuka zainab tace." Yanzu kenan karya yake min kullum yay ta moremin jikina!" Cikin sallallami umman tace." Anya kuwa zainab kina son gamawa da duniya lpy? Yanzu seyay miki karyar kenan kike yadda dashi koh! Haba ashe duka kaifin naki ne, ke kika jawa kanki! Wlh idan kinason dacewa duniya da lahira to kibi mijin kina da ilimin addini kinsan hakkin mijin ki akan ki base na sake nana ta miki ba, in kina ganin hakan wasa ne keda Allah"

   Tunda Zainab take bata taba jin tsanar Eshan ta mamaye mata zuciya ba irin ranar tsana takin kara wa makuwa saboda raina mata hankalin dayay kuma ya mata karya, sun kusa raba dare umman tanai mata nasihohi sosai kana suka kwanta, washe gari kuwa tunda Eshan yazo zainab inuwar sama taki kalla tunda ta gaishe dashi kanta a sunkuye bata kuma cewa kala ba, kuma daman yasan za a rina haka, haka sukayi musu sallama suka tafi gidan Hashmat don yi mata sallama, itama anan tagaya mata komai tana kuka abin tausayi, haka yayar tata kamar zatayi mata kuka tace." Ay dama zeetah in banda abinki yaudarar kanki kawai kike" " to yaya Hashmat meyasa zeyi min karya ya raina min hankali wanda kuma hakan yasa na tsane shi fiye da komai a duniya na tsani makarya ci a rayuwa ta" tabbas Hashmat tun daga nan tasan akwai matsala saboda tasan yadda zuciyan kaniwan tata take lallaba tayi tayi ita dayi mata nata nasiho har suka fito suka same shi a mota Hashmat tana tausayin sa suka tafi gida daman babu abinda ya gaya wa 'yan gidan nasu dan gane da abinda yake faruwa, kawai dai ya sanar dasu baze iya barin ta anan bane ya tafi shi kadai, Esmaeel yana ganin yanayin na Zainab yasan ba lafiya bah koma dai meye yasan baya wuce akan Omar ne, suma sallamar sukai musu suka wuce kano,

   Tun daga wan nan rana zainab taki kula Eshan koda inda yake bata kalla duk kuwa irin magiyan da yake mata indai kaga murmushin ta to tana tare da Omar farouk sweetheart dinta tana masa wasa, gaba daya wata soyayyar ta ta dora ta akan wan nan dan nata wan kan jegon ta kuwa daga shanono din aka kawo mata me wanka tana kulawa da ita, Eshan har seda ya fara mata kuka akan tayi hakuri yasan bai kyauta ba amma baze kara ba, to se a wan nan lokacin ne Zainab tayi masa martani tana kuka tace.

    " Meyasa zaka raina min hankali haka, kayi amfani da yarin tata kayi abinda ranka yakeso, to me kuma zaka cemin yanzu? Kayi min karya abin kunya da girman ka kana irin wan nan karyan, hakan yasa na tsane ka a yanzu ko ganin ka banason yi kaine sanadin da aka rabani da masoyi na kana da son kanka dayawa taya zanga farin ka kuwa? kome kayi min kuma kaje don kan ka!" 

   Eshan rintse idanun sa yayi zuciyan sa na masa kuna yayi nadamar yi mata magana da yasan maganar da zata furta kenan da be barta ta furta ba, gara suyi ta zama a haka, kuma yana kara tabbatar wa kan sa yayi matukar kuskuren bida ida ta hakan, har mamakin zuciyan ta yake yadda ta rufe ido ta ci masa mutumci son ranta, a haka suka cigaba da rayuwa dattijuwar matan dake mata wanka ne take kara tausar zuciyan ta kullum don taga irin zaman da sukeyi a gidan nasu har sukayi arba in ta hada i nata i nata ta tafi hakan yasa rashin jin dadin ta zainab ya karu, shi kuwa Eshan damuwa ta taru tayi masa yawa babu kwanciyan hankali nan danan ya rame yay duhu ko a karatun sama dena fahimta yay sosai, a time din kuma mahaifin sa ya mallaka masa company na sarrafa abubuwan more rayuwa bags shoes daya gina anan KANO din abin seya kara masa yawa ga tension na gida dana company, ciwo kuwa ya kamashi wata rana ya dawo daga skull iya kacin sa parlour ya yanke jiki ya fadi, Zainab tai matukar kidimewa tana barza uban kuka ta lalubi number din doctor dinsu dake dubasu ta kirashi yazo suka tarkata sukai hospital, bawan Allah har hawan jini ya kamashi, ba karamin tashin hankali iyayen sa suka shiga ba dasuka sami labari mussam man da suka zo suka ga yadda dan nasu ya koma, mahaifiyar sa harda masa kuka, ita kuwa Zainab ta wani irin rakube abinka da mara gaskiya se hawayen take itama, su umman ta na samun labari suka tafi suma suka dubo shi, suka dawo gida aka bar mata ummah don taci alwashin cin uban Zainab la ada waje, 

   Suna zuwa gida kuwa ta tsare ta seda ta gaya mata irin zaman da sukeyi ita da mijin nata, ay kuwa ta kulle daki tai mata dukan tsiya tai mata laga2 cikin kuka tace ummah ke rokon ta." Na rokeki Zainab kada ki kashe musu da ki jawa kanki tsiniwa da zagi! Ki rufa mana asiri ki sauya halin ki, duka cikin 'ya'ya na kece Allah yayo daban, ace ke bazaki dauki kaddara ba! Anya kina neman rahmar Allah kuwa?" 

   Sosai zuciyan Zainab ta kara karaya ganin umman tata na kuka, cikin kukan ne itama take cewa." Ummah don Allah kiyi hakuri wlh na dena in Sha ALLAH bazan sake ba nayi miki alkawari zanyi masa komai, ki dena kuka Ummah Allah na tuba, zan nemi gafarar mijina ya yafe min" sosai umman taji dadin wan nan maganar tata tace." To Allah yasa Zainab zan dage dayi miki Addu'ah don kinyi nisa" 

   Hakan data fada din kuma ya kasance Zainab ta nemi gafarar mijin ta tana masa ladabi yadda ya dace idan ze neme ta ko sai nawa ne a rana bata gazawa sedai shi kadai yake kidan sa yake rawar sa shi kadai yake sha anin sa don bata tayashi nan danan ya soma murmure wa duk da ba wata hira dake shiga tsakanin su sosai indai kaji dariyar ta da kara dinta to tana tare da sweetheart dinta in suna tare da Eshan kam kamar ruwa ya cinye ta ganin abin nata bana kare bane kullum akan bed shi kadai yake aiki yasa seya soma siyo mata abubuwa nasa feeling sosai batare da ta sani ba wataran har a abin sha yake karmatsa mata Zainab babu wayau ta kasa ganewa tadai ga nata canjin kwana biyu don in da abinda yafi mar tani ma tana maida masa jin dadin sa kawai yake idan yana son ganin fara ar tane to seya faran tawa sweetheart din ta yay dariya shine zesa kuwa taita yage masa baki wan nan dalilin ne yasa dayaga ta soma sakewa dashi, wata rana suna zaune yake gaya mata ay mahaifin sa ya bashi company tunda yaga ya fara tara iyali gara ya rike business domin kula da iyalan sa, murmushi kawai Zainab tayi tace.

   " Allah ya sa alkhairi ya tsare yasa an bude a sa a, Allah kuma ya baka ikon kulawa damu" murmushin jin dadi yayi don sosai yaji dadin kalamin ta kusa da ita ya kara zama ya amsa Omar cikin sanyin murya ya kira sunan ta hakan yasa ta dago tana kallon sa itama seda ya sauke ajiyan zuciya tukunna yace.

   " Please Zainab ina neman alfarmar ki soni ko yaya ne a zuciyan ki ina son ki samanin matsuguni kome kikai ban taba daukar sa a matsayin laifi, saboda ina matukar kaunar ki Zainab sonki baze iya fita a zuciya ta ba seran da na dena numfashi, kullum sonki karuwa yakeyi a zuciya ta ko yaya ne ya kamata kiyi min adalci ki soni ko yaya ne" sosai Zainab taji tausayin sa kuma duk da hakan be hanata furta masa." Har yanzu ban taba jin sonka a zuciya taba... Zata kuma magana ne kawai ya toshe mata baki don baya kaunar sake jin irin wan nan furucin Omar kawai ya aje mata ya koma dakin sa,

   A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka saka sweetheart dinta a school shakuwa me tsanani ce ta shiga tsakanin sa da iyayen nasa mussam man Ammin tashi yadda suka shaku da kyakkyawan fahimta juna kamar ba uwa da daba Zainab bata kuma haihuwa ba tun daga kansa hakan yasa son duniya ta dorawa Dan nata koda rashin lpy yake haka zata sashi gaba tana kuka,tun tasowar Omar yasoma sanin rayuwar aure ya fahimta akwai gyara a zaman takewar auren na iyayen sa basa nuna wa juna kauna irin ta masoya ibadar kawai akeyi na zaman aure a wan nan lokaci ne kuma Allah ya nufe shi da zama dan majalisan tarayya murna gurin 'yan uwa da abokan azziki ba a magana se tururuwar zuwa taya murna ake hajiya zeetah kuwa an zama manya girma ya karu an kara hawa sama ta kuma murje wa abinta sam babu wanda zece itace ta haife Omar kamar budurwa hutu iya hutu ta sameshi ga kuma kyan jiki da Allah ya bata ga shagwaba halin ta daya gama bi mata jinin jikin ta, duk da irin wan nan matsayin datake ganin ta taka hakan besa ta mance da Omar din taba yana zuciyan ta tana tunanin sa ko yana ina a wani hali yake, family din Eshan kuma se suka sako sa a gaba seya kara aure saboda sam Zainab taki aminta tabishi gurin aiki idan meeting ne dashi in meye sedai yaje Abuja ya dawo sosai yaso ta bishi Abuja firr takiya, se gida ya siya musu a unguwan nasu wanda yafi wan nan haduwa da tsari,hakan yasa suka takura yay aure ay ba girman sa bane zama da mace daya wan nan dalilin ne yasa Eshan duk wani guri da zashi in ma kasar ze bari tare da Omar yake tafiya, hakan ne yasa Omar tun yana karami yaga duniya ta ganshi komai na kasuwan cin sa gaban dansa yakeyi komai yasani, wan nan dalilin ne yasa duka miskilan lan cin uban sa ya dauke sa baya son magana sosai seda shakikan sa wato iyayen sa ko kuma abokin karatun sa Farid sun shaku matuka karatu tun suna 'yan dagwai2 suka kulla abota, sam kuma be taso da son bin kyale kyalen 'yan mata ba duba da yadda yaga halin daddy nasa duk da dai ance kowa da irin nashi hali, to shima dai Omar be tashi dason yin soyayya ba don besan taba bema san yadda ake yintaba sedai ta tsakanin iyaye da Da, yana shekara ta 19 kaddarar su ta samesu na hatsarin Eshan dayay akan hanyar sa ta zuwa shanono har masu tsaron sa babu abinda yay rai a cikin su an kuwa shiga tashin hankali mara misaltuwa mahaifin sa kamar zeyi hauka, haka Zainab tayi kuka tayi kukan ta gode Allah ita abinda yafi tsaya mata arai shine, har ya bar duniya Eshan bashi da burin daya wuce Zainab ta furta masa kalmar so koda sau daya ne, kuma bata taba furta wa ba hakan ba karamin tsaya mata yay ba tana kumajin babu dadi, Omar kam har seda aka ringa masa rubutu gurin malamai tukunna yasoma dawowa dai dai ba karamin dukan sa mutuwar taiba, ya kara komawa so silent sosai, kuma kakan sa wato inuwa mu'az shanono, yadora sa kan duka wani harka businesses na mahaifin sa  ya dora daga inda aka tsaya tunda shine magaji kuma yasan komai, tun yanajin far gaba akan lamarin harya soma sabawa, duba da kan kantar Omar a harkar business dinne yasa inuwa mu'az kara masu tsoron sa domin kare lafiyan sa saboda ba karamin surutu Omar kesha ba akan ragamar company da aka sakar masa shi kadai har a gidan masu tsaro sosai inuwa mu'az yasaka na mussam man domin tsaron dan lelen jikan nasa da kuma sarakuwar sa Zainab, tunda Eshan ya rasu ta kasa tan tance yanayin da take ciki na happy or sad, gata nan ne dai har ta gama takaba!!

         CIGABAN LABARI...✍️