🧑‍🍼 RABO...❣️

6

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB


Episode six 

A yau ta kama ranar zagayo war haihuwar Omar ya cika shekara 20 cif cif, Zainab ta tara jama a naban mamaki domin taya tilon dan nata murna, manyan mutane sun halacci wan nan taron da family da abokan azziki, gidan Eshan an masa gyara yasha kyale kyale tamkar shugaban kasane ze zauna gurin se hada hada akeyi Omar kuwa tsaya wa fadin haduwan dayay bata lokaci ne duk inda ya gitta se yaja idanun al ummah yasha black suit se sheki take bare kuma uwar gayyar Zainab tasha wani Blue lafaya me matukar kyau da ado zam ta dawo Indiana kamar Prinyanka Chopra, kana kallon face din sa zakasan baya wal wala dukda al ummar data taru saboda shi, kuma ba komai ya dame shiba se mutuwar mahaifin sa wan ne taron farko dazeyi ba tare da mahaifin nasa ba videos iri iri ake sha gurin taron nan ta hotuna  'yan gidan talabijin inji bahaushe 😂 sune kala kala suke zaga gurin koda yazo yanka cake babu kuzari a jikin sa kowani time tare suke yanka cake shida abban shi, Zainab din ce ta rike masa hannun suka yanka cake ta hanga me baki tana jira ya saka mata, hakan yasa shi yin murmushi ya juya akalar sa yaba wa kanin mahaifin sa Esmaeel, tunawa da halin Ammin tashi dayay ne yasa shi juyowa da sauri ya mika mata cake din ilai kuwa yaga harta kwabe fuska zata fara halin nata ga mutane sun tara, cikin basar wa ta anshi cake din a hannun sa tasa a baki harda lumshe idanu saboda dadin sa seda ta yanko nata cake din ne Tamika masa har seda ya sunkuya ze ansa ta janye hannun ta zuwaga Farid ya anshe cake ya cinye yana ma Omar dariya ta lakuta cream ta goga masa a goshi tana murmushi me sauti ganin yana hararar Farid, lakuta yay shima kamar ze gogawa Farid din Zainab seji tayi ya shafe mata shi a kumatu ai kuwa ta la kuto daya wa ganin hakan ne yasa shi buya bayan Esmaeel yana murmushi, seta zagayo tanan seya zaga ta can harta gaji Esmaeel nata mata dariya yace.

   " To auntie ki hakura mana ramawa fa yayi!" Cikin tura baki gaba ta kwaba masa shi a fuska anata musu dariya, umman ta tace." OH ni naga sanda Zainab zata girma kalli yadda taiwa fuskan Esmaeel" Hashmat dake gefen ta tace." Ki barta ai ga matar sa na gani tsaf zata shigar masa kinsani, dole a ringa cewa ba ita ta haife Omar ba" haka suka cigaba da gudanar da taron su kowa yaci 🍰 me azaban dadi ga kuma ice creams kala kala da snacks se wanda mutum ya zaba, ya sami kyautut tuka dayawa Omar music nata tashi abokan karatun Omar yadda sukaga shakuwa gurin ta da dan nata abin na matukar burge su yana basu dariya, to bayan tayi wa kowa godiya na halartar sa taron nasu da kuma Addu'ah a karshe jawabin nata ne bewa Omar dadi ba haka mutane ma suka shiga mamaki, Esmaeel sam beyi mamaki ba don kam yasan tsohuwar zuma ce zata motsa, babu shakkar komai tace asanya mata wakan da Omar masoyin ta yake sanya wa a shagon sa wakar India, kusan shigan ma saboda masoyin nata tayi don tasan yanaso, zama tayi har wani kada kai take alamun wakan ya kai mata har ka tana zabga uban smile ita kadai tasan abinda take tunowa, duka wata annurin dake fuskan Omar seda ta dauke, mutane har an fara tsegumi kuwa akan waye kuma masoyin ta ne? 

    Tana daga zaune din ne ta hango yadda Omar yay kicin kicin da fuska   hakan yasa ta dawo wa hayyacin ta heart din ta na wani irin bugu se a yanzu take dana sani furta kalmar datayi, jiki a sanyaye ta mike zata isa gare shi yay azamar tashi ma yabar gurin, kwallah taf a idanun ta ta koma ta zauna tanajin babu dadi, da haka taro ya watse kowa ya tafi da Zainab a baki, koda suka koma cikin gida bayan sum gama sallamar bakin su kin yadda yay su zauna guri daya sosai abin ya dameta gashi da sauran family basu tafiba dole ta kyale shi tukunna, maganar da ake cikin family din har kunnen ta ya dawo saboda maganar da tayi gurin taro, abin duk ya hanata sukuni,

   Se a washe gari ta same shi a parlour din sa yana karatun exam da sukeyi, tunda suka gaisa be kara tanka taba gefen sa ta zauna tana kallon sa nadan wasu minutes tukunna tace.

  " Sweetheart why kake son sani a damuwa ne, akan abinda be taka kara ya karya ba?"

   " Zai karya ne nan gaba, Ammi gaba daya wan nan halin naki na yanzu ya gama bani mamaki, gaba daya na rasa meyake mun dadi, a yanzu har a gaban al ummah kina shaida musu kinada masoyi wayasan meze faru kuma a gaba? Ko kunyar su Abba Esmaeel bakyaji kika fadi magana son ranki, duka wani taro dazamu yi a gidan nan komu halatta sekin bar abin fada, sam bakya damuwa da abinda kikai mana jiya ze iya jawo mana problem Wai waye wan nan masoyin naki? Har da yafi daddy na a gurin ki, wai yanzu aure kike so ki kumayi?" 

  Idanun ta cike da ruwan hawaye tace." Please my son kadena ganin laifi nah, daddy ka shine ya rabani da masoyi na ya aure ni, kayi min adalci mana, laifi ne donna ambaci masoyi na yanzu? Tunda kake baka tabajin na ambace shiba a bakina se yanzu saboda ina daraja mahaifin ka, kome kakeyi yanzu zan maka uzuri don bakason meye soba bakason yadda yake ba, kullum da ita nake tare a zuciya ta"

   " Is good ay, kiyi soyayyar ki nidai ina bayan daddy na duk rintse ni bazan kishi ba duk da baya raye, kuma idon haka son yake kada Allah ya dora min shi har abada" magana zata kuma yi yace." Please Ammi kinga fa ina karatu ne kada na kasa exam dina gobe" bakin ta taja tai shiru tana murmushi ta mike tafice abin ta don tasan baze taba fahimtar taba a yanzu, da idanu ya raka ta yana cike da mamaki na Ammi tashi, tana maganar masoyi yanzu abinda be tabajin ta furta ba tsayin rayuwar su to shikuwa waye wan nan masoyin nata kuma yana ina? Tsaki kawai yaja yana gyara zaman sa yana cewa." Kai mutuwa me tonon silili duk mutuwar daddy ne yasa Ammi ta koma haka, Allah jikan ka da rahama daddy ka mutu ka huta kabar mu da gwagwar maya.

                ABUJA

Unguwan wuse gidan Omar shad, bah gidane wanda kallo daya zaka masa kasan nera na magana a gurin nan, haka shima skin dinsa taji hutu kamar saurayi abinsa don sam be dirka irin mugun kibar nan ba sedai ta hutu daya samu chocolate skin dinsa tanata sheki, duka iyalan nasa sun hallara a parlour suna dinner abinsu  bisa al adar sa indai yana nan akan senter carpet me laushi suke cin abinci, to wan nan karon yana nan ne shiyasa suna kasa basu hau kan dining ba, matar sa daya Maya se ya'yan su biyu mata ta fari itace Fanan se autar su Zainab,auren sa da Maya kuwa hadin iyaye ne sune suka aura masa ita duba da irin kaunar da mayay din ke masa matuka gaya, badon yana soba aka daura masa aure da ita, gata kuma 'yar gidan aminin mahaifin sa, sosai take ji da mijin ta Maya kauna da kulawa babu irin wadda bata masa kamar ta goye shi don tattali badon komai ba se don kada ya kula wasu matan a waje saboda irin zafin kishin da take dashi sau tari ansha rigima da ita mussam man a ma aikatan sa don be isa yay hulda da mata ba tana gani rigima akesha rikak ka, bisa dole kawai yake zaune da Maya batare da ya taba nuna mata ba koda sau daya, haka be taba bata labarin soyayyar dayay a daba, ganin irin kishin da Allah ya mata har Allah ya azurta su da 'ya'ya Fanan itace me shekaru 14 Zainab kuwa shekarun ta 12, Maya tana matukar kaunar autar tata zainab babu wanda ya isa ya taba mata ita ya zauna lpy ta mugun sangar ta Zainab ta lalata ta abinda take so shine takeyi tabara kala kala babu irin wadda batayi a gidan nan, she's so cute masha Allah, kaman ta daya da Omar haka kalan skin din suma daya sedai zata darashi hasken fata kam yadda take lazy haka take da lazy eyes, tom shima Omar indai kaji ban bamin sa to an taba masa sweetheart din tasa zainab, 

    Sabanin Fanan da babu ruwan ta nutsatsi yar yarinya komi nata a nutse takeyi ga hankali da hakuri kome Zainab tayi mata bata biye ta shiyasa baka tabajin kansu suna fada shakuwa ce me karfi a tsakanin su, ita Fanan itace ta biyo maman tasu har hasken fatar, ita kuma Zainab abban ta, wan da wan nan dalilin ne yasa Maya ke kara kaunar autar tata komin ta irin na daddy ta, kowa yanata cin abincin sa ban da ita ta tasasu gaba tanata shagwaba, kamar zatayi kuka tace.

  " Momcy please ku temaka min kun san bazan iya cin komai ba yanzu ice cream kawai nakeso please momcy!" Dama indai tana neman abu haka take kiran maman tasu da momcy tana lallaba ta, cikin rarrashi Omar yace." Haba sweetheart, ki daure mana kici abinci ko yaya, kinaji fa abinda doctor ya fada a kanki sanyi ya fara miki illah, ki hakura da ice cream yau se gobe, kinga se ki ringa 3 days kafin Kisha" kuka kawai Zainab ta fashe dashi ta mike taje ta kwanta kan kujera tanayi, hakan yasa Maya mikewa, zuwa gareta ya dakatar da ita da hannu ta koma ta zauna, yana me cewa " kyale ta kawai wan nan uwar darun" 

  " Mom Allah Baby idan bata sha ice cream din nan ba zata hanani bacci yau, please Dad ka sa a kawo mata kawai mu huta" Fanan tayi maganar cikin damuwa, shikuwa murmushi yayi yace." Wlh yau bazata sha ice cream din nan ba kinji ma na rantse, tunda bata da hankali ay mu muna da shi, haka kawai muyita siya mata abinda ze cutar da lafiyan ta, idan ma zata koyi cin abinci da dare ta koya" 

  Abincin su suka cigaba da ci suka kyaleta tanata lalatan cen kukan ta akan kujera harta gaji ta juya ga TV hankalin ta duka yay kan TV din daga karshe ma remote ta dauka tana canza channels, tana cikin kaiwa ne tasaka wani gidan TV da suke haska wani taro, sosai tasaki hanci na da baki tana kallon TV don wani hadadden guy ne ake nunowa yanzu, sosai yay matukar burge ta har tana sakin smile batare da tasani ba, dama gata dason abu me kyau, yana saurin daukar hankali ta, wan da kuma ba kowa ta gani ba se Omar Eshan, a ranar taron birthday dinsa, Omar na zaune yana cikin cin abinci sa yaji muryan da baze taba manta wa da itaba a rayuwar sa ta shige masa kunne da brain kasa kai spoon yay bakin sa ya juya slowly ya kalli TV din sam besan sanda spoon din ya fadi ba yana kara ware idanun sa kan TV din ko nace Zainab time din tana jawabi akan sa na wakar datace a saka mata domin shi, yana son wakar sosai yake murmushi don harga Allah yama mance a ina yake yanzun, cikin farin cikin daya dade be shige shiba yace.

   " Allah sarki abar kauna ta, ashe har yanzu baki manta da dani ba Allah ne kadai yasan nufin sa na rabamun dayay ada, naga hadarin da mijin ki yay a jarida harya rasa rayuwar sa, nayi tunanin kin wuce class dina yanzu shiyasa ban neme kiba, Bi'izi nillahi rabbi Zainab semun zama ma aurata" yanata sun batun farin ciki se gani yay duff an kashe TV din hakan yasa ya juya gurin da Zainab take kwance a mugun fusace, se ganin Maya yay a tsaye kansa da remote din hannun ta se huci take kamar kumurci, idanun ta ya kada yay jajir saboda masifaf fen kishi cikin tsananin tashin hankali tace.

   " Wacece ita din da kake wan nan sunbatun a kanta? Ay dama tun tuni nasan da kawai abubuwan da kake boye min a zuciyan ka, duba da irin mafar kan da nake ganin kana yi shiyasa kullum nake hauka akan wadda ta rabe ka, ashe a banza nakeyi yau Allah ya nuna min ita, wacece wan nan harda kake tunanin auren ta? Kuma wlh muddin ina raye aure kam sedai kaga anayi!" 

  Tun da suke da Omar be tabajin tsanar taba seyau, shima kuwa cikin fushin da bata taba sanin yana dashi ba yace." Kunna min TV!" 

   " Idan naki fa!" Ta fada a har zuke, wani irin kallo yake watsa mata yace." Muddin kika kuskura aka cire abinda nake kallo a TV din nan ba tare da kin kunna min ba, sekin raina kanki sekin san waye Omar wlh!" Gaba daya mamakin sa yasa tama kasa magana ganin yayo kanta ne yasa ta cilla masa remote din ta durkushe a gurin ta saki kuka me cin rai, kusa da TV din ya matsa ya cigaba da kallon sa kamar ze shige ciki, Fanan kuwa tunda fada ya kaure a tsaka nin iyayen nasu ta kama hannun Zainab sukai sama, ya kafe TV da ido har aka cire taron zeetah din tashi Maya na zaune tana kallon ikon Allah, bayanin da akayi taron kona su waye yasata rike wa a kwanyar ta iyalan marigayin, murmushi tayi kona miye oho ta mike tai nata gurin tabar shi anan donshi cikin wan nan daren, tsohon ciwon sane Zainab ta tado masa dashi sabuwar kauna ce ta motsa cikin wanga dare....✍️