🧑‍🍼 RABO...❣️

7

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode seven 

Washe gari koda suka tashi Maya ta gama da hidimar yaranta aka mika su school gogan kuwa Omar ko sauko wa daga saman sa beba hakan yasa itama ta shige nata dakin ta kwala ma aminiyar ta kira a waya, 20 minutes basu shude ba kuwa se gata ta iso gidan masu aiki sun rigada sun san matsayin ta shiyasa ma babu wanda ya tsaida ta ta wuce har dakin Mayan dama jiran ta take tana shiga ta murza wa kofan key da Ganin alamu ba hiran azziki ba zasu tattauna, seda suka jima cikin dakin tukunna suka fito ta rakata suka tafi, Omar besan wainar da take Toya waba,

    Cikin kwana ki biyun nan Zainab da dan lelen nata basu dawo dai dai ba sam baya ma son su zauna suyi hira harkar business dinsu kawai yasa gaba da karatun exam da sukeyi ta karshe a secondary, hakan ne yasa ta kyale shi bata ta kurasa, to yauma kamar kullum Omar yana school around 12 na rana tana zaune a parlour din ta tana watching TV wayan ta ya soma ruri koda ta duba taga ma aikatan gidan ne ta daga, suke shaida mata ai tayi baki ne kuma bakuwar fuska ne, tadan ji mamaki dajin furucin su tadai ce kawai sukai su dakin baki tana zuwa, mikewa tayi ta sauya kayan jikin ta zuwa wani hadadden leshi me tsadar gaske, an cika su da kayan ciye ciye tun zaman su, an karrama su, da sallamar ta Zainab ta tura kofan tashiga wata faduwa gaba ta sameta ganin ko su waye bakin nata, wan da ba wasu bane illah Maya matar Omar da aminiyar tata sadiya, sosai take kallon sadiya don tabbas bazata manta da fuskar taba domin ta tuna itace wadda ta likewa mijin ta kafin ya rasu tazame masa karfan kafa, ita ma kuma sadiya tsaf ta gane ta wanda hakan ne yasa take watsa mata wani irin kallon tsana, don dama can ta tsane ta saboda itane Eshan yaki ta a rayuwar sa yaki auren ta, tunda Maya ta mata bayani dama da biyu ta zuga ta don suzo gidan, tom itama Maya wani irin azabab ben kishi ne ya turnuke ta ganin baiwar da Allah ya hore mata, setaga ashe a fili ma tafi kyau, kan a TV data ganta, cikin gadara da wulakan ci sadiya ta fara magana.

    " Zainab manyan kasa! Kin kanai naye mijin ki keke kadai kinhana kowa ya rabe shi, yanzu kuma da kasa ta rufe masa ido shine zaki koma kan mazajen mutane, dama abinda yake tafe damu kenan, Zainab idan kinason zama lpy to ki rufawa kanki asiri ki Nissan ci mijin aminiyar nan tawa, inba hakaba kuwa! To zaki saka kanki a masifar da bazaki iya fita ba har abada, gara tunda azziki ki samawa kanki lpy, ki canza guri" saurin tarar numfashin ta Zainab tayi tana cewa.

   " Haba baiwar Allah, lafiyan ki kalau kuwa? A haukan ki ke kishi kike dani har yanzu? Yaza kizo min gida kina min shouting! Akan banzan maganar ki da bansan inda ta dosaba!" Mikewa Maya tayi ta aje mata hoton Omar a gaban ta wanda sukayi su biyu ta makale masa a jiki sunyi kyau sosai, galala Zainab ke kallon hoton cikin tuhuma Maya din tace.

  " I hope yanzu kin fahimta inda maganar tata ta dosa Koh? Kuma meye alakar ki da mijina?" Shiru Zainab ta mata tana kara kallon hoton dakyau ganin yadda Maya ta lafewa Omar din a jiki, wani irin abune taji yana taso mata na takaici hakan yasa ta dauke idanun ta ta dorashi akan Maya tana mata kallon sama da kasa cike da rainin hankali, mai maita tambayar ta kumayi." Shin menene alakar ki da mijina?" Banzan tsaki Zainab taja tana me harde kafa tace." Kece matar Omar din kenan!" Cikin masifa Maya tace" Ban saniba! Ki bani amsar tambaya ta meye hadin ki DASHI!!" 

   " Cike da mamaki Zainab take kallon Maya ga takaicin daya cikata, tace." Kai duniya inda ranka kasha kallo, wai yau ni ake tambaya meye tsakani na da Omar dina! Ke duk zaman ki dashi be taba baki labari naba, ko matsayin ki bekai na ya gaya miki yadda nake a zuciyan saba? Ke in banda kaddara ta riga fata ma ko farcen sa kin isa ki mallaka ne bare shi kansa, wai ke me miji! kinzo donki min burga, ai keya kamata nacewa ki kama kanki kibi a hankali don inba hakaba akaina Omar ze nuna miki keba komai bac.....pauuu!! Maya ta dauke Zainab da mari jikin ta har rawa yake Saboda bacin rai, sosai ta dafe kuncin nata don har wani duhu seda tagani harta mance yaushe rabon ta da ko tsawa ma bare Mari, wani irin kallo Zainab ke mata tana ganin yadda take wani irin huci, cikin bala i tace.

   " Wlh ki kama kanki! Don akan miji na tsaf zan iya halaka ki wlh kinji na rantse miki!!" Sosai abin yaso bawa Zainab tsoro ma cikin murmushi sadiya tace." Ay baki fara ganin komai bama Zainab idan kuma baki da hankali ne zaki cigaba da bibiyar sa kiga meze biyo baya Kuma" 

   " Kedai anyi jahila Wlh! Mijina ya mutu amma haryanzu kina kishi dani saboda bakida ilimi, kuma bari kuji ku duka keda ita nafi karfin ku haka zaku ganmu ku barmu, kuyi gaggawar barmin gida yanzu tun kan nasa securities su wulakanta ku, so amma bazan so hakan ba koba komai zakuci darajar masoyi na, salin alin kawai ku tashi ku bar min gida!" 

  Cikin fushi Maya tace." Anki a fita din! Kisa abinda yafi securities ma su wulakanta mu kema kiga naki karshen" bata kobi takan taba Zainab ta dauki wayar ta ta fice ta basu guri Maya nata aikin masifa, ga mamakin su se ganin securities din kuwa sukai harda bindigu gasu marasa imani, tun kan suce wani abuma sukayo waje ciki na durar ruwa, kamar wasu almajirai haka suka tasosu har waje hakan ne yasa suna shiga mota Maya ta fashe da kukan takaici tana cewa."  Na shiga uku sadiya kinga wan nan tsinan niyar matar da kyau kamar aljana ita mijina keso, ay nariga da na gama tashi aiki nabari tazo min gida matsayin kishiya, bazan taba lamin taba indai kuwa haka ne na kusa yin kisan kai wlh!" 

   Dafata sadiya tayi tace." Haba Maya, ki kwantar da hankalin ki ay seki bani kunya haka da wuri kin karaya, ay kidena maganar wani kisa akwai abinda zanyi mata wanda se taji dama batazo duniya ba, don sena tozar tata na wulakan tata a idon duniya muddin ina numfashi" sanyi Maya taji a ranta domin tariga tasan kawallin tata ba wasa, koda suka bar gidan Zainab kasa haura wa tayi koda saman tane tana parlour se zubar hawaye take ga wani irin kishi dayake cinta inta tuna hoton Omar din data gani shida Maya ta makale shi gaba daya zuciyan ta a cunkushe take cikin wani irin kuka tace.

   " Wai yau ni aka mara akan masoyi na Omar, harda cin mutum ci, koda wasa ban taba tunanin haka ba, Omar meyasa zaka auri wan nan matar sam batada kirki bakayi sa ar mata ba gaskiya" 

   Karfe 2 da kusan rabi motocin Omar suka sawo kai cikin gidan, kuma har a time din Zainab tana nan parlour bata haura sama ba, idon ta yay jajir saboda kukan datayi har kanta ya sara,  Koda ya shigo mamaki ne ya kamashi ganin Ammin tashi dayay a zaune a parlour yau ko welcoming din ma baze samuba, ta dai dago kawai tana kallon sa, wani irin mummunar faduwan gaba ne ya sameshi ganin halin da take ciki tuni ya mance da wani rashin shiri da sukeyi, karasa wa yayi ya tsugunno ta gaban ta yana me rike mata hannu zafi yaji sosai alamun zazzabi na a ajikin ta.

    " Subhanallah! Ammi bakida lpy haka? Meyasa baki kirani ba ko doctor?" Bata ce masa kala ba se idanu kawai datake binsa dasu har yanzu, mikewa kawai yay ya dauko wayan sa daya aje kan senter table ya dawo kusa da ita ya zauna, yanajin gaba daya babu dadi ganin ta dayay cikin wan nan hali, murya a sanyaye yace." Please Ammi menene yake faruwa haka?" Se yanzu ta kar kato ta kalle shi da kyau tana shirin yin magana ne yakai hannun sa kan face din ta ya juyo da fuskan sosai yadda zega abinda yake tsamma nin dakyau, ya kuwa ga shatin yatsun Maya rada rada a kuncin nata yay ja gurin, tsabar kaduwa Omar yama kasa magana kallon ta kawai yake nan danan idon sa yasoma rikide wa da zallan bacin rai, 

   " Ammi Yanzu waye kika bari ya shigo har cikin gidan nan yay miki haka?" Idanun ta tafda kwallah tace." Calm down weetheart babu abinda ya same ni ka kwantar da hankalin ka" sororo kawai yake kallon ta don bata taba masa karya ba se a yanzun, cikin wani yanayi mara dadi yace." Kada mu fara haka dake Ammi please ki fada min wanda yay gan gancin marar min ke haka! Bazan iya jurar ganin ki a hakaba, ki kalli shatin mari a face din ki,don Allah ki gaya min" murmushi ta kakalo a iya bakin ta tace." Babu komai sweetheart na gaya maka, kaje ka shirya kazo muyi lunch tare nima inajin yunwa" tana gama fadin haka ta mike ta haye saman ta yabita da kallon mamaki a memakon yayi nashi guri seyay waje ma gurin securities yana tambayar su wanda yazo gidan, tass suka masa bayanin komai, sosai yake mamakin to suwaye wadan nan kuma ba a cikin family suke ba, CC TV camera yasa a tariyo masa baya yagan su Maya ko kadan be taba ganin su bama, yana tunanin meya hadin su da mahaifiyar sa ne Kam, kyale komai yay sayi maganar da ita ya koma ciki, yana hayewa ba jumawa ta fito itama time din ma doctor yazo, kafin ya fito ne shi yayi abinda zeyi ya bata maganin daze bata ya tafi, jin shiru ne yasata binsa dakin nasa taji zubar ruwa a bathroom da alamu wanka yake, hakan yasa ta zama a dining din tana jiran sa harya fito, tana cikin yin serving dinsu yace.

   " Ammi kimin alfarma daya kawai ki sanar min suwaye sukazo gidan nan ban taba ganin suba" 

   Abincin ta ta faraci kamar bazata ce kala ba dai tace." Nima ban san suba, wayace ma ka cika bincike haka banaso" shiru kawai yay yafara cin abinci sa suna gama wa ya tafi masjid don yin sallan la asar,

        Yauma kamar kullum Fanan da Zainab suna school, shikuma Omar yaje shanono wan nan dalilin ne ya bata damar kiran aminiyar tata sadiya harda zama a parlour suna kulla makircin su, 

   " Maya taya zamu hada taro ne a gidan nan wanda zamu gayyata mutane da dan dama?" 

  " Taro Kuma! Meyasa kike tambaya?" 

  " Waccar matar nakeso mu gayyato domin tazo tayi bayani sala sala" 

   Dariya Sosai Maya tayi gami da cewa." Kai kawata bakida dama wlh kin san takalan mugun ta kala kala gashi kinyi maganar akan gaba next week zamuyi taron birthday dinsa, kin san muna aika mata da invitation zuwa zatai ita me masoyi" wata shewa sadiya tayi harda tafa hannu tace." Good!! Kinga a matsayin shine zamu tura mata da katin gayyata tana zuwa tata ta kare, wlh nayi alkawarin sena sata a kuncin da bazata taba manta waba sena sa hawayen ta ya kare saboda kuka, zata dan dani abinda na kunsa" 

  " Kai sadiya naga ma kin fini tsanar matar nan!" 

  Maya ta fada tana dariya, sadiya tace." Ke kinsan kuwa irin kuncin dana shiga akan matar nan gurin malamai kala kala naje ance asiri baze cishiba indai yana tare da ita bare kuma ita kanta  sam baya daraja ni ke har Kano din fa nake binsa fa amma nida banza duk daya yagani yake son ransa gashi na gama mutuwa akan sa, yanzu baya duniya kuma zata dawo kan naki mijin" saurin katse ta tayi da cewa." A ah ina bata isa bafa Omar dina nan gani nan bari" cikin murmushi keta sadiya tace" kedai bari kawai ni zanji da ita" 

   Bayan wasu 'yan kwanaki Zainab tana parlour dinta Lisa me kula da ita tana mata massage a kafafun ta tana daga kishin gide dan lelen nata yana company don yanzu can yake yini tunda sukai graduation dinsu na secondary, wayar tace ta hau ruri  Lisa ta kawo mata wayan tana dubawa taga securities ne gaban tane ya fadi ba tare da tasan dalili ba, tana dagawa suka sanar mata ai an kawo mata sakone daga Abuja, mamaki ne karara a fuskan ta kashe wayan tayi ta tura Lisa ta amso mata jikin ta har bari yake don so kawai take ta buda taga menene, se ganin wani kyakkyawan invitation tai ya fado cikin akwatun cikin kaguwa tasoma Karan tawa, abin mamaki nan da nan tasoma sakin wani al murin smile harta gama sam ta mance Lisa na dakin ma ta manna shi a kirjin ta cikin farin ciki tace.

   " Masoyi nah dama nayi shiru ne inji ta ina zan jika, in Sha ALLAH kuwa zaka ganni, dole zuwa abuja ya kamani ashe acan kake da zama yanzu, lallai wahalal lar matarka tun daga can tazo guna kenan, ai kuwa tayi a banza" tanayi tana tabe baki ta mike ta shiga master bedroom dinta tanajin wani irin nishadi yana ziyar tat ta, a gaban mirror ta tsaya tana juyi tana murmushi kamar shine a tsaye tana cewa." OH Allah Omar zaka ganni duk na tsofe maka, Allah yasa dai haryanzu kana sona kamar yadda nake kaunar ka" tura baki tayi gaba cikin shagwaba tace." To yanzu kuma idan kace baka sona fa? Kai impossible nasan ina nan daram a zuciyan ka, tunda har ka gayya ceni taron birthday dinka" Shiru tayi tana tunani kawai ta dafe kirjin ta da hannu biyu tace." Na bani wata sabuwa, yanzu ya zanyi da sweetheart rigimam man yaro, muddin yaji inda zani akwai kura gara nayi tafiya ta batare da yasan ma ina naje ba, cikin sauri ta dauke invitation din da wasikar dake ciki taje cikin wardrobe ta boye su, ta koma kan bed ta harde kafa tanajin wani irin dadi tayi dariya tana cewa.

   " OH ni Zainab tun kafin ma na ganka ina ta murna da zumudi....✍️