🧑‍🍼 RABO...❣️

8

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

NA* 

       NANA BMB

Episode eight

Sai wajan karfe 5 Omar ya dawo gida a gajiye yana shiga parlour yasoma jiyo kida yana tashi sama sama daga part din Ammi tashi kai tsaye ya wuce saman da mama kin sa ko knocking beba saboda bajin sa ma zatai ba ya murda handle ya shiga ita kadai abinta take rawa tamkar yarinya kana ganin ta base ancema tana cikin farin ciki ba, tsaya wa yay kawai yana kallon ta tana juyowa ta ganshi tayo gunsa ta kamo masa hannuwa tana juyawa dashi tana kara fadada fara ar fuskan ta, girgiza kansa kawai yay ya cire hannun sa a nata yaje ya kashe kayan kidan ya nemi guri ya zauna yana cewa.

   " Ammi wani irin rawa ne haka kikeyi yanzu? Kin kure volume na waka" pillow ta dauka ta cilla shi akan laps dinsa ta kwantar da kanta a kai tana maida numfashi don ta tiki rawa kam, seda ta huta tukunna tace." Son yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa har inajin yau rana ce ta mussam man a gare ni" be tanka mata ba shidai  ma kallon ta kawai da yake a zuciyan sa yana cewa." Zanga ranar da zakisan kin girma Ammi"

   Yau takama ranar tafiyan Zainab Abuja duka wani shirin ta ta kammala an zana mata kunshi na haduwa ya zauna a farar fatan ta yay maroon sosai, koda Omar ya tambaye ta dalili ta sanar dashi bikin wata aminiyar ta ne akeyi a cikin gari, sam zuciyan sa ta gaza aminta da ita kwana biyun nan duba da irin shirye shirye da take kamar itace amaryar, da tashi da wuri ta shirya abinta kamar zata dinner, shikuma shirin fita aiki yay ya shiga gurin nata, da mamaki yace." Ammi da wuri zaki tafi gidan bikin ne?" Murmushi tayi tana shafa wayan ta tace." Yanzu zan tafi my sweetheart se kirana ma takeyi" 

     " Wai Ammi wacece kawar nan taki ne da kike zumudi haka a kanta?" 

  Shiru ne ya wakana a dakin don bata ko kalle shiba bare ta bashi amsa, seda yazo fita ne yace." To ki fito semu wuce mu fara kaiki gidan bikin san nan na wuce aiki" cikin saurin tarar numfashin sa datayi ne tace." A ah katafi abinka kawai dai inason ka tanadar min bodyguards mu tafi tare" beyi magana ba ya fita don ya fahimta bata son yaje gurin ne barin ta kawai yayi se idan ya dawo aiki ya kira guards din daya bar mata su sanar dashi inda ake bikin yaje, seda ta tabbatar da ya isa company tukunna tasa Lisa ta dauko mata trolley din ta suka fito, tana ma bodyguards din warning  kan su kashe wayan su kada su kuskura su bari Omar ya same su a waya don tasan tabbas seya kira kuma tafiyan su doguwa ce Abuja ma zasu seda ta musu jan kunne me kyau tukunna suka dauki hanya, sosai takejin zuciyan ta na wani irin bugu da karfi sanyin da jikin ta yay ne yasa ta zamewa ta kwanta tana tunani kala kala shin ta sauka gidan Omar din ne ko kuwa ta kama hotel don sam batasan kuma ganin matar nan tasa, wata zuciyan kuma tana gaya mata *meyasa zakiyi tafiyan nan batare da kowa ya sani ba, bakya tunanin hakan ze jawo miki matsala?* Saurin girgiza kan ta tayi tana kara rintse idanun ta,

                ABUJA

Omar Abuja yana dakin sa a zaune kan sofa yana tunanin Zainab na invitation din daya aika mata dashi, a fili yake furta." Anya Zainab zatazo kuwa? Kai bana tunanin haka, to idan kuma zata zofa? Kai idan ma baki zoba Zainab bazan rufe kwana biyu ba sena ganki, domin nasan kema kina da bukatar ganina, kai kuma idan kikazo nasan Maya bata da hankali tsaf zata nemi ci miki mutum ci, ai kuwa Maya da kinyi nadamar hakan akan Zainab tsaf zan nuna miki karshen ki gara kada ki fara ma kodan ki zauna lpy" yay zurfin tunani yaji ana masa knocking juyawa yay ga kofan yana murmushi domin yasan babu me masa irin wan nan malalacin knocking din se autar sa Zainab,

" Come in" 

Shine abinda yace, ta kuwa turo kofan ta shigo kai ko kallabi babu daga ita se wani dan doguwan riga iya gwiwa gata me karamin hannu idanun ta sunyi ja saboda kukan datayi cikin tura baki gaba ta zube a gaban sa tana shasheka nan danan annurin fuskan sa ya dauke.

  " Sweetheart meya faru dake haka kike kuka?" Kukan da take danne wane ya kufce mata, hankalin sa ne ya kara tashi cikin rudu yace." Me akai mike ne?" Dago kan ta tayi cikin kuka tace." Auntie fadima ce" wani dogon tsaki yaja yace." Ay dama nasani! Badai tazo ba yanzun zata hana minke jin dadi a gidan nan, bakuma zanyi tolerating hakaba tsaf sena wartaka ta ta koma gida, me takuma yi miki yanzu?" 

   " Dad tuwo fa sukayi a gidan nan, sun san kuma banaci, nace amin girki auntie fadima ta hana wai idan bazan ciba sedai na bari, saboda kuma na fara kuka ta koreni!" 

  " Tashi muje gun nata inji meye matsalan ta dakene"

   Tana biye dashi har suka sauko parlour su fadima na zaune da ragowan 'yan uwa ta hango su sosai tasha jinin jikin ta, don tariga da tasan waye yayan nata tsaf seya kunya tata cikin mutane indai akan Zainab ne, mikewa tayi tun kan su karaso taje ta samesu.

   " Wai ke fadima meyasa bakyaji magana ne? Narasa dalilin dayasa kaf gidan nan Zainab kika takura wa, common saboda abinci zaki saka min ita kuka haka! Saboda me to?" 

  Jikin ta a sanyaye tace." Kayi hakuri Yaya, amma kai kanka kasan sangar tar yarinyar nan yayi yawa, abinda ta ga dama shi takeyi, macace fa ita kada ka manta, idan ta taso ahaka akwai matsala kada ka manta gidan wani fa zataje, dole tayi aure ta zauna karkashin ikon sa, rayuwa babu yadda bata kasance wa da bawan sa" 

   " Fadima banason nasake jin irin wan nan maganar, babu abinda 'ya'ya na zasu nema inada shi dai aduniya nakasa yi musu babu shi, ina raye babu namijin daya isa ya tozar tamin yara, harna mutu 'ya'ya na suna karkashin kulawa ta ba aure ba kome sukayi don haka kisan me kikeyi!" Juyawa yay gare ta yana cewa." Sweetheart yanzu me kikeson kici a girka miki?" Cikin tura baki gaba tace." Ni nafasa cin abinci danbun kaza nakeso!" 

  " Abu me sauki ma! Je dauko hijab dinki mu tafi mu siyo se kinci kin ture" 

   Cikin murmushin jin dadi tace." Thank you Dad!" Shima cikin murmushi yace." Maza ki dauko hijab mu tafi"

  " Dad wlh hijab din zafi kasan banason zafi mu tafi kawai haka" 

  " No bazaki fita haka ba jeki sauya dressing dinki ya rufe miki jiki kizo mu tafi" badon ranta yaso ba ta juya ta koma ciki, dagowa yayi yana kallon fadima da takaicin su ya gama isar ta, gyaran murya yay yace." Fadima daga yanzu inason kisaka ido akan masu zuwa har zuwa goben koda Allah ze kawo Zainab na fita, kinsan dai halin waccar shasha Shan Maya" 

   Cikin kwalalo idanu fadima tace." Yaya waca Zainab kuma kake nufi?" Hararar ta yayi gamida da cewa." To yimin shouting har mutane susan me muke cewa, bayan Zainab 'yata wacce kika sani a rayuwa ta?" Ya karashe maganar cikin jin haushi, baki bude take kallon sa har yay shiru.

   " Zuwa zatayi Yaya?" 

  " Babu tabbas kedai kawai kisa ido" 

  " Angama in Sha ALLAH baka da matsala" ta karshe maganar cike da mamaki tanason kuma tambayar sa Zainab ta dawo kawai ya rike mata hannu suka fita kasa ko motsi fadimatu tayi seda suka fice ta jin jina kai tana cewa.

  " Har yanzu dama Zainab bata manta da Yaya ba, lallai wan nan soyayyar taku abar a duba ce, taff ga kuma matar ka Maya, ashe akwai karamin yaki a gidan nan, ay kusan hauka nasan Maya zakiyi kikaga Zainab"

   Abinda Omar be saniba shine, duka wani motsin sa da yakeyi a yanzu kan idon maya yake da sadiya yake yinsa, harta da invitation din daya tura suna sane dashi wan nan dalilin ne ma yasa suka fasa aika mata da wani invitation din tunda yama tura, Maya tana me kara yin mamakin mijin nata kuma, abu iri iri babu wanda basu tanadar ma Zainab ba, Omar Abuja suna tafe shida Zainab driver na tuka su se zuba surutu take, har suka isa hadadden gurin kayan kwalan da makwala she, ya siya mata danbun kazan da Kuma gas meat, suka zauna su biyu abinsu suka ci sukai nak san nan sukai takeaway na mutan gida, da driver, sedai koda fitowan su tai kememe taki shiga mota ita seya siya mata ice cream zasu tafi gida,shima kuwa ya kafe yace baze siya mata ba ay jiya Tasha, sosai ta saki masa kuka gami da sakin ledojin hannun ta tana dire dire a gurin,

   " Ya Salam!! Zainab meyasa ke kinfiya rigima ne, sam ke bakya tattalin lafiyan ki, jiya kinsha ice cream din nan se jibi keda ki kuma shan sa, ay haka mukayi dake dama, don haka shiga mota mu tafi gida!" Ya karashe maganar cikin fada, sam be ankara ba se gani yay ta nufi titi gadan gadan tana cewa." Wlh Dad bazan koma gida ba seka saimin ice cream din bayan na riga na ganshi" 

  Cikin tashin hankali ya bita yana cewa." Zainab baki da hankali dama bakiga titi zaki hauba bazaki dawo ba! Ko mutuwa kikeson yi!" Cak ta tsaya jin ya ambata mata mutuwa amma bata dena kukan ba yana karaso wa gurin ta ya rike mata hannu Gami Da sakin ajiyan zuciya yace." Yanzu da ban dakatar dake ba kan titi zaki hau? Kika kara yin gan gancin nan sena zane miki jikin ki!" Ya karashe maganar cikin bacin rai,da mamaki ta kwalalo idanu waje ta tace." Dad ni zaka Zane?" 

  " Sosai kuwa abinda yafi duka ma sena yi miki shi idan kika sake nufan titi da gudu zakiga yadda zanyi da dake, wuce mu tafi gida!" Ya kama hannun ta amma ta tirje cikin zubar hawaye tace." Yanzu Dad bazan sha ice cream din nan ba!" Seda ya kare mata kallo tukunna yace.

  " Zainab kwadayin ki gaskiya yasoma bani tsoro, wani irin naci ne haka? Gaskiya dole nasan abinyi akanki, don wan nan kwadayin naki yayi yawa" 

   Horn din da aka soma yi musu ne ya dauka hankali su suka juya a tare suna kallon motocin dake gefen titi kusa da su sun Parker, motan tsakiyan dimdin take da tinted shiyasa basa ganin kowa na ciki, se a hankali aka soma sauke glass din motan, nan danan zuciyan Omar tasoma wani harbawa so be karasa tsinkewa da lamarin ba seda yay tozali da fuskan masoyiyar sa Zainab, tanata zuba masa murmushi me daukar hankali, kamar an dasashi a gurin haka ya koma har guards din nata suka bude mata mota ta fito direct tai gunsa har yanzu murmushi dauke a fuskan ta ta karasa gaban sa ta tsaya suna karema juna kallon yaushe gamo, nan danan hawayen farin ciki ya taru a idanun ta, baki bude Zainab ke kallon masoyiyar Dad din tata kasa hakuri tayi don sosai  ta burge ta takai hannun ta riko tana kallon zanen kunshin dake jiki tana murmushi, 

   Sun kuyowa Zainab din tayi tana kara fadada murmushi ta dai dai fuskan ta ta sunkuyo tace.

   " My baby me kike sone?" 

  Se Yanzu ma ta tuno da fushin da takeyi ta cukule gami da cewa." Dad ne ya kisaya min ice cream!" Murmushi kawai take wa Zainab din tashi ganin kamar su da tayi, daya daga cikin bodyguards din ta kira ta turashi ya amso ma diyar tata ice cream, cikin hanzarin sa kuwa ya nufa inda su Omar din suka fito, hawaye take share mata tana cewa." Sorry my daughter dena kuka yanzu za a kawo miki ice cream" kare mata kallo tayi dakyau San nan tace.

  " Who are you?" 

Murmushi tayi tana cewa." Ki tambaya Dad din ki ze fada miki ko wacece ni" 

" Umm ummm, ni ba ruwana da Dad yanzu mun bata tunda yace ze zaneni" 

  " Ina! Bazan bari ya dakeki ba indai ina nan kuwa" hannun ta ta riko tana cewa." Ayni yanzu ma kece Dad din nawa indai zakina siya min ice cream" 'yar dariya Zainab tayi tana cewa." Lallai kam, yau nazama Dad kenan" 

  " Ya Allah!! Wani irin farin gani ne haka? Allah kaine abin godiya daka sake nuna min wan nan rana ALHMDLH" Kallon sa kawai Zainab take tanajin duka wasu damuwa da fargabar dake tare da ita babu sayau take jinta, cikin zolaya yace."  Zainab haka kika zama babban hajiya? lallai girma yazo" 

   Tana murmushi ta rufe fuskan ta da tafukan hannayen ta tana cewa." Kaga na tsofe dayawa Koh" 

" Kawai ki fito ki fadi gaskiya kice Omar kayimin tsufa yanzu!" Yana maganar yana dariya, pouting din small mouth dinta tayi tana masa harara kasan ido tace." 

  " Ba wani kawai ka fadi gaskiya, ai dama nasan na maka tsufa yanzu!" 

  " La ilaha illahu! Yanzu nan Zainab halin ki har yanzu babu abinda ya sauya! Kai amma wlh zaki bani kunya, kinga yadda kike da baki kamar tawa Zainab din!" Ya karashe magana yana mata dariya, saurin riko mata hannu Zainab din tashi tayi tana cewa.

   "Lah!! Auntie sunan mu daya dama?" Cikin yashe hakora tace." Dagaske sunan ki Zainab?" Saurin daga mata kai tayi tana murmushi me sauti, hakan yasata sunkuce ta cikin farin ciki tana cewa." WOW Alhmdlh masha Allah, Yanzu na tabbatar da haryanzu masoyi na yana kaunata" 

   " Tabdijan wlh na yarda yanzu me hali kam baya fasa halin sa Zainab kiga abinda kike a gurin nan, in banda kedin waye zeyi haka kuwa?" Tsaya wa tayi da juyin da takeyi itada Zainab din tashi tasha mur ta na kallon sa tace." What the you mean?" Sosa kai ya fara yana cewa." Babu komai, dama canai mu tafi gida" cikin hanzari ta rike haba tana cewa." Rufa min asiri ni ba gidan ka zan sauka ba ina hotel,ni ina zan iya da masifar matarka" katse ta Omar yay dace wa." Shin Zainab a ina kikasan Maya?" Kwalalo idanu tayi tana bude baki alamun ta kwafsa, basarwa kawai tayi tace." Ban san taba kawai ande sanar min tanada kishi ne" sosai ya kura mata ido don be yarda ba zallan rashin gaskiya yake gani tare da ita, dama tun fil azal idan batada gaskiya bata yadda su hada ido hakan ne ya darsa masa tunani kala kala a zuciyan sa, kallon ta yake harta sauke Zainab dinsa ta kama mata hannu tana cewa." Mu tafi kinji nikam yau nasami abokiyar hira" 

   Gurin da driver sa yake ya wuce yashiga motan yasa ya sanar dashi hotel din da zasu nufa su duka suka rankaya suka bishi su Zainab din, yana daga zaune cikin motar sa duka wani abu daya wakana tsakanin su Omar kan idanun sa koda suka tafi shima murmushin mugun ta ya saki yana me rufa musu baya, 

   Seda suka isa hadadden hotel din Omar yaje dakan sa ya kama mata daki ita guards din nata, Zainab dinsa tanata zubawa zeetah surutu abin se dariya yake bata sam ba a son ransa ze bari Zainab tayi kwanan hotel ba sedai yana tuno da halin Maya zega hakan ma yafi zaman ta a nan din domin yaci alwashin tabbas ta tabo masa zeetah dinsa ta tsokalo wa kanta bala i, dakuna uku ne nata a tsakiya sena guards din guda biyu gefe da gefe, seda suka shiga ciki yace.

   " Zainab ki kulamin da kanki sosai kinji" ya mika mata wani dan kati da keys din dakin nata yace." Idan kina da bukatar wani abu just call me, duk da anjima zan dawo na taho miki da autar taki ta tayaki kwana, kada ki zauna da yunwa kome kikeson ci kisa a kawo miki kafin nadawo"

  Cikin murmushi ta daga masa kai tana cewa Zainab." Naji dadi kawallin yau ashe tare zamu kwana Dad din ki ze kawo min ke kin yarda?" 

   " Ni bazan kwana a nan ba!" 

Kamar yadda tayi maganar Zainab tayi itama a marairai ce tace." Saboda me?" 

  " Nida Yaya muke kwana kullum, kuma idan na barta yau bazata ji dadi ba" kallon mamaki tasoma ma Omar tana cewa." Yaran ka nawa ne?" 

  " Daga ita se yayar ta" ya bata amsa komawa tayi da kallon ta kan Zainab din tace." Ya sunan sister din taki?" Cikin iyayi tana shan ice cream din ta ta gaya mata, murmusa wa tayi ta kuma cewa." To shikenan tunda baki kwana a guri na ita sister din taki seta zo ai nasan ita bazata kiba" 

   " No base anyi haka ba auntie zan zoma fa se naba yaya hakuri" 

" Good" zeetah tace gamida mika mata hannu suka kashe, hannun ta Omar ya kama suka fita tana musu Allah kiyaye hanya, suna fita ya dawo ya zura iya kansa cikin room din yana cewa." Yaufa amin tanaji domin zance zanzo ni anjima!" 

  Dariya ta soma ganin harda tsare fuskan nan yake, kanne mata ido kawai yay cikin farin ciki ya juya ya fita, kishin gidewa tayi kan bed din fara ah ta keta yi da jin dadi card din daya bata take ta kallo da ledojin daya aje mata, sosai ta manta yaushe rabon ta da farin ciki irin wan nan harta manta jinta take wasai a fili ta furta.

  " OH Allah! Ashe zan sake ganin wan nan ranar nida masoyi na....✍️