🧑‍🍼 RABO...❣️

10

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode Ten

Tausayin tane ya kama shi, yayi maza ya hada alluran ya mata, sosai ta kan kame sa tun tana iya shafa shi slow slow har jikin ta ya saki bacci yay awon gaba da ita ga wani gumin wahala dake tsatsafo mata, gyara mata kwanciyan yayi akan bed san nan ya lullube ta da duvet me laushi kana ya sauke ajiyan zuciya yasoma bin dakin da kallo ya mike yana duba ko ina, amma sam bega alamun zainab tasha wani abuba seda ya gama duba ko ina tukunna ya fito ya rufo mata kofan yana tambayar guards din ko wani yazo gun Zainab din kafin yazo, cikin mamaki suma suka gaya masa duka abinda ya wakana tsakanin su dasu Goga, san nan yanzu ma yana fitowa itama ta fito daga dakin tana tambayar su badai yallabai fita yay ba, suka bata amsa da eh fita yay, harda hanzarin ta ta tafi tana cewa hajiya ce tace a kirashi bari nayi sauri kada ya tafi, to dawowan da sadiya batayi ba kenan, harya dawo gurin ta ya mata alluran, wani irin gumi ne yasoma tsatsafo wa Omar mussam man ta cikin kansa, cikin bakin ciki da takaici yace.

   " Amma wlh bakuda amfani! Akan me zaku bari su shiga gurin Zainab bayan fuskan tama a rufe take, gaskiya in hakane bakusan meye aikin ku bama, don me ta taho daku nan din?" Sosai zuciyan Omar take tafar fasa, dayan sune ya rusuna, yace." Yallabai afuwan ai Madam itace ta dakatar da mu akan su domin tace tasan da zuwan nasu, sunce kaine ka turo su gurin ta" 

Cike da mamaki Omar yace." Ita da kanta ta amsa muku tasan da zuwan ta?" 

" Da bakin ta ta amsa yallabai" 

" No No gaskiya wan nan abin babu kamshin gaskiya a cikin sa, ya Allah gamu gare ka meke shirin faruwa kuma damu ne? Ka karemu daga sharrin makiya, ko kadan ni babu wanda na turo gurin Zainab yanzun ya kalar namijin dasuka zo tare yake?" Bayani suka masa yanata jimama abin, suna cewa." Laifin na gurin hajiya ita ta amsa mana da tasan da zuwan nasu, tabbas da bata amsa ba ma wan nan mutumin semun kamashi yanayin sa duka 'yan basaja ne" 

Share gumin fuskan sa yayi yace." Yanzu duka aje Komai zamuyi se Allah ya kaimu gobe, ta tashi a bacci koma meye se muji meya faru a bakin ta, kuma abin mamaki babu wanda yasan tazo garin nan ta bangare na dai sedai idan bangaren ta nake tunanin"

" Ay yallabai in bandamu babu wanda yasan tazo garin nan harta dan lelen nata bata sanar dashi ba wayoyin muma ta hanamu amfani dasu don kada a samemu"

" Ya Salam!!"

Shine abinda Omar yace." Ita kuwa Zainab meyasa zatayi haka tafiya babu wanda yasani, ita bata gudun ma a samu matsala, gashi yanzu ba damar yin magana da ita, koma dai me gobe da wuri zanzo don mu dauki mataki akan wan nan lamarin, seda suka hadu da bodyguards din duka suka zagaye hotel din akai checking sosai, aka kara bata tsaro Omar ya tafi, yana cikin motar sa tunani kala kala yakeyi yadda Zainab ta rikice haka tabbas koma meye me nikab dince zatayi mata koma menene, 

" INNA LILLAHI WA INNA LILLAHI RAJI UN!! Shikenan tafaru ta kare tana dakin time din da abun nan ya faru tsakani na da Zainab shikenan ta rigada ta gama damu, ajikina nakeji wani abu mara kyau ze faru, shin wai wacece wan nan me nikaf ne? babu wanda yasan Zainab tazo tabbas sedai in daga bangare na kenan!" Cikin takaici ya daki sitiyarin motar yana cije lips din sa yace." OH! NO! Maya babu abinda bazaki iya ai katawa ba indai akan kishin kine na hauka, to wlh baki isa ki tozarta Zainab ba muddin ina raye" cikin wani irin azabab ben gudu ya finani motan, 

    Sadiya kuwa Omar na fita ta sami dama jiki na bari tacire gaba daya cameras din data saka cikin jakar ta tayi waje ko kadan kuma Zainab bata ganta ba saboda ta kifane akan bed din ga murkususun da takeyi, kai tsaye bayan hotel din ta zaga inda Goga yay parking motan nasu ta shige jiki nata tsuma hakan yasa Goga sakin dariya yana cewa." Hala dakyar kikasha ko?" Cikin Maida numfashi sadiya tace." Kai wlh yau zuciya ta kiris ya rage bata bugaba domin duk a tunani na ya riga ya ganni, gani gasu ingaya maka, gaskiya yau rashin kiba ta yayi min rana" tana maganar suna kara shekewa da dariya Goga yace." To yaya aiki dai yayi kyau, ko tsoro ya hanaka tabuka komai?" Wani kallo ta watsa masa tana cewa." Da kuwa nayi asara ace banyi komai bah, ay nayi nasara ko a yanzu nacisu wasa wlh duka wani bincike da za ayi na daga bayane yanzu, kaima a gobe zaka bar garin nan in case, kafin nan dai yanzu ka kammala aikin ka donni na gama nawa, idan kayi abinda ya kamata zakaji cikon kudin ka ta asusun ka in bahaka ba kuwa kasan a yadda zamu kare" cikin yashe baki Goga yace." Haba aiki ay kamar anyi shine ma a gobe da wuri sakon nan ze isa shanono, kedai kisa ido kawai kiyi kallo gobe" " sawa kai dole nasaka ido naga yadda tsinan nan matar nan zata wulakanta yanzu dai muje sauke ni gida se a gobe Maya zata ganni itama taga meke wakana, don sena biya ta gurin mala mina ma zani gurin ta domin a goben nakeso matsala mu tazo karshe" batare da ya tanka mata ba Goga yaja mota suka tafi.

     Gudu Omar yake na tashin hankali harya isa gidan nasa time din kowa ya kwanta ya wuce direct dakin nata, Maya cikin bacci kawai taji anyi sama da ita hakan yasa ta bude baki zata kurma ihu ya matse mata baki ya ajeta gamida da kunna hasken dakin, sosai ta tsora ta da ganin Omar cikin wan nan halin don haka sam bata masa musu ba daya kama mata hannu har dakin sa yasa key ya kulle, tamkar sauna haka take binsa da idanu cike da mamaki, sedai bata kara shiga tashin hankali ba seda taji maruka a fuskan ta tai wani irin kifawa kasa kuwa babu shiri ta saki kuka na azabar dataji, sunkuya wa yay saitin face din ta ya dago fuskan tata yace.

" Kalle ni Maya!"

Cikin kuka ta daga kanta tana kallon kwayar idanun sa wanda ba komai take hangowa ba cikin idanun nashi se zallan masifa da bala i, cikin karaji yasoma cewa." Maya baki isaba wlh ina raye ki wulakan ta Zainab kinyi kadan, muddin kika bari wani abu ya faru da Zainab to ina me tabbatar miki sena daureki, don kin kusa kiyi ta auren ki indai akan Zainab ne!"

Tuni Maya ta manta da wasu zafin maruka daya mata tamkar yana watsa mata garwashi haka take jin magan ganun sa cikin firgice tace." Wacece Zainab??" Idon ta kamar zasu zazzago, wani banzan tsaki yaja ya cigaba da cewa." Taya ma akayi kikasan Zainab tazo garin nan har kikasan inda ta sauka, then wacece kika tura ta yaudare ta? Sosai nakejin tsanar ki Maya amfani da kikai da sunana gurin cutar min da Zainab, Maya ki fita a sabga ta tsakani na da Zainab inba hakaba kwabar ki zatayi ruwa, ada ina kyale ki kiyi abinda kikeso but yanzu kinzo inda akafi karfin ki don haka kizuba idanu kawai kiyi kallo!"

  Wani irin cakuma Maya tawa wuyan rigar sa tana cewa." Karya kake Omar baka isaba wlh ni zakazo cikin wan nan daren kafara cin zarafi na akan abinda bansan mekake nufi bama, kuma Allah ya toni asirin ka yau dubin ka ta cika, nasani kuma kasani wlh wlh muddin ina raye babu wadda ta isa ta rabeka!" Tamkar tababba haka Maya ke magana se kuma ta sake rushewa da kuka tana cewa." To aikin gama ai ya gama tunda harkaje ka ajiye ta inda kake so batare da kowa ya saniba, sam ba haka kake ba yaushe ka sauya halayyen ka, ka fadamin wacece ita din? Haduwan mu bazeyi kyau ba da ita, kuma a yau ka tabbatar min da banida muhimman ci a rayuwa ka tunda har waccan karuwar banzar ta Fi...  Tasssss!! Ya kara dauke ta da mari ya nuna ta da yatsa yana cewa." Can kinemi karuwa amma badai a guri na ba next idan kika kuma kiran Zainab da karuwa, abinda zan miki seyafi wan nan se ki gwammaci dama baki sanni ba a rayuwar ki, kuma bazan taba yadda dake ba akan bakisan komai ba just tell me wacece kika tura gurin Zainab? In ba hakaba Maya duka abinda ya biyo baya ke zan kama"

  Shiru Maya tayi tana kallon sa cike da al ajabin abinda yake mata yanzu, cikin zuciyan ta tana cewa." Ina wlh dasake Omar bazan barka hakaba, ni kake ciwa mutum ci akan wata yau! Koma wacece sena halaka ta" katse mata tunanin daya kuma yine cikin tsawa yasata mikewa ta dora hannu aka tasoma kururuwa tana." Nashiga ukuna na lalace jama ar gidan nan kuzo ku temakeni wai yau mijina ne yake cin zarafi na haka!! Akan abinda bansan hawaba ban san sauka, to bazan juraba wlh gidan mu zan tafi ai bansan haka kake ba dama se yanzu, dukan dakamin kuma nabar ka da Allah, da namijin kenan indai kamasa dare seya maka rana!!" 

  Jikin Omar ne ya fara yin sanyi yana tunanin to kodai Maya ba ita bace batasan komai ba, to amma idan ba ita bace waye?? Hayagaga da takeyi ne yayi masa yawa aka ga gidan shiru yasashi mikewa yana cewa." Enough Maya bakisan dare yayi bane? Ko so kike ki tara mana jama ar gidan a nan" cikin daga murya again tace." Bazan yi shirun ba ay kowa seyaji haka nakeso tunda yaudara ta kakeyi harda duka na yau akan mace wlh bazan yarda ba" girgiza kai Omar yay cikin takaici yace." Haba Maya! Ki nutsu mana muyi magana gaba daya hankali nah a tashe yake dame kikeson naji? San nan kiyi rantsu wa da ubangi jinki akan cewar bakisan abinda ya faru ba" cikin zubar hawaye Maya ta ringa rantse masa akan cewa batasan komai ba, cike da mamaki yake kallon ta a fili ya furta." to su waye wadan nan? Gaskiya sena tsanan ta bincike da gaggawa tun kafin wani matsalan ya faru" 

   Zuwa yanzu mamaki ya gama lullube Maya tana tunanin to wai meya faru ne haka daya rude ya rikice, koma dai meye tabar wa gobe ta jira sadiya tazo ta gaya mata me tayiwa wa Zainab din ne haka ya gigice, sam beko kuma bi takan taba ya cire kayan sa yay bathroom zuciyan sa na kuna, itama kuwa tai ficewar ta ta koma daki tana tunanin matakin dazata dauka kan Omar.

            WASHE GARI

Omar kano ne a babban parlour din gidan nasu yakasa zaune ya kasa tsaye ga waya a hannun sa eyes dinsa sunyi jawur saboda daren jiya be samu ya rintsa ba hankalin sa yakai kololuwa gurin tashi ya gagara samin Ammin tashi a waya ya kuma kasa kiran kowa ya sanar dashi, cikin damuwa ya dafe kansa dake tsananin masa ciwo yace." Why ban biki bane, taya ma na bari kika tafi gurin da ban saniba, meyasa zakiyi min haka? Baki taba tafiya kin barni ba haka, bansan wani hali kike cikiba a yanzu, ki temaka ki kunna wayarki!" Kirjin sa ya dafe dayake tsananin buga masa a yanzu ya nemi guri ya zauna yana lumshe eyes yace." Oh God! Kasa wan nan abun danake ji lpy ne, ka tsare min ita aduk inda take Allah ka kareta!"

  Rurin da wayan sa yasoma ne yasa shi hanzarin bude idanun sa ya kalli wayan sedai ba kiran da yake so bane Farid ne ma yake kira,wan nan dalilin ne ya maida idanun sa ya kulle har kiran ya yanke wani ya kuma shigo wa, se a time din ya daga kamar ze yi kuka yace." Farid ina cikin damuwa please kazo gida ka same ni" ba tare da yajira me ze ceba ya yanke wayar,
   A hankali tasoma bude idanun ta dasuka mata nauyi harta gama bude su tangaran tana bin dakin da kallo sannu sannu duka wani abu daya faru daren jiya ne yashiga dawo mata cikin brain slowly siraran hawaye ke sauka gefen face din ta ta yaye bargon da aka rufa mata taga yadda take hankalin ta ya kara tashi hawayen ta ya karu kamar an balle fanfo.
        Ko 30 minutes ba ayi ba sega Farid din yazo don yadda yaji muryan aminin nashi yasan ba lafiya ba securities sun rigada sunsan matsayin Omar a gurin sa don haka kai tsaye ya wuce ciki hatta securitie din kofan ya sani, koda ya shiga kwance ya samu Omar din kan sofa, seda ya kare masa kallo tukunna yace." Ya Salam! Omar meyasa meka haka one Time ka rame haka?" A hankali Omar ya bude jajayen Idanun sa ya kalle Farid." Subhanallah!! Omar what's going on!! Look at your eyes, meya same ka haka?" 

  Kamar yay kuka Omar yace." Ammi na Farid! Ban san inda ta tafi ba hatta guards din dasuka tafi tare wayan su a kashe inajin tsoron wani abu ya sameta, taba heart dina kajee yadda yake bugawa ko bacci na kasayi" Omar ya karashe maganar yaname kai hannun Farid din saitin heart dinsa, cike da fargaba da tsoro shima Farid din yace." Omar taya ka bari ta tafi inda baka saniba? Ko baka san ma ta tafi ba?" 

  " Nasan da tafiyan Farid wai bikin wata aminiyar ta akeyi karkaso kaga yadda mukai da ita common don nace zan kaita gidan bikin gashi tace 2 days zatayi, dagewa dataya ne yasa nabari kawai idan na dawo office zanma guards din waya su sanar dani inda ta tafi sedai ta ganni, karshe gashi na kasa samun koda tasu wayan" 

Sauke ajiyan zuciya yayi Farid yana cewa." To Allah yasa lpy, ay ba zama ya kama cemuba ka tashi kayi wanka kai breakfast mu fita duka inda ake wani events, ko kuma ayi tracking numbers din nasu" mikewa kawai Omar yay yace." Babu abinda zanci kawai mu tafi babu wani abunda zan iya, duka yin tracking yanzu ba wahala bane adan lokaci duka inda kae wani biki zamu sani ay banyi wan nan tunanin ba se yanzu" 

  " Please Omar ko bazaka yi wanka ba kayi breakfast semu tafi!" 

" Bazan iya ba Omar, ay dama haka takeso na zauna da yunwar, tunda ta kashe min waya jiyama wayau tayi min tace zata gaya min inda suka tafi amma karshe ta kashe wayan ta gaba daya har yanzu switched off meyasa?" 

  Murmushi kawai Farid yayi yana cewa." Omar tunda harkayi waya ma da ita aise ka kwantar da hankalin ka, maybe kaine bataso kaje inda take" 

" Farid zanfi kowa farin ciki idan hakan ne, amma kasani tabbas wan nan bugun da heart dina yake bana lpy bane nayi dreams marasa dadi nata dole tana cikin wani hali!" Ganin hankalin na Omar yagama tashi ne yasoma rarrashi sa dakyar yay wanka yadan sha ruwan tea suka fice....✍️