11
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode Eleven
Ta kusa awa anan kwance san nan ta daure ta sauka kan bed din tashiga bathroom tagama bukatan da zatayi ta fito ko mai bata iya shafa ba ta bude jaka ta dauki kaya ta saka, jiki babu kwari haka tayi sallah bayan ta gama Addu'ah ne ta mike ko ina seda ta leka tana neman sadiya bata ganta ba, wan nan dalilin ne yasa jikin ta kuma yin sanyi ga abincin dataci jiya shima babushi ba dalilin sa ko lemon babu komawa tayi ta zauna tana cigaba da zubar hawaye ta furta.
" Ya Allah! Ina cikin wani hali, meke shirin faruwa danine haka?"
Maya taci kuka ta koshi ido yay luhu luhu ta tasa sadiya a gaba tana cewa " sadiya kinfi kowa sanina akan kishi babu abinda bazan iya aikata wa ba mussam man wan nan Zainab din danake jin tsanar ta har cikin jinina wai jiya Omar saboda itane ya mammare ni abinda ko a mafarki ban taba tsamma niba cin mutum ci jiya na ganshi wai ni zecewa ze kulle aure na kuma wai yana rawa akanta!!"
Ta karashe maganar cikin kuka, murmushi kawai sadiya tayi tace." Haba maya sekace bakya dani a duniyar nan zaki tsaya kina wani kuka akan namiji, komai ayau zezo karshe sha kurumin ki, yanzu dai buda Data din wayanki kisoma ganin abinda yake faruwa shiga YouTube kisha kallo" cikin jin haushi Maya tace." Haba sadiya mezanyi a wani YouTube yanzu? Ki gaya min abinda yake faruwa mana!" Wayar tata sadiya kawai ta dauka ta shiga YouTube din ta kamo abinda take da bukata ta mika mata wayan tana dariya harda buga kafa, kurawa wayar ido maya tayi kamar ta shige ciki, hawaye zafafa na sintiri akan idon ta, kasa karasa ganin vidio din tayi ta rintse idanun ta cikin wani irin yanayi tace.
" Sadiya dagaske mijina ne yashiga duniya haka, agaban wan nan ta tattar karuwar, hakika tayi asara wan nan dama daga nin ta kalar karuwai gareta, Allah na gode maka daka saka tsoron ka cikin zuciyan mijina be biyewa wan nan shedaniyar matar ba, kuma in Sha ALLAH sena dagar gaza mata baki tunda tawa mijina kiss sena karairaya mata hannuwan iskancin, haba shiyasa jiya yabi daga hankalin sa ashe ga abinda ta aikata, shiga me masoyi ya to Allah ya toni asirin matsiya ciya, sadiya taya kika shiga wan nan dakin batare da sun ganki ba, gaskiya zuwa yanzu lamarin ki ya dena bani mamaki se tsoro"
Cikin dariya sadiya tace." Hmmm!! Wan nan vidio kadan ne daga cikin wanda nayi musu bazan iya nuna miki bane don zuciyan ki tsaf zata buga, kuma yanzu ma saboda mijin nakine yasa bansa an dora video duka ba, a yanzu haka wan nan vidio yana gabda zaga family dinsu ma, ita da farin ciki fa sedai taga anayi, yanzu dai mijin ki shine ya rage mana don muddin muka barshi haka nida ke gaba daya muna ruwa, hakan kuma daya faru baze sa ya dena bibiyar taba don akan sonda yake mata a yanzu kema sheda ce"
" Wlh sadiya indai ina raye Omar be isa ya auro min waccar karuwar ba" Maya tasoma maganar cikin fushi da daga murya, hakan yasa ta riko mata hannu tana cewa." Haba maya kin manta gidan cike yake da mutane, ki nutsu mana ay seda ma nasama mana mafita nazo gurin ki, bari ki gani"
Wani abu sadiya ta ciro jakar ta shiba fata ba shiba tsumma ba, ta soma cewa." Ki saurare ni dakyau Maya! Wan nan maganin na hannu na muddin yacisa a abinci to ya rigada ya zama salla mamme se yadda kikai dashi, da akwai laya a cikin sa ita kuma karkashin da yake kwanciya zaki saka ina nufin kasan katifan sa zaki ajeshi, maganin kuwa bayan kin cire layan yawun ki zaki tofa a ciki yadda ze isa ki yamutse sa seya dan dauki mintina zaki juye shi cikin abincin dazeci muddin yacisa tofa mun gama yin nasara don koda wasa be isa ya tuno da wata Zainab ba a rayuwar sa indai kin bashi yaci ya kwanta kan layar nan an wuce gurin"
Sosai Maya kebin abun hannun sadiya da kallo ta wani fannin zuciyan ta na tsoro ta wani bangare tanajin dadi mussam man idan tuna da abinda mijin nata ya mata, hakan yasa cikin murmushi ta ansa tana cewa." Ay ni indai ze manta da shegiya babu abinda bazan ba kuma naji dadi sadiya tabbas yadda kika tema keni kika faranta min yanzu kema zan jikaki da nera"
Sadiya baki ta soma yagewa itama tana zuba godiya najin dadi, mikewa Maya kawai tayi tana cewa." Bari kiga na tashi aikin nan ay babu sanya a cikin sa, nasan beyi breakfast bah bari naje na cika aiki ay bani zan kai masa bama fadima zan bawa ta kai masa tunda jiya munyi rigima" sadiya tana mata dariya ta fice sauri sauri ta gama hada masa komai maganin kuwa cikin farfesun naman ta zuba masa shi kuma kadan ta zuba iya cikin sa yadda baze rageba, ta fito direct ta bawa fadima tray din tana cewa." Fadima don Allah mikawa yayan ki abinci mana, nasan yanzu yana daf da fitowa kuma be karyaba, fita zeyi, gurin su Baby zani yanzu" Sam fadima bata kawo komai ba don tasaba kai masan haka yasa ta ansa tray din ta haura saman nashi ita kuwa Maya Addu'ah kawai take yaci farfesun nan,
Koda fadima tayi knocking kai tsaye ya bata izinin shiga dakin tana shiga ta samesa ya gama shirin sa nit turare ma yake fesawa, cikin mamaki fadima tace." Yaya badai fita zakayi bakai kummalo ba?"
Murmushi karfin hali yayi yace." Fadima waida fita zanyi, donma na makara da tuni na fice"
" A ah Yaya duk sauri kuwa ka tsaya ko yaya kayi kummalo don Allah baka tafi da yunwa ba" harga Allah dama Omar yunwar yakeji don rabon sa da wani abu tun naman da sukaci a jiya shida baby, beyi garda maba yace." To zubamin nayi sauri naci don gaskiya sauri nake" murmushi kawai tayi ta zuba masa farfesun da Irish gami da hadadden tea dinsa, ta fita shi kuma ya zauna sauri sauri yakecin komai don gaba daya hankalin sa naga Zainab ita kawai yake da burin gani da kuma lafiyan ta, sedai kuma me yana cikin sipping tea din bayan ya cinye farfesun tass yasoma jin kamar wani abu na masa yawo aka nan da nan kan yasoma sara masa har yana lumshe eyes dinsa yana ganin wani jiwa sama sama, aje cup din yay ya dafe kansa yanajin zuciyan sa na masa wani irin tukuki.
" Ya Salam!!"
Shine kawai abinda Omar ya iya furta wa daga nan ya fara gani dishi dishi sam besan sanda ya sulale a gurin ba,
Shanono
Gidan inuwa mu'az, yana gida kuwa anyi sa a bayan dawowan su daga sallan juma a ne aka hallara a babban parlour ana fira kamar yadda aka saba sedai banda Esmaeel da tun da sassafe ya tafi Abuja gurin aminin nashi Omar, sako ma aikatan gidan suka kawo ma Alhj inuwan wanda har hajiya sa a tana yin tsaki gurin cewa." Kalli yanzu neman temakon ma na mutane an koma kawo maka cikin envelope saboda samun guri" murmushi kawai yay irin nasu na dattijai yace." To idan ma bukata ce aiba aibu bane don an sakaya" yana maganar yana budewa, duff yay kamar ruwa ya cinye shi arba dayay da abinda ke ciki, daya bayan daya ya gama zaro hotunan ya kallesu tass, kaf dakin shi aka zubawa idanu mussam man hajiyan data zuba masa ido ta kasa hakuri tace." Hotunan menene haka a ciki?"
Sauke ajiyan zuciya yayi yana cewa." Taso ki tayani gani" zumbur kam ta mike ta zauna gefensa ya mika mata hotunan yana cewa." Tayani gani, wan nan kamar Zainab matar Eshan dina" jikin ta har bari yake ta ansa hotunan tana kalla cike da matukar mamaki tace." kai anya wan nan Zainab ce da wan nan dan yen aikin?" Tabe baki yay gami da cewa." Koma meye dai zan gasgata ta cikin wan nan disk din, zaro shi yay cikin envelope din ya mike kai tsaye yay dakin sa yabar kowa da sakak ken Baki, tashin sa keda wuya kowa yaywa hajiya rumfa don ganin me hotunan suka kunsa, sakin musu kawai tayi itama ta mike tabi bayan sa, time din harya saka faifan sidin ma cikin laptop dinsa, suka fara gani tare, ai kuwa hajiya ta fara salati da sallal lami tana cewa.
" Wlh ko kaffara bazan ba wan nan Zainab ce, ga muryan ta radau inaji, kadubi yadda take nanewa namiji yana tureta saboda asara wan nan video karya take tace hadashi akayi! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! Shine abinda ta soma furtawa saka makon fuskan Omar da aka nuno yanzun, hannun ta yana rawa ta nuna shi tace." Wan nan Alhj kamar tsohon saurayin nan nata tun a hoton can naso ganeshi gashi yanzu ya bayyana, HASBINALLAH WA NI'IMAL WAKIL!! Tabbas wan nan tsohon saurayin tane bazan manta fuskan saba dukda ya girma!"
Jikin Alhj inuwa a sanyaye yake kallon ta wanda idanun sa suka rikide da tsananin bacin rai yace." Toh!! Wan nan tsohon saurayin nata kenan kike nufi?"
Shifa wlh Alhj shine harka mance fuskan sa aminin Esmaeel kuwa Omar" idanun sa tafda kwallah yace." Haba Zainab! Daga mutuwar dan nawa!" Sakayyar da zakiyi mana kenan? Yanzu wan nan abin ya baza duniya ina za zan tsoma rayuwa ta harkar siyasa ta, ni kaina se anyi min sharri"
" To kasani ma ko tun yana rayen take cin dunduniyar sa se yanzu dubun sa ta cika! Wlh Wlh da gaya min akayi bazan yadda ba segashi Allah ya nuna min kiri kiri, kai wan nan yarinya baki kyauta mana ba haka baki kyauta wa kanki ba, yana dafe da kansa cikin tunanin sa yace." Kai wan nan lamarin fa akwai daure kai wan nan aminin nashi ba a Abuja yake zaune ba, Zainab da take kano ba inda take zuwa! Sedai in biyo ta yayi koh? To amma ay gurin sama fa Esmaeel ya tafi yau"
" Wlh Alhj wan nan Zainab ce ko kaffara bazan ba, bawani biyo tan dazeyi kabar mutum da abinda yakeso in karshe duniya ne Zainab binsa zatai"
" No bari dai na kira layin ta kai tsaye" koda ya kira number din Zainab din yaji ta a kashe hakan yasa shi cewa." Omar din nata ai yana gida yanzu tunda baya fita aiki da wuri ranar Friday bari na kirashi ya hadani da ita....✍️