12
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode twelve
Koda ya kira Omar ringing 2 ya daga, sedai a yadda yaji muryan nasa ne yasa ya tambaye sa." Bakada lpy ne Omar?" Ay koda yaji haka seya aro jarumta ya mike daga lafewan dayay kusada Farid yana cewa." Ina lpy kaka inajin gajiya ne" eyyah sannu kajee dama Ammin ka zaka hadani da ita muyi magana naji kamar baka gida ma kana hanya" ina hanya dai yanzu idan na koma sena hadaku a wayan"
"A ah kawai idan ka koma ma ka shaida mata ta shirya tazo nan gidan inason ganin ta" kirjin Omar na dukan hudu hudu ya tattaro maganar a bakin sa yace." Ina fata lpy dai kaka nah"
" Ina fata lafiyan dai ya dore yaron kirki, yaudai kasheda mata ta iso shanono don maganan mu me muhimman ci ce" koda Omar yaji haka jikin sa na wani irin karayin sanyi ya kashe wayan nasa gaba daya, ya dora kansa a shoulder din Farid kamar zeyi kuka yace." Farid wlh Ammi tasani a trouble wai ina tashiga haka? Yanzu ya takeso nayi da life ditane, mezan cewa grandpa yana neman ta so take se kowa yasan bata gida ne?" Farid ganin aminin nashi hankalin sa ya tashine ya karasa hugging dinsa yana rarrashin." Haba Omar dayar dar Allah babu abinda ze faruma, so please calm yourself down"
Da jajayen Idanun sa ya kalle Farid yace." Me kakeso nacewa grandpa meyasa ma zata kashe wayan ta haka, dole tsan hankali nah ze tashi why!!"
Sosai Farid ke tausar sa harya dan sami nutsuwa,
Ita kuwa Zeetah tana nan kwance ta rasa meke mata dadi a duniyar me nikab dince dai ta tsaya mata a zuciya ita da namijin da suka zo mata, ganin tunanin bashi ne mafita ba ta mike ta dauka wayan ta dake kan mirror ta kunna hawaye sabbi na zubo mata tunowa datayi da dan lelen nata ta tabbatar da yanzu duk inda yake hankalin sa ba a kwance ba, hakan yasata soma kiran sa a waya taji switched off, hankalin ta yay matukar tashi tsoro na shigan ta ta furta.
" No my son kardai baka da lpy gashi ba kowa a tare dakai, gaskiya bazan iya zama ba dole na tafi gida yanzun, don lafiyan yarona tafiye min komai a rayuwa ta" cikin sauri ta gama hada komatsen ta in 15 minutes ta gama shirin ta gaba daya hankalin ta baya jikin ta seda ta kama handle zata bude kofan ta tsaya saboda zaryan da Omar Abuja ke mata a zuciyan ta, rintse idanun ta tay tana cewa." Kayi hakuri Omar wlh kunyar kama nakeji har yanzu baka dawo guna ba, hakan ya tabbatar min da cewa fushi kake dani abinda nayi maka jiya, sam ba a hayyaci na nakeba ban san meya sameniba, kada kayi tunanin nazama mutuniyar banza ne yanzu, gaskiya ya kamata nayi maka bayani kafin na tafi, koma wa tayi ta zauna ta duba cards din daya bata ta saka contact dinsa ta kirashi har sau babu adadi amma beyi picking ba, sosai jikin ta ya karayin sanyi hawaye yaki daukewa a fuskan ta seda taga tana kara batawa kanta time ne ta mike ta gyara face din ta, cikin aro jarumta ta fita, suka gaisa da guards din ta shaida musu ay tafiya zasuyi yanzu, duk irin sonsu da suji meke faruwa ta sharesu haka suka saka kayan ta a mota da abinda zasuyi suka dauki hanya,
Omar Abuja yana kwance kan bed dinsa yanata bacci abinsa tunda Maya tashiga dakin a Time din taga halin dayake ciki saboda hauka farin ciki ne ya kamata, cikin saurin ta taje ta daga katifa tasaka layan da sadiya ta bata kuma ta site din dayake kwanciya, bayan hakane ta tasheshi ya koma kan bed din batare da gadda maba ya kwanta, shine haryanzu be farkaba har la asar na shirin gotawa, mutan gidan kuwa seta shaida musu ay bashida lpy, to a yanzun ma ta shigo ne ta tashesa ya shirya don mutane sun gama taruwa, koda shigowan ta dakin ta hangi wayan sa nata haske akan mirror, direct ta wuce gurin wayar dama bata da shamaki da wayan sa tana bude security na wayan tasoma cin karo da messages din Zainab da missed calls dinta, seda ta gama karance sakonnin tass na ban hakuri da masa bayanin abinda ya faru, Maya tai wata shewa gamida goge su duka har calls din kuwa taje tayi blocking number din tata kuma, ranta fess batajin komai taje ta tasheshi a baccin yana mikewa suka hada idanu ya sunkuyar da nashi kan, hakan yasa ta sakin smile cikin cool voice tace.
" Se yanzu ka tashi"
Shima dan guntun murmushi yay gami da cewa." wan nan baccin ayke kika sani yinsa gashi naga time yaja dayawa banyi sallah ba"
" To naji, yanzu dai kanada wani appointment ne yau?"
Shiru kawai Omar yay yanason tuna wasu abubuwa amma ya kasa yanaji kamar ana maida masa tunanin wani kala, kawai seya girgiza mata kai alamun a ah, cikin jin dadi tace.
" Ohk, ya kamata ka shirya mutane na jiran mu cake din ya iso ma ba jimawa" daga mata kai kawai Omar yay yana sauka kan bed din yana wani lumshe idanu jin wani bakon yanayi dayake a tare dashi mara dadi mussam man kansa dake sara masan a yanzu, hakan dai ya shiga bathroom din ita kuma ta fita ranta fess,
Omar kano, kana ganin sa ze baka tausayi halin da ya shiga, duka wasu manyan holes da ake biki babu inda basu zaga ba, basuyi nasaran samun Ammin tashi ba, gashi ya kasa kunna wayar sa saboda besan meze ce masaba, sosai yake nadamar karyan daya fara ma kakan nashi daya sani gaskiya kawai ya sanar dashi, sosai yake bukatan hutu Omar don dakyar yake iya bude eyes dinsa nauyin da sukayi masa na rashin bacci dayay daren jiya, hakan yasa dole suka koma gida ranar fita aikin da beyi ba kenan, zuciyan sa fall da tunani shiba abin ya nemi jami ay ba, tunda ba bata tayiba, yarasa dalilin ta nayi masa hakan, tashin hankalin daya kara samun Omar kuwa shine, suna isa gida suka tarar da Alhj inuwa dakan shi da hajiyan Kuma, suna jiransa, kunya ce yakamasa over cuz kallo da yaga kakan nasa na masa, suduka suka tsugunna suka gaisa, duk jikin Omar yay sanyi suka haura saman,
" Omar banyi tsamma nin karya daga gareka ba, hasali ma bansan ka iyata ba seyau, yaushe ka soma boye min lamuran cikin gidan nan haka?" Alhj yake masa magana tun kafin su zauna,
Sosai Omar yakejin zafin abinda Ammin tashi ta aikata a yanzun, cikin wani irin yanayi Omar yace." Kayi hakuri sam ban taba tsamma ni tafiyan Ammi ze kasance hakaba, nima kaina bansan ina tajeba, duka ta rufe layikan ta don kada na sameta ma, yau ban fita aiki ba saboda neman ta, duka hankali nah a tashe yake, bata taba yin hakaba se wan nan karon, banason nasaku a damuwa shiyasa nayi maka karya a dazu bansan abin yakai hakaba, ka gafarce ni"
" INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! Wlh Alhj ta tabbata wan nan Zainab ce, wan nan yarinya zata samu a bakin duniya, kai amma Allah ya wadaran halinki Zainab" shine kawai abinda hajiya take mai maita wa, kamar me koyon magana Omar yace.
" Wace Zainab kike nufi ne hajiya?"
" Zainab mahaifiyar ka, tadauko mana magana Omar san nan ta zubar da mutumci ta a idan duniya" sosai heart din sa ke tafasa jin yadda hajiya ke ciwa Ammin tashi mutum ci ido cike da kwalla yace.
" Meta aikata haka?"
Katse shi Alhj yay da cewa." Omar bata sanar dakai inda ta tafi bane? Kuma me tajeyi ne?"
Shiru Omar yadan yi don se ayunzun ma yasoma wan nan tunanin kodai bata garin nema gaba daya, don ita dai bata ce dashi a nan kano din ake bikin ba, meyasa nema beyi wan nan tunanin ba seyanzu? Jiki yayi sanyi kalau ya dago yana cewa.
" Tace zata bikin aminiyar ta, but bata sanar dani inda ake bikin ba, bata ma so naje inda take din"
" Ay kam bazata so ka bita ba don ba abin azziki take yowaba, gaskiya Zainab kin bani mamaki matuka" Alhj yana maganar yana jinjina Kai, hakan yasa Omar cikin tashin hankali yana cewa." Ammin tawa!! Metayi ne haka? Taya kuka san bata gida? Ina ta tafi?" Duka yake jero musu tambayoyi, cikin wani irin fushi hajiya ta jefa masa envelope din ya tsura mata ido ko tabata ya kasa don tabbas yasan ba abin alheri bane a ciki, seda hajiyan ta masa magana ne akan ya bude tukunna yasoma budeta, zuciyan sa na lugude, yasoma zaro hotunan ciki, hannun sa na kakkarwa ya sakesu su biyu kawai ya iya gani cikin photos din, ganin haka ne yasa hajiya mikewa ta cira disc din taje zata saka ma Omar din ya gani Alhj yasoma mata magana kartayi haka, amma sam batama sauraren sa seda ta gama kunna kayan kallon ta sakawa Omar faifan nan sam kasa jurewa yay yaje ya kashe kayan kallon ya koma yay zaman dabaro ya hade kansa da gwiwa yanajin kamar ze tarwatse kasa jurewa yay yasoma Kuka Hajiya ta cigaba da cewa.
" Kaf family mahaifiyar kace ta fara mana irin wan nan bankadar, koma meta ke aikata wa ma yau Allah yayi dubun ta ta cika, asirin ta ya tonu, saura ta dawo muga mezata ce kuma" Omar gani yake kamar yana dreaming ne ga magan ganun hajiya na sukar shi, cikin tausa yawa Alhj yace." Tunda naga abun nan Omar kaine kawai ka fara bani tausayi da mahaifin ka, dole zakayi kuka, amma banason haka sam namiji ba ason sa da raguwan zuciya ba, sam ba a kanmu aka fara ba, kuma baza a kare kanmu ba, don haka dena kukan nan, yanzu ka kuma kira mana ita muji in za a sameta"
" Omar yanajan wani irin ajiyan zuciya ya kunna wayar nashi hannun nasa yana rawa saboda tsananin bacin rai da bakin ciki, cikin 'yan sakanni da kunna wayar sega kiran Ammin nashi yana shigo wa, yaname jin zafin ta kuwa ya daga kiran yana kuka yana cewa.
" Ammi meyasa zakiyi min haka? Yaushe kika zama haka kuma? Kin bani mamaki wlh kinyi abinda ban taba tunani ba a rayuwa ta"
Hankalin ta yay matukar tashi dajin muryan sa datai cikin kuka, cikin zubar hawaye tace." Son kayimin afuwa ka gafarce ni nima banyi tsamma nin haka ba, amma na kusa kano in Sha ALLAH yanzu zan karaso gidan"
" What!! Serious dama garin kika bari?" Kasa ce masa komai Zainab tayi ta kashe kiran, bin wayar Omar yake da wani irin kallo yana ayyana abubuwa da dama a ransa, duka wasu alamomin rashin gaskiya data fara nuna masa kan tafiyan,
" Ashe bata cikin garin kano ma! Taya akai kuka sami vidio din nan?"
Hajiya tace." Indai masoyin nata tabi to tana Abuja, don canne inda Omar din yake zaune da iyalan sa yanzu"
Tsamm!! Omar yaji saukan maganar hajiya a brain dinsa, cikin wani kalar mamaki." Yace Omar Kuma! Shine wanda take magana akansa kenan?"
" To karewar magana ma gashi ka gansu tare ta bishi" sauke idonsa yay daga kan hajiya yana kara nanata sunan Omar a bakin sa, cikin bacin rai Alhj inuwa yace." Wai meta fada maka ne? Tanada niyyar dawowa ko kuwa shanya mu zatayi anan?" Cikin takaici ya sanar musu ay ta kusa karaso wa, gudu sosai sukayi a motan nasu kamar sa tashi sama duka hankalin ta a tashe yake cikin mintuna da basu 30 bah suka iso gidan kota kan kaya bata tsaya biba tai ciki Zainab,sam bata kula da Farid bah dake zaune a parlour hankalin yay upstairs seji tai yana mata sannu da zuwa harta so tsorata ma dan murmushi ta kakalo masa tace
" sweetheart din nawa yana cikine?" Ta tambaye sa, " Eh suna sama shida su kaka" sosai taji kirjin ta yana bugu tadan tsura masa idanu cikin kaduwa san nan ta wuce, a yanayin data samesu ne ta san da akwai matsala kusa da Omar din ta zauna jiki a sanyaye tace." Hajiya sannu ku da zuwa" suduka idanu suka zuba mata bawanda ya iya ce mata kala slowly ta kalli Omar da har yanzu hawaye ke fita a idanun sa, kallon sa datayi ne yasa idanun ta saukan kan hotunan da akayi mata, ganin kamar gizo hotunan ke mata yasa mika hannu ta dauki hotunan, sakin su tayi hotunan ta dora hannu wa biyu duka aka tana jera Addu'ah duk wadda tazo bakin ta a kufule hajiya tace.
" Babu wani borin kunya dazakiyi Zainab Allah ya riga ya toni asirin ki, kuma wlh kinyi asara, mamaki kikeyi yadda wan nan abin ya same muko? To bari ma ki kara gani" hajiya ta mike ta kunna mata kayan kallon, zubawa TV din idanu Zainab kawai tayi tsananin mamaki ne kawai ya hanata koda motsi hatta hawayen ma ta nemesu ta rasa saboda tsananin tashin hankali,
" Zainab shin kinada ja akan wan nan video?" Alhj ya tambaye ta, shiru Zainab tayi ta kasa cewa kala kirjin ta kawai ta dafe wanda takejin kamar ze balle saboda bugawa zama hajiya tayi tana cewa." Zainab amsa daya tal zaki bamu, shin kece wan nan koba ke bace?" Kallon ta Omar yake so yake kawai yaji amsar dazata bada, ai kuwa seji yay tace.
" Nice hajiya amman na rantse da girman Allah bansan taya hakan ta kasance ba" dakatar da ita Alhj yay yace." Ay shikenan kuma magana ta kare Zainab tunda ke dince, banason kumajin wani bayani dazakiyi bashi da amfani, kin rigada kinci amana Zainab dole na kira iyayen ki sena dauki mataki akanki inaji ina gani bazan bari ki lalata min rayuwar jika ba"
Omar kuwa tunda ta amsa itace ya rintsa eyes dinsa yanajin wani nauyi a heart dinsa se a time din takejin hawaye masu zafi na bi mata fuska....✍️