🧑‍🍼 RABO...❣️

13

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode thirteen 


Rarrafawa tayi kusada Alhj tana me sakin kukan tausayi." Abbah koda wasa wlh bantaba tunanin cin amanar kuba niba mutuniyar banza bace kowa yasani, sedai amma yanzu banida wata mafita akan wan nan seyanzu nake gani babban wautar danayi, kuma babu komai Allah yanan nan shine shedatah!"

Cikin fushi hajiya tace." Ai dama Allah ba azzaluman bayin sabane, sam baki taba tunanin idan kikayi iskancin ki ze iya dawowa garemu ba, mayau dariya anmiki rana kinyi wa mutu ne dare kin kunya tamu, gara da Allah yasa dana baya raye, dayanzu yayi mugun ji da mugun gani, sam Allah baze barkiba Zainab! Iyayen ki zasuji mugun labari ayko hakkin tarbiyyar dasu ka miki baya bari kisha ruwa ba a duniya" 

   Zainab ki fadamin tsakani da Allah,yaushe kika zama haka? Kodama halinki ne bamu saniba?" Alhj yake tambayar ta cikeda mamaki ta har yanzu, rikeshi Zainab tayi cikin matsanan cin kuka tace " narantse da girman Allah Abbah ban taba aikata zinaba sam ba halina bane, banje Abuja da wani mugun nufi a zuciya ta ba se alkhari, bansani wani makiyin nawa bane wan nan yamin haka har yanzu nagaza yardar ma kaina abinda nake gani yanzu, wlh koda wasa bansan taya na aikata hakan ba Abbah ka yarda dani don Allah, koda kowa be fahimce niba kada ku kullace ni ina rokun ku!!" 

   Tana maganar tana wani irin jan numfashi, seda tayi shirune tana gunjin kukan ta Alhj yace " dole Omar yazo gobe ya samemu ay se anyi zama akan wan nan lamarin zanji idan ma wani abu ne yabaki kikasha gaskiya zatayi halin ta gobe dayar dar Allah" 

  " Abbah shima fushi yake dani nasan ma baze zoba koda an kirashi, amma nikaina yanzu abin yafi karfin tunani na zuciya ta zata iya bugawa wlh bansan waye yamin hakaba!"

" Badai kyaso yazo ya fadi gaskiya ne, saboda kinsan abinda kika aikata akan me zakice fushi yake dake" hajiya tana maganar tana galla mata harara, " Aikuwa dole yazo nan, zan kira ma Esmaeel nashaida masa lallai lallai ya tahomin da Omar gidan nan gobe" 

   Anan take ya kira Esmaeel din kam ya shaida masa, daga haka ya sallami kowa yace kafin goben, inda aka shirya musu domin kwanciya bacci suka wuce, hajiya nata hararan Zainab, wadda ita kuma zuwa tayi ta rike hannun dan nata tana cewa " Sweetheart kaima ka yarda zan aikata wan nan laifin?" Murmushi dayafi kuka ciwo Omar yayi san nan ya kalle ta yace " why not Ammi? I'm ashamed to call you my mother! I don't know what I call you now, kin bani mamaki" kasa tanka masa tayi ta cigaba da kuka me cin Rai, zuciyan sa na tafasa  ya fisge hannun sa yay gaba, sam Farid besan Omar ya sauko bama hankali sa naga waya fuskan sa tana dauke da shock seda Omar ya kare masa kallo tukunna ya zauna gefensa yana me kai idanun sa kan wayar yaga meya dauki hankalin sa haka, sedai abinda yay tozali da shine yasa shi wartar wayan Farid din batare da yasani bah yana kallo yana kara mitsitsi k idanun sa murya na sarke wa yace " Please Farid karka cemin ta YouTube kake ganin vidio din nan!" Cikin kidima shima yace " No!! oh God! karkace min Ammi ce wan nan!" Yafada kamar zeyi kuka, ay besan sanda yasaki wayar ba Omar ya fada jikin Farid yana me cigaba da kuka

   " INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! Wlh ko a tatsuniya ban taba zaton haka zata kasance bah, Farid vidio din Ammi har a YouTube shikenan tariga da ta cuceni" kara rungume shi yay Farid cikin muryan tausaya wa yace " gaskiya ko waye wan nan baya kaunar Ammi ko kadan, wani irin tozarci ne wannan? Am so sorry Omar!" Mikewa yay ya dauka wayan ta Farid ya kuma haurawa saman yana bude kofan ta dago dara daran idanun ta tana kallon sa wanda sunyi jajir saboda kuka, tsugunna wa yay a gaban ta inda take a durkushe, ya kunna mata vidio din yana cewa " vidio din ki Ammi a YouTube, Allah ne kadai yasan iya adadin mutanen dazasu miki mugun fata, shin kekuwa garin ya kikayi haka Ammi? Meyake shirin faruwa damu ne haka? Tunda fari karya kikai min, saboda haka kada kiga laifi na donna ki yarda dake yanzu! Wan nan ba masoyin ki bane makiyin kine, kalli abinda kika jawo mana yanzu" 

   Hannun sa ta rike cikin kuka zatayi magana ya kwace hannun sa ya mike don bayama son jin komai daga gurin ta, hakanne yasata kamo legs dinsa cikin jan zuciya tana cewa " koda kowa ze kini be kamata kayi min hakaba my son please kada ciwon zuciya ya kamani, kafi kowa sanin halina a duniya meyasa zakayi min haka dame zanji ne nikam Zainab!"

  Sunkuya wa yayi ya banbare hannayen ta akan legs dinsa seta kuma kankame masa hannun tana cigaba da kuka dakyar ta iya furta " sweetheart please!" Wani irin takaici ne ya kara kamashi jin sunan nan dayay, ta karfi ya jaye hannuwan sa ya dora kan shoulder din ta, cikin tuhuma yace " meyasa kike kirana da sweetheart?" Kallon sa takeyi don takasa furta ko kalma daya, " meyasa kike cemin haka? Saboda sunan masoyin kine Koh, ban tabajin tsanar sunana ba se yanzu, ashe komai naki da biyu kikeyin sa akai na, meyasa hakan Ammi nakasa jure wan nan bakin cikin naki meyasa ke kuwa?" Ganin tana shirin karyar masa da zuciya ne yasashi ficewa a fusace yabar dakin, duk da yadda taketa kiran sa be wai waye taba, hakan yasata kuma kifa kanta kan cinya ta cigaba da kuka me ratsa zuciya mumini,

    Dakyar Farid ya rarrashe Omar ya dena kuka anan parlour din ma ya kwanta ko saman ya kasa haura wa, shikuma Farid din ya tafi gida don wan nan family issue ne be kamata ya cigaba da zama.

                WASHE GARI

  Tun da wajan 12 iyayen zainab suka iso baba ummah  yaya Haseen da auntie Hashmat, a yadda suka sameta ta basu tausayi sosai sedai koda hajiya ta nuna musu hotunan nan zance yasha ban bam donma Alhj ya hanata kunna musu video din, kuka kawai ummah tasaki wanda ita kuma auntie Hashmat mamaki ya hanata magana wani irin tausayin kanwar tata ne yake kara shigar ta ko kadan bata aminta da wan nan abun ba koma meye tadai san akwai wata a kasa,ita kadaice take rarrashin ta, Esmaeel da Omar Abuja kuwa seda la asar Allah ya musu isowa, tare da ginbiya Maya, yadda taga Zainab ta koma ne yasata yin farin ciki matuka seda sukaci abinci sukai nakk aka zauna Kuma, kamar yadda Zainab ta kasa kallon masoyin nata haka shima ya kasa koda daga kai ya kalla ragowan mutan dakin, Shima Esmaeel yana gefen sa yana kallon ta ta bashi tausayi matuka yana kuma da yakinin Omar masoyin nata ze kareta yanzu, gyara murya Alhj yay gami da cewa

   " Omar inason cikakken bayani dangane da wadan nan hotunan, ka gaya min taya wan nan abin kunyar taku ya fara yawo a duniya harya iso garemu" Omar Kano na zaune zuciyan sa na wani irin suya Omar Abuja kawai yake kallo cike da tarin takaici jiyake kamar ya shakeshi ya huta yanata ayyana dama shine Omar din to dame wan nan zefi daddy sa, kansa akasa Omar Abuja ya fara cewa " Alhj kuyi hakuri da wan nan abun daya faru tun tuni dama abinda nake guje mana kenan, nida ita, shiyasa naketa nisan tarta tana kara kusanto ni, na hada taron birthday dinane se gashi ta kirani wai hartaje Abuja dinma ta sauka hotel tazo tayani murna, nayi mamaki sosai da dai har ban yardaba natafi da wani abokina gurin nata, anan taso rinjiya ta dai Allah ya tsare, wan nan vidio din kuwa da hutuna ina da tabbacin abokin danaje dashi hotel din ne, tunda yana zaune a parlour muna ciki babu abinda baze iyayi bah, ahalin da ake ciki na baza jami ay ana neman sa don ko a lokacin ban fito na sameshi a dakin ba sam bansan meye ma anar bazawa duniya wan nan vidio dinba duka mutum cin mu gashi ze zube ta dalilin sa, kuma guduwar da yayi yasa na kara tabbatar da shine ya mana haka kuma da yardar Allah ya kusa shiga hannu "

   Kaf mutanen dakin nan babu wanda mamaki be baiyana a fuskan saba, ummah da baba basu taba tsamma nin Omar ze iya furta irin wan nan magan ganun a gaban suba, Esmaeel poster yay yana kallon shi, cikin wani irin al ajabi Zainab ke kallon Omar din a yanzu, batasan sanda ta tsince kanta a gaban saba tana jan numfashi dakyar tace " Omar shekara sama da 20 ina dakon sonka ban tabajin tsanar ka ta darsu a zuciya taba se yau, inajin tsanar ka na mamaye min ilahirin zuciya ta, meyasa zakayi min haka? Saboda matarka ko zakayi min wan nan kazafin, bazan yafe maka bah Omar!!" 

  Sosai kalaman ta suka doki zuciyan Omar haryana rintse idanun sa, ganin hakan ne yasa Maya fara magana " Zainab meye haka kuma? Nade tabar mar kunya da hauka, donkin ganki gaban 'yan uwanki zaki fara fuffuka iska hankali ne an koya miki idan zakiyi shi sekiyi, ina kuma me rokon ki daki fita sabgar mijina don Allah, in banda Allah ya kiyaye da tuni ta sanadiyyar ki aure na ya mutu saboda nasan waye mijina ne yasa muka zauna yamin magana ta fahimta da yanzu lamarin mu ya lalace, Zainab ina rokonki ki nutsu ki kama kanki ki kyale min miji haka!" Maya tasaki kukan munafun ci, 

   Kasa jurewa Zainab tayi ta cakumi wuyan rigan Omar din tana kaima sa duka da mari tafashe da wani irin matsanan cin kuka " Omar Allah ya isa tsakani na dakai bazan yafe maka ba butulu kawai macuci!!" Cikin wata irin zuciya yayan ta Haseen ya mike yaje ya fisge ta jikin Omar yasoma sharara mata mari harta kifa kasa, " kinyi asara Zainab kin bani mamaki, kin ban kunya aikece butulu Zainab ba kowa ba, ai bansan kin rika kin fara bin maza ba haka, kinci amanar tarbiyyar mu gareki Zainab Allah baze barki hakaba daga yau bani bake Zainab nariga na sallama ki kuma, tuntuni kike dauko min magana akan Omar to yanzu Alhmdlh ga sakayyar da yayi miki" 

  " Baba na rokeka kar kayimin wan nan hukunci koda zan mutu ya kasance dai bana cikin fushin ku yazanyi da rayuwa ta baba!!"

  Ke kika sani Zainab! wlh ke kika san yadda zakiyi da rayuwar ki! Saboda soyayya kika watsar da tarbiyyar ki kina sabon Allah, dama so kike bakin cikin ki ya kashe ni Zainab haka kikeso dama Koh?" Tasowa tayi cikin tashin hankali tayo gun umman tata tana cewa " Don Allah Ummah ki yafe min kiyi hakuri bansan taya zaku fahimce niba!" Cikin tsawa ummah tace " karki kuskura! Ki karaso inda nake! Sha shashn banza kawai taya zamu fahimce ki dama, ai bamu san irin son da kike masaba koh! Abinda zakice kenan, to ay ga irin tanan Omar din ya koya miki hankali, in banda baki da hankali dama Omar zeki matar sane a yanzu yasoki keda bakida hankali har yanzu" 

  Fadawa tayi jikin auntie Hashmat suna kuka wiwi a tare hakan ne yasa baba jan tsaki, ya mike tsaye yana cewa ku tashi mutafi, Alhj nariga na sallama Zainab gaskiya duk hukunci daka yanke mata a yanzu ya zauna don mukam tafiya ma zamuyi bazamu kara zama nan ba" kallon auntie Hashmat yay daketa faman barzar kuka yace " taso mu tafi malama kin zauna kina tayata kuka saboda Rashi sanin ciwon kai" magana zatayi yaya Haseen ya buga mata uwar tsawa hakan yasa da kyar ta banbare Zainab daga jikin ta ta mike, ayda gudu Zainab taje ta kan kame baba ta bayansa kuka take sosai ko magana ta kasa, 

  Tasssss!! Esmaeel ya dauke Omar Abuja da mari wanda yaketa tambayar sa dalilin yin hakan dayay ya masa shiru zuciya ta kwashe shi ya zuba masa mari kuwa ya nunashi da yatsa cikin karaji yake cewa " karya kake Omar wlh baka isaba dakai da banzan matan taka ku wulakan ta Zainab ina raye, idan ma wani abun tamaka matar taka can ku karata amma baka isaba butulu mugu ka bani mamaki Omar wlh, kuma duka wan nan magan ganun naku karya ne sam bazan yarda dakai ba seka gaya min gaskiya abinda ya faru tsakanin ka da ita! Wani irin azzalu mai ne ku? Sekace bakaga halin daka sata a ciki ba iyayen ta kakeso rabata dasu! Dame zataji ne da yama didin da kuke da ita a duniya ko kuwa da fushin iyaye? Wlh Omar alhakin ta baze bar kuba, kuma ka rubuta ka ajiye kaida ita har abada nine zan aureta kariga kayi bari da damar ka har abada!" 

   Tsawar da Alhj ya daka ma Esmaeel din yasashi sakin wuyan rigan Omar don harya shakesa, cikin fushi da bacin rai Esmaeel yace " haba baba! Don Allah yaza kuyiwa Zainab haka dame zataji ne a rayuwa common saboda yazo ya Karanta muku banza anan karya yake bada gaske yakeba duka sharri zasuyi mata!!.....✍️