15
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode sixteenth
Esmaeel na parlour se jiyo salatin Omar yay kamar ze kifo daga saman steps din sakin wayan hannun sa yayi ya isa gareshi ya tallafa masa sukayi waje da ita aka saka a mota hijab dinta dukya jike da kayan ta a kidime Esmaeel ya koma ya dauko wayan sa yamaida kofan ya rufe suka tafi hospital, batare da bata lokaci ba kuwa aka shiga bata temakon gaggawa kuka Omar yake Sosai sekace karamin yaro Esmaeel nata rarrashin sa da bashi hakuri amma kamar zuga sa yakeyi har zuwa bayan la asar basu sami magana daga gurin Dr hakan yasa jikin su karayin sanyi dama Omar yace ta riga ta mutu boye musu kawai sukeyi sedai ban baki kawai da Esmaeel ke masa, se wajan bayan magrib tukunna Dr din yay musu jagora har office dinsa yake shaida musu su kwantar da hankalin su Zainab tana raye kuma akwai buguwa data samu akan ta ga heart attack dake shirin barazana wa rayuwar ta sedai suna kan shawo matsalan ta bama zasu samu damar ganin taba a yau din sedai gobe, Allah sarki Omar ya Kara shiga tashin hankali seda Esmaeel ya masa jan idanu tukunna ya wuce suka koma gida, tunanin Maya yakasa barin sa da magan ganun ta, koda suka isa gida be shiga ciki ba seya tsaya gurin securities yasa aka binci ko masa vidio din su Maya CCTV camera ga mamakin sa kam yaga Maya cedai ashe tazo dama har gida ta maran masa Ammi se sadiya dayake ta kalla tunanin sa ya tsaya yarasa inda itama yasan ta, kawai mikewa yay yashiga cikin gidan ya kira Farid a waya,
Hankalin sa ya gama dugun zuma dakyar ya haura sama yay wanka idonsa yay jajir ya zuro jallabiya ya fito abinsa kafin ya gama sauko wane sega Farid ya shigo dama yana hanya, suka zauna dining area duk da baya tunanin yanada nutsuwar cin abinci duka wani abu dayaji gurin Maya seda ya gaya masa komai dake faruwa, cikin matsanan cin tausaya wa aminin nashi ya riko masa hannu yace
" Wlh Omar koda wasa dama nakasa aminta da wan nan abunda ya faru, Ammi mutuniyar kirki ce bazata iya aikata wan nan abun ba da hankalin ta dai, to ashe kaji wani masifa da tayi gamo dashi makircin mata kai Allah kai mana tsari dashi tabbas wan nan mata bata kaunar Ammi tabdijan!" Sosai abin yasha kan Farid " Farid wlh na tsani Omar din nan da duka shine silar komai meyasa zeyiwa mahaifia ta haka a gaban iyayen ta da sirikai meyasa ze tozar tamin ita haka? Tanata kaunar sa ashe makiyin tane ma bata saniba, koma meye akan shi wan nan matar tayiwa Ammi haka kuma she will pay it wlh zatasan ta tabo family inuwa, duka senasa an zomin da duka bayanan danake bukata akan ta da kuma wan nan wadda suke taren har nagano Ammi batada laifin komai, wlh nayi rantsuwa Farid itada farin ciki a duniya sedai taga anayi amma ba itaba"
" Cool your mind Omar, ay batun gaskiya ma Ammi ce da ita, komai a sannu zamu bishi Abuja dinma idan takama se muje"
" Me kuke shirin yine?"
Suduka suka juya suna kallon Esmaeel daya juma yana sauraren tattaunawa tasu, " you should be careful fah Omar, Maya matar aure ce, sam ba sa ar yinka bace kada kana fushi kaje kayi aikin dana sani" cike da mamaki Omar ya mike yaje gaban shi yana cewa " yanzu Abbah Esmaeel saboda matar aurece taci bulis kenan abinda tayiwa Ammi? Ta zubar mata da mutumci na har abada, sanadiyyar bakin cikin tane gatacan kwance a hospital, bayan su zakabi kenan yanzu?"
" Listen Omar karka kara tunanin ina goyon bayan sune, duk wan da yaci mutum cin matar yaya na kamar nine yaciwa mutum ci, so kadena wan nan tunanin ma,ko sheda daya a yanzu baka da ita daze nuna gaskiyar abinda kake fada, tabbas Maya ta cika shedaniya, sam ba ita yakama ta kayi magana ba, Omar din dai shine wanda zamu tsanan ta binci ke akansa dole seya fadi gaskiya abinda ya faru domin karyace a jiya yayi ta ba gaskiya ya fada ba dole akwai wata a kasa"
" Dole dasaka hannun matar sa a cikin wan nan zalinci itace ma kan gaba gaskiya kuma zatayi halin ta nan da dan lokaci kowa yasan gaskiya"
" Anyway tunda zakayi binci ke dakan ka nibase na yiba, abu daya zan gaya maka Omar shine kada kasa wasa a lamuran rayuwar ka kaiba rago bane duka kula da kowa na cikin gidan nan yana hannun ka hakkin kane yanzu Abbah ya yarda da hankalin ka nutsuwa tunani shiyasa ya sakar maka business na mahaifin ka, so please kada kayi abinda zebamu kunya kada kudi yasa ka canza halayyen ka Omar" cikin ladabi Omar din yace " in Sha ALLAH Abbah bazan baku kunya bah"
" To shikenan Allah ya maka albarka ya albarka ci rayuwar ka yakare min kai daga sharrin masu sharri "
" Ameen summa Ameen "
Sallama kawai ya musu ya wuce gurin kwanan sa, sun jima suna tattauna wa da Farid yakara kwantar masa da hankali sosai harya samu yaci abinci, san nan suka tafi shida guards dinsa suka kaishi har gida suka dawo, tun a hanya yaketa tunanin daddy nasa wan nan dalilin ne yasa suna dawowa gidan ya zarce part din daddy din, yayi amfani da spare key din dake gurin sa ya bude kofan ya shiga duk da komai na dakin a rufe yake amma wani sashin yay kura lights kawai ya kunna yasoma bincike a dakin duka wani ma ajiyan takaddu da abu me mahimmanci ya duba har dan library din dake ciki duk ya hada uban gumi seda ya duba cikin can cikin drawers din gurin ne ya gano 'yar akwatin dayake nema, cikin hanzari ya dauko ta ya goge amma a kulle take ya kasa budewa to gurin neman keys dinne yasashi harya raba dare be ganiba ya gaji matuka ko fita ya kasayi nan ya zube kan carpet ko Addu'ah be gama bacci ya dauke shi, wanda bashi ya farka ba kuma se da rana ma ta fito wajan 6: 30am seda ya gama karan to Addu'ah tashi a baccin ne yay mika tukunna ya mike ya suri akwatin yay waje ya maida kofan ya kulle, sallah ya fara tukunna yashiga wanka a gaggauce sauri sauri yake shiri domin hankalin sa gaba daya yana gurin Ammi sosai yake kewanta don ruwan wanka da tuni ta hada masa kafin ya fito ta dauko masa kaya yau shine yay komai abinsa, yana aikin fesa turare ne Esmaeel ya dan masa knocking gamida shiga dakin, fuskan sa dauke da damuwa shima yace
" Omar zomuje hospital din nan muga jikin Zainab nima dole naje shanono manahil batada lpy a hospital suka kwana suma" manahil matar Esmaeel kenan, damuwa Omar ya kuma shiga jin Abban nashi ze kuma tafiya ya barshi yana masa jaje da sannu suka tafi hospital din, hankalin Omar ba karamin tashi yay ba bayanin da Dr ya musu matsalan Ammi tashi, brain dinta tana cikin wani matsala ne kuma tasamu buguwa sosai a cikin kanta, wanda Alhmdlh sunyi kokarin shawo matsalan yanzu, batun farka warta kuma tana under coma se ta yadda Allah ta kasance mata walau farkawa ko kuma daga haka shikenan be iya furta komai bah Omar yafice tunda Dr ya sanar dashi room din da take ya tafi yanaji a jikin sa ze iya tashin ta, koda ya shiga tsayawa kawai yay yana kallon ta kamar wadda ta Shekara tana ciwo itaba bacci ba ita ba a mace ba seka kura ido dakyau za aga tana numfashi, hawaye wani na bin wani ya isa gareta yasaka gwiwan sa a kasa cikin muryan kuka yace
" Ammi yanzu ni kadai zaki bari na cigaba da rayuwa? Karkiyi min haka please, koda yaushe ina bukatar ki komai nawa tsaya wa zeyi idan babu ke kada kiyi min haka" ya kwantar da kansa a shamulal len cikin ta yanata zubar hawaye abin tausayi wayan sa tasoma ringing karan daya isheshi ne yaciro ta zesa ta silent yaga kakan sa ke kira, picking yay suka gaisa a cikin damuwa ya sanar dashi halin da Ammin tashi ke ciki, sosai ya jimama abin gaskiya yakuma jadda da masa zasuzo, daga karshe ya shaida masa ya koma company akwai ayyuka dayawa sun taru, seda Esmaeel yagama tattauna wa da Dr ne yabiyo Omar sedai a yadda ya sameshi ne ya bashi tausayi sosai su biyun suka hadu sukayi mata Addu'ah sosai san nan Esmaeel din ya masa sallama ya tafi bayan ya shaida masa zasu dawo tare dasu Abban,
To a haka kwanaki suka soma shudewa satittika na tafiya babu wani abun cigaba kan lamarin Zainab sadaka da sauka Omar ya bada ayi har babu iyaka Addu'ah kuma yinta yake babu fashi tun yana kuka inyana tare da ita harya ware ya koma aiki seya dawo company yake zuwa gunta cikin dan lokaci ya rame dole Farid se gidan ya dawo da kwana saboda debewa aminin nashi kewa duk duda weekend Esmaeel anan yake yinsa shima, batun rashin lafiyan ta Omar sam be sanar da su Ummah ba su auntie Hashmat basu san halin da zeetah din tasu take cikiba,
Yau Monday kamar kullum Omar Kano yana lumtsume men office dinsa yana aiki cikin computer sakatariyan sa ta sanar dashi Joseph ne yazo, cikin zakuwa kam yake shaida mata ya shigo, cikin ladabi yashiga korama Omar bayani dangane da aikin daya basu cikin yaren turanci yake masa jawabi harya kare murmushi sosai Omar keyi har beauty points dinsa na bayyana komai daka tawa dayi yay yana sauraren Joseph kusan 30 minutes suna tattauna wa san nan ya tafi, cikin jin dadi ya makawa Farid waya ya sanar masa yadda sukayi da shi Joseph din....✍️