3
***
*KUNDINA*
*NAFISATU SASAAL*
3.
A hankali na zame kwaɗon zuciyata na tsananta bugu.
Idona a runtse na buɗe littafin, shafin farko ya bayyana, kamar mai tsoron ganin mugun abu haka na buɗe idona a hankali.
Vintage stickers da quotes stickers ne suka ƙawata Kundina a shafi na farko.
Shafi na biyu kalaman soyayyan da saurayina Sadiq yake yawan turomin ta waya ne a waccen lokacin.
Tsananin daɗinsu da yadda suke tashin kaina yasa na ke kwafesu ina ta maimaita karanta su inajin daɗi.
A haka sai da na buɗe shafi goma sha, duk kalaman soyayyar Sadiq ne, masu tsananin daɗin dake nuna irin son da bazai iya rabuwa da ni ba.
Ban wuce kalma ko ɗaya, ba tare da na nanata karantawa haɗe da haddaceshi ba, saboda gujewa kuskuren da na tafka a baya.
Shafi na gaba, wanda ya kama shafi na goma sha biyar, jirwayen ruwan hawayena ne da ya bushe, da stickers na ƙunci kala-kala.
Shafi na goma sha shida mannanen hotonmu ne, ni da yayyena biyu Mata da Mahaifiyarmu.
Hannu na rawa na wuce shafin ina runtse idona.
A shafi na goma sha bakwai na fara rubuta labarin ainihin abinda *KUNDINA* ya ƙunsa.
Idona na ƙara runtsewa gam, na kulle littafin da miƙe da sauri, kamar an mintsine ni.
Inda na ɗaukoshi na mayar na ajjiye, na dawo gefen gado na tsugunna, na fashe da kuka.
Ban san sanda barcin wucin gadi ya ɗaukeni ba, sai da nayi mafarki mara daɗi, na farka a firgice tukunna.
Miƙewa nayi jikina a mace na duba wayata na ga ashe har ƙarfe 9 ta wuce.
Washroom na shiga na wanko fuskanta, sannan na ɗauko wadaccen Hijjabi na saka, haɗe da barin sashen.
Sashen Hajiya Babba, Mace ta farko a wajen mahaifinmu na nufa.
A sashenta nake karɓa abincin safe rana da na dare kullum.
Kai tsaye kitchen ɗinta, da ke da tazara da ƙofar shiga parlonta na nufa.
Na kuwa yi sa'a babu kowa, har ƴan aikinta duk sun tafi makwancinsu.
Na yi niyyar na ɗauki abincina ba sai na shiga na gaisheta ba, amma tuna halinta na mita yasa na fasa, na nufi hanyar shiga parlon.
Yawan takalman da na gani ne yasa na ji kamar na juya, don ga dukkan alamu tana tare da baƙi. Amma sanin irin surutun da zansha idan tasan na zo na ɗauki abinci ban shigo na gaisheta ba, yasa kawai na danna wireless doorbell, ina jiran su buɗe min....✍🏻
Ku yi min afuwa In Sha Allah daga gobe zamu fara pagi mai tsaho na gode🙏🏻