KUNDINA

4

by @nafisatusasaal01

***

*KUNDINA*

*NAFISATU SASAAL*
      ***

4


Sai da na fara gajiya da tsayuwa, sannan aka buɗe min. 

Farida ce ƴar autar Hajiya Babba, Fuskarta a ɗaure da alama ba ta so zuwa buɗewa ba aka taso ta.

Ba ta cemin komai ba nima ban ce mata ba, ta juya ta shige na bi bayanta.

Kamar yanda nayi hasashe hakan ce ta faru.

Aunty Amarya, ƴar gidan Attajiran da Babanmu ya aura bayan Mahaifiyata ce a zaune, cikin adon da yake ƙara bayyana baiwar tsananin kyan halittar da Allah ya yi mata ita da Danginta. 

A gefenta Namiji ne ƙosasshen saurayi wataƙilama Magidanci ne, shima dai kyankyawan gaske ne irinta.

Ƙamshinsu duk ya cika parlon. 

Fuska a sake, zuciyata na tsananta bugun gudun wulaƙanci daga Hajiya Babba na ƙarasa gefen da Hajiya Babban take zaune na zauna, ina yin ƙasa da kaina.

Ita na fara gaisarwa ta amsa kamar kullum, fuskarta babu yabo babu fallasa, sannan na gaishe da Aunty Amarya itama dai kamar yanda halinta yake na shan ƙamshi da nuna sanin darajar kai, haka ta amsa min.

Murya a sanyaye na gaishe da baƙon da ko tantama ba na yi, ba zai wuce a cikin ƙannenta da basa rabo da zuwa duba lafiyarta ba, kuma indai su ka zo sai ta kawosu sun gaishe da abokanan zamanta, ko kuma tasa masu aiki su rakosu.

Kamammiyar kyakyawar fuskarsa a sake ya amsa min.

 Na shi amsawar sai ya fi min na su Hajiya Babba armashi da nuna kulawa a gare ni, don har da ɗan murmushinsa wajen amsa min.

Nima murmushi na saki, sai dai kafin nawa murmushin fuskar ya ɗauke na jiyo muryar Hajiya Babba ta na cewa;

"Ɗazun Alhaji yake sanar da ni zaki koma makaranta, na ce to dai wannan karon sai a kiyaye, kiyi karatu, ki koyi riƙe mutuncin kanki, ba wai ki je  ki ƙara kwaso mana wani abinda kunyar da zaki rabamu da  Alhaji ba, tunda kin raba kanki da taki Mahaifiyar."

Ɗif murmushin fuskata ta ɗauke, wani irin fargaba da kunya suka ziyarceni.

A hankali na ɗago kaina ina kallonta, sai na ga idonta ƙyam akan ɗan uwan Aunty Amarya. 

Anan na fahimci wataƙila ta faɗamin hakane saboda fuskar da ta ga ɗan uwan Aunty Amarya ya sakar min, kar daga baya ya ce yana so na, ko wani abu makamancin haka ya biyo baya.

Daga Aunty Amarya har Ɗan uwan na ta babu wanda ya tofa, sai kallon da Aunty Amarya ta yimin ta ɗauke kai, kamar ma bata ji abinda Hajiya Babban ta faɗa ba.

A gefena da Farida take zaune ina jiyo sautin murmushinta, da alama furucin mahaifiyarta ta yayi mata daɗi.

 Kasa jurewa na yi, ƙwalla ya cika min ido. Da sauri na gogeshi ina ƙara gyara zamana.

A daidai lokacin Aunty Amarya ta ce;

"Hajiya mu zamu wuce, ga wannan Aliyu ya ce a baki, Fatima gobe kema ki zo ki ƙarbi na ki"

Aunty Amarya ta ƙarasa  faɗa tana kallona haɗe matsawa kusa da Hajiya Babba ta ajjiye mata  baƙin ledan da na ke kyautata zaton kuɗi ba ne a ciki.

Baki Hajiya Babba ta washe a zahiri, ta na cewa;

"Ohh Hanifah(Aunty Amarya) shi dai wannan bawan Allah baya gajiya, gaskiya ya kamata ya kawo mana ziyara wata rana mu ganshi a gaisa"

Aunty Amarya bata bi takan maganganunta ba ta ce;

"Jamil tashi mu tafi ko dare ya na yi"

Matashin da Aunty Amarya ta kira Jamil miƙewa ya yi yana cewa Hajiya Babba;

  "sai da safe"

Ni dai idona ya na kan yanda Hajiya Babba take banka mu su harara ta ƙasan ido, amma muryarta a sake da fara'a take cewa;

"To Jamil mu kwana lafiya"

Bayansu Aunty Amarya na bi kallo, a raina ina jinjinawa yanda Allah Ya ke halittar wasu bayin Na sa ya haɗa musu komai, kamar su suka yi kansu.

 Ban taɓa ganin mai duhun fata a danginta ba, ga su masu tsaho da kyan jiki Masha Allah.

Sai da suka ƙarasa ficewa na dawo da hankalina kan Hajiya Babba. 

Irin hararar da take aikomin da shi ne, yasa na miƙe a hanzarce ina cewa;

"Dama Hajiya abinci na zo ɗauka shine nace na shigo na gaisheki. Zan tafi sai da safe"

Maimakon ta ce min sai da safen da nake son ji sai ta fara mitar;

"Ai da baki ɗauke idonki daga kallon bayansu ba, tunda ke mayya ce, ba dama ki ga maza, shinkenan sai ki fito da maitarki fili, to waɗannan dai ba irin ruɓaɓɓun Samarinki ba ne balle ki saka rai.

Sha-sha-sha idan kinga dama ma wannan karon ki je ki kuma biyewa maza su ɗuro miki ciki mahaukaciya kawai, dallacan fice ki bani guri"

Dama abinda nake jira naji ta ce a ƙarshe kenan, don haka na fice a hanzarce na bar Sashen....✍🏻

Ayimin afuwa🙌😂