5
5
SASAAL
***
FATIMA;
Ina tafe ina tunanin hassada irin na Hajiya Babba. A ce abokinyar zamanki duk lokacin da ƴan uwanta suka zo sai ta kawo su kun gaisa, har suyi miki alkhairi amma ace bazata saduda ta daina yi mata hassada ba.
"Shi fa wanda ya fi ka, ya fika"
Na faɗa a zahiri ina ƙara hasaso irin zaratan samari da kuma kyawawan maza da matan da suke yawan zuwa wajen Aunty Amarya.
A hankali na buɗe Sashena na shige, maganganun Hajiya Babba suna dawomin, sai dai ban bari sun dame ni ba, balle su ɓatamin rai.
Shinkafa da miyar da na taho da shi, na tsakura, na ajjiye ragowar.
Wanka na yi nayi wanke bakina, sannan na ɗoro alolan kwanciya.
Cikin ikon Allah ina kwanciya barci mai nauyi ya ɗaukeni.
★washe gari sai gabannin Asuba na farka.
Anan inda nayi sallar Asuba, barci ya ƙara ɗaukeni, ban farka ba sai wajen ƙarfe takwas da na duba wayata.
Jiki a mace na wanko fuskata, na zame Hijjabin kaina, na canza wani.
Takardun makaranta ta na kwaso, na nufi Sashen Baba.
Ban jima ina ƙwanƙwasawa ba, Hajiya Babba ta buɗemin, ban yi mamakin ganinta ba.
Har ƙasa na ranƙwafa na gaisheta, ta amsa tana yamutsa fuska haɗe da shigewa ta bar ni a tsaye..
Sai da na tabbara ta ɗan yi nisa sannan na zura kafata da sallama a bakina.
Tun daga nesa Baba yake ƙaremin kallo, kamar ya na tantace sahihancin sauyin da na ce masa nayi.
Ina zuwa kusa da shi, na raɓa ƙasan ƙafarshi na zauna, na ce;
"Baba ina kwana"
Amsawa ya yi muryarsa a cunkushe.
A take na ji bugun zuciyata ya sauya.
Kafin na gama saita kaina na ji yana cewa;
"Fatima wato bazaki sauya halinki ba ko? Maiyasa bazaki ko yi kama kanki ba? Yanzu da Ɗan uwan Mamanku Hanifah ya ganki jiya kina Kallonsa fa me zaki ce eh? A haka kike so na ƙara baki dama ki koma Jami'a? Sau nawa kike so nayi miki faɗan idan lokacin aurenki ya yi ba sai kin tallata kanki ba eh?"
Zugum nayi har Baba ya gama faɗansa, zuciyata tana tsananta bugu.
Sai dai tuna yanzu ba lokacin shiru ba ne, lokacin kare kaina ne.
Kuma idan na yi masa ƙarya zai iya ganewa, don haka na fara bayanin aihin dalilin da yasa nake kallonshi.
"Wallahi Baba ba ina Kallonsa da wata manufa ba ne sai mamakin yanda Allah Ya haɗawa su Aunty dukiya da kyau. Kuma tun da na shiga ban kalleshi ba, sai lokacin da Hajiya Babba take min faɗan saura idan ka turani makaranta, na je yi ta bin Maza kai ma na rabaka da su kamar yanda na raba kaina da mahaifiyata"
Na ƙarasa maganar muryata ta na rawa.
Cikin danne fushin da na ji yo a muryarsa Baba ya ce;
"Ita Hajiya Babban agaban Jamilun tayi wannan batun"
Da sauri na ce; "eh"
A ɓoye na kalli inda Hajiya Babba take zaune.
Gaba ɗaya manyan idanunta ta zaro.
Ta na yunƙurin kare kanta Baba ya ɗaga mata hannu.
"Fatima tashi ki je anjima zan nemeki"
Jikina ya na rawa na miƙe, na ajjiye Takardun da na taho da shi na a gefensa.
Ban kalli inda Hajiya Babba take ba, na fita daga sashen.
Ina fita na sauke ajiyar zuciya haɗe da ɗan murmushi.
Na san yau Hajiya Babba zatasha faɗa, kuma anjima ta huce a kaina.
Amma ko ba komai, ba ta yi nasarar saka Baba ya hanani komawata makaranta ba.
Da ɗan hanzari na nufi sashen Hajiya Babba na karɓo abun kari.
Masu aikinta suna miƙomin na juya a hanzarce, gudun kar ta dawo daga Sashen Baba mu haɗu da ita.
Har na ɗauki hanyar Sashena na tuna da abinda Aunty Amarya tace na zo na karɓa.
Tuna wataƙila ba ta tashi ba, yasa kawai na haƙura na koma Sashena.
Ina karyawa, ina tuna irin jarumtar da na nuna wajen yiwa Baba bayani.
"Ohhh ashe shiru baya ƙwatar mutum, da yanzu matar nan ta cuceni"
Na faɗa a zahiri ina sakin ƙaramin dariya jin daɗi.
Bayan na karya a gado na miƙe na kunna Data ina ƴan kalle-kalle na.
Sai da naga ƙarfe 10 tayi, sannan na ajjiye wayata, na zura Hijjabi na nufi sashen Aunty Amarya cikin zumuɗi.
Buri na bai wuce ace kuɗi zata bani ba, na samu nayi siyayyan ƙananun abubuwan amfanin da ba ni da su.
Ina isa sashen suna fitowa ita da Ɗan uwanta.
Wani irin kallo Jamil ɗan uwan Aunty Amarya ya yi min irin na mamakin da safe nan har kin zo.
kunya ce ta kamani, tuna abinda Hajiya Babba ta faɗa a gabansa, da kuma zuwan da nayi safe kafin ya bar gidan.
A tunani na zai ce wannan ba dai son duniya ba.
Wayancewa nayi zan koma.
Aunty Amarya ta ce;
"A'a Fatima ƙaraso mana, ai nice na ce ki zo da safe ko?"
Ai tana cewa haka na ji kamar na nutse cikin ƙasa, domin a jiya ba tace na zo da safe na karɓa ba, ta dai ce nazo gobe.
Soshe-soshe gefen fuskata na fara yi, cikin kame-kame na ce;
"Ina kwanan ku Aunty, an tashi lafiya"
Ita kaɗai ta amsamin Jamil inda ake ajjiye motoci ya na nufa ba tare da ya waiwayo ba, balle na sakaran zai amsa.
Murmushi Aunty Amarya ta saki, ta ce;
"Shiga ciki ki jirani ina zuwa"
Kamar zan ce mata a'a saboda kunya, sai kuma na fasa sum-sum na shige sashen inaji a raina dama na haƙura ban zo ba...✍🏻