Chapter 6
...RIGAR ƘAYA!*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
Page 6
"Ki zauna mana" Cewar Khalid yana ta kallonta.
Ta girgiza kai tana kokowa da hawayen da yake neman ƙwace mata ta ce"Ka ba ni kawai sauri nake yi".
Ya tsura mata ido yana tuna lokaci na farko da ya kasance da Hasina a wani Hotel, sai ya ji kamar da ita ne, ya aikata ne saboda kammanin da take yi da Muhasin ɗinsa, a ganinsa hakan zai huce masa takaicin rasa ta, zai ji kamar da ita ya kasance, yau ga Muhasin ɗin a gabansa, a ɗakin hotel inda babu wani wanda zai kwaɓe shi, amma sam bai ji a ransa zai iya kawo mata wannan maganar ba, ko da kuwa ba ta da aure, tana da kwarjini da kamalar da ta wuce ya yi mata wannan tayin, uwa-uba kuma ba ta taɓa sanin yana neman mata ba, ba zai so ta sani ba, saboda yana burin aurenta nan gaba, ba zai shafawa kansa baƙin fenti a wajenta ba.
Ya sauke numfashi "Mujasin anya kina jin daɗin auren nan naki kuwa? Jawad ya fi ƙarfin kuɗin nan fa".
Hawayen da take riƙewa ya sakko mata "Ka ce za ka taimake ni, idan ka fasa na yi tafiyata".
Ya girgiza kai "Ban fasa ba, kula ina shirye da taimakonki a kodayaushe ba sai ba kuɗi ba ma".
Ya miƙa mata jakar ya ce"Ga miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar, ko za ki buƙaci wani abun da sauran canjin".
Ta karɓa ta ce"Na gode sosai Khalid, Allah Ya saka da alkhairi, Allah Ya ba ka mace ta gari".
"Ni ne da godiya, kuma ina cike da farincikin na taimaki wacce nake so, mata ta gari kuma ke ce".
Ta juya za ta fita ya ce"Ki ajiye takardar nan ta hannunki, ta zama shaida ko da matsala ta taso ki ce kin kama hotel ne saboda kina neman kaɗaici silar damuwa da kuka shiga".
Gabanta ya faɗi ta juyo ta ce"Me ya faru ko kuma me zai faru?"
"No, incase dai".
"Ok, na gode sosai".
"Kin cancanci fiye da haka My love, ina sonki har abada".
Ba ta sake cewa komai ba ta fita, dana hijjabi ne a jikinta don haka ba ta sha wahalar ɓoye jakar ba, ta fito ta tari adaidaitasahu ta hau ta tafi, gida ta wuce kai tsaye, ta yi wa jakar kyakkyawan ɓoyo, ta watsa ruwa sannan ta fito falo.
A gurguje Jawad ya yi wanka ya fito yana kiran wayar direban nasa, ya faɗa masa sunan hotel ɗin, ya figi mota da sauri, bai tarar da direban a harabar wajen ba, ya kira shi a waya ya ce"Kana ina?"
"Ga ni a gida, ba ta daɗe ba ta fito shi ne na sake bin bayanta, yanzu dai ga ta a gida".
"Ta dawo gida?" Jawad ya tambaya a rikice
"E tana gida".
"Ok ga ni nan zuwa, kar ka sake bari ta fita".
A rikice ya shigo cikin gidan, lokacin yunwa ta ishe ta ta shiga kitchen ta ɗakko biskit da lemo, suka yi kiciɓis a falon, ya yi kanta a guje kamar zaki ya damƙo ta ya da wata irin murya ya ce"Ina kika je? Daga ina kike!?"
Tashin hankali ya rufto mata, ta shiga firgici "Daga gidan yari, ai can na ce maka zan..."
Gigitaccen marin da ya sauke mata ya katse mata maganar, ya sake cewa "Daga ina kike?"
Tun da ta ga haka ta tabbata ya san daga inda take, tashin hankalinta ya ninku, wani irin tsoro da firgigici suka dirar mata, amma cikin ƙarfin hali ta ce "Ai ka san duba Mama na je".
Ya daki bakinta nan take ya fashe sannan ya shaƙe wuyanta "Wajen uban wa kika je a hotel? Me kika je yi?"
Ƙoƙarin ƙwatar kanta take yi ta kasa saboda riƙo ya yi wa wuyanta ba na wasa ba, duk da yake siriri kuma mara tsayi amma ta yi mamakin ƙarfinsa, magana take yi amma ba ta fitowa saboda shaƙar da ya yi mata, ganin da gaske so yake ya katse mata numfashi ya sa ta tattara ƙarfinta duka ta hankaɗe shi, ai kuwa sai ga shi a ƙasa don bai yi zaton za ta yi hakan ba, ta yi ɗakinta da gudu, ya mara mata baya, amma ta yi sa'ar rufe ɗakin kafin ya ƙaraso, ta murɗa key, ya shiga dukan ƙofar yana faɗin ba za ki buɗe ba? Wajen wa kika je? Dama bin maza kike yi da aurena?"
Ta fashe da kuka "Ka yi haƙuri amma ban kai wa kowa ziyara ba, ban je wajen kowa ba, na kama ɗakin ne saboda na samu sauƙin ƙuncin da yake raina, kuma ma ban dade ba na ga rashin dacewar hakan, ka yi haƙuri"
Ta ɗakko takardar ta jefa masa ta window, ya ɗauka yana huci ya duba ya ga tabbas ita ce ta kama ɗakin, amma duk da haka bai yarda da ita ba, ya bar wajen don ya san ba za ta buɗe ba.
Ya daɗe zaune a falo yana jiran fitowarta ba ta fito ba, sannan ya tashi ya bar gidan, sai da ya je har hotel ɗin ya sinnawa wani ma'aikaci kuɗi ya tambaye shi Muhasin, ya tabbatar masa ita kaɗai ta shiga kuma ita kaɗai ta fita, sannan ba ta taɓa zuwa ba sai yau ɗin, kuma ba ta daɗe ba, har zuciyarsa ya ji ya yarda da ita, don dama zai yi mamakin a ce ta aikata ɗin, ya san tana da kamun kai, da dai Hasina ce zai iya yarda kai tsaye.
Ita kuwa Muhasin kuka sosai ta ci, musamman da ta kalli mudubi ta ga yadda fuskarta ta yi, bakinta ya kumbura ya fashe, ga Khalid sai kiranta yake a waya ta ƙi ɗauka, ƙarshe ma ta kashe wayar zazzaɓi ya kama ta nan take.
Shi ma sun yi sun gama da Hasina, domin da ta kira shi hoto ko bidiyo ta nema kai tsaye, ya ce mata bai yi ba, ta hau shi da faɗa kamar ɗanta ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, abun ya ba shi haushi ya kashe wayar, ban daa lalacewa irinta zumunci a ce 'yar'uwarka ce me neman faɗuwarka? Tausayin Muhasin ya kama shi.
Sai da aka yi sallar azhar ta lallaɓa ta fito bayan ta yi wanka da Sallah, ta ci abinci kaɗan duk da tana jin yunwa, amma ya za ta yi da sleeming ɗin da take so ta yi? Ta sha magani ta kunna wayarta ta kira Anyi Su'ada, suka gaisa ta ce"Anti ga kuɗin ya samu, idan da dama ki zo ki karɓa, ba zai bari na fito ba".
Anti Su'ada ta ce"Alhamdulillah! Shi ne ya bayar?"
"E shi ne".
"To ga ni nan zuwa yanzun nan".
Ai kuwa babu jimawa ta zo da murnarta, sai dai ta yi saranda saboda ganin yanayin 'yar'uwar tata, "Ke Muhasin mene ne ya sake ki?"
Kuka ya ƙwace mata ta ce"Babu komai, faɗa muka yi da shi a kan kuɗin shi ne har ya sake ni, amma ya ba ni haƙuri shi ne kuma ya ba da kuɗin".
Jikin Su'ada ya yi sanyi ta ce"Kenan dole kika yi masa? Amma ban ji daɗi ba, har da duka?"
Ta ƙaƙalo murmushi tana share hawaye ta ce"Ba ga shi ya bayar ba? Ai komai ya wuce babu komai".
Su'ada ta ce"Amma fa Muhasin namiji me duka..."
"Babu komai Anti, mun yafewa juna, bari na kawo miki kuɗin, yanzu ya ce zai dawo ya kai ni asibiti".
Ta shiga ɗaki ta ɗakko kuɗin ta ɗauki dubu ɗari biyu ta ba ta sauran, Su'ada ta buɗe kuɗin tana jin farinciki ta ce"Kin ga ranar auren me kuɗi, talauci bai yi ba, baban Sadik kullum da zancen nan take kwana yake tashi amma ba shi da kuɗin da zai taimaka, ki yi masa godiya Allah Ya saka masa da alkhairi Ya ba ku zaman lafiya".
Ta amsa da amin.
"Fuskarki ta kumbura".
"Yanzu zai zo mu je asibiti".
Ta ɗauki kuɗin tana yi mata sallama ta tafi.
Sai la'asar ta kira Khalid a waya, yake tambayarta ya ake ciki, ta kwashe komai ta faɗa masa, ya ji babu daɗi ya ce"Sorry Allah Ya saka miki, yanzu kin sha magani? Ya kai ki asibiti?"
Ta share hawaye "Na sha magani, bai kai ni asibiti ba".
"To ko na zo na kai ki? Please, hankalinsa ya tashi".
"A'a na gode, idan ban warware ba gobe sai na je".
"Sorry Allah Ya ba ki lafiya, kin ci abinci?"
"Na ci, Anyi ta karɓi kuɗin ɗazu, na gode sosai Khalid Allah Ya bar zumunci".
"Babu godiya a tsakaninmu Allah Ya tsare na gaba".
Ta amsa da Amin suka yi sallama.
Ta yi shiru tana tunanin yadda za su kwashe da Jawad don ta san ba haƙura ya yi ba.
Bayan sallar isha'i Jawad ya dawo gidan, ta san idan ya dawo da wuri haka to zai yi life ne a tiktok, sanda ya dawo tana kitchen kuma sam ba ta ji dawowarsa ba ya shammace ta, yau ɗin gajiya ta yi da horon yunwa da take yi wa kanta, don haka ta zuba abinci da yawa kamar yadda ta saba ci, ta fito daga kitchen ɗin kenan suka haɗu a falo, gabanta ya ba da rass har ta ji kamar ta koma da gudu, ta sunkuyar da kai ta zo za ta wuce shi.
"Keee!" Tsawar da ya daka mata ta hargitsa ta, saura kaɗan ta zubar da abincin.
"Na'am" Ta amsa tana dawowa da baya
Ya nuna mata kusa da shi, babu musu ta zo ta zauna a ƙasa, tsoro fal ranta, a tsanake ya ce"Ina kika je ɗazu? Kar ki sake ki yi min ƙarya".
Kai tsaye ta ce"Hotel".
"Wajen wa?"
"Ba wajen kowa ba je na, na je sabunta iska ne da kuma neman kaɗaici, silar ƙuncin da na shiga sakamakon ganin halin da mahaifuyata take ciki".
Tana rufe baki ya ɗauke ta da mari, ta dafe kuncinta ƙwalla tana zubowa.
"Wannan shi ne gargaɗin da zan yi miki na ƙarshe a kan wannan haukan da kika yi, ko da wasa daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarki ta sake ayyana miki ki je hotel da aurena don neman kaɗaici sai na ba ki mamaki".
Cikin kuka ta ce"Ka yi haƙuri".
"Idan ban haƙura ke kin isa na zauna da ke na yi miki gargaɗi? Da tuni na shaƙe ki kin mutu ai, kalle ki, wata jibgegiya da ke amma sai girman jikin babu hankali, wannan uban abincin da kika zubo duka za ki juye shi a cikinki, ba dole ki yi ta hawa ba kamar buhun fulawa, mata sirara 'yan shafal-shafal suna nan a titi da media gwanin sha'awa, daɗin soyayya, ka ɗaga su ka cafe, ka goya su, su kwanta a ƙirjinka, amma ke waye zai fara wannan da ke? Ina son na ga mace cikin ƙananun kaya amma babu dama, tun da ba kyau za su yi miki ba, komai sai dai ki saka babba, kai sam ban yi dace ba".
Ta dinga hawaye tana jin ƙarshen muzanci.
Shi kuwa ya ɗora da faɗin "Don Allah kalli ƙirjinki, kamar za ki shayar da yara goma, ina zan kaisu? Ba ki lura ƙananun sun fi kyaun gani ba? Babban tashin hankalin ma an ce idan kika haihu komawa za su yi har cikinki, gaskiya ba zan ɓoye miki ba indai ba ki rame kin zama mace ba ba za mu taɓa shiryawa da ke ba".
"Zan rame in sha Allah" Ta faɗa da rawar murya.
"Sai batun zuwanki hotel, idan kin san kin fara zuwa ne don ki fara tallata kanki ki yi min bayani, na san ma haka ɗin ne, to zan ɗauki mataki, zan dinga ba ki kullum na zame miki bunsuru don kar ki fara nema a waje ki kwaso min wata cutar, don haka idan kin gama lodawa cikin naki abinci ki shiga ɗakina ga ni nan zuwa".
Ta share hawaye ta tashi ta ce"A kawo maka abincin?"
"Na ƙoshi".
Sai ta tafi ɗakinta da abincin nata, amma ta saka shi a gaba ta kasa ci, baƙinciki ya gushe mata ciki, ta tuna Khalid shi yabon jikinta ma yake yi tun sanda tana buduruwa, har yana faɗin yana son mace me ƙiba, yana so idan sun yi aure ƙibarta ta ɗa ƙaru yadda zai dinga more komai, to shi Jawad me yake son mora a rama? Mata da yawa suna neman ƙibar nan, wasu suna neman ƙara girman ƙirjinsu, ita ga shi Allah Ya ba ta su, komai a ciki ma sha Allah, amma mijinta ba ya so, idan ta ƙi cin abinci ta rame shin shi ma ƙirjin zai take ko kuwa sai ta nema masa maganin da zai ragu ɗin? A gaskiya tana tsaka mai wuya, ta san ba ya kyauta mata a abubuwa da dama, soyayyar da take yi masa ce kawai take wanke laifukansa a idonta, kaɗan ta ci abincin ta je ta ajiye, har yanzu yana zaune a falo, ta je ta yi wanka ta saka rigar bacci ta zo za ta wuce ɗakinsa, ya bi ta da kallo me kama da harara, ganin yadda manyan mazauna ta suke juyawa, a wajensa abun ya wuce misali.
"Ke Muhasin"
Ta juyo, ya bi ƙirjinta da kallo, nan ma takaici ya kama shi, ya ce"Don Allah ki dinga saka bra da pant Wanda za su kama jikinki".
Ta sunkuyar da kai "Wanda nake sakawa e su ne size ɗina".
"Ke dalla sai dai over size kike sakawa, zan ɗauki mataki kuma".
Ta haɗiyi yawun takaici ta shiga ɗakin, ta daɗe a zaune tana tunani da kallon kanta, kafin ta kwanta, bacci ya fara ɗaukarta ya dawo ɗakin, kamar yadda ya saba da kariya yau ma ya yi amfani, kafin ya matsa gefe ya yi baccinsa.
***