RIGAR KAYA

Chapter 7

by @sadiyaabdulrazak954

*....RIGAR ƘAYA*



          BY
SADIYA ABDULRAZAK 


PAGE 7

 
     Washegari tun sassafe Anti Su'ada ta kira ta a waya da tambayar yadda za a yi wajen fitar da Mama, ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta tambayi Jawad za ta fita ba, don haka ta ce mata ta yi komai da ya kamata ba zai bar ta ta fito ba, Anti ta ce"Wai ni kam Muhasin anya kuna zaune lafiya da mijin nan naki kuwa?"

"Lafiya ƙalau wallahi, kawai shi haka yake ne".

"To Allah Ya shirye shi, shikenan zan je gidan Kawu Musa sai ya shige gaba, tun da ga kuɗin nan ai dai ba zai ƙi ba da gudunmawar ko iya lokacinsa ba ne".

"Haka ne, sai kun dawo".

 Sai da aka yi kwana uku kafin a gama komai Mama ta dawo gida cikin aminci, a ranar da za ta dawo da sassafe Muhasin ta faɗawa Jawad, ya yi kamar bai ji ba, ta sake maimaitawa "Zaujee yau Mama za ta dawo gida".

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce "To barka".

Ta ji wani iri ta ce"Haka kawai za ka ce?"

"To me kike so na ce? Na tashi na yi ta tsalle saboda surukata za ta fito daga gidan yari? Ni wallahi fatana ma kar Ummi ta ji zancen nan, don idan kika sake ta san babarki ta je gidan yari silar cin bashin da ta yi don ta yi ƙarya a lokacin bikinki tsanar da take yi miki ce za ta ƙaru".

Ranta a ɓace ta ce"Ka ga Jawad ya isa haka, wannan ai wulaƙanci ne da cin fuska, kar ka sake cewa babata ta yi abu don ƙarya..."

Ya katse ta da faɗin "Idan ba ƙarya ba meyasa ba za ta zauna a matsayinta ba? Dole ne? A kawo ki a haka mana ko ta yi iya ƙarfinta".

"Don Allah Jawad daga yau kar ka sake saka baki a batun iyayena, idan ni ka yi min na jure ba damuwa, ni ce na ja wa kaina, tun da ni na aure ka kuma nake sonka, amma ba zan ɗauki kalaman cin mutunci ga uwata ba".

"Yanzu ma ni na saka baki? Ke ce kika saka ni, ni wallahi zan ji daɗi ma a ce ba kya yi min zancen danginki duka, don ke nake aure ba su ba, kuma idan kika ce za ki yi min rashin kunya zan sassaɓa miki kamanni yanzu a nan".

Ya tashi ya shiga ɗakinsa, ita kuma ta yi zaune a wajen, ya ɗan daɗe sannan ya fito cikin shirin fita, yana waya, ta ce"To zan je gidan, yau a can zan wuni".

"Ban yi miki izini ba" Ya faɗa yana ficewa ba tare da ya tsaya kallonta ba.

Zuciyarta ta ƙuntata, ta ji kamar ta rushe da kuka, wajen sha ɗaya ta tashi ta ɗora girki, ta yi abinci me rai da lafiya, da ɗan dama ta zuba a kula ta bawa direba da kwatancen gidan nasu ya kai, bai jima da kai wa ba Su'ada ta kira ta, ta ɗauka suka gaisa ta ce"Muhasin kika aiko da abinci, ba za ki zo ba ne?"

Ta ce"E yana gida ne ba shi da lafiya".

"Kuma abun har ya yi tsananin da ba zai iya kula da kansa ba? Yau dai ɗaya ki zo ku gana da mahaifiyarki? To sannu 'yar daɗi miji".

Ta ji babu daɗi don ita kanta ta san bai kamata ba, ta ce"Zan zo gobe in sha Allah, ina Maman?"

Su'ada ta miƙawa Mama waya, ta ce"Muhasin".

Ƙwalla ta zubo mata ta ce"Na'am Mama ya jiki?"

"Da sauƙi, ga ni dai a gida ruwa ne ma a hannuna, in sha Allah tun da nan ɗin da kulawa ba sai an zauna a asibiti ba, amma Su'ada za ta zauna da ni har na warware".

"To sannu Mama Allah Ya tsare, akwai kayan abinci a gidan kuwa?"

"Su'ada dai za ta siyo anjima ta ce akwai sauran kuɗi a hannunta, wannan mijin naki Allah Ya saka masa da alkhairi, ki ce masa na gode Allah Ya ba ku zuri'a ɗayyiba".

Muhasin ta ji wani iri, ta so a ce da gaske shi ne ya bayar ɗin, ya Mama za ta ji idan ta ji cewar wani saurayi ta kula da aurenta har ta je hotel ta karɓi kuɗin?

"Ameen Mama Allah Ya sawaƙe".

Suka yi sallama, sai ta ƙara jin girman Khalid sosai, da ta gan shi online ta sake yi masa godiya, daga nan suka dinga chatting, yana yawan yabonta, tare da kushe mijinta.

A ranar da daddare da ya dawo tana ɗakinta, ya ɗaga waya ya kira ta ta fito falo, ta gan shi da leda babba yana zaune, ta ƙarasa ta yi masa sannu, yana miƙa mata ledar ya ce"Yawwa, ga wannan kayan, su nake buƙatar ki dinga sakawa".

Ta karɓa ta buɗe tana faɗin "An gode".

Ta fara fito da su, ƙananun kaya ne da kayan bacci masu kyau da tsada, amma duk sun yi mata kaɗan, ta ce "Sun yi kyau sosai, amma ba size ɗina ba ne".

Ya haɗe fuska "E na sani, amma su nake buƙatar ki saka a haka, indai za ki dinga biyewa jikinki kina saka kaya size ɗinki ai kin ga haɓɓaka kenan, amma idan kina matse jikinki dole za ki dinga kamewa kina raguwa, wallahi na ƙi jinin na ga kina tafiya bayanki yana juyawa, ko ƙirjinki yana motsi, ba na so sam".

Ta ɗaga pant ɗin da ta san ko cinyarta ba za su shiga ba ta ce"Amma Zaujee saka abin da ya matse ni akwai takurawa gaskiya".

"Ai kuwa dole ki saka, idan kuma kin fi so na cigaba da kallon yadda nake so a media shikenan tashi ki ba ni waje, kai siraran mata duniya ne wallahi, da tuni kodayaushe matata tana cinyata".

Kishi ya kama ta ta ce"Zan saka in sha Allah".

Ta tashi za ta tafi da ledar kayan.

Ya ce"Muhasin".

Ta dawo ta zauna

"Idan har ba za ki bi umarnina ba to wallahi ba za ki taɓa gane kaina ba, mun yi magana da wani abokina ne ya faɗa min wannan ma kawai zai saka ki rage ƙibar nan, idan kina saka bra ɗin da ta yi miki daidai ƙaruwa girmansu yake yi, don haka wannan ƙananun su nake buƙata, pant ɗin ma haka, ki je ki gwada ki zo na gani".

Da ta shiga ɗakin sai ba ta yi yadda ya ce ba, ta zauna a bakin gado ta fara hawaye, a ranta tunanin wai ƙibarta ta yi yawan da har za a kushe dama? Me yasa wani bai taɓa faɗa mata ba ko da kuwa a cikin ƙawayenta ne?

Jin shiru ba ta fito ba ya sa shi ɗaukar waya ya kira ta, kamar ba za ta ɗauka ba, sai da ta kusa katsewa ta ɗauka "Kin manta ina jiranki ne?"

"Ok" Kawai ta ce ta tashi ta zazzage kayan tana kallon su, zuciyarta ta rabu gida biyu, wata na faɗa mata Jawad yana cin zarafin ta ne, wata na faɗa mata sonta yake yi da son a zauna lafiya shiyasa yake so ta zama kalar ra'ayinsa, ta ɗauki bra ɗin tana kallo, ta ina? Amma a haka ta saka, duka rabin jikinta a waje, pant ɗin kuwa kamar yadda ta yi zato bai shiga cinyarta ba ma, da ta matsa kishi sai ya fara ƙara kamar zai farke, ta cire, ta saka rigar bacci ita ma da ƙyar, duk da jikinta roba ne amma sam ba size ɗinta ba ne, ta ji ta a matse gam, ba ta, numfashi ma yadda ya kamata, kuma ita kanta ta san ba ta yi kyau ba, kunyar fita ya ganta a haka ta kama ta, amma ya zama dole ta fita ɗin.

Yana danna waya ya ji ƙarar buɗe ƙofarta, ya ɗago yana kallonta, bai san sanda ya saki dariyar takaici ba, har ta ƙaraso ta zauna a gefensa, ya ce"Kin gani ko, sai da kujerar nan ta yi ƙasa, ina tunanin zan ware miki kujerararki ta da ban a gidan nan, don kar ki kashe min kujeru".

Tunawa da ta yi da shi ya yi kayan ɗakin ya sa ta ji tamkar ya yi mata gori ne, kuma ranta ya ɓaci da yadda ta yi yadda ya ce ɗin amma babu alamar zai yaba, ban da sharrin Jawad ina ta ga ƙibar da za ta motsa kujera?

"Ba ki yi kyau ba sam, abun babu tsari da kyaun gani" Ta ji maganarsa, wacce ta daki zuciyarta

Ya tashi ya fara zagaye ta yana kallon ko'ina, ya ce"Ba ki da shape kwata-kwata, ji yadda kayan ya yi a jikin wannan matar, ɗazu na siye su online" Ya yi maganar yana nuna mata wayar shi, ta ƙi kalla ƙwalla na taruwa a idonta.

 "Kai fa ka kawo ka ce na saka, me yasa ka zaɓi wulaƙanta ni da halittata?"

"Ni ban wulaƙanta ki ba, kawai ina so ki rage ƙiba ne, wallahi ƙiba cuta ce, nan gaba tsaf za ki gamu da wata jinyar, kuma sannan sam ba kya kyaun gani".

Ya zauna "Zan ba ki shawara, da farko dai dole ki rage cin abinci, kar ki sake cin ƙwai ko kaza, madara ma haka, sannan zan yi binciken abubuwan da suke ƙara ƙiba duka ba za ki ci ba, za ki dinga training kullum, zan siyo miki wani abu da na gani na ɗaure tumbi, ki dinga ɗaurewa, za ki ragu in sha Allah".

Ko da take da ƙiba ba ta da mummunan tumbin da za a ce ta rage shi, ta san abun nashi har da wulaƙanci, "Na gode" Kawai ta ce ta tashi ta bar wajen.

Ta juya a hankali ta koma ɗaki, tana shiga ta sake kallon kanta a mudubi, ita ɗin ce dai, jikinta ne dai wanda Khalid kullum yake yabawa, amma me yasa shi Jawad yake ganin muninta? Kalamansa suka dawo mata 'Ba ki da shape kwata-kwata' Da ciwo a ce mijinka ya faɗa maka haka, amma laifinta ne? Haka Allah Ya yi ta ba yadda za ta yi, amma za ta dake dagewa don ganin ta rame ɗin, ƙiba ba za raba ta da mijinta ba, don ta fara tunanin nan gaba zai iya auro mara ƙibar, kuma ta san ba za ta taɓa ganin daidai ba.

 Amma gaskiya ta ji haushin yarfin da ya yi mata sosai, ta cire kayan ta saka wanda ta saba ta kwanta, ta ɗauki wayarta ta kunna data, saƙonni sun gama shigowa tass, ta ga na Khalid, shi ta fara buɗewa, gaishe ta ya yi da faɗa mata yana kewarta, ta amsa gaisuwar, yana online ya sake mayar mata da amsar "Matar ɗan tiktok, ga shi can na ga ya hau live yanzu, ba kya kalla?"

Ta ce"Ban cika bin live ɗinsa ba, saboda ba na jin daɗin yadda yake kula mata".

Ya ce"Ya kamata ki bi na yau, don a kan mata masu ƙiba yake yi".

Mamaki ya kamata, ta ce "Ok".

Ta tafi tiktok ɗin duk da ta ga Khalid ya cigaba da wani typing ɗin.

Ta yi searching sunan shi ta shiga live ɗin, daidai inda wata mace me siririyar murya da azarɓabi take yi masa tambayar "To idan bayan ka auri mace ta yi ƙiba ya za ka yi?"

Ya yi dariya "Zan ɗauki mataki ne, dole za ta rame idan ba haka ba..." Sai ya yi shiru yana dariya 

Mutum biyu suka tambaye shi me zai yi.

Yana kallon Muhasin ta yi join, ya ce"Ba wani abu da zan yi, sai ta riƙe ƙibarta ni kuma na auri kalar wacce nake so, kun ga ba cuta ba cutarwa kenan".

Live ɗin ya kaure da hayaniya, mafi yawan maza nuna masa falalar mace me ƙiba suke yi, wasu daga cikin matan ma haka, amma shi ma yana ta jero amfanin auren slim, takaici ya ishi Muhasin, ta fita daga tiktok ɗin, ta dawo whatsApp.

Khalid ya ajiye mata saƙonni, na ƙarshe dai ya ce mata "Na ga kin hau live ɗin, sai ki yi haƙuri na san da ke yake, amma gaskiya Muhasin wannan mijin naki ba shi da kirki sam, wannan fa kamar ya sanar da ke zai yi miki kishiya ne a live, wallahi sam irinki ba su dace da zama da kishiya ba".

Ta ce"Kowa da ra'ayinsa, da gaske ba ya son me ƙiba, zan yi iya ƙoƙarina na ragu ko yaya ne".

Ran shi ya ɓaci "Ba ya son me ƙiba me yasa ya aure ki? Ko tuwo ne a idonsa da bai ga yanayin ƙirar jikinki ba sai da ya aure ki? Ki yi haƙuri da maganata, amma mijinki bai da kirki gaskiya".

"Ka daina ce masa haka, ni na ga zan iya ai".

Ya ce "Ok".

Ta ce"Amma Khalid don Allah da gaske ƙibata ta yi yawa?"

"Ni dai ban gani ba, daidai ke nake so ko ma ki ɗan fi haka, shi kuma tun da ba ya ra'ayi zai iya ganin haka".

"Shikenan sai da safe". Suka yi sallama, tana ta tunanin mafita har bacci ya ɗauke ta, ba ta je ɗakinsa ba.

 Washegari da safe sai ta ga fuskar shi da walwala, suka gaisa har yana rungumarta, tana ta ɗari-ɗari wajen cin abinci ta rasa me za ta ci, ta haɗa shi da suga kawai, ya ce "Ai ina ga koko ba ya daka ƙiba, zan saka a kawo gero anjima sai kina karyawa da shi".

Ta ce"To".

Ya ce"Ki yi haƙuri fa, ba wai ba na son ki ba ne wallahi, so ne ya kawo haka Wify, ina so mu gyara zamanmu ne, mu dinga soyayya irin wacce na tanada zan yi wa matata, to kin ga idan ba ramewa kika yi kika yi yadda nake so ba abun ba zai yiwu ba, ina sonki wallahi, ba wai takura ba ce ba".

Har ta yi mamakin kalamansa, kuma ta ji daɗi sosai, ta ce"In sha Allah zan yi ƙoƙari, zan nemi magungunan sleeming ɗin ma".

"Ma sha Allah, ni kuma zan biya kuɗin ko nawa ne, sannan yanzu ki shirya za mu je mu yi wa Mama sannu da zuwa, sai na bar ki ki wuni a can ko?"

Jawad fa ya kashe ta da mamaki, amma ta shanye ta ce"To na gode, bari na shirya, ta tashi ta koma ɗaki, don shi s shirye yake, kafin ta fito ya gama karyawa yana jiranta, abaya ta saka ta yi rolling da mayafi medium, ya sakar mata murmushi "Wow! Kin yi kyau sosai, kamar ba mu taɓa yin hoto tare ba ko?"

Ya matsa kusa da ita ya daga wayarsa ya yi musu hoto, suka yi kyau kuwa don duka suna murmushi ne.

Ya ce"Kamar ya kamata ki yi mata girki ko?"

Don zumuɗin ganinta da take yi ta ce "Ai kuma na riga na shirya, na yi mata a can kawai".

Ya ce"Shikenan zan yi order sai a aiko anjima, mu je ko".

Suka tafi, da kan shi yake driving suna tafe suna fira, daɗi kamar ya kashe Muhasin, ya shiga har cikin gidan suka gaisa da Mama, amma tsohon mikin rasa Hasina ya rage masa walwalar da ya ara a yau ɗin yake pretending, yana tuna rabuwarsu ta ƙarshe a zauren gidan, ranar da ta kalle shi ta ce "Ka yi haƙuri Jawad, gaskiya ni ban shirya aure yanzu ba, sai idan za ka jira zuwa lokacin da zan shirya"

A zatonsa wasa take yi masa, duk da kuwa dama yana ta karɓar canje-canje daga gare ta cikin satin, murmushi ya yi ya ce"Ai aure ko ba ki shirya masa ba, shi ya shirya miki ba, gara ma kawai ki ba da kai bori ya hau, don kwanaki uku kamar yau ne, kamar yau ne kin zama tawa, ni kaɗai" Ya ƙarasa da kashe mata ido

Ta ɓata rai ta ce"Wallahi da gaske nake Jawad, ko zan aure ka to ba yanzu ba, ni a gaskiya ma yanzu sam babu sonka a raina, don haka babu batun auren nan, ban shirya kashe rayuwata ba, ga kayan lefenka nan ban taɓa komai ba, kuɗinka ma na san za su fito, Allah Ya ba ka wata ta gari".

Ta juya ta shiga gidan ba ta saurari kiran da yake yi mata ba, duk da ya san da wasa take yi amma jikinsa ya yi sanyi, sai kuma ya yi murmushi ya fice ya tafi gida, washegari aka wayi gari da mummunan labarin Hasina ta bar gida a daren, ta ajiye wasiƙa da cewar ta fasa auren, a mayar masa da kayansa, tashin hankalin da ya shiga ba ya musaltuwa, duk ya ruɗe, kuma ba wanda yake samun wayarta, ƙaddara da kalmar matar mutum ƙabarinsa ce ta sa shi jin nauyi a lokacin da aka roƙe shi ya auri Muhasin a maimakon Hasina, amma sam ba ita zuciyarsa take so ba, kuma har yanzu yana son Hasina, don a jininsa yake, ita ce kalar shi, musamman yanzu da ita ta yi sleeming, sannan yana son wayayyiyar mace mai tsayawa a kan ra'ayin kanta, ba irin Muhasin ba wacce ta bari so yake canza mata ra'ayi.

Godiya sosai Mama da Anti Su'ada suka dinga yi wa Jawad, Mama tana ta shi masa albarka, har ya yi mamakin yadda godiyar ta yi yawa, don a tunaninsa ta auren Muhasin da yake yi ce kawai, tun da ba su ambaci kuɗin ba, suka yi sallama da Muhasin yana faɗa mata zai aiko da abincin.


***