SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....!💔 Chapter 3

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!* Arewabook@ayshadansabo

Paid book

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 3

Ahankali ta miƙe akan ƙafafunta domin barin wajen ta isa bedroom ɗin Momy,sai dai kuma ko taku guda batai ba ta jiyo muryar Momy na faɗin,"Amal jeki kiyi serving Yayanku breakfast ki kawo masa nan."Amal ta haɗiye wani abu mai nauyi kafin ta saita muryarta wajen faɗin,"To Momy."Tana gama faɗin hakan ta nufi ɓangaren dining ɗin tana sake jin tsanarsa da tuna irin yadda Yayarta ta mutu da baƙin cikinsa na sake hauhawa farashin tsanarsa a cikin zuciyarta.Ta sani da ace Momy da Daddy sun san haƙiƙanin ɓoyayyen halin Yaya Zayd da irin ta'asar da yake aikatawa da basu yi sha'awar sake wanke ɗiyarsu su bashi ba,sai dai abin takaicin daga ita sai Yaya Hameedah suka sanshi da wancan ɓoyayyen halin." Amal ina so ki rufe sirrin mijina kada ki taɓa bari Iyayenmu sun san abinda da yake aikatawa,idan kikai mini hakan tabbas ko bayan raina zan cigaba da yin alfahari dake,idan har banyi tsawancin rayuwa ba ina fata ki riƙe mini Abdallah kada ki taɓa bari yayi maraicin rashina,nasan kin tsani Yaya Zayd amma ina so a kullum kika ji tsanarsa ki tuna cewa ƴar Uwarki Hameedah tana sonsa,da soyayyarsa aka halicci zuciyata kuma da sonsa za a zare numfashina,Amal Zayd nada wani ɓangare dani kaɗai nasan sirrinsa,hakan yasa soyayyarsa ta zame mini tamkar SARTSE A ZUCI mai wuyar cirewa......"Waɗannan kalaman suka haska a cikin kan Amal,tana hasko lokacin da Hameedah ke furta mata masu.Wasu irin zafafan hawaye suka sulmiyo daga cikin idanunta tayi gaggawar sharesu tana ƙarisawa gaban dining ɗin ta fara serving ɗinsa abinda tasan zai ci,ta haɗo komi a ƙaramin tray ta kawo gaban Momy ta aje tana kallon yadda ya rungume Abdallah a jikinsa.Wani abu ya motsa zuciyarta tayi gaggawar ɗauke kanta daga dubansa lokacin da take faɗin,"Momy gashi." Momy ta aika mata harara tana maida dubanta kan Zayd tace,"Son bani Abdallah ka daure kaci wani abu please!" Yadda Momy take lallashinsa tamkar ƙaramin Yaro ya sanya zuciyar Amal sake matsewa waje guda.Ta miƙe da sassarfa domin barin wajen,tayi taku biyu ta juyo muryar Momy na faɗin,"Hala an bashi abincinsa ya ƙoshi ne?" Amal bata juyo ba ta baiwa Momy amsa da faɗin,"Eh Momy,ai yana sha sosai."Daga haka tayi gaggawar shigewa corridor ɗin dazai kaita room ɗin Momy hannunta riƙe da wayarta.Zamanta daga bakin bed ɗin Momy yayi daidai da shigowar saƙo cikin wayarta,koda ta duba taga sunan Ya Zayd ne sai taji gabanta ya yanke ya faɗi.Cikin sauri ta buɗe saƙon tana karanta taƙaitattun kalaman dake ƙunshe a cikin saƙon,"Ki sameni a bakin swimming pool ina son yin magana dake." Waɗannan sune kalaman data gani a rubuce a jikin saƙon.Ta samu kanta da sake bitarsu tana mamakin ƙarfin halinsa,taja dogon tsaki tana ayyana yadda zatai ignoring ɗinsa.Sai dai kuma tana kaiwa kwance da zimmar kwanciya a saman bed ɗin Momyn taji ƙaran kira ya shigo,still daga Ya Zayd ɗin ne don haka tayi receiving call ɗin tare da saka wayar a speaker.Wannan ƙasaitacciyar muryar tasa ta doki kunnuwarta time ɗin da yake faɗin,"Am waiting for you."Daga haka kiran ya yanke ba tare da ya bata damar cewa komi ba.Ta sauke wani irin ajiyar zuciya tana miƙewa a nutse ta gyara zaman veil ɗin dake kanta,koda ta fito bata tadda kowa a cikin falon Momy ba alamun Momyn sun nufi ɓangaren Daddy kenan ita da Abdallah.Ta sauke numfashi mai ɗumi tana fitowa daga ɓangaren ta zagaya ta baya ta nufi ɓangaren swimming pool ɗin,tun daga nesa ta hangosa sanye da baƙar singlet da threequater wando a jikinsa saɓanin baƙar jallabiyar data gansa dashi a ɓangaren Momy.Zuciyarta ta sake ɓaci wani tsanarsa dana halayensa suka sake dabaibaye zuciyarta,fuskarta tamkar za ta yi aman wuta haka ta haɗeta tana takunta a nutse har ta isa bakin swimming pool ɗin da aka jera wasu irin Lounge sofas a wajen.Nesa kaɗan dashi tayi tsaye tana kallon yadda ya harɗe ƙafafunsa ɗaya kan ɗaya,fuskarsa tamkar ko yaushe babu ɗigon fara'a bare annuri a samanta.Hannunsa riƙe da wayarsa ne yana faman dannawa kuma sarai ƙamshinta ya sanar dashi isowarta wajen,amma hakan baisa yayi alamun ɗagowa ya dubeta kamar yadda itama bata yi sallama domin ya gane ta iso ɗin ba.Ta ƙasan idanunsa yake kallon irin tsayuwar da tayi a fusace tana aiko masa kallon rainin daya tsana,ya saki wani murmushi acan ƙasan zuciyarsa yana mamakin rashin kunya da taurin kai irin na Amal Taheer Lawal.Suka share fiye da mintuna goma a haka babu alamun ɗaya zai nuna yasan da wanzuwar ɗan Uwansa a wajen,ƙaran shigowar kiran Aman cikin wayarta ya sanya tayi gaggawar ɗagowa ta saci dubansa taga har time ɗin hankalinsa nakan wayar hannunsa.Sai kawai ta fara taku a nutse ta nufi bakin ruwan sosai tana ƙoƙarin amsa call ɗin Aman Shehu Kurfi,har tayi receiving call ɗin takai wayar kunni sai ji kawai tayi an zare wayar daga kunninta ta baya.Kafin kuma tayi yunƙurin waiwayawa ƙamshinsa daya cika kafofin hancinta ya sanar da ita wanda yayi mata hakan,ta kuwa juyo a fusace suka zubawa juna fitinannun idanunsu kafin ta kausasa murya tana faɗin,"Miye hakan kenan?" Ya aika mata wani matsiyacin kallo daidai da kashe wayarta baki ɗaya da yayi ya jefa a aljihun wandon dake jikinsa.Ranta ya sake ɓaci ta juya masa baya ta fara taku domin barin masa wajen baki ɗaya,amma kuma taku ɗaya biyu taji ya janyo gyalenta ta baya.Ta tsaya cak! Tare da waiwayo slowly ta sake zube masa manyan idanunta dake firgita nutsuwarsa amma a ɓoye,"Mi zanyi maka ne wai?" Ta tambaya a fusace tana sake jifansa da ƙasƙantaccen kallon ɗaya tsana.Baiyi magana ba har ta fisge gyalenta daya riƙe,ta sake juyawa domin cigaba da tafiya amma sai taji ya sake janyo rigarta tayo baya tamkar za ta faɗo jikinsa.Bai jira komi ba ya ƙarisa janyota baki ɗaya ta kwanto a jikinsa ya sanya ƙafarsa guda ya tokare nata ƙafafun dake shirin kaiwa ƙasa,cikin dakakkiyar muryarsa ya furta,"Amal har yanzu ba za ki koyi tausasa harshenki a kaina ba ko? Karki ga ina ɗaga miki ƙafa ki ɗauka cewa Zayd na shakkarki ne don kawai kinsan wani ɓangare na sirrin rayuwata da ba kowa ya sani ba,oya wuce ki zauna muyi magana tun raina bai gama ɓaci da fitsararki ba ƙwaila kawai marar kunyar ƙarya." Ai tuni kalmar ƙwailar data tsani ya kirata dashi ya sake dugunzuma zuciyarta.Tayi wani irin fisge jikinta daga garesa tana zuba masa harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa,cikin rawar murya ta furta,"Kaima kanka kasan cewa na wuce wannan sunan wallahi,domin ko ƴan iskan daka saba lalubewa zai wahala ka....." Ta kasa ƙarisa kalamanta sakamakon wani irin bugu daya kaiwa bakin tsiwar nata.Ta nufi wajen Lounge sofas ɗin dake bakin ruwan takai zaune tana furta kalmar Allah ya isa ƙasa-ƙasa ta yadda bazai jiyota ba,gefe guda kuma zuciyarta na sake cika da wani irin tsanarsa mai zafin gaske.Kusa da ita yakai zaune fuskarnan tasa tamkar za ta yi aman wuta,sai da ya tsareta da manyan rinannun idanunsa na tsayin seconds kafin ya fara magana a kausashe yana faɗin,"Amal nasan kinsan cewa nan da 3 week's masu zuwa za ki fara amsa sunan mata a gareni,don haka ina shawartarki da ki fara shiryawa kanki yadda za ki yi rayuwar aure dani ki kuma cigaba da rufe wancan sirrin kamar yadda Hameedah tayi,domin fallasuwan sirrin nawa bazai taɓa tasiri wajen hanani na mallakeki a matsayin wacce za ta maye mini gurbin matata dana rasa ba,don haka ki nutsu kiyi gaggawar cire soyayyar wancan Yaron dake cikin zuciyarki domin bazan lamunci zama da macen da zuciyarta ke ga wani na ba." Ya dakata da kalamansa yana kallon yadda Amal ke kukan hawaye.Ta ɗago manyan idanunta dake cigaba da zubda hawaye ta dubesa duba mai cike da tsana da kuma ƙyama,muryarta a harɗe ta fara faɗin,"Ƙarya kake Yaya Zayd,wallahi ƙarya kake kace za ka raba soyayyar dake tsakanina da Aman Kurfi,sannan ina so kasani ka je ka fara shirya yadda za ka rayu cikin ƙunci matuƙar baka sanya Daddy ya janye ƙudirinsa na haɗani aure da fasiƙi irinka ba,domin bazan taɓa maye maka gurbin Yaya Hameedah ba har abada,bazan taɓa yarda na haɗa jiki da......"Kalamanta suka tsaya cak! Sakamakon wani irin fisgota da yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana amfani da ƙarfi wajen ɗago fuskarta ya haɗe fuskokinsu waje guda.Cikin matuƙar ɓacin rai da tafasar zuciya ya shiga faɗin,"Ke ƙaramar mara kunya ce Amal,kuma maganar aure tamkar anyi an gama,domin saina mallaki wannan jikin da kike ganin tamkar yafi ƙarfin na mallaka nayi yadda naso dashi,dole ki haɗa jiki da fasiƙi ki kuma ɗauki cikin da za ki haifesa cikin watanni tara domin na nuna miki cewa ke ɗin ƙaramar mara kunya ce." Yana kammala faɗin hakan ya saketa yana jin yadda ta fashe da kuka cikin ƙaramin sauti.Ko kaɗan bata yi mamakin jin kalamansa da yadda duk yake mata ba domin tafi kowa sanin shi ɗin tantiri ne na bugawa a jarida,a idanun Iyayensu ne kaɗai yake mutumin kirki kuma Ustazin ƙarya wanda za ka rantse da Allah bashi ke aikata duk wata ɓarnar da yake aikatawa ba.Har ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa,ta miƙe a nutse domin barin masa wajen amma sai ya daka mata tsawar daya sanyata saurin dubansa tana kallon yadda idanunsa suka rine da ɓacin rai."Koma ki zauna ban sallameki ba,stupid gal kawai." Ya furta cikin ɗaga sautin muryarsa domin zuciyarsa zafi take idan yana tuna a yanayin data taɓa riskarsa wanda shine silar da tayi masa wani irin rainin da ko kaɗan bata shakkarsa bare ganin girmansa.Amal ta koma ta zauna zuciyarta na rawa,amma ba za ka taɓa gane hakan ba domin a zahiri wani irin mugun kallon tsana ta jefa masa tana faman taɓe baki."Me da me Abdallah ke buƙata domin gobe zan wuce Rivers?" Ya jefa mata tambayar yana tsareta da idanunsa domin jin amsar da za ta bashi.Sai dai ga tsananin mamakinsa wani harara ta dalla masa tana ɗauke kanta ta mayar wajen kallon garai-garai ɗin ruwan dake cike da kwamin wankan,tsananin son shiga cikinsa tayi nutso na mamaye zuciyarta.Shuru ya ratsa a tsakani kafin ta mula don kanta ta furta,"Bani wayata please!" Ya kuwa fusata ya daka mata tsawa wajen faɗin,"Ba tambayarki nake akan me ɗana yake da buƙata ba Amal?" Sai ta juyo a fusace tana ɗaga sautin muryarta tace,"Bansani ba Yaya Zayd,bansan me yake da buƙata ba domin idan ma yana da buƙatar bana buƙatar ya samu daga gareka nima ina da wadatar da zan biya masa buƙatarsa bama buƙata daga gareka." Ta ƙare kalamanta tana sake jefa masa kallon rainin da yafi tsana fiye da komi a cikin rainin da tayi masa.Tamkar zai yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe yana zaro wayarta daga cikin aljihun wandonsa ya cilla mata,saura kaɗan wayar ta faɗi a ƙasa tayi nasarar cafketa tana jan dogon tsaki daya ji zafinsa har cikin zuciyarsa.Ƙwafa kawai yaja ya juya ya fara taku cikin wannan takun nasa irin na cikakkun mazan da suka amsa sunansu na mazaje,domin shi ɗin irin tsayayyun mazannan ne masu cikar mazanta da kwarjini mai dukan zuciya.Kyakykyawan gaske ne black beauty daya mallaki duk wani abin tinƙaho da ɗa namiji zai yi alfahari dashi,kana kallon fuskarsa a kallo ɗaya za ka fahimci cewa baya cikin jerin mazan da Ke ɗaukar raini.Miskili ne ajin ƙarshe wanda zai yi wahala kaga murmushinsa bare kuma dariyarsa,bashi da yawan magana sai idan ya sanya kansa ko kuma yana gaban Daddy ne ko Momy ko kuma Marigayiya Matarsa Hameedah.Waɗannan jerin mutanen su kaɗai ne yake iya sakin jiki dasu har suyi doguwar hirar da za ka iya jiyo dariyarsa ko kaga murmushi a saman fuskarsa,amma baya ga su dukkanin kafatanin ƴan gidan kowa shakkarsa yake.Akan idanunta ya fice daga wajen taja dogon tsaki tana saurin kunna wayarta,idanunta akan wayar yake hakan yasa sam bata ga dawowarsa ba sai da ƙamshinsa ya fara yawa a cikin hancinta.Still bata ɗaga kanta ta kallesa ba sai amon muryarsa data jiyo yana faɗin,"Bana son ki fara gigin fita mini da Yaro ko'ina,iyakarki dashi raino a cikin gida amma duk inda za ki fita ki tabbatar yana wajen Momy ko Anty Mamah,sannan ina sake jaddada miki ki rabu da wannan Yaron domin bana fata a ɗaura miki igiyoyin aurena a kanki kina cigaba da mu'amala dashi,idan kunni yaji..."Bai kuma ƙarisa karin maganar ba ya juya ya bar wajen yana jin rakiyar idanunta har ya fice daga wajen baki ɗaya.Amal da tayi ƙuri tana rakashi da idanunta bata san lokacin da wasu hawayen tsananin takaici da tsanarsa suka cika idanunta ba,"Wai shin da gaske dai Daddy ke yi sai ya rabata da masoyinta Aman Kurfi ya jogana mata auren mutumin da ko kaɗan bata taɓa yinsa ba a cikin rayuwarta?Mutumin da mutunci da ganin girmansa suka gama tsiyayewa a cikin idanunta,tabbas idan har da gaske Yaya Zayd shine zai zama mijin aurenta to kuwa su Daddy za su haɗashi da rashin kwanciyar hankali da samun nutsuwa ne a gidan aurensa,ita kuma za ta yi zaman kwasan zunubi da ɗaukar haƙƙin aure ne domin ba za ta taɓa yi masa biyayya ba,kamar yadda ba za ta taba iya rabuwa da Aman Kurfi ba domin shi ɗin SARTSE ne a cikin ZUCIYARTA da bata ma san ta inda za ta fara ƙoƙarin ciresa daga cikin zuciyarta ba.Tunaninta ya katse a lokacin da kiran Momy ya shigo cikin wayarta,cikin sauri ta dawo cikin nutsuwarta tana saurin ɗaga call ɗin tare da saka wayar a speaker."Amal kina ina ne?" Momy ta jefo mata tambayar cikin muryarta mai kauri."Momy gani a wajen Swimming yanzu zan dawo ciki." Ta furta hakan a sanyaye kafin ta jiyo muryar Momy na faɗin,"Okay ina son ganinki yanzu,ga Abdallah nan ma yana son yayi rigima may be ya fara jin yunwa ne."Mom ɗin na gama faɗin hakan tayi saurin kashe wayarta tabar Amal na saurin miƙewa tsaye jin cewa Abdallah nacan zai fara rigima.Ta kalli time a jikin wayarta tana auna awanni nawa kenan da bashi abincinsa? Ganin kusan awanni uku kenan ya sanyata fara tafiya domin baro ɓangaren swimming pool ɗin ta nufi na Momy zuciyarta na sake cushewa da zafin kalaman Yaya Zayd da suke sake hargitsa nutsuwarta.......✍🏻