GANIN IDO

1

by @mamuhgee

GANIN IDO 2026🔥

Mamuhgee

1

BismillahirRahmannir Raheem.

Ya Allah yanda ka bamu ikon farawa lafiya ka bamu ikon gamawa lafiya.AMIN

Meeting ne yake gudana a cikin lafiyayyan kebataccen qaramin Meeting room din dayake kamfanin da sukayo tattaki tin daga qasar dayake yaxo attending da kansa sbd mahimmancin Meeting din.

Babu kowace irin hayaniya ko daya ko kadan datake iya ratso gurin sbd tsari da tsaron dake hanyar zuwa floor din da Meeting din ke gudana dan mutanen dake cikinsa babu wanda bazaa iya yaqin qasa akansa ba idan wani abu ya samesa musamman fleet ADM dake gurin wanda akansa gabaki daya building din zagaye yake da sojojin ruwa masu karfin gaske sanye da uniforms dinsu wanda zai tabbatar maka da kai tsaye fleet nasu yana gurin dan a matakin da matsayin dayake kai ransa kadai tamkar ran qasa ne gabaki daya.

Kowace Meeting da aiki a kamfanin an dakatar da shi tinda ya iso ya shigo kamfanin saiya fice sun samu tabbacin labari me dadi tukuna zasu koma kowane aiki.

Tin daga qasan lift na hawa sama navy officers dinsa ne suna tsaye babu wanda idonsa da kunnuwansa da hankalinsa baya kan kowace motsin dake gudana wanda take akai shutting hawa sama sai ya bar building din tukuna.

A cikin asalin main Meeting room din duka duka masu meeting din mutum takwas ne sai shine na goman sai personal person nashi da babu yanda zaayi ya kasance a guri batareda ka gansa a gurinba dan haka ake kirasa da fleetShadow sbd idan kanason ganin FLEET ADM saika gansa kusan fiyeda uku kafin kasamu damar ganin ADM idan ya yadda da hakan kenan dan kuwa kaman shine zai baka damar ganin fleet din.

Fara Meeting din akai akan wata alaqa me karfin gaske da zaa kulla ta business din qasashen biyu a karan farko tinda ya hau nasa matsayin na fleet admiral na shekaru bayan gwagwamaryar shekaru da qarar da kuruciya a yaqi cikin ruwa da bawa qasa tsaro ta cikin ruwa.

Wani irin tsararren nutsatsen asalin turancin America ne yake tashi a cikin dakin dayake cike da ratsa kunnuwan manyan suna saurara suna karban kowane bayani a natse da kwanciyan tareda zallan ilimi da qwarewa akan sanin kare haqqin qasar da kowannensu yake can.

Lieutenant commander IMRAN NIFAR Dake tsaye gefen Fleet nasa shi kadaine a tsaye duk dakin kaf sbd matiqar akwai wani tareda uban gidansa baya taba yadda ya zaune sbd tsaro a tsaye yake sai idan su biyu ne kadai yake zaunawa suyi maganarsu sbd yasan babu komai ko kowa dazai iya zama matsala,

hannu ya miqa a natse a ga qatuwar iPad din dake hannunsa yana daukan wasu bayanan yayi zooming wasu bayanan da akeyi yana ajiyewa gaban uban gidansa gefen sunansa dake rubuce gabansa inda aka rubuta FLEET ADMIRAL OF THE NAVY RAHEEM HAKEEM JEERAH.

LC Imran a dauke hannunsa a natse bayan ajiye masa ya gyara tsayuwarsa yana maida kallansa akan Meeting din daidai lokacin Fleet RAHEEM HAKEEM JEERAH of the navy ya motsa a cikin wata irin nutsuwa da kwanciyan hankali tareda kamewan datake bayyanarda zazzafan kwarjininsa da girmansa tareda matsayinsa ya dago fararen idanuwansa masu haske da girman da suka fi na matasa da babu adadi kyau da tsari da wata irin daukan hankali da saka faduwan gaba ya sauke akan iPad din yana kallan screen din a natse.

Bayanan yabi tsaf ya gama saurara tsawon lokaci kafin kowane babba da kalan nasa matsayin kusan daya dana Fleet din na qasashe daban daban suka fara bayaninsu da fadar nasu hukuncin da tsayayyar maganar duka yana sauraransu batareda dagowa ya kalli kowannensu ba har suka gama gurin ya dauki tsit tukuna ya dago idanuwansu da suka saka kowannensu zuba masa ido sbd asalin namijin da babu tsoro ba shakka ba fargaba ba slow a kowace magana sbd gogewansa a fagen da sai namijin daya cika namiji ne yake iya tsayuwa cak a matsayin.

Bude bakinsa yayi yafara jero bayanansa da babu kowace irin tsari irin na kowa a cikinsu sai nasa.

Tsit gurin ya sake dauka ana sauraron bayaninsa da muryansa dake tabbatarda tsayayyen namiji ne yake magana sbd kaurinta dake bada bayanin kakkarfan soldier ne ke magana dan kuwa muryansa bata taba nunawa ko bayyanarda shi shi din me shakaru ne dan kuwa har wani amon kakkaurawa muryan ke bayarwa.

Koda ya dasa bayaninsa babu wanda bai gama gamsuwa da bayanin ba tsaf dan haka take aka tsayu akan nasa tsarin da bayanin daya saka aka kammala Meeting a cikin aminci da girmamawa aka miqe.

LC Imran ne take ya miqa hannu ya dauke ipad din dake gabansa yana basa hanya sbd take ya miqe wainda basu gama zama matsayinsa ba a gurin suka sara masa ya daga musu hannu cikin girmamawa sauran masu irin matsayin nasa kuwa hannu suka miqawa juna a cikin class da wayewa ta wainda suka jiqu a ilimi da gwagwarmaya sunkai matsayin hutu kawai yanzu.

Lc imran ne ya isa kofar tini cikin girmamawa da kulawa me zurfi ya bude masa kofar wadda yana isowa ya saka kai ya fice navys biyu dake kofar take suka bi bayansa Imran na gefensa yana fiddo wayoyin fleet din dan ciresu daga flight mode.

Koda suka iso elevator an bude musu shi da fleet admiral na qasar china suka shiga tare suna magana a natse sai Lc imaran da navies dinsa biyu dana china din biyu.

Koda suka iso qasa securities din sun jeru a shirye tsaf nasa dana fleet Gou minqi take suka nufi qaje aka rufa musu baya babu ta inda babu tsaro dan haka koda suka bayyana a harabar kamfanin take yan jarida dake gurin suka fara daukan hotina daga inda suke tsaye sbd ba daman matsowa securities din a tsaye suke qam da tsaro.

Imran ne ya bude masa mota bayan yayi bankwana da fleet m

Gou ya shiga motar a natse take aka rufe suka tada motocinsu suka bar harabar gurin kowa da securities nasa.

A natse imran ya juyo ya kalli Ubangidan nasa daya dago a natse ya miqa masa wayarsa yana bude baki da sanyin jiki yace

'SIR JEERAH is calling'

Wayar ya kalla da wani irin nutsuwa da kamewa yana miqa hannunsa daya ya karba sbd Sir jeerah da duniya ta sani shine mahaifinsa daya haifesa wanda shine tsohon fleet admiral na baya da shima haryanzu duk wani navy soldier yana alfahari dashi dan kuwa yayi jagoranci na gaskia da jajircewa da rashin tsoro da wani irin zafin gaske rashin hkr ko wasa wanda suke gani da karban irin komai nasa a gurin dansa da a yanzu yakeda wata irin kwarjini da zafin dayake daidai dana ubansa.

Daukan wayar yayi tareda dorawa akan kunnensa ya bude baki cikeda dukkanin girmamawan da bayan ubangidansa ubansa ne kadai a duniyarsa da mahaifiyarsa suke samun wannan girman a gurinsa dan kuwa shi sedai a girmamasa ba shine me girmamawan ba.

'SIR' Ya fara furtawa sbd kalman daya taso akan kiran mahaifinsa kenan kafin ya dora da gaisuwan girmamawa daga can bangaren aka yankesa cikin nutsuwa da isa da nuna iko da cewa

'Fleet Adm RAHEEM HAKEEM JEERAH inaga yakamata kasan bayan haqqin qasa dayake kanka yakamata kasan akwai wani haqqin daya kamata kasan girmansa,

Akwai abubuwan da idan sun zama dalilin fita to baa rasa dalilin dazai saka su zama na shiga,

Ina buqatan ganinka komai girman aikin dayake gabanka.'

Yana gama fadan hakan ya kashe wayarsa yabar fleet adm na sojojin ruwan da wayarsa a hannunsa wanda yasan koda zai rasa ransa ne saiya tabbatarda yabar umarnin akai gawarsa ta isa gaban mahaifinsa kaman yanda ya bada umarnin son ganinsa bisa umarnin da order da babu wasa a lamarin mahaifinsa ko kadan.

Bude baki yayi batareda ya kalli imran ba yace

'SIR na buqatan ganina'

Juyowa Imran yayi ya kalli RAHEEM JEERAH din cikin yanayi na son tabbatarda abinda yaji sbd magana ake ta zuwa Nigeria bayan yasan can ne guri na karshe da ubangidansa xai iya zuwa tin bayan binne gawar rabin jikinsa da yayi acan,

komawansa na nufin yaga lullubin da yayiwa radadin rashin rabin jikinsa dake zuciyarsa.

Numfashi mara sauti ya sauke take yana daga wayarsa dan fara gudanar da shirin tafiyar wadda take SIR JEERAH ne kadai yakai wannan matsayin duk duniya ga FLEET RAHEEM JEERAH.

Maimakon ma su tafi masaukinsu kai tsaye hanyar airport imran ya bada umarnin su nufa sbd su koma gida RAHEEM din ya samu shirin wucewa sbd baitaba tafiyar da bai bawa iyalansa daman yin bankwana dashi ba.

#MAMUH

#BEST LOVE

#RAHEEM JEERAH

#BEST AGE GAP LOVE

#ROMANCE

#SIR JEERAH

#CRAXY COUPLE CHEMISTRY

#GANIN IDO2026

GANIN IDO 2026

By Mamuhgee

1k

Vip 5k

0022419171 AccessBank maryam sani gummi