SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....!💔 Chapter 4

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!💔* Arewabook@ayshadansabo

Paid book ***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 4

Amal na karya kwanar da zai sadata da ɓangaren Momy ta hango Yaya Zayd ya gifta da alamun ɓangaren Daddy zai nufa,taja numfashi ta fesar zuciyarta na sake cika da wani yanayi mai zafi a kansa.Jikinta da zuciyarta duka a mace suke haka ta isa zuwa part ɗin Momy tana tunanin me kuma za ta taras? Tana sanya kanta cikin falon bakinta ɗauke da sallama idanunta suka sauka akan Momyn dake zaune saman 3 seater,daga saman cinyarta Abdallah ne a zaune yana faman shan Kamunsa da Momy ta dama tana bashi domin ta kasa haƙuri har Amal ɗin ta shigo ta haɗa masa da kanta."Momy har kin riga kin dama masa abincin?" Amal ta tambaya tana kallon yadda Momy ta ɗago tana kallonta fuskarta a sake ba kamar ɗazu da fuskar babu walwala ba."Ya fara kuka ne Amal,zo zauna ki ƙarasa bashi."Momy ta faɗi hakan tana kallon fuskar Abdallah dake zillo yana miƙa ma Amal hannu alamun so yake ta ɗaukeshi.Amal ta ƙarisa ta ɗaukesa daga cinyar Momy tana sakin masa lallausar murmushi,ya kuwa ɓangale mata baki yana ta murnar ganinta.Zama tayi daga ƙasan ƙafafun Momy ta cigaba da bashi yana sha tana jin yadda idanun Momy ke yawo a kansu,"Amal me Daddy ya sanar dake ɗazu da kika je ɓangarensa?"Momy ta jefawa Amal tambayar tana sake tsareta da idanunta da babu alamun wargi a cikinsu.Wani abu ya harba a cikin zuciyar Amal,ta ɗaga kanta da sauri ta kalli Momy tana saurin faɗin,"Akan dai maganar Yaya Zayd ne Momy,cewa yayi wai nan da sati uku za a ɗaura,please Momy ki....." Kalamanta suka katse time ɗin da Momy ta ɗaga mata hannunta tana katseta da faɗin,"It's okay Amal,basai kin sake nanata komi ba,ina so kiyi haƙuri ki amince da zaɓin da mukai miki domin yin hakan ne kaɗai zai sanya musan cewa mun isa dake kuma za ki iya sadaukar da farin cikinki domin ki faranta mana,Zayd nagartaccen Namiji ne abin alfaharin duk ɗiya macen da za ta mallakesa a matsayin miji,basai an zauna ana sake zayyana miki nagartarsa ba domin ke kanki shaida ce akan irin yadda ya rayu da ƴar Uwarki cikin soyayya da riritawa,Hameedah bata taɓa kawo mana ƙararsa ba har ta koma ga Allah,don haka ina da tabbacin zai riƙeki da amana ya kuma baki dukkanin kulawa da soyayyar da kike mafarkin samu daga Aman,don haka kiyi haƙuri ki daure kiyi wannan sadaukarwar ki maye masa gurbin Hameedah domin ku taru ku riƙe ɗanku ku bashi tarbiyya ta yadda zai taso ba tare da yayi kukan maraicin rashin Uwa ko rashin Mahaifi a kusa dashi ba,Daddy ya riga ya kammala dukkanin shirinsa na ganin cewa kin maye gurbin ƴar Uwarki zuwa nan da sati uku masu zuwa,kuma Zayd shine da kansa ya buƙaci hakan,meyasa ke ba za ki amince dashi ba?"Momy ta rufe kalamanta da jefa mata tambayar daya sake dugunzuma zuciyarta.Momyn bata bada damar amsa tambayar data jefeta dashi ba ta cigaba da sanar da ita tsarinsu ita da Daddy na ganin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin wannan auren ya tabbata,don haka ya rage nata idan an ɗaura tayi musu biyayya tabi mijinta sau da ƙafa ko kuma ta bijire musu.Daga ƙarshe ta saita mata hanyar barin mata side ɗinta sakamakon kukan da Amal ɗin ta kece mata dashi tana sake jaddada mata cewa ba za ta iya kallon Yaya Zayd a matsayin mijinta ba alhali ya rayu da Yayarta da suka fito ciki guda,haka ta baro ɓangaren Momy tana kuka tana kuma rungume da Abdallah tsam a ƙirjinta tana zuba sambatun cewa inama itace mutuwa ta ɗauka ba Yaya Hameedah ba.A haka ta isa ɓangaren Anty Mamah ta zube a cikin seater tana sakin wani gigitaccen kukan daya janyo hankalin Anty Mamah data fito daga ɓangaren bedroom ɗinta,cikin sauri Anty Mamah ta isa wajen ta karɓe Abdallah daga hannunta tana tambayarta,"Lafiya Amal,me yafaru ne?"Cikin rishin kuka Amal ke sanar da ita yadda sukai da Momy ta rufe maganar da faɗin,"Anty Mamah na tsanesa sam bana ƙaunarsa,bazan iya zaman aure dashi ba domin bamu dace da juna ba,Yaya Zayd bashi da kirki Anty Mamah kune baku san asalin wane ne shi ba." Amal ta furta kalaman cikin ficewar hayyaci da tarin tashin hankali dake neman rabata da dukkanin nutsuwarta.Anty Mamah hankalinta yayi masifar tashi tayi saurin kaiwa zaune tana fuskantar Amal ɗin da dukkanin nutsuwarta,cikin muryar rarrashi take faɗin,"Amal ki nutsu ki sanar dani koma mene ne don Allah,sanar dani wasu halaye gareshi da mu bamu san dasu ba?"Amal ta ɗago rinannun idanunta ta kalli Anty Mamah tana hango tsagwaron tashin hankalin daya haska a cikin idanunta,nan take ta gane cewa taso ta saki layi a cikin kalamanta.Cikin sauri ta girgiza kanta tana faɗin,"Anty Mamah ina nufin shi kansa ba sona yake ba zai amince dani ne kawai domin bazai iya sanar da Daddy cewa baya sona ba,bana jituwa dashi tun farko Anty Mamah,to ta yaya rana guda za a ce lallai sai ni ce zan iya maye masa gurbin Yaya Hameedah alhali ba halinmu ɗaya da ita ba,ita suna son junansu ita da shi saɓanin ni da sam bama shiri da juna,Yaya Hameedah nada haƙuri da kawaicin data iya jurewa dukkanin miskilancinsa ni kuma bani da wannan zurfin haƙurin da za mu iya daidaitawa da juna,don Allah Anty Mamah ki fahimtar da Daddy cewa ba ina son bijirema Umurninsu bane,zuciyata Aman take so shi kaɗai ne namijin da nake hangowa zan iya gina rayuwar aure dashi,don Allah....." Anty Mamah takai hannu ta rufe bakin Amal tana hanata damar cigaba da furta dukkanin kalaman data san cewa ba za su taɓa sauya komi ba.Domin bata hango wani abu da zai iya sawa Daddy ya janye ra'ayinsa ya kuma sauya hukuncin daya yanke na cewa nan da sati uku masu zuwa zai ɗaura musu aure ita da Zayd ɗin ba,don haka take ganin cewa babu amfanin ta cigaba da sauraren Amal tana karya mata zuciya alhali ba za ta iya sauya ƙaddarar dake tunkarota na auren mijin ƴar Uwarta ba."Amal kiyi shuru ki daina ɓata bakinki domin ban hango cewa akwai wasu dalilai ko kalaman da zan tunkari Daddynki dashi su hana aukuwar wannan auren ba sai in dama can Allah baiyi nufin kece za ki maye gurbin ƴar Uwarki Hameedah ba,dukkanin rarrashi da hujjojin da kike tunanin zan iya kafawa Daddy ya saurareni na gwada faɗinsu a gabansa hatta guiwoyina guda biyu saida na aje a ƙasa ina masa magiyar ya duba lamarinki da Aman amma Daddy yayi rantsuwar cewar bai ga wata hujja dana kawo da zai iya sawa ya baiwa wani aurenki alhali ga ɗan Uwanki da yafi kowa buƙatar ki maye masa gurbin matarsa daya rasa ba,ya shaida mini cewa Zayd da kansa ya durƙusa ya roƙi alfarmar a bashi aurenki domin bai hango wata mace da zai iya aure ta maye masa gurbin Hameedah a cikin zuciyarsa ba face ke." Anty Mamah ta dakata daga nan tana kallon yadda Amal ta zabura ta miƙe tsaye tana faman zaro idanunta waje tamkar bata yarda da abinda kunnuwarta suka ji daga bakin Anty Mamahn na cewa Yaya Zayd da kansa ya roƙi Daddy alfarmar a bashi aurenta ba.Muryarta na wani irin kakkarwa tace,"Anty Mamah kina nufin Yaya Zayd ne da kansa ya nemi ayi wannan haɗin gambizar?" Anty Mamah tausayin Amal ya sake cika zuciyarta tayi saurin jinjina kanta tana faɗin,"Tabbas hakan ne ya kasance Amal,shiyasa nake son kiyi haƙuri ki miƙa lamuranki zuwa ga Allah ki cigaba da addu'a domin mu dake bamu isa sauya ƙaddararki ba,idan har ƙaddararki ce auren mijin Yayarki bamu isa mu hana aukuwar hakan ba,don haka ki nutsu ki kwantar da hankalinki don Allah Amal." Anty Mamah ta ƙare kalamanta cike da rarrashi da magiya tana kallon yadda Amal ke sake ficewa daga cikin hayyacinta tana wani irin kuka mai motsa zuciya.Amal ɗin bata iya cewa uffan ba illa kwasa a guje da tayi ta nufi room ɗinta tana sake sakin gunjin kuka,babu abinda ke sake kiɗimata irin kalaman Anty Mamah da tace wai Yaya Zayd ne da kansa ya fara roƙon cewa a bashi aurenta.Tabbas idan ko hakan ne yana da wata gagarumar manufa a kanta da yake neman ya rusa rayuwarta,domin idan ba hakan ba bata hango wani dalili da zaisa ya zaɓeta alhali yasan cewa basa ga maciji da juna tun bayan data san asalin wane ne shi da kalar tsiyar da yake shukawa ba.Ta zube daɓar akan gadon ɗakin baccinta tana jin yadda idanunta ke bushewa,zuciyarta na wani irin ƙeƙashewa ta yadda daga hawayen har kukan da take suka tsaya cak! Zuciyarta tayi wani irin shuru tamkar numfashinta yabar gangar jikinta,wani lokaci can baya na asalin tarihin rayuwarsu da Ƴar Uwarta da yadda suka taso cikin shaƙuwa da ƙaunar junansu ya shiga haskawa a cikin idanunta.

WAIWAYE.....(ADON TAFIYA)

Alhaji Taheer Lawal Ƙaura haifaffen garin Zazzau ne da aka haifesu a Unguwar Ƙaura dake cikin birnin lardin Zazzau ɗin,Iyayensu su uku suka haifa gaba da baya kuma shine babba a cikinsu sai mai bi masa mai suna Abdallah.Daga Abdallah ne Mahaifiyarsu ta share tsayin shekaru goma kafin ta haifo Autarsu mai suna Zainab amma suna kiranta da Abu,daga kanta Mahaifiyarsu Hajiya Ameena bata sake haihuwa ba ko yin ɓari har ta bar gidan duniya.Mahaifinsu Alhaji Lawal Ƙaura Babban Mallamin addini ne da yayi fice a cikin birnin lardin Zazzau baki ɗaya,Mallamin Izala ne masanin Fiqhu sosai da sosai.Sannan kuma a gefe guda ɗan boko ne domin yayi karatun zamani har sai da yakai matakin kammala degree ɗinsa a fannin daya Shafi kasuwanci,don haka suma suka taso cikin neman ilimi na zamani dana addini sosan gaske.Alhaji Taheer kusan shine ya gado Mahaifinsu ta fannin zurfafa ilimin addini sosai da sosai,saɓanin Alhaji Abdallah da yafi fifita karatun boko duk da cewa shima ya tsaya ya samu ilimin addinin mai zurfi amma dai bai kai ɗan Uwansa Alhaji Taheer yin zurfi a ɓangaren addini sosai ba.Sun taso cikin gata da kulawa domin Alhaji Lawal Ƙaura yana da tarin rufin asirinsa kasancewarsa babban ɗan Kasuwa,kuma manomi daya riƙe harkar noma da kiwo da muhimmanci sosan gaske.Don haka ya basu ilimi mai zurfi tare da ɗaurasu akan sana'arsa na ɗinka manyan riguna yana sayarwa,da kuma harkar noma da kiwo da yafi fice a cikinsa.Don haka suka taso kowa nada sana'arsa daya dogara da ita,kusan ma za a iya cewa da waɗannan sana'o'in daya ɗaurasu akai suka riƙe kansu da ɗaukar nauyin karatunsu har suka kammala jami'ar Ahmadu Bello University dake birnin Zazzau.Alhaji Taheer ya karanci fannin Kasuwanci tamkar Mahaifinsa,yayinda shi kuma Alhaji Abdallah ya karanci Economics.Lokacin da suka kammala bautar ƙasa ne bada jimawa ba cikin manyan mutanen da Mallam ke hurɗa dasu wani commissioner ya amshi takardarsu su duka biyu domin nema musu aiki,Alhaji Taheer aka sama masa aiki anan State House dake Kaduna,yayinda Alhaji Abdallah shi yayi sa'ar samun aiki a ma'aikatar NHIS(National Health Insurance Scheme) aka ajesa a reshensu dake jihar Kano.Alhaji Taheer nada shekaru biyu da fara aiki yayi auren farko ya auri matarsa mai suna Ayshatu,wacce asalinta ƴar jihar Borno ce a cikin ƙabilar Shuwa Arab.Mahaifinta Shuwa Arab ne yayinda Mahaifiyarta kuma Kanuri ce,sunyi aure ne na soyayya da ririta juna domin Aysha wayayyace daya aureta bayan kammala deegree ɗinta.A garin Zaria suka fara zama gidan da Mallam ya gina musu shi da ɗan Uwansa Abdallah kowanne da ɓangarensa,Alhaji Taheer da Hajiya Aysha basu samu haihuwar fari da wuri ba saida suka share tsayin shekaru uku sannan ta samu ciki.Shima kuma da aka tashi haihuwar ɗan sai ya kasance yazo babu rai,tun kuma daga lokacin Aysha bata sake samun cikin daya zauna ba sai yawan ɓari.Data samu cikin baya wuce wata ɗaya biyu ya ɓare,a haka suka samu shekaru biyar da aure kuma zuwa lokacin Alhaji Taheer ya fara samun buɗi sosai da sosai domin duk abinda ya taɓa arziƙi yake zama masa.Sam bai dogara da aikin Gwabnati ba,yana haɗawa da noma da kiwo ga kuma babban business ɗinsa daya fara na shigo da kayan gina-gine daga ƙasar China yana rabarwa ƴan sari.Da kuɗi ba masu yawa can sosai ba ya fara,amma da yake hanyar arziƙinsa ne nan da nan yayi shuru ya fara yin fice a cikin harkar.Ita kanta matarsa Aysha bata zauna haka ba domin sosai business ɗinta na saida turarukan wuta da ake aiko Mata daga gida Maiduguri ya amsheta.Ta fara sanuwa sosai a Filin Mallawa Unguwar da suke zaune,cikin ikon Allah itama ta fara bada sari ana zuwa a siya a kuma sara a hannunta.Sun shiga shekaru na shida da aure shima Abdallah Allah ya haɗashi da Asiya,ba a ɗauki dogon lokaci ba akai bikinsu bayan anyi bincike an gano cewa Iyayenta mutanen kirki ne kuma daga gidan asali da dattako ta fito.Zaman Aysha da Asiya zama ne na amana da shaƙuwa,ko kaɗan basu san wani abu wai shi kishin sauri da wasu ke ɗaurawa kansu ba.Asiya na shigowa gidan da watanni tara ta samu ciki,murna a wajen Aysha da Alhaji Taheer ba a magana domin kaikace sune za su samu haihuwa ba ƙanin nasa ba.Lokacin da cikin ya isa haihuwa ne Allah ya sauki Asiya lafiya ta haifo bouncing baby boy ɗinta mai kama da Mahaifinsa tamkar kwabo da kwabo,Yaro kyakykyawan gaske domin Abdallah kyakykyawa ne hasken fatarsa ne kawai Jaririn bai ɗakko ba.....✍🏻