Chapter 56
by @zahrabmrs02
56⌨️💬
Rainon tagwaye a garin Massachusetts ba wasa ba ne. kukan Khalil da Sultana a lokaci guda yakan sa Farhana ta ji kanta yana juyawa. Ga shi kuma hutu ya ƙare, dole ta koma karatu domin last season dinta tunda su nan 3 years ne kuma a 200lvl ta fara .
Nene tai ta faman masifa a duk lokacin da ta ga Farhana ta ɗauki littafi ko laptop. "Ke Maryam! Wane irin boko ne wannan na dole? Yara suna kuka, ke kuma kina ta duba takardu? A Matazu ai mace idan ta haihu, wata biyu ba ta taɓa komai sai riritar jarirai."
Farhana ta yi murmushin gajiya, "Nene, karatun nan shi ne zai taimaki yaran nan a nan gaba. Kiyi haƙuri, Sameena tana taya ni ay
Kamar ya shi zai taimake su,suna jikokin Gwamna mai zasu rasa?
Shiru farhana tayiwa nene dan she’s speechless a halin yanzu .
Farhana tana zaune tana ba Khalil nono, sai ta fara rera masa waƙar lallashi a hankali. "Yi shiru Lamidona... Khalil ɗan gidan Abdulkadir . Lamido babban mutum, mai kwarjini..."
Ta dade tana son sunan Lamido saboda tunawa da tsohon saurayinta Farooq (Lamido), wanda har yanzu akwai sauran gurbin soyayyarsa a can ƙasan zuciyarta, duk da ta fara son AK.
AK ya shigo ɗakin sanye da rigar sanyi, ya ji lokacin da take kiran yaron da "Lamido." Ya tsaya cak, fuskarsa ta sauya. Ya ajiye briefcase ɗinsa ya ƙaraso kusa da ita.
"Wifey, me kika kira shi yanzu?" AK ya tambaya muryarsa a dake.
Farhana ta ɗan razana, amma ta daure. "Lamido nake kiran sa. Sunan ke mun dadi
AK ya zauna a gefen gadon, ya zuba mata ido. "Meyasa Lamido? Ibrahim sunansa, kuma Khalil muke kiran sa. Daga ina sunan Lamido ya fito? Ban taɓa jin kowa a danginku ana kiran sa Lamido ba."
Farhana ta ɗan shafa kan Khalil, zuciyarta tana bugawa. "Honey, kinsan ni Bafulatana ce. Kuma tun ina yarinya nake son sunan Lamido, ina jin daɗin sa a baki. Ba wani abu ba ne, kuma Kaga dan fari ne shiyasa nake kiransa Lamido.
AK ya kura mata ido kamar yana son karanto abin da yake cikin ranta. "Lamido... sunan yana da nauyi. Ina fata dai ba wani kake tunawa ba kake sanya wa ɗana sunan sa."
Farhana ta yi dariya ta magance zargin, "Haba Honey! Wane zan tuna bayan kai? Kawai dai buri ne nake son cikawa."
Can ƙasa kuwa, Nene ta kusan doke Brianna da ludayi. Brianna ta sanya kwanukan da Nene ta tuka tuwo a ciki cikin dishwasher, Nene kuma ta ce dole sai an wanke su da hannu da daddawa don ƙanshin tuwon ya fita.
"Ke yar aiki Fito da kwanukan nan! Wannan akwatin naku ba zai iya wanke kunkumin tuwo na ba. Abdulkadir! Zo ka gaya wa wannan yarinyar ta fita idona!"
AK ya karaso yana dariya, . "Nene kiyi haƙuri, Brianna tana taimaka miki ne."
Farhana tana kwance, Sultana tana bacci a gefenta, amma Khalil (Lamido) ya ƙi bacci. Ta kalli AK dake ta faman latsa waya fuskarsa a murtuke. Ta san maganar sunan nan ta sosa masa rai.
"Honey, har yanzu fushi kake yi akan sunan Lamido?"
AK ya juyo ya kalleta, "Ba fushi nake ba Wifey. Kawai dai ina mamakin yadda kika nace akan sunan ne. Amma shikenan, tunda kina so, zan barki. Amma ki sani, kishi na ba irin na kowa ba ne."
Farhana ta ji jikinta yayi sanyi .Ta sani cewa tana wasa da gobara, amma kiran Khalil da "Lamido" yana ba ta wani irin sanyi daban wanda ba za ta iya bayyanawa ba.
Watanni uku sun gudu tamkar kifawar ido. Khalil (Lamido) da Sultana sun yi bul-bul da su, fatarsu tana sheki saboda kulawar Nene da kuma ni’imar garin Massachusetts Khalil yana kara girma, kamaninsa da AK yana kara fitowa, amma duk lokacin da Farhana ta kira shi "Lamido," wani sanyi take ji a ranta.
Ganin yaran sun yi karfi, Nene ta fara shirin komawa gida. Farhana ta shiga damuwa sosae, har kuka take yi tana lallashin Nene.
"Nene, don Allah ki kara ko wata biyu ne. Kinsan yanzu zan fara karatun karshe sosae, kuma na saba da ke a kusa da ni," Farhana ta fada tana share hawaye.
Nene ta tabe baki tana nade kayanta Ke Maryam, sakar min hannu! Na gaji da zaman dakin nan, kullum kankara, kullum sanyi. Ko rana ba a ganinta sosai. Na yi kewar garina, na yi kewar daddawa ta da kukan gida. Yaranki sun riga sun yi Kwari ban ga dalilin zaman garin nan ba,ke da ya zame miki dole kiyita zama ,wanan ay sai Ka Hauka ce ni tunda nazo banga masu jin Hausa ba sai ku
AK ya shigo dakin, fuskarsa dauke da wani babban envelope. Ya san irin kokarin da Nene da Sameena suka yi, musamman yadda Nene take tuka tuwo wa farhana ,tana riritar tagwaye a daren sanyi.
"Nene, dama na zo ne na miki albishir tunda Kin fada min zaku tafi ," AK ya fada yana mika mata takardun. "Amma kafin ku sauka a Najeriya, na biya muku Umarah ke da Sameena. Zaku sauka a Saudiyya ku yi ibada, sannan ku wuce gida."
Nene ta zaro ido, ta kalli takardun sannan ta kalli AK. Ta saki wata uwar guda, sannan ta fadi a kasa tana birgima saboda dadi.
"Abdulkadir! Allah ya maka albarka! Allah ya bar ka da Maryam! Umarah? Ni Nene zan taba kasa mai tsarki? Ashe asalin daukakar kenan! Sameena, zo ki gani, rabon ki ya fito!"
Sameena ta rugo da gudu tana kukan murna. Farhana ma ta kasa daina kuka, tana murna da wannan babban alkhairi da mijinta ya yi wa kakarta da kanwarta.
Ganin yadda Farhana take ta faman kuka saboda kewar su Nene, AK ya dafa kafadar ta, ya rada mata magana mai dadi.
"Wifey, karki damu sosae. InshaAllah idan yaran nan suka cika wata shida (6 months), zamu shirya gaba dayan mu mu nufi Najeriya ganin gida. Zaki ga Abbi, ki ga Diddi, kowa ya ga tagwayen Massachusetts
Wannan magana ta sanyaya ran Farhana sosae. Ta san cewa nan da watanni uku kenan, zata koma gida tana taku a matsayin uwar tagwayen AK.
Ranar tafiya ta zo. Nene ta ci ado cikin wani old leshi, ta daura jacket din sanyin ta a kai. Brianna ma ta zo da kuka, domin ta saba da Nene duk da rigimar da suke yi.
"Ke yar aiki (Brianna), kiyi wa Maryam aiki sosae. Idan na dawo na ji kin bata mata rai, zan miki dure da kukar Matazu," Nene ta fada tana nunawa Brianna yatsa.
Sameena tana ta faman bidiyo tana cewa, "Off to Makkah with Nene! Thank you Brother AK."
Farhana ta rungume Nene tana kuka, "Nene, kiyi mana addu'a a can."
"Zan yi Maryam, zan yi sosae. Amma ki kula da yaran nan, musamman wannan 'Lamidon' naki da baya yarda da kowa ," Nene ta fada tana shafa kan Khalil.
Har suka bace wa ganinsu, Farhana tana ɗaga hannu. Ta juyo ta kalli AK, ta ji wani irin nauyi. Yanzu ita kadai ce zata fuskanci rainon Khalil da Sultana da kuma karatunta a Boston. Amma zuciyarta tana can Najeriya, tana hango ranar da zata sauka a filin jirgi na Abuja dauke da tagwayenta.
Bayan tafiyar su Nene, gidan Chestnut Hill ya yi wata irin tsit mai ban tsoro. Duk da cewa AK ya yi ƙoƙarin sauƙaƙa wa Farhana ta hanyar ɗauko mata Nanny (mai rainon yara) sannan Brianna ta dawo gidan da zama gaba ɗaya, hakan bai hana Farhana jin wani irin kaɗaici ba.
AK ya koma bakin aiki gadan-gadan, babu hutu, babu sassauci. Yawancin lokaci yana tafiya kafin ta tashi, ya dawo kuma tana ta faman lallashin yara ko tana barcin gajiya.
A hankali, damuwar haihuwa (Postpartum) ta fara kama Farhana. Ta tsinci kanta cikin wani yanayi na yawan kuka, rashin cin abinci, da kuma jin kamar ta gaza. Tana yar shekara 20 kacal, tana fuskantar ƙalubalen da ya fi ƙarfin shekarunta; ga Final Year a jami'a ga kuma tagwaye masu buƙatar kulawa 24/7.
Wata rana da daddare, Khalil (Lamido) da Sultana suka ƙi yarda da Nanny, suka ƙi yarda da Brianna. Kukan su ya karade gidan. Farhana ta fito daga ɗakin karatu kanta yana sarawa saboda binciken da take yi na Project.
Ta karɓi Sultana, ta karɓi Khalil, amma dukansu suka ƙara sautin kuka. Farhana ta zauna a ƙasa a tsakiyar parlon, ta sanya su a gaba, ita ma ta fashe da wani irin kuka mai cin rai.
"Wayyo Allah na! Me na yi wa kaina? AK ba ka nan, yaran nan sun ƙi shiru, karatu na ya tsaya. Na gaji! Wallahi na gaji!" Ta faɗa tana kuka mai ban tsausayi da na tsananin gajiya.da kyar Briana da Emily suka rarrashe ta a ranar
Wayar Farhana ta zama tamkar kayan ado. Ta kan yi kwana biyu ba ta kunna ta ba, ba ta ma san abin da yake faruwa a duniya ba. Ko Diddi suka kira, sai dai su kira ta wayar Brianna ko ta AK. Ba ta da lokacin kanta, balle na hira a WhatsApp ko kallon tv
Emily ta ƙaraso cikin damuwa, "Mrs. Farhana, please give me the babies. You need to rest. You look very pale."
Farhana ta girgiza kanta, hawaye suna zuba, "They want me, but I don't even have the strength to hold them. Where is AK? Why is he never here when I'm breaking down?"
Wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, AK ya shigo gidan. Ya tarar da Farhana a kwance a doguwar kujera, idonta ya yi lulu-lulu saboda kuka, gashin kanta ya hargitse.
"Wifey, me ya faru? Emily ta gaya min kinyi kuka sosae yau," AK ya faɗa yana ƙoƙarin taɓa goshinta.
Farhana ta ture hannunsa, ta tashi zaune da ƙyar. "AK ba kuka kawai na yi ba, hauka nake kusa yi. Kana ganin ɗauko Nanny shi ne mafita? Ina buƙatar ka! Ina buƙatar mijina a kusa da ni. Na zama kamar matar takaba a gidan nan, kullum ni ɗaya da yara da littattafai."
AK ya sauke numfashi, "Farhana, kinsan ina ƙoƙarin kammala wasu ayyuka ne kafin mu tafi Najeriya nan da wata uku. Komai nake yi saboda ku nake yi."
"A'a! Saboda kanka kake yi!" Farhana ta daka masa tsawa tana kuka. "Saboda burinka kake aiki, ka bar ni ina narkewa. Dubi ni, na zama uwa mai shekaru 40 alhalin shekaruna 20 ne kacal. Idan har haka zaman Massachusetts yake, na gwammace in koma Matazu in zauna a rumbu!"
AK ya tsaya yana kallonta, ya ga yadda ta rame, ya ga yadda annurin fuskarta ya ɓace. Ya tuna ranar da ya fara ganinta a matsayin "'daliba ," tana cike da fara'a. Yanzu kuwa, damuwar raino sun sa ta zama wata daban.
"I'm sorry, Farhana. Na yi miki alkawari, daga gobe zan rage ayyukan ofis. Zan rinka zama da ke mu yi rainon tare," AK ya faɗa yana rungume ta.
Farhana ba ta ce komai ba, sai ajiyar zuciya take saukewa. A can ƙasan zuciyarta, tana tunanin: "Shin hakan zai yiwu? Ko kuwa lallashi ne daya saba?" Tana kallon Khalil dake bacci a gadonsa, ta rada a hankali, "Lamidona, kai ne kaɗai kake kusa da ni a lokacin da nake kuka." Ba ta sani ba, ashe AK yana jinta, kuma sunan "Lamido" ya ƙara masa wani irin daci a rai, amma ya zaɓi ya yi shiru domin yanayin da take ciki.
Duk da alƙawarin da AK ya yi wa Farhana na rage ayyukan ofis, abin bai sauya ba. Kullum tana farkawa tana ganin gefenta wayam, tana kwanciya kuma barci ya yi awon gaba da ita kafin ya shigo. AK ya zama tamkar baƙo a gidan Chestnut Hill; ofis ya zama gidansa na gaskiya, Chestnut Hill kuma ya zama otal ɗin barcinsa.
Farhana ta zama tamkar mutum-mutumi. Tana tafe tana kuka, tana zama tana kuka. Jikinta ya yi sanyi, idanunta sun shige ciki saboda rashin barci da damuwa.
A can Najeriya, Zee da sauran ƙawayen Farhana sun shiga damuwa. Tun rabo da su ji muryar Farhana tun Bayan tafiyar nene , sako (message) idan sun tura ba ta buɗewa, kiran waya kuma ba ta amsawa.
Wata rana Zee ta ƙara kira sau biyar, Farhana ba ta ɗaga ba. Zee ta harzuƙa, ta tura mata saƙon bacin rai a WhatsApp:
"Farhana, wai me kike nufi ne? Don kawai kin haifi tagwaye a Boston shi ne kika daina kula mu? Kin manta ke wace ce kafin ki kai nan? Ko kiranmu ma ya zama ɓata lokaci ne a gare ki?"
Farhana tana zaune tana ƙoƙarin rubuta Thesis dinta yayin da Khalil yake ta faman kuka a hannun Nanny, ta buɗe wayar ta ga wannan saƙon. Wani irin zafi ya turnuƙe ta. Ta danna kiran Zee, tana ɗagawa, Farhana ta fara masifa.
"Zee, kinyi asara ! Ba kya gani ne? Ba kya tunani? Ina rainon tagwaye ne ni kaɗai a ƙasar sanyi, ina karatu, kuma mijina ba shi da lokaci na. Maimakon ki tambayi halin da nake ciki, kina zargina da girman kai? To bari kiji, na daina kula ku ɗin! Idan ba za ku iya taya ni da addu'a ba, ku fita daga rayuwata!"
Zee ta firgita, "Haba Farhana, magana muke yi ta mutunci..."
"Ba wani mutunci! Kowa ma maƙiyina ne!" Farhana ta daka wa wayar tsawa sannan ta kashe ta gaba ɗaya. Ta yi jifa da wayar a kan gado, ta kifa kanta a kan tebur ta ci gaba da kuka mai ban tausayi.