Chapter: 17
by @zmchubado
BAFULATANA
Zm~Chubaɗo
017
murmushi yayi sannan yace,"ngde Ummie."
Ɗaga masa kai tayi sannan ta harɗe hannunta a saman ƙirjinta still tana kallonsa da murmushi akan fuskarta, wani irin kallo take masa mai tarin manufofi wanda kai tsaye mutum ba zai iya fassara ma'anarsa ba. kusan a tare suka shiga cikin gidan wanda ya sha gyara na musamman duk saboda zuwansa.
Miƙewa yayi direct to part ɗin da ya saba sauka idan yazo ƙasar ita kuma Ummie ta tsaya a harabar falon tana mai yiwa bayansa rakiya da kamilallun idanunta, har ya kai bakin ƙofar part ɗin zai murɗa handile ɗin ƙofar ta ce," idan kayi wanka ka huta pls kazo daining kaci Abinci."
Ɗan murmushi ya ƙarayi sannan ya ce,"Okay!" sannan ya kunna kai zuwa cikin part ɗin, bedroom ya shige tareda rage kayan jikinsa zuwa singlet with boxer wanda hakan ya baiyana murɗaɗɗun laps ɗinsa, a hankali yake takawa harya isa cikin ƙayataccen toilet ɗin wanda aka wadashi abubuwan ƙyale-ƙyale iri-iri, tsayawa yayi yana kallon kowace kusurwa dake toilet ɗin bisa ga mamakinsa komai an sauya masashi daga waƴanda ya sani a baya zusa Sababbi, a nitse yake takawa cikin takunsa harya isa gaban wani baban Abu wanda yafi kamada bahon wanka na zamani, ruwa ya tara a cikin ƙaton bahon me ɗan zafi tareda zuba shower gel ɗin daya saba amfani dashi samfurin Olay me bala'in ƙamshi, take kumfa ta cika bahon.
Murmushi yayi sannan ya shiga cikin Ruwan ya zauna tareda lumshe manyan idanunsa yana jin yanda zafin ruwan ke ratsa tsokar jikinsa, sosai ya kejin daɗin yanda zafin ruwan ke Ratsashi ya jima a ciki daga baya ya buɗe ruwan ya wuce sannan ya tare wani yayi wankan ya fito. Bayan ya fito daga wankan be wani tsaya shafe-shafe kamar yanda ya sababa ya shirya cikin kayan sport marasa nauyi tareda kabbara sallar dake kansa, ya jima yana sallar sannan ya idar ya fara gabatar da Azkar ɗinsa kamar yanda alƙur'ani da sunna suka kawo.
Yana miƙewa kiran ya shigo wayanshi, daga yanayin ringing ɗin ya Fahimci cewar Abie ne, zama yayi daga bakin gadon dake ɗakin tareda kara wayar a kunnensa da sallama yace "Abie ya gida? Ɓangaren Abie yayi murmushi mai sauti yace "lfy lau Babban mutum ya gajiyan Hanya?"
Shagwaɓe fuska yayi sannan ya ce"uhm wllh Abie akwaita sosai a tareda ni, kagafa se yanzu na yi wanka tun shigowana ƙasar." Dariya Abie yayi sannan yace "Ka kula da kanka sosai Ina da tabbacin za ka yi aikinka da cikakkiyar nasara" Muzaffar yayi murmushi yace " sure Abie in sha Allah."
Mom dake zaune gefan Abie haka nannsai ta samu kanta da rashin nutsuwar zuciya, gabaɗaya hankalinta ya gaza kwanciya tunda muzaffar yayi tafiyar, jiki babu ƙwari ta karɓi wayar daga hannun Abie cikin tattausan lafazi ta ce "Boy ya dai ina fatan kana lfy?"
Ɗan shafa gefan fuskarsa yayi kana yace "I'm fine mom and why your voice is so cool?"
"I really don't know why darling! na kasa natsuwa da wannan tafiyar taka, hakanan nake ji a jikina something is definitely happen to me wanda bansan mene shi ba. But Pls take good care of yourself kaji yaron kirki? Sannan kasa ido sosai akan duk wani motsin waccan makirar matar Aisha kaji ko?"
Shiru yayi bece komai ba a haka suka katse wayar Abie na binta da kallon mamaki ya ce,"why are you behave like this Hajiya Saratu? Meyasa ke bakya ƙaunar kiga an zauna lfy ne? shekaru nawa ana wannan abin ai yaci ace yanzu kun haƙura kun zubar da duk wata ƙiyayya da kukewa juna saboda kwanciyar Hankalina."
Cikeda karyewar zuciya mom ta ɗaga ido ta kalleshi sannan ta buɗe baki tace "Abie ba zaka gane komai ba shiyasa kake faɗar hakan, taya matar data nunawa ɗana tsana tun yama ɗan ƙaramin yaro kayi tsammanin cewar yanzu ba zata iya cutarmin dashi ba? Ni fa uwa ce Abie taya ba zanyi yaƙi da duk wani me neman cutar min da rayuwar ƴaƴana ba? Ga dukkan alamu ka manta da wacece matarka Aisha kasancewar bata taɓa haihuwaba tunda ta hafi ƴarta batazo da raiba take ƙoƙarin ganin bayan nawa ɗan har zuwa lokacin daka ɗauketa tabar ƙasar nan. Wllh nasan she can do anything don ganin ta lalata mini rayuwar Ahalina amma nasan oneday one time you will understand what I mean in sha Allah."
Shidai Abie girgiza kai kawai yayi tareda miƙewa ya faɗa toilet ta bisa da kallo,
*******
Ɓangaren Muzaffar kuwa Ajiye wayar yayi ya fita saboda wani irin juyawa da cikinsa keyi saboda yunwa, yana fita a falo ya samu Ummie tareda mai aikinta Maryam. kallo ɗaya zakayi mata kasan ƴar Nigeria ce, a ƙalla shekarun Maryam zasu kai 40 tun lokacin da Ummie tabar nigeria Suka taho tare.
da fara'a Ummie ta tarbeshi suka nufi daining ita kuma Maryam ta durƙusa tana gaisheshi with so much respect, murmushi ya sakin mata sannan ya wuceta ba tareda ya amsa ba, Hajiya Aisha da kanta tayi sarving nashi Abincin wanda keta zuba uban ƙamshi sannan ta miƙa masa flet ɗin gabansa itama ta xauna ta fara zuba nata Abincin wanda keda banbanci da nasa kasancewar tana da ciwon suger.
Kusan a tare suka fara cin Abincin har wani lumshe ido Muzaffar keyi saboda yanda abincin ya masa Daɗi, hakan ne yasa yaci sosai har ummie tayi mamakin hakan, saboda a iya sanin da tayi masa bayacin abinci sosai.
bayan sun gama cin Abincin ne Maryam ta miƙe ta kwashe kayan Abincin takaisu kicin ta gyara gurin, zama su kai a falon suna ɗan taɓa hira duk akan abinda ya kawoshi India.
wani tayi murmushi wani kuma ta kalleshi, wayarta ce tayi ƙara hakan yasa ta maida hankalinta ga wayar tareda karawa a kunnenta Tace "bari zamuyi magana yau in sha Allah komai zai kammala ba tareda anci lokaci sosai ba." Ta faɗi hakan tana satar kallon muzaffar wanda ya maida duk hankalinsa akan System ɗinta dake gabansa.
a nitse yake gabatar da komai cikin nutsuwa ba zato ba tsammani yaji cikinsa yay wani irin juyawa sannan ya farq muɗa masa, dafe cikin yayi da hannunsa na dama sannan ya zube gwiwowinsa a ƙasa ya saki wata irin ƙara wadda ta firgita Hajiya Aisha da me aikinta Maryam dake kicin tana wanke kwanikan da akaci abinci dasu, Sakin wayar Hajiya Aisha tayi sannan ta nifeshi gadan-gadan tana raba idanu, hanyar kicin ta kalla ganin babu wanda ya taho yasa ta ɗagoshi tana kallon fuskarsa kimanin 5second jin tafiyar Mutum daga hanyar kicin ɗinne yasa itama ta saki ihun neman taimako.
A gigice maryam ta ƙaraso gurin idanunta a waje saboda tashin hankali tana kallon Ummie lokaci guda kuma ta sake maida kallonta ga muzaffar wanda ke fitarda farar kumfa daga bakinsa hakanne ya bata tabbacin Guba yaci.
Cikin tashin Hankali maryam ta dora hannu aka tace "innanillahiw'inna'ilaihirraji'un mun shiga uku Hajiya!"
a gigice maryam ta nufi wayar telho ɗin dake ajiye bisa wani ƙaramin table ta shiga kiran wayar Babban Asibitin dake kusa dasu koza'a samu a ceto Rayuwarsa cikin Sauƙi.
Ummie kuwa ta kasa motsin kirki balle har ta tsinana wani abin arziƙi a gareshi, take wani irin gumi ya fara keto mata tareda nadama mara misaltuwa, babban abinda ke ɗaga mata hankali a wannan lokacin shine da wani ido zata kali Abie bisa wannan abinda data kasance itace silar Faruwarsa?
tabbas duk irin son da yake mata a wannan zata gane kurenta don wllh ta san ba zata tsira a hannunsa ba musamman Saratu. Idan taji cewar tayi poisoning ɗin ɗanta tabbas akwai gagarumin yaƙi a tsakaninsu........
*** *** *** *** ***
*RUGAR ARƊO*
Da ƙyar Jaddah ke jan numfashi saboda azabar da takeji a ƙasanta, ko hannunta ta kasa ɗagawa balle tasa ran zata iya miƙewa, seda suka gama zuba Rashin imaninsu sannan suka tattara komai suka tafi dashi bayan sun gama ketawa Yara ƙanana haddinsu a gaban idon iyayensu, a wannan rana rayuka dayawa sun sosu da baƙin ciki mara misaltuwa haka kuma zuciyoyi sun baƙanta, a wannan tsukun ne Mahaifin Ruƙatu Babbar Aminiya Rabe ya rasa Rayuwarsa al'amarin daya ƙara ɗaga mata hankali kenan.
sosai malam iro ya zubar da jini har hakan yasa suka fitar da ran cewar ze tashi, moddibo kuwa gabaɗaya ya kasa cewa komai duk a sanadin bala'in daya sameshi, baya iya furta komai se ido da yakebin kowa dashi, miƙewa yayi ya shiga ɗakinsa da sauri don ganin halinda Jaddah ke ciki, da sauri ya kauda kansa sabida ganin irin Rashin imanin da suka aikata mata komai bushewar zuciyarka dolene ka tausaya mata muddin kanada imani, da sauri ya isa gareta sabida ganin yanda jini ke zuba daga ƙasanta duk yamda yaso ya taimaka mata kasawa yayi dole ya zube a gurin ya saki kuka me sauti da ban tausayi, itama kanta Jaddan kuka takeyi tareda tausayawa kanta da irin Rayuwar da zata fuskanta a nan gaba.
Sai da yayi me isarsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin ya haɗo ƙirare ya kunna wuta tareda ɗora ƙatuwar tukunya akai, cikin mintunan da ba zasu gaza 20 ba ruwan ya tafasa wata babbar fanteka ya ɗauka ya zuba ruwan a ciki kimanin rabin fantekar sannan ya ɗauka ya shiga da ita ɗakin ya zuba wani garin magani a ciki take kallar ruwan ta sauya ya koma kore, seda ya ɗan sha iska sannan ya kinkimeta ya zaunar da ita cikin ruwan, wata uwar ƙara ta saki kamar zata fasa masa kunne.
cikin ikon Allah jinin ya tsaya har taji ɗan dama-dama a jikinta, seda ya gana bata duk wani taimakon da yake ganin ze iya bata sannan ya fita zuwa waje ya fara duba sauran jama'a ba tareda ya damu da jinin dake zuba a kansa ba. *_(Allah sarki modibo haqiqa kyakkyawar zuciya halitta ce ba kowani mutum ne ke tuna al'uma ba a lokacin da musiba ta sameshi, mafi yawan mutane kowa kansa yake fara ginawa sannan daga baya ya tuna da al'uma amma shi kuma moddibo yace "al'uma ita ce farko kafin kansa. Ya Allah ka cire mana son kai da ƙyashi daga zukatan mu🤲)_*
A hakan seda ya tallafawa kowa sannan ya agazawa kansa daga baya. Baze iya furta komai ba a irin wannan halin baƙin cikin da yake ciki ba, amma yana roƙon Allah ya saka musu bisa zalincin da aka aikata musu.
******
The fulani girl:
Tafiya take tana shan mangwaron dake hannunta har ta fito daga dajin zuwa titi, tsayawa tayi tana ƙarewa titin kallo kamar yanda tayi a baya, a hankali ta ɗaga ƙafarta ta taka titin kamar me koyan tafiya saboda gani take at any time zai iya zurmawa da ita.
ba zato ba tsammani wasu farar motoci samfurin formatic C350 suka dano kai cikin jerin gwano kimanin guda 6, a wannan lokacin ta riga ta kai tsakiya ƙarar hon ɗin da suka matsa mata ne ya ƙara gigita mata lissafi, sai kawai tsaya cak ta ƙanƙame idanunta zuciyarta na bugawa da mugun ƙarfi.
Cikin rashin sa'a motar dake gaban ta gaban tai sama da Ita, take ta zube a saman kwantar jini na ɓulɓula ta hancinta bakinta.
A gigice Drivern dake motar ya tsaida motar ya fito a kiɗime wannan yasa motocin dake binsa a baya suka tsaya sabida ganin tsayawarsa, kwance yake cikin motar dake tsakiya ya lumshe kyawawan idanunsa yaji motocin sun tsaya, a hankali ya buɗe idanunsa ya kalli drivern dake jan motar da yake cikin ya ce "what's wrong?"
Cikeda girmamawa matashin Drivern yace "I don't know sir but let me check." ya firta hakan cikin alamun girmamawa.
Maida idanunsa yayi ya lumshe ba tareda ya damu da abinda ke faruwan a waje ba yaji an ƙwanƙwasa glass ɗin motar da yake ciki, cikeda damuwa Wanda ya ƙwanƙwasa ɗin ya ce "im sorry sir hatsari muka samu, tsautsayi tasa mun bige wata yarinya."
Da wqni irin sauri guy ɗin ya buɗe idanunsa tar akan wanda ya kawo masa labarin, sannan ya buɗe murfin motar ya fito hankalinsa a tashe, sanye yake cikin dakakken yadin filtex maroon colour wanda ya zauka a jikinsa, dogo ne sosai ma'abocin cikar zati da haiba, yana da duhun fata sosai wanda kai tsaye ba za'a saka shi cikin jerin maza masu hasken fata ba amma yana da gogewar fata sosai irinta ƴaƴan masu hannu da shuni.
Gabansa ne ya faɗi a lokacin da yayi arba da jinin dake fita ta hancinta da bakinta, a hanzarce ya tsuguna ya ce, "muyi hanzari a kaita Asibiti tana zubar da jini."
Babu ɓata lokaci suka sanyata a cikin ɗaya daga cikin motocin ba tareda sunyi la'ajari da kar jinin ya ɓata musu mota ba suka kwasa da wani mahaukacin gudu suka nufi wani ƙaramin hospital dake cikin wani ƙaramin ƙauye dake maƙotaka da dajin. Babban abinda ze bawa me karatu mamaki shine har lokacin tana riƙe da wannan jakar da Baffah ya Rataya mata.
Ina yiwa ɗaukakin al'umar musulmi barka da shigowar Azumin watan Ramadan, fatan Allah Ubangiji ya sa muyi ibada karɓaɓɓiya, bayin Allah mu dage da ibada har zuwa lokacin da zamuga ƙarshen wannan watan karmu gaza, don wataƙila shine damar mu ta ƙarshe ba lallai mu sake ganin wani watan Ramadan ɗin ba. A nan zan tsaya sai bayan sallah idan Ubangiji ya ara mini ran da zan ɗora🥰
I love u all.
thanks 4d love guys
comment
nd
share
***