SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....! Chapter 5

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!* Arewabook@ayshadansabo

Paid book

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 5

Tunda Aysha ta ɗaura idanunta akan Yaron ƙauna da soyayyarsa ya shige cikin zuciyarta farat ɗaya,aka sake jarabtar zuciyarta da son haihuwa.Haka shima mijinta Alhaji Taheer ranar daya dawo daga Kaduna ya ɗaura idanunsa akan Jaririn da Mallam ya zaɓa masa suna Zayd sai yaji ƙaunar Yaron ya shiga cikin jininsa,ya rungumesa tsam a jikinsa a lokacin Aysha na gefensa tana sakin masa lallausar murmushi yace,"Allah ya raya mana Zaidu."Aysha ta amsa da cewa,"Ameen Daddyn Zayd." Tun daga ranar da akai haihuwar Zayd har kawo gama wankansu Aysha bata taɓa hutawa wajen yin hidimarsa ba domin da gaske ƙaunarsa take ji mai zafi a cikin jininta,haka Alhaji Taheer duk zuwan da zaiyi weekend yana shigowa cikin gidan zai zarce zuwa ɓangaren ɗan Uwansa Alhaji Abdallah ya duba Baby Zayd.Dukkanin ƴan Uwan Asiya sun yaba da ƙauna da hidimar da Aysha keyi da Asiya da ɗanta Zayd,hakan yasa koda yaushe nasiharsu ga ƴar Uwarsu Asiya shine su zauna lafiya kada ta taɓa bari shaiɗan da kuma shaiɗanun ƙawaye su shiga tsakaninsu domin mai ƙaunarka da gaskiya ne kaɗai zai iya yi mata abinda Aysha tayi mata.Haka akai jegon Zayd cikin ƙoshin lafiya da kulawa,daga shi har Asiya suna samun kulawa da soyayya daga wajen Alhaji Abdallah wanda yake zuwa musu weekend duk bayan sati biyu daga Kano.Inna Ameena Mahaifiyarsu Alhaji Taheer itama ba a barta a baya wajen basu kulawa ba,domin duk bayan kwana biyu take wanke ƙafafunta taje duba masu jego.A gefe guda kuma tana cigaba da sanya Aysha da Alhaji Taheer a cikin addu'arta tana roƙa musu a basu rabo mai amfani,bata taɓa gajiyawa ba domin itama burinta shine taga jinin Taheer kamar yadda taga na Abdallah.Kwanci tashi Zayd ya fara girma da wayo koda yaushe yana ɓangaren Aysha tana hidimarsa babu gajiyawa,da yawa masu zuwa sayen turaren wuta suna ɗauka cewa itace ta haifi Zayd ba Asiya ba domin zaiyi wahala ka ganshi a hannun Asiya matuƙar ba shayar dashi za ta yi ba.A haka har yayi shekara guda da haihuwa yana gudunsa ko'ina,duk inda suka shiga sai an tamka kyawunsa da kalar skin ɗinsa wanda yazo ba fari ba kuma ba za a kirashi baƙi kai tsaye ba.Sosai yake girma kyawunsa da kammaninsa da Abbansa Abdullahi na sake fitowa sosai,tamkar jira ake ya cika shekara guda Asiya ta fara laulayin wani cikin.Ganin hakan yasa Alhaji Abdallah cewa maza a cireshi a bakin nono tunda Allah yasa yana cin abincin gwangwani da mai gishiri,gashi yana gudunsa ko'ina cikin ƙoshin lafiya da girman jiki.Asiya tabi Umurnin Abdallah domin itama tana ganin hakan shine samun sauƙi a gareta,aiko ranar da aka yi yayen Aysha ta haɗa kayansa ya koma ɓangarenta wanda shine mafarin zaman Zayd a hannunta.Alhaji Abdallah da kansa ya samu ɗan Uwansa Alhaji Taheer yayi masa albishiri da cewa ya sadaukar musu da ɗansa Zayd,yana fata su haɗu shi da nagartacciyar Matarsa Aysha su bashi ingantacciyar tarbiya.Wannan kyauta yayi ma Alhaji Taheer da Hajiya Aysha daɗi,haka Inna Ameena da Mallam Lawal sosai suka ji daɗi suka kuma sanya ma Asiya da Abdallah albarka.Aysha sai taji a lokacin tamkar anyi mata kyautar Aljanna ne sabida farin cikin cewa Zayd zai tashi a hannunta a matsayin ɗan da ba za ta taɓa so yasan cewa ba itace ta kawosa duniya ba,a ɓangaren Asiya ko kaɗan bata damu ba domin da shawara da amincewarta Alhaji Abdallah yayi ma ɗan Uwansa kyautar Zayd.Ta kuma haƙiƙance cewa ko bayan ranta tana da tabbacin cewa Aysha ba za ta taɓa cin amanarta ta wofintar da Zayd ba domin ƙaunar da take masa daga Allah ne,shiyasa hankalinta kwance ta cigaba da rainon cikin da Allah ya sake bata ba tare da damuwar komi ba.Koda watannin cikin ya isa haihuwa cikin ikon Allah ta sake haifo ɗanta Namiji ƙaton gaske,kyakykyawa dashi wanda ya ɗakko kammaninta sai hasken fata ne kaɗai ya ɗakko na Ubansa Abdallah domin shi fari ne yayinda Alhaji Taheer kuma ya kasance chocolate colour irin skin ɗinsu ɗaya da Zayd.Yaro yaci suna Sulaiman sunan Mahaifin Asiya,anyi shagali sosai kafin taro ya watse su cigaba da jegonsu cikin ƙoshin lafiya.Watannin Sulaiman huɗu da haihuwa Allah ya kawo wa Aysha babban rabo ta fara laulayi,murna a wajen dukkanin ahalin Lawal Ƙaura abin baya faɗuwa domin kuwa an taya su murna ba kaɗan ba.Autar Inna Abu wacce a lokacin tayi aure tana zaune a garin Jos da mijinta har Zaria tayo tattaki domin taya Aysha murna,a lokacin tana goyan ƴarta na fari mai suna Sakinah.Alhaji Taheer ya ɗauki burin duniya ya ɗaura akan cikin dake jikin Aysha,baya iya jira sai weekend ya dawo sai ya koma dawowa duk ranakun Wednesday da Friday.Asiya sosai take tausayawa Aysha irin laulayi mai wahala da take yi,ga kuma hidimar Zayd da baya sakin jiki da kowa sai Momynsa kamar yadda yake kiran Hajiya Aysha ita kuma Asiya ya kirata Umma kamar yadda Aysha ta raɗa masa.A haka akai rainon cikin yau ciwo gobe lafiya har watannin haihuwa ya kama,ranar wata asabar Alhaji Taheer da Abbah Abdallah na gida naƙuda ya kama Aysha aka wuce da ita asibiti.Bata sha wani wahala sosai ba ta haifo Ƴarta mace ƙatuwar gaske,jajir da ita tamkar balarabiya domin babu inda ta baro a kammanninta da Aysha.Asiya sosai taji son baby girl ya shiga cikin zuciyarta,musamman wannan kyakykyawar dake riƙe a hannunta tana kallonta tana ji inama itace ta kawota duniya.Kafin kace kwabo aka cika asibiti, ƴan Ƙaura gaba ɗaya suka hallara har da Inna Ameena.Mallam Lawal na isowa ya ɗauki Yarinyar yayi mata addu'a da sanya mata albarka yace,"Allah shi raya mana Hameedatu."Su Daddy suka amsa da Ameen yana jin farin cikin sunan na ratsa zuciyarsa.Aysha da akace Yarinyar taci suna Hameedah itama addu'a tayi akan Allah ya raya musu,ana sallamarta suka koma gida Alhaji Taheer ya kira Iyayenta dake Borno ya sanar dasu haihuwa.Aiko kwana biyu da haihuwa sai gashi Mahaifinta ya turo ƙannensa uku da ƙannen matarsa wato Mahaifiyar Aysha su biyu sai ƙanwarsa mai suna Yaganah da za ta zauna tayi mata zaman jego har su gama wanka.Bayan anyi gagarumin taron sunan da Alhaji Taheer ya kashe dukiya dangin Aysha suka koma Borno,aka barta da Yaganah domin yi mata zaman wanka.Sai da sukai arba'in da sati biyu sannan ta koma gida Borno da tarin abin alkhairin da Alhaji Taheer da ƴan Uwansa suka cikata dashi,Aysha tayi kewa sosai domin Yaganah akwai daɗin zama ga barkwanci.Haka dai ta haƙura ta rungumi Zayd da ƙanwarsa Hameedah ta cigaba da basu kulawa cikin tsantsar ƙauna da soyayya,ita kuma Asiya na cigaba da rainon Sulaiman wanda yake gudunsa ko'ina har ta jima da yayesa ma.Hameedah nada watanni uku Allah ya ɗauki rayuwar Inna Ameena,mutuwar daya jijjiga kafatanin ahalin Alhaji Lawal Ƙaura.Faɗin irin tashin hankalin da Ƴaƴanta su Alhaji Taheer da Auta Abu suka shiga ciki bazai misaltu ba,domin sun ɗauki dogon lokacin kafin Allah ya dubasu ya basu dangana.Mallam lawal kansa rashin matarsa ɗaya tilo daya mallaka ya taɓa shi sosai,amma haka suka dangana suna cigaba dayi mata addu'ar dacewa da rahamar Ubangiji.Aysha da Asiya dukkaninsu mutuwar surukar tasu ya taɓasu domin Inna Ameena mutum ce,ta nuna musu ƙauna ta ɗaukesu tamkar Abu data haifa a cikinta.Shiyasa mutuwarta ya taɓasu sosai, ƴan Uwansu sunyi musu kara wajen zuwa makoki domin Mahaifin Aysha da Mahaifiyarta Hajiya Safiyyah duk sunzo daga Borno sunyi ta'aziyya.Inna Ameena bata rufa watanni huɗu da rasuwa ba Mallam Lawal ya sake auren wata bazawara mai suna Rakiya,itama Inna Rakiya anyi sa a mace ce mai kirki da son mutane.Cikin lokaci kaɗan ta shiga ran su Alhaji Taheer sabida yadda take sake musu fuska da girmamasu a matsayinsu na manyan ƴaƴan Mallam ɗin,Hameedah nada shekara ɗaya da rabi Alhaji Taheer ya biya ma su Aysha kuɗin kujerar Hajji ita da Mallam Lawal.Don haka tabar su Zayd a hannun Asiya suka wuce ƙasa mai tsarki tare da surukinta Mallam Lawal Ƙaura,sun tafi cikin farin ciki bayan sunyi sallama da dangi.Aysha kafin tafiyarsu har Borno taje tayi sallama da Mahaifanta,kuma lokacin tare dasu Zayd ta tafi wanda kafatanin danginta ke masa kallon ɗan daya fito daga jikinta sabida yadda take nuna masa ƙauna suma haka suke gwada masa.Sunyi aikin Hajji cikin nasara kafin babban tashin hankalin da ba za su taɓa manta shi ba ya faru na rasuwar Mallam Lawal Ƙaura,ya rasu a wata safiyar juma'a yana tsaka da zagaye ɗakin Allah.Wannan mutuwa ya gigita kafatanin zuriyyan Mallam Lawal Ƙaura,domin sunyi babban rashin da suka kasa maida makwafinsa.Hajiya Aysha tafi kowa gigicewa domin a lokacin data samu labarin rasuwar surukin nata sumewa tayi gau,ta dinga ganin komi tamkar a mafarki bata gasgata cewa da gaske sunyi rashin Mallam ba sai da lokacin kwaso alhazai yayi taga sun dawo gida ba tare da Mallam da sukai tafiya ƙafa da ƙafa tare da shi ba.Ta dawo ta samu mijinta Alhaji Taheer cikin halin kewar rashin Mahaifa abin tausayi,sosai aka ɗauki dogon lokaci mutuwar Mallam bai saki kowa a cikin zuriyyarsa ba musamman ƴaƴansa uku Alhaji Taheer,Alhaji Abdallah da kuma Auta Zainabu.Shekara guda da rasuwar Mallam Lawal Allah ya sake baiwa Hajiya Aysha wani cikin,a lokacin Hameedah nada shekaru biyu da rabi.Tuni Yaya Zayd kamar yadda Sulaiman da Hameedah suke kiransa suka shiga skull shi da Sulaiman,ajinsu guda domin sun taso kansu ɗaya ne tamkar twins.Zayd kawai zai nunawa Sulaiman tsayi da girman jiki ne,domin shi Sulaiman ƙaramin jiki garesa amma kuma shima yana da dogayen sahu.Lokacin da haihuwa yazo Hajiya Aysha ta sake haifo Ƴarta mace ƙatuwar gaske,daga Alhaji Taheer har ɗan Uwansa Alhaji Abdallah sunyi burin Momy ta haifo ɗa namiji ne domin yaci sunan Mallam amma sai Allah ya kawo mace.Babu wanda baiyi tunanin cewa sunan Inna Ameena Yarinya za ta ci ba,amma da Daddy yayi mata huɗuba sai ya raɗa mata suna Amal.Domin a cewarsa bazai iya sanyawa ɗiyarsa sunan Uwarsa ba sabida yana gudun lokacin da za ta iya saɓa masa ya ɗaga hannu a kanta ko yayi mata mummunar kalami,lokacin da yake faɗin hakan murmushi Hajiya Aysha tayi amma a cikin ƙwayar idanunsa take hango zurfin soyayyar da yake wa Amal har fiye da yadda ta hango a lokacin da aka haifi Hameedah.Kowa yazo barka sai ya tafi da kyawun Amal a baki domin da yawa na faɗin cewa tafi Hameedah tsagwaron kyau,ita Hameedah za ta nuna wa Amal manyan kyau ne yayin da ita Amal kana zurfafa kallonta ne kana sake gano tsagwaron kyawun da Ubangiji ya halittota dashi.Gagarumin bikin suna aka yi tunda Allah ya riga ya buɗewa Alhaji Taheer ƙofofin arziƙinsa,shima kuma Alhaji Abdallah haka ne ta ɓangarensa domin shima yayi kuɗi sosai dukkaninsu bada aikin Gwabnati suka dogara ba.Sannan lokacin da aka raba gadon Mallam Lawal shima sun sami kuɗi da ƙaddarar gonakin noma da gidan gona na kiwo,sai ya kasance sun sake maida hankali wajen haɓaka harkokin noma da kiwo.Kason Abu duk yana hannun Alhaji Taheer ne shi ke riƙe ma Abu dashi duk shekara yana saka kuɗi a noma mata gonakinta biyu data gada,kuɗi kuma sun damƙa mata ta sake faɗaɗa business ɗinta na saida spice's tana haɗawa da ɗinka zannuwan gado.Sosai suke kulawa da ita a matsayinta na ƴa mace tilo da suke da ita,basu taɓa bari tayi kukan maraicin rashin Uwa kona Mallam ba su da matayensu da ke matuƙar kulawa da ita da Ƴarta Sakinah wacce duk hutu mai dogon zango a Zaria take yinsa bata ɓangaren Asiya bata na Momy.Sannu a hankali rayuwa ta miƙa musu cikin haɗin kai,rufin asiri da kuma ƙaruwar arziƙi.Amal ta dinga girma da wayo har zuwa lokacin da aka yayeta tana da shekara guda da watanni shida,cikin ikon Allah a lokacin Asiya tana ɗauke da ciki ɗan watanni shida.Koda yaushe Amal da Yaya Sulaiman suna tare domin sosai yake ƙawazucinta,yayinda Yaya Zayd da Hameedah nasu tafi zuwa ɗaya domin sam baya damuwa da Amal musamman daya kasance Amal tafi zama a ɓangaren Umma Asiya kamar yadda suke kiranta.Cikin Asiya nada watanni bakwai Alhaji Abdallah ya ɗauketa suka tafi Kano domin halartar taron bikin ƴar abokin aikinsa,ranar asabar da safe suka kama hanya da zimmar su dawo Sunday shi kuma ya sake juyawa Kano Monday.Sai dai kuma daga shi har Asiya ashe ajali ne ke kiransu domin sun kusa Kano a daidai garin Kura suka zabga mummunar haɗarin da yayi ajalinsu baki ɗaya,domin a yadda labari yazo wa su Alhaji Taheer ance Alhaji Abdallah ko shurawa baiyi ba nan take aka zare ransa.Asiya kuma sai da aka danganata da asibiti kafin rai yayi halinsa,daga ita har cikin jikinta suka amsa kiran Ubangijinsu sai gawarsu aka dawo dashi Zaria.Mutuwar Asiya da mai gidanta Alhaji Abdallah mutuwace daya gigita duniyar ƴan Uwansa su Alhaji Taheer domin kowa ya shaidi cewa Alhaji Abdallah mutumin kirki ne,haka matarsa itama mace ce ta gari abin alfaharin duk wani namijin da yasan kansa.Alhaji Abdallah mutum ne mai yawan haƙuri da yafiya,ga zumunci da son kyautatawa ƴan Uwa da dangi.Shiyasa family ɗin Lawal Ƙaura suka shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa,domin rashi ne da aka kwantsama musu mai matuƙar gigitarwa.Hajiya Aysha ta gigice ta kuma fice daga hayyacinta,sosai mutuwar Asiya da Abbah Abdallah ya wujijjigata tare da tsaya mata a zuci.Lokacin da aka kammala zaman makoki ƴan Uwa da dangi suka watse,sai ya kasance Hajiya Aysha tafi jin mutuwar tare da jin gabaki ɗaya zaman gidan babu Asiya da Abbah yayi mata ƙuncin da bazai misaltu ba.Kuma mafari kenan data hurawa Alhaji Taheer wutar cewa ya maidasu Kaduna subar Zaria domin gidan da garin gabaki ɗaya yayi mata zafi,tunda sun wayi gari babu Inna Ameena babu Mallam sannan gashi yanzu babu Asiya da Alhaji Abdallah don haka bata ga amfanin zaman garin ba.Cikin ikon Allah Alhaji Taheer ya amince da shawararta ya kama musu wani gidan haya a Millenium city Kaduna,babban gida ne babu laifi mai ɗauke da 3 bedrooms da komi da komi a ciki.Sannan daga backyard akwai ɗakunan masu aiki da wasu single room guda biyu,daga wajen gate kuma akwai ɗakin mai gadi.Hajiya Aysha ta taho da masu aikinta biyu Rayyah da dattijiya Babah Salame,sosai take jin daɗin aiki dasu da yadda suke kula mata dasu Amal da gidan baki ɗaya.A hankali Unguwar ya fara yi musu daɗin zama,su Zayd aka sanyasu a Essence International School.Driver ke kaisu ya ɗakko su wani bin kuma Momy da kanta,tun su Amal na yawan tambayar ina Umma Asiya da Abbansu Abdallah har suka fara dangana domin koda yaushe aka yi zancensu sai Yaya Zayd ya sanar dasu cewa sun rasu suyi musi addu'a kamar yadda Daddy ke faɗi musu.Sulaiman dake da naci shima haka ya haƙura ya daina tambayarsu,shi ko Zayd da yake shine mai wayon sosai kuma dama ba shaƙuwa yayi sosai da Umma Asiya da Abban nasu ba sam baya ma hirarsu sosai.Amal nada shekaru uku aka sanyata a school kamar yadda aka sanya Hameedah,suka taso kusan kansu guda da juna ita da Hameedah domin tseran aji ɗaya ne kawai a tsakaninsu kamar yadda Zayd da Sulaiman suka tashi suma kansu guda.....✍🏻