RIGAR KAYA

Chapter 8

by @sadiyaabdulrazak954

*... RIGAR ƘAYA*




            BY
SADIYA ABDULRAZAK 


 PAGE 8


   Wuni Mama ta yi tana shi masa albarka, musamman da ya aiko abincin har da siyayyar kayan abinci, ita kanta Muhasin ta ji daɗi duk da tana mamakin wannan canjin nashi na lokaci ɗaya, da yamma suna zaune Muhasin ɗin tana tsigar zogale za a dafawa Mama take yi wa Anti Su'ada zancen maganin rage ƙiba, ta ce "Anti don Allah ko kin san inda zan samu wani magani da zai rage min ƙiba? Ko ya rage min ƙirjina da hips?"

Da mamaki Antin take kallonta "Muhasin ban gane ba, ke a kan me za ki rage?"

Ta ɗan yi jim kafin ta ce"Dama shi ne yake cewa ƙibata ta yi yawa, shiyasa nake so na ɗan ragu".

Ta ɗauki salati ta dire kafin ta hau sababi "Ya ce ƙibarki ta yi yawa? To ai ko da kike gida kafin auren a haka kike kaɗan kika ƙara ƙibar ita ma ta zaman waje ɗaya ce tun da kin daina yawon kasuwa siyan kayan ɗinki, don dai ba ta kwanciyar hankali ba ce, tun da ban ga alamar shi ba, kuma da zai ce ki ragu me yasa ya aure ki ya san kina da ƙibar? Ai da tun lokacin sai ya ce ba ya son me ƙiba, to wallahi ki dawo cikin hayyacinki, indai kika ce namiji za ki biyewa duk abin da ya saka ki ki yi sai ya kai ki ya baro, kashe ki zai yi murus, domin kuwa ba karamar wuya za ki sha ba, ƙibarmu ta gado ce, irin wacce ko mutum ba ya cin abinci wadatacce sai dai ya ragu ba dai ya yi ramar da mijinki yake nufi ba, kuma idan kika wahalar da kanki kika sakawa kanki jinya ke ce a wahale, ban da ke shashasha ce har ko biyewa namiji wai ki rage ƙiba, mata suna neman ƙiba ke kina neman ragewa? To sai kin gama tarawa kanki jinya kin ragu ɗin sannan ya dawo ya ce me ƙiba yake so, kin ga sai ki dawwama cikin canza halittarki".

Muhasin sai ta yi nadamar yi mata zancen, a tunaninta za ta ba ta goyon baya, tun da kamar gyaran aure ne ai, ashe saɓanin haka ne zai faru.

Anti Su'ada ta kara da faɗin "Kin yi min shiru, kina kan bakanki ko za ki ji shawarata?"

Mama dake bacci ta yi juyi don ta farka ta ji ƙarshen maganar Su'ada, ta ce "Shawarar me kuke magana a kai?"

"Mama kin ji wai mijinta ne ya ce ta rage ƙiba ba ya son me ƙiba, wannan ai jahilci ne ma".

Mama ta ce"Allah Ya kyauta, ki rage ƙiba Muhasin ko dai ki lalata jikinki? Kawai tun da ba ya so sai ki kiyaye abin da zai ƙara miki ƙibar, amma ragewa kam ai sai Allah ya nufa".

"A to namiji ne dai, kina iya ramewa ramar da ke da ƙiba kun yi hannun riga kuma ya ce me ƙiba ce take burge shi, ya auro ta ta yi ta miki juyi a cikin gida, me ake yi da rama?"

Muhasin dai ta yi shiru, ba don ta gamsu ba, saboda a ganinta ai gyaran aure ne da neman maslaha, tun da shi ga ra'ayinsa, so ake ya sake ta ya auri kalar wacce yake so ko yaya?

Mama ta canza akalar firar da faɗin "Hasina tana can tana yin abin da ta zaɓa ko?"

Anti Su'ada ta ce"Ko jiya na ga posting ɗinta a tiktok, wai cikin satin nan za ta dawo Nigeria, ashe ba ta ƙasar ma"

Mama ta ce"Ba ta ƙasar? Lallai!".

Muhasin ta ce "Ni ma ina ganinta, na ga ma posting ɗin da ta yi ranar da za ta tafi ai, kuma na san ita da wani suka tafi".

 "Shi ma mijinki haushi yake ban idan na ga vedionsa, ya dinga abu har da rawa babu kamun kai, ba za ka ce ma yana da aure ba, kai Allah Ya kyauta".

Nan take maganar ta bawa Muhasin haushi, mijinta ne wai babu kamun kai, ita, ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.

Da daddare ya zo ya ɗauke ta suka tafi, a hanya ya tsaya ya siya pepper chicken guda ɗaya, ya saba siyo irinta, kuma tana sonta, amma da suka dawo gida sai ta ga ya baje ya fara ci ba shi da niyyar yi mata tayi, ta haɗiyi yawu kamar mayya, ya kalle ta ya ce"Oh! Sorry, je mota akwai leda ki ɗakko".

Ta tashi ta je ta dakko ta kawo masa ya ce"Naki ne".

Ta buɗe ta ga ledar kilishi ya ce"E kilishi za ki dinga ci sau ɗaya a sati biyu, ina tunanin shi ba zai saka ƙiba ba, akwai wando a ciki, kuma na rage hips ne da tumbi".

"To" Kawai ta ce.

Ya ce"Je ki gwada wandon ki zo na gani".

 Ta tashi gabanta yana faɗuwa ta tafi ɗakinta, tana ɗaga wandon gabanta ya faɗi, saboda ganin shi ba me faɗi ba, duk da dai roba ne, amma a ƙa'ida ba masu irin jikinta ne za su saka shi ba, maganar Anti Su'ada ta faɗo mata, nan take ta kau da zancen ta hanyar cire doguwar rigar jikinta, ta hau saka wandon, sai dai ya yi gardama a cinyarta, ya ƙi gaba, ta yi alƙawarin sai ta saka ko don ta biya shi ladan faranta mata da ya yi yau ɗin, don haka ta dinga jan shi sama, daga ƙarshe ta ji ya tafi ya shiga, sai da ta kalla ta ga ashe yagewa ya yi, hantsar shi ta yage, sannan ƙugun ma gefe da gefe duk sun farke, ji ta yi kamar ta rushe da kuka don takaici, tana cikin tunanin yadda za ta yi ta ji ya kwala mata kira "Wify".

Gabanta ya ba da ras, a dole ta saka hijjabi ta fito, tun kafin ta ƙarasa ya ce"Meye kuma na rufe jiki?"

Sai da ta ƙarasa ta cire hijjabin, tana kallon shi kuwa ta ga fara'ar fuskarsa ta ɗauke gabaɗaya ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kai, da muryar ɓacin rai ya ce"Muhasin! Kin san nawa na yi order wannan wandon kuwa?"

"Ka yi haƙuri dama ka san ai ba zai shige ni ba".

"Ta ya zai ƙi shigarki tun da roba ne? Ko jikin naki na reza ya zama ban sani ba?"

Ya ɗauki wayarsa ya fara danne-danne, ya haska mata fuskar wayar, wani vedio ya bayyana, wata baturiya ce take saka irin wandon, ya zauna ɗam a jikinta, sai dai siririya ce ita.

Ya ce "Ki duba ki ga abun sha'awa, kalli cinyarta yar suwal da ita, ji cikinta kamar ba ta taɓa cin abinci ba, kalli ƙirjinta ɗan cin daidai hannun mutum..."

Ta katse cin mutuncin nasa da faɗin "Amma idan ba sun so yaudara ba ai me ƙiba ya kamata su ba wa ta yi tallan tun da ba su yi abun don marasa ƙiba ba".

"Yeen rufe min baki, ke dai kawai ki ce ba ki da fasali, ban da haka ya sabon wando bugun Company zai farke?"

Sai kuma ya tuna da plan ɗinsa, ya ga ashe ya kwafsa, za ta koma ɗaki ya janyo ta jikinsa, ya share mata hawayen da ya sakko mata, ya ce"Shikenan ya isa, kawai dai ban ji daɗi ba gaskiya, don Allah Sweetheart ki rame kin ji? Ba na son ƙibar nan".

"In sha Allah zan zama yadda kake so".

"Thanks i love You".

"Me too".

Yana shafa bayanta ya ce"Gobe za mu yi baƙuwa fa".

Ta ce"To daga ina?"

"Ƙanwata ce Safiyya, ta zo hutu dayake a waje take karatu, shi ne ta ce a gidanmu za ta yi hutunta, ina fata za ki karɓe ta?"

"In sha Allah, Allah Ya kawo ta lafiya".

Ya amsa da amin, kafin ya ce"Ki ci kilishin mana ko ba kya jin yunwa?"

"Ai zan ci abinci kaɗan".

"A'a daga yau kin daina cin komai da daddare, sai dai ki dama koko, ɗazu da rana an kawo gero yana kitchen, ina so daga gobe a fara".

Sam ba ta ji daɗi ba, don ita ba masoyiyar koko ba ce, amma ta daure ta ce"To in sha Allah".

Ta gama cin kilishin ta je ta cire wandon ta yi wanka ta saka kayan bacci cikin matsattsun da ya siyo mata, duk da da ƙyar take numfashi amma da ita ta kwanta don ta burge shi, kuma hakan bai hana ta farka tsakar dare ta ji yana yi wa mace voice note da faɗin yana missing ɗinta ba, amma ta yi shiru ba ta nuna ta ji shi ba.


        FIRDAUSI 

   Yusuf ya yi ƙoƙari ya siyawa Firdausi abaya gida biyu masu sauƙin kuɗi, ya ɗinkaata atamfofi guda biyu, takalma flat masu sauƙin kuɗi guda biyu, jaka guda biyu, sai mayafai guda biyu hijjabi biyu, dayake shi tele ne ya tsantsara mata ɗinkuna masu kyau, ranar da ya je ya kai mata ya haɗa da dubu biyar ya ce ta siya kayan kwalliya, sosai ta kasa ɓoye murnarta, ta dinga yi masa godiya, shi kuma faɗi yake "Ai yi wa kai ne, ni ne da godiya ma" Saboda a yadda yake ganin kyaunta gani yake alfarma ta yi masa da za ta aure shi.

Da ta nunawa Kabiru tana murnarta sai ya taɓe baki ya ce"Haba Sister kar dai me aka yi aka yi wannan kayan? Dubu nawa ya kashe duka ma? Allah Ya sa dai ba haka kika nuna masa kaya sun yi kyau ba".

Ta ɗan ɓata rai "Haka na nuna masa tun da ai ya yi ƙoƙari sai kashe kayan saka rana".

"To wallahi wannan kaɗan ne cikin abin da za ki samu, bari ki ji kar ma ki bari fa ki fara son shi, don wannan ba kalar mijin da za ki aura ba ne, ki ɗauka shi Yusuf bene ne da za ki taka ya kai ki ga mijinki".

Jikinta ya yi sanyi, don gaskiya tana tunanin ba za ta samu wanda ya fi shi ba.

  Haka Yusuyya cigaba da hidima, duk ribar shi a siya mata kayan ƙyale-ƙyale take ƙarewa, zuwa lokacin ta ƙara ƙiba sosai haskenta sai ƙaruwa yake yi, Kaka ta yi mitar har ta gaji, da farko da ta yi ƙibar sai da kakar ta duba idonta da hannunta wai kar ta je ta yi ciki tana gabanta ba ta sani ba, sannan ta fara faɗan bleeching amma Kabiru ya dinga kare Firdausi da faɗin yanayin zafi ne, ita ma ta kalli kanta a mudubi ta ga yadda ta ƙara haske, ai kowa ya yi haske saboda canjin yanayi.

Kaka cikin faɗa ta ce"Tun kafin a haifi uwarka da ubanka ake canjin yanayi, ƙarya kake yi, ai ina lura da ƙulle-ƙullenka, Allah kaɗai Ya san abin da kuke shiryawa, idan ma kai ne kake koyawa mata bleeching kuma kake ba ta sha-ka-fashe to kanka ka cuta, tun da 'yar'uwarka ce".

Ya yi dariya "My grand kenan, ke ma fa idan harkar nan ta faɗa za ki shiga ciki, so nake Sister ta auri wanda zai siya miki gida mu bar gidan nan, kuma in sha Allah zai tabbata, ke dai naki ido".

Ya fice daga gidan ta yi kan Firdausi da faɗa tana ta yi, ita kuwa kallonta kawai take yi, don ba za ta ɗauka ba ita ma.

Ana haka ne ogansu Kabiru ya tashi yin aure, wato manager gidan man da yake aiki, ɗan wani mai kuɗi ne, don gidan man na baban shi ne yake kula da shi, Kabiru ya san dole masu kuɗi za su je wajen, don haka ya ɗaura aniyar dole sai Firdausi ta je, haka ya samu Yusuf ya ce masa za a yi bikin ƙawarta kuma kunya take ji ta faɗa masa kuɗin anko, Yusuf ya ce"Ban da abun Firdausi ai an zama ɗaya, zan yi mata in sha Allah".

Kabiru ya ce"Ni ai gani na yi ma ba ta wani kyau da atamfa, dama abaya ka siya mata tun da wajen dinner ne".

Yusuf ya ce"In sha Allah gobe zan siyo mata".

 Ai kuwa ya cika alƙawari, washegari sai ga shi da abaya tsuleliya da takalmi da jaka, ba ƙaramin daɗi ta ji ba kuwa, don zuwa yanzu ta tabbatar da cewar ta fara son Yusuf, saboda kyautata mata da yake yi, kullum da daddare sai sun daɗe suna waya, sannan su yi ta chatting.

 Ana gobe dinner hankalin Kabiru duk a tashe, saboda ya rasa get fast, guda ɗaya ya samu shi ma da ƙyar aka ba shi, ya rasa yadda za a yi Firdausi ta samu, da ya zo ya faɗa mata suka dinga jajantawa, zai iya ba ta ita ta je shi ya haƙura, amma a yadda yake ganin ba ta ɗauki lamarin na gaske ba tsaf za ta je ta ci abinci ta dawo, amma idan suka je tare shi ya san yadda zai yi ya tallata ta cikin hikima, tsaf za ta yi samari goma ko ashirin ma, kuma kowa zai ba shi dama sai ya fitar da guda uku ƙwarara wanda za su zame musu saniyar tatsa, sai ga shi burinsa yana neman mutuwa.

Washegari tun safe ya fita ya dinga bulayi yana bin gidajen abokai, da ƙyar ya samu wani abokinsa ya ba shi na shi fas ɗin, saboda shi yana fama da zazzaɓi, godiya kamar Kabiru ya goya shi.

 Kuɗi ya ba ta cikin albashinsa ta je wajen me kwalliya ta yi mata ta dubu biyar, ta saka abayarta, sai yau ya yarda lallai ta murmure ta yi ƙiba, ya dinga koɗa ta yana zuga ta, ita kuwa tana murna tana ta kashe hotuwa, ta turawa Yusuf, sannan ta kashe data suka tafi bayan sallar isha'i.

 Tabbas biki ne na manyan mutane, domin kuwa tun daga motocin da suke wajen za ka tabbatar, Kabiru jikinsa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu ya za a yi kenan? Kar mu jera a ƙi kula ki a ce ni mijinki ne ko saurayi, kar kuma na bar ki ki ƙi yin abin da za ki yaɗa manufarmu".

"Zan yi in sha Allah".

"To ki kula don Allah, idan kin ga taron maza sai ki je wucewa, kuma ki dinga shige da fice tsakanin waje da hole ɗin, kamar dai kina amsa waya irin hayaniya ta hana ki ji ɗin nan, ki canza murya, ki canza tafiya, don Allah my favourite sister ki tashi kan gayun wajen na z har dattijan ma kar ki ƙyale su".

Ta yi murmushi ta ce"To".

Ya ce"Kar ni fa ban yarda da ke ba, gwada min tafiyar na gani".

Ta yi gaba cikin salon tafiya mai daukar hankali, ya fara tafa mata yana faɗin "Wow! Ai wallahi ko gwamna ne ya taya ki yau sai na ja masa aji, bari na fara shiga, idan na yi wasu mintuna ke ma sai ki shigo, zan nunawa abokaina ke ko a cikinsu ma za a samu masu tayawa, kin ga ko kuɗin mai ma dinga samu a wajen 'yan wahala".

Ta yi dariya, ya shige ciki, ita kuma ta tsaya tana kashewa kanta hotuna.


***