2
by @mamuhgee
GANIN IDO
Mamuhgee
2
Pearl Harbour HAWAII
Audi Q7 ce shiny black da BMW X5 itama shiny black da suke tafiya akan titi da nutsuwa bayan dauko fleet admiral dinsu gaba daya daga tafiyar dayayi wadda babu wanda ya saka ran dawowansa a ranar sbd a jiya yayi tafiyar dan haka ko kafin su taso daga california Lc imran ya kira ya sanar da saukansu dan haka ne tini motocin daukosa din suka zama ready a airport har saida ya iso.
Hanyar gidansa aka kama wanda street din yake kusan na soldiers din navy gabaki daya sbd suke da kusan anguwan mataki mataki kowa da gidansa daidai tsarinsa da ikonsa dan haka anguwan take da securities tako ina dan kuwa masu gadin qasar ne a cikinta rayuwansu me matiqar mahimmanci ce kuma qarin samun tsaro da karfin anguwan kasancewan daya daga cikin fleet nasu na qasar yana anguwan da family dinsa wato FLEET RAHEEM JEERAH,
Imran akan waya yake tinda suka sauka yana wayoyi da duba ipad yana kokarin fara clearing schedules na fleet da shiryar da duk yanda tafiyar zata kasance a cikin daidai nutsuwa da kwanciyan hankalin uban tafiyar dan kuwa hatta duk abinda zasu buqata a Nigeria kafin isarsu zai tabbatarda samar dashi dan kuwa babu tafiyar da zasu zuwa kowace qasar dabai gama samar da tsarar da komai ba na comfort din fleet.
Tafiya mai dan tsayi sukai kafin suka iso gidan dayake dauke da sunansa baro baro a jikin wata kyakkyawar block symbol dake waje babba datake bayyanarda rank dinsa,
Securities da soldiers din dake gurin miqewa sukai gabaki daya suna sarawa motocin dawowan tasa aka bude babbar gate din suka shige take aka rufesa ruf kowa na sake qamewa sbd saiya fito ya shige ciki ko zasu iya saukewa dan haka tsit koina ya dauka.
Parking motocin akai take soldiers din ciki suka fito suna jerawa suka qame imran ya fito da sauri ya bude masa motar yana matsawa gefe kadan.
Kafafunsa dake sanye cikin black santoni leather Oxford shoes ne ya ziro waje a natse tareda fitowa gabaki dayansa take duka soldiers din suka sake qamewa ya taka a cikin wata irin izza da karfin powern dayake riqe da ita ya nufi ciki imran na bayansa a take cikin tasa izzar ta soldiers da Allah yayi musu.
Kai tsaye kofar shiga main sitting room na farkon gidan imran ya rigasa isa ya bude masa kofar yana bude baki a natse ya masa a huta lafiya sbd bazai shiga ba a lokacin zaije bangarensa ya tabbatarda kammaluwan aikin dake gabansa na tafiyar da babu shiri musamman tafiya ce zuwa inda gudanar da komai yana nan zai musu wuya amma komai wuyar abu babu qasar da bayajin zai iya komai ko baya qasar matiqar akwai technologies da networks.
Yana shigewa rufe kofar imran yayi yabar gurin yana wucewa nasa bangaren dake gidan.
Lafiyayyar sitting room ce mai girman gaske dake qasa wadda tako ina luxuries ne amsa kuwwa da zuba sbd tsarin palon da kalar duk abinda yake ciki wanda yake off white da navy blues marasa duhu sosai.
Maids din gidan guda uku ne suka fito daga wata hanya me kyau da mirrors ne koina gurin dauke da trays masu dan girma da kyau zasu kama hanyar Dining room na palon su shige hancinsu da idanuwansu sukai girmamman ganin wanda basu taba saka ran gani ba sbd sanin baya gari yayi tafiya kuma idan yayi tafiya baya dawowa da wuri irin haka dan haka suka saurin dakatawa cak kowannensu na dan sauke kai cikeda girmama suna masa barka da dawowa.
Bai wani cika jin maganar mata ba sbd kunnuwansa da suka saba jin amon muryan mazan fama dake tabbatar maka da namiji kake magana dashi dan hakanne sam baya bawa maganar mata mahimmancin dama zai jita a kunnuwansa dan baya ma buqatan jin duk muryan da zatai masa magana tamkar iska a kunnuwan yafison yaji muryan da zata taho masa tamkar guguwan tahowan ruwan ocean.
Muryan mahaifiyarsa data matarsa saita 'yar cikinsa ne kadai muryoyin matan da sautinsu ke isa cikin kunnuwansa ya jisu a yanda suke amma bayan nasu yanada matsalar jin kowace sauti daga mata sosai.
Hakanne ya saka bai amsa ba sbd baima gansu ba sbd daga gefe suke sosai,
Kai tsaye hanyar staircase ya nufa ya fara hayewa a kamale
Harya isa sama gabaki daya babu alaman ansan da dawowansa dan haka lafiyayyar palonsa dayake hanya daban ya nufa ya shige tareda rufowa ya nufi hanyar bedroom dinsa dayake da tsananin girman da tsarinsa yake daban a kaf gidan sbd ko gadonsa me girman gaske ne da zai iya daukan mutum hudu dan kuwa kusan komai na bangarensa asalin asalin luxury ake magana dan iya girman closet dinsa dake cikin dakin girmanta zaifi wani dakin dan kuwa babu designer brand din da babu a ciki tin daga kan sitirar sakawa dataji bangaren guda zuwa bangaren shoes dinsa da bazasu kirgu ba zuwa watches na gold da diamonds da asalin masu tsada da neckties,da socks da eye glasshouse guda dake jere shima a gefe na designer shades dake daukan ido komai gefensa daban,hatta towels da undies nasa tamkar siyarwa akeyi sai bangaren zallan tirarikansa da tamkar dukiyar gado ce zaa barwa zuria sbd asalin tsadarsu da kudinsu.
********Kofar dayar hanyar ta sama aka bude sbd jin tsit daga waje gabaki daya yanayin ya sauya sbd waso lokutan akanji magana ko hayaniyar securities kadan idan suna exercise ko wani abin nasu amma jin shiru ya sakata leqawa sbd abu daya ne yake saka wannan shirun.
Window ta nufa kai tsaye bayan ta tashi daga zaunen datake tana waya hankali kwance.
Electric curtains din dake palon nata ta dan taba ta bude tareda kai idanuwanta masu haske ta kalli babbar harabar gidan da wasu ruwa ke gudana masu haske da kyan gani an tsarasu gefe guda na harabar gidan suna saukan ido taga motocinsa a tsakiyar harabar ba inda ake ajewa idan yayi tafiya ba take ta dawo da idanuwanta akan wayarta dake hannunta ta nemo numbernsa ta saka kira taji still a kashe bata shiga.
Ajiyan zuciya ta sauke me sanyi tana baro bakin windown ta ajiye wayarta a natse tareda nufar kofar fitowa daga palon nata dayake kusan iri daya dana mijinta amma nata baiyi girman nasa ba.
Tana bude kofar ta sako kai waje kamshin MAISON BACCARAT ROUGE 540 ya shiga hancinta wanda tin daga qasa daya keto hanyar babu inda bai bar lafiyayye sanyayye tsadaddiyar kamshinsa ba da itace take sanar da wanzuwansa a duk inda ya doso.
Dakatawa tayi tareda lumshe idanuwanta tana jan numfashi me sanyi ahankali tareda saukesa tana jin kowace gaba ta sassan jikinta da ruhinta na sake mutuwa kowace daqiqa na tsananin son mijinta da shine rayuwarta,ruhinta,jininta,bugun zuciyarsa,farin cikinta kuma sanyin idaniyarta.
Takawa tayi xuciya cikeda farin ciki da samun nutsuwa ta nufi hanyar palonsa tana sake shaqar qamshinsa.
Tana shiga kai tsaye bedroom dinsa ta nufa ta bude ta shige daidai lokacin ya fito daga closet dinsa dake da wani hasken led light masu kyau babu komai a jikinsa sai towel me fadi sosai blue wanda yake daidai iya qugunsa dayake a tsane qam da wani irin karfin dake nuna shi din kakkarfan gaske ne dan kuwa duk da yana babba jikinsa a tsane yake sosai da murdewa sbd har lokacin bai dena geamin ba sbd sabo da maidasa kaman cikon aladar rayuwarsa dake qarawa jikinsa lafiya da jinsa daidai.
Dago fararen idanuwansa yayi masu daukan hankali da saka gaba faduwa ya sauke mata su cikin wani irin yanayin dake sake kasheta da mutuwa akansa sbd tin tana budurwanta son RAHEEM JEERAH shine kaddararta kuma jarabawarta da harta mutu tasan bazata taba fita ba dan kuwa kallansa kadai wata wuta yake hadawa a jinin duk macen dazata samu rabon kallan nasa.
Zubawa fuskansa ido tayi tana kallan takunsa kafin ta motsa tana tahowa da sauri ta iso garesa ta miqa masa hannu tana sake fuska sosai da dariyar murnan dawowansa tace
'SIR Fleet'
Kallo daya yayi mata daya tayar da tsigar jikinta kafin ya miqa hannunsa daya bai kama natan ba ya fizgota jikinsa ya rungume a natse tareda sauke ajiyan zuciya sbd tinda mahaifinsa ya kirasa bai sauke numfashi ba sai yanxu sbd yariga yasan me kiran yake nufi da kuma girman dalilin daya saka dole zai amsa kiran ya tafi qasar da baitaba tinanin zuwa ba ayanzu...
Baice komaiba itace ta motsa tanason bude baki zatai magana wayarsa dake gefen table dake tsakiyar dakin tayi ringing din daya saka idanuwansa kaiwa ga wayar kai tsaye sbd sunan mahaifiyarsa da wayar ta ambata.
Ita kanta madam meenah matarsa dakatar da maganarta tayi jin sunan DR MUM daga cikin wayar,
Sakinta yayi yana nufar closet ya janyo bathrobe ya saka a jikinsa dan bawa kiran girmansa Tukuna ya iso ya dauka daidai tana yankewa yabi kiran da nasa kiran kai tsaye.
Zaunawa yayi anatse daidai lokacinda ta dauki kiran tareda ambatar sunansa kai tsaye da duk duniya a yanzu babu wanda yake kiransa da sunansa kai tsaye kaf dan hatta ubansa da Fleet JEERAH ko admiral yake ambatarsa ita kadai ne take da wannan ikon da isar na kiransa kai tsaye da ABDULRAHEEM.
A cikin tsakiyar kunnuwansa da kansa yaji kalamanta data ambaci sunansa dasu kai tsaye cikin sautin dayake bayyanarda akwai fushi da bacin rai datake dannewa a kalamanta sosai dan haka bude baki yayi da nutsuwa ya zai ambaci sunanta da gaisuwa ta katsesa da cewa
'Ina buqatan ganinka a mu fuskanci juna'
Numfashi mara sauti me nutsuwa ya sake sbd ya tabbatarda matsala dayace ta fallasa da zata saka iyayansa da basa tare tsawon shekaru tinda sauran kuruciya fuskantar juna a yanzu.
Ajiye wayarsa yayi batareda yace komaiba sbd ta riga ta kashe wayar.
Miqewa yayi yana sake tabbatarda lokacin fuskantar abinda bai taba bi takai ba yayi dan haka dole mahaifinsa daya fara kiransa qasarshi zai fara zuwa kafin isa ta mahaifiyarsa daga baya.
#MAMUH
#AGE GAP
#JEERAH
#BESTLOVE
#LOYALTY
#FLEET OF THE NAVYS
#GANIN IDO 2026
1k
5k vip
0022419171 AccessBank maryam sani gummi