BAYAN AURE

1

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 1.

Sarac Stars R Pen...✍️

MARUBUCIYAR...
Ƙarshen makirci.
Ƙaddararren Al'amari
Akan idona
Ƙazamin tabo
Rayuwar suhailat
Lubabatu
Zamani
Gashin ƙuma
Alhaki
Abun da ciwo
Kazamar amarya
Amaryar zayyad
Ƙangin talauci
Mijin aro
So da Manufa
Komai yayi farko.

Gargaɗi

*Ƙirkirarren labari ne, ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a bar mini sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye.* 9 April 2026.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

HAMIDA.

Sautin tsayuwar motoci a ƙofar gidansu shi ne ya tabbatar da cewar 'yan ɗaurin aure sun dawo daga gidan ƙanin mahaifinsu da yake can hayin banki, nan take matan cikin gida suka fara sakin guɗa, wasu kuma suna addu'ar Allah ya sanya alkhairi, ɓangaren masu sakin habaici kuwa suka fara yada magana saboda mutane da yawa sun kasa ɓoye hassadarsu akan irin mijin da Hamida ta samu. Shigowar Baba ƙarami cikin gidan tare da tawagar dangi yasa aka fara gaishe-gaishe ana taya juna murna, Baba Ƙarami Sai washe baki yake yi yana faɗin.

Ai Hamidan Hajjo tayi dace da miji ɗan babban gida, duk da iyayensa ba wasu bane amma shi Hafizu ya kama ƙasa dan ma'aikacin banki ne, a wajen ɗaurin aure naji mutane suna ta ambaton Manaja, ashe mai babban muƙami ne, kai Alhamdulillahi! Allah yasa sauran 'ya'ya su dace suma.

Amin malam, ai da kaga gidan da za a kaita shi ne zaka tabbatar yarinya ta dangwalo arziki. Wallahi in faɗa maka kayan katakon da muka kai mata sai da na rainasu ganin irin tafkeken gidan, shiyasa ya ce basa buƙatar kujeru kayan gado kaɗai ya isa, kayan kitchen ma a ɗakinta muka bari dan ba irin waɗanda ake jera wa bane a kitchen ɗin masu hali.

Cewar goggo Larai yayar babansu Hamida, shi kuma baba ƙarami sai faɗar madalla yake yi yana ƙari tare da girgiza kai, sauran mazan da suke tare da shi suma suna taya shi, sai Fatsime kishiyar mama ta kaɗe baki tace.

Wlh yaya Larai ni fa gani nayi kamar alfarma yayi wa yarinyar nan daya aure ta, saboda sam ban hango dacewarsu ba domin ruwa ba sa'an kwando bane...

Amma ai Allah ba ruwansa domin lamarinsa yafi gaban kwatance, irin wannan auren sai rabo ya kashe mutum, sannan babu wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi Imani.

Cewar Kawu Rabo yayan mahafiyarsu Hamida da ya katseta, nan kowa ya shiga gasgata maganarsa, wasu kuma suka shiga tunanin kyashin hassadar Fatsime ne ya motsa dan kaf 'ya'yan gidan ba wacce ta auri miji kamar na Hamida. Haka su baba suka gama gaishe-gaishe tare da yin addu'a ga marigayi Jafar mahaifinsu Hamida, kafin suka yi sallama ga matan gidan suka wuce.

Ɓangaren Hamida tana ɗakin mahaifiyarta zaune a gefen gadon ƙarfe, ƙawayenta suna gewaye da ita suna bata shawarwarin zaman gidan miji, dan kusan rabinsu duk suna da aure wasu ma har da goyonsu, duk maganganun su Baba Ƙarami a kunnensu hakan ya tabbatar musu da an ɗaura auren Hamida da Hafiz, a lokacin Inna Jamila Ƙanwar mama ta shigo ɗakin da guda, sai Hamida ta farka firgigit tamkar wacce ta tashi daga bacci, nan ta tabbatar ba mafarki take yi ba da gaske ne ta zama matar Hafiz, sai ta fashe da kukan murna hawaye ya soma kwaranya a kuncinta har ya fara ɓata kwalliyar fuskarta.

Haba Hamida meye na kuka.? ai tashi za kiyi ki fito tsakar gida kina fara'a dan ki bawa maƙiyanki haushi, Aure dai ya ɗauru mahassada sai dai su ji kunya.

Cewar Inna Jamila, sai ta ratso cikin tsakiyar ɗakin ta kamo hannun Hamida ta miƙe tsaye ta share mata hawayen fuskarta wanda kuma wasu suna ƙara biyo kuncinta, Hamida tace cikin rawar murna.

Innanmu kukan farin ciki ne, ji nake tamkar a mafarki wlh, ina jina kamar sabuwar mutum.

Dole kiyi murna yarinya sai ma kin ga irin gidan da Allah ya kai ki, ai Hamida kin gama dacewa a duniya dole maƙiyanki su zama fadawanki domin kin fita zakka, kuma In Sha Allah a dalilinki sai mun keta hazo mun kai ziyara ƙabarin Monzon Rahma.

Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Duk mutanen ɗakin suka ambaci haka cikin amon murya da farin ciki, sai Inna ta cigaba da cewa.

Muje ɗiyar albarka muyi murna a tsakar gida da hotunan tarihi.

Ba musu Hamida tabi bayanta tare da tawagar ƙawayenta suka yada zango a tsakar gidan suka cigaba da hidimar biki, hotuna suke ɗauka har dana gayya, sai dai suma sauran matan gidan da suke adawa da auren dole suka yada makamansu da suka ga ba Sarki sai Allah, saboda ba zasu tsaya a baya ba dan kar su rasa damar shan romon damakwaraɗiyya a nan gaba. Haka suka yini ana biki amarya sai sauya kaya take yi cike da izza, kuma gaskiya an zuba mata kaya masu matuƙar tsada da kyau saboda akwati biyar da kit dangin ango suka kawo shaƙe da kaya, har da extra gana mazgo da aka zubo jakukuna da takalma, a cikin kit har da ɗan kunne da sarƙar gwal, wannan yasa mutanen gidan da 'yan unguwa suka gigice aka shiga zancen auren Hamida lungu da saƙon layin, wasu ma cewa suke yi ɗan yankan kai ne, dan in ba haka ba me zai yi da Hamida yarinyar da ba wani kyau gareta ba sannan ga tarin jahilci, banda tallar shinkafa babu abunda ta sani a rayuwarta, samarinta ma duk 'yan cikin unguwa ne talakawa, daga masu walda sai ɗinki, amma ace rana tsaka wannan mutumin ya fito aurenta a ƙasa da wata huɗu ga shi har an ɗaure, ire-iren waɗannan maganganun ake yi kuma haka zancen ya dawo kunnen Hajjo mahaifiyar Hamida, amma sai ta toshe kunnenta tace sun ji sun gani baƙin ciki kawai ake yi wa ɗiyarta zata shiga cikin daula, sannan bata yi ƙasa a guiwa ba tun farkon haɗuwar Hafiz da Hamida ta saka aka bincika mata waye shi.? kuma Alhamdulillahi basu ji wani mummunan abu a tare da shi ba, dan an tabbatar musu da aikin banki yake yi kamar yadda ya faɗawa Hamida, ga shi kuma yanzu baba Ƙarami ya ƙara tabbatar musu da Manaja ne na banki, shiyasa ta tsaya kai da fata har sai da aka ɗaura wannan auren kafin hankalinta ya kwanta, yanzu babban burin ta shi ne Hamida ta kasance a gidan aurenta ta fara samo mata kuɗin da zasu gina kansu.

....

Bayan sallar la'asar Hamida ta gudu daga wajen ɗaukar hoto ta shigo ɗaki dan amsa kiran Hafiz, koda ta ɗaga shuru ta yi tana sauke numfashi a hankali ta kasa magana dan zuciyarta tsinkewa tayi ta rasa abun cewa, Hafiz ya ɗan saki murmushi ya ce cikin natsuwa.

Mrs Hafiz ina taya ki murna da zamowarki ɗaya daga cikin ahalina, da fatan zaki kasance mai yi mini biyayya da Uwargidata, kin san nasha faɗa mini farin cikin Laila shi ne nawa ba zan ɗauki duk wani abu da zai kawo mata ɓacin rai ba, na aure ki ba dan bana son matata ba sai dan kema ina sonki, shiyasa na daidaita ƙimarta da naki dan ina kyautata miki zato.

Ya ƙare maganar yana jan fasali, Hamida dum-dum ƙirjinta yake bugawa dan duk sadda Hafiz zai yi magana ɗaya biyu to na ukun dole sai ya sako zancen Laila a ciki, ita kuma hakan yana karya mata zuciya sai take ganin kamar alfarma yayi mata da zai aure ta, bai taɓa faɗar wani aibu na matarsa ba sai dai ya yabeta tare da tsantsar son da yake yi mata, ga dukkan alamu baya haɗa son da yake yi wa Laila da kowa, giuwarta yayi sanyi kamar kullun kuma hakan kesa take ganin Hafiz yafi ƙarfinta kawai Allah ya ƙaddara zata zamo matarsa ce, gishiri-gishiri data ji a bakinta shi ne ya sa ta gane hawaye ne ke bin kuncinta, amma cikin dakiya tayi saurin gogewa tace a sanyaye.

Nagode daka bani gurbi a cikin gidanka, sannan kamar kullun In Sha Allah ba zaka same ni da wata matsala ba, ina son anty Laila da 'ya'yanku, domin dole na taya ka son abunda kake so.

Allah ya yi miki albarka, kiyi haƙuri ba zan samu zuwa ba saboda bayan la'asar zamu gabatar da walima, amma bayan an kawo ki gidana zamu ɗauki hoton tarihi a cikin ɗakinki. Da fatan mai hoto ya zo ko.?

Tun ɗazu ya zo yana ta ɗauka, Kuma muma mun yi a waya.

To yayi kyau ki tabbatar kun shirya da wuri ana yin magariba zamu zo ɗaukarki, dan ina so bayan sallar isha'i na sallami kowa da wuri.

In Sha Allah zuciyata za a yi yadda kake so.

Cewar Hamida cikin sakin murmushi wanda sai da yaji sautinsa, shima murmushi ya mayar mata mai haɗe da sautin dariya kafin ya kashe wayar, sai ta sauke ajiyar zuciya tana hura isa daga bakinta tare da fifita da hannu dan ta haɗa gumi, sai ta zauna a gefen gado tana mayar da numfashi a nutse tare da lumshe ido tana jin wani shauƙin begen mijinta yana ratsata, har ga Allah ta ƙosa a sadata da gidan Hafiz domin ba ƙaramin shiri Inna Jamila tayi mata ba da kayan gyara wanda duk sadda taji muryarsa take shiga ɗimuwar kewarsa da jin ƙosawar kasancewarsu tare. Muryar Haulat ƙawarta ta ji daga waje tana ambaton sunanta yasa ta miƙe da sauri ta fito.

Haba anata nimanki ashe kina ɗaki.

Waya nayi da zuciyata, kuma yanzu ba zan saurari kowa ba wlh sai nayi sallar la'asar.

Cewar Hamida tana lumshe ido tare da yin murmushi. 

Iyeee su zuciya anji jiki, to sai ki fito da ita ki gasa masa ki bashi ya ci sai mu tabbatar da kin gama mallaka masa zuciyar, shigiya kina sumsum da ke amma rashin kunya ce fal cikinki.

Ya son ranki, yarinya ta kai mulzali ayi-ayi a kaini wuri na ƙurewa hahaha.

Cewar Hamada da ta ƙare da dariya sai ta jawo ƙofar ɗakinsu dan babu kowa a ciki ta rufe, saboda Hajjo ta hana a zauna dan kar a yi musu satar kayan lefe. mutane kuma kowa yana ɗar kar wani abu ya faru a zarge su, shiyasa kowa ya samu wajen zama a tsakar gida da sauran ɗakuna gidan. Hamida ta zari wata buta dake ƙofar ɗaki ta wuce hanyar bayi, Haulat data hangame baki tabi bayanta da sauri tare da sauran ƙawayensu suna yi mata surutu, wasu kuma suna cewa ta bar yin sallar sai anjima dan tana yin alwala zata ɓata kwalliyarta, bata saurare su ba ta wuce abunta ta ɗauro alwala har ta gama ta wuce su suna yi mata ƙorafi, ta shiga ɗakinsu ta gabatar da Sallar la'asar dan ba zata yarda ta ƙi yin sallah ba kamar yadda wasu amare suke tara sallah a ranar aurensu har sai dare yayi kafin suke haɗawa suyi. Bayan ta idar ta cigaba da zama tana karanta wasiƙar jaki, shigowar Hajjo ya katse mata tunani dan duk jikinta a sanyaye yake ganin zata bar gidansu na har abada ta shiga wata sabuwar rayuwa.

Ke Hamida ki taso haka mana kin bar mutane ana jira, ki fito a cigaba da hoton nan tunda ba ke zaki biya mai ɗaukar hoton ba.

Hajjo sallah na idar yanzu.

Yo sallar ma ai da kin jira sai anjima bayan magariba in kinyi wanka ki haɗa su kiyi, na yau dai kawai, ai Allah zai karɓi uzurin ki tunda hidima ce kike ciki na rana guda da ba zaki sake maimaita irinta ba a duniya.

Hajjo sallah tana gaba da komai fa, kuma kin san ita mutuwa bata jira ko, dan haka ba zan iya jinkirta sallah ba, kuma...

Dalla ki rufa mini baki, ai dama ke ba a binki bashin zance, in ba mugun nufi ba miye na kawo zancen mutuwa ana farin ciki. To kiyi ki fito kinsan dai kuskure kaɗan mutanen gidan nan suke jira su yi mana dariya, gwara ki lallaɓa ni mu rabu lafiya.

Hmmm Hamida ta ce fuskarta ɗauke da murmushi tasan halin kayan ta shiyasa bata ja ba ta cire sabon hijab ɗinta ta ninke ta ɗaura saman akwatinta sai ta ɗaura ɗankwalinta ɗaurin Zahra Buhari ta fito ba tare da ta duba madubi ba dan bata so ta ƙara goga powder, ita da zasu kyaleta ma da bata cigaba da ɗaukar wani hoto ba su barta da fargaban da zuciyata ke ciki. Tasan tana son auren amma tunanin irin zaman da zata yi a gidan Hafiz take yi saboda tare da matarsa Laila zasu zauna gida ɗaya falo ɗaya, kuma da su Inna suka je yin jeren kayan gadonta sun tabbatar mata da matarsa ta fita komai kyau da tsarin halitta dan hutu ya nuna sosai a jikinta, shiyasa ta ƙara gasgata maganar Hafiz akan yana son matarsa fiye da son da yake yi mata, wannan yasa take tambayar kanta meyasa ma ta amince da aurensa.? sai dai irin gudummawar famfon da Hajjo take kora mata na aurensa shi ne hanyar arzikinsu ya sa ta yi saurin amincewa har take hango kanta a matsayin mai sa'a, sannan irin soyayyar da Hafiz ya nuna mata da kuma kuɗin da yake kashe mata yasa ta fahimci itama yana sonta kuma ta samu babban matsayi a zuciyarsa, sai dai a can ƙarƙashin zuciyarta ta dasa mata raunin yafi ƙarfinta kawai dai Allah ya ƙaddara zasu zauna a inuwa ɗaya ne, kamar bata kai ya aure ta ba dan ba tada kyan azo a gani siririya ce ita sosai kuma ga duhun fata, abu mai jan hankali a jikinta shi ne manyan ido farare da wushiryar saman haƙorin da suke farare saboda tana da baƙin dashishi, sannan ita ba mai ilimi can ba ne iyakarta secondary shima a shiririta ta gama, bata iya turanci ba sai kaɗan amma tana iya jin duk turancin da za a yi mata mayarwar ne aiki, islamiyya kuwa aji biyu ta tsaya ta watsar sai tallar shinkafa da take yi a ƙofar gidansu, tun sha biyun rana in ta fito bata komawa sai bayan Magriba bayan ta gama sayar da tuwon yamma, sai kuma yawan zuwa biki da Partyn birthday da duk wani abu ɗaya shafi sharholiya baya wuce ta, rayuwa take yi na rashin mafaɗi dan ma kakarsu tana saka ido da tsawatar musu domin macece mai tsantseni tana ƙoƙarin nusar dasu tarbiyya, da yake Hamida a ɗakinta take kwana shiyasa rayuwarta take a seti dan duk son sharholiyarta tana da natsuwa, dan kaka tana iya ƙoƙarin nuna mata haƙƙoƙin Allah, sannan a wajen kaka ta iya wasu Azkar da yawan yin nafila, sallar walha baya wuce Hamida duk safiya sai tayi shi, ga kuma na dare da kaka in ta tashi sai ta tasheta tayi ko raka'a biyu ne, wannan yasa Hamida take da natsuwa ba tada hargagin sauran yara, tana kuma da gudun zuciya shiyasa take takatsantsan wajen kuskure wa Hajjo saboda ita tana da faɗa bata ɗaukar raini. Shi yasa idan ta duba rayuwarta dana Hafiz sai taga kamar ba suyi matching ba du ba da tazarar arzikin da ke tsakaninsu.

Bayan sallar magariba tayi wanka ta kintsa cikin tsadadden leshi mai ruwan Zuma da ratsin fari, ta saka farin mayafi, inna Jamila ta bulbuleta da turaren feshi, ɗakin ya buɗe da ƙamshi mai daɗi, tana zaune akan tabarma kamar yadda 'yan uwan baba da mama suka sakata a tsakiya suna yi mata faɗan yadda ake yi na al'ada, ita kuma ruwan hawaye suna bin kuncinta har suka gama, goggo Larai ta ce.

Hajjo baki ce komai ba kin bar mu muna ta magana.

Haba yaya Larai ai kun gama cewa komai, sannan ma ni tun da watan auren ya tsaya nake jelar yi mata faɗa, dan haka na gama nawa saura ita ta nuna mana cewar ita ɗin 'yar halak ce ta bawa mara ɗa kunya ta zauna gidanta cikin aminci kamar yadda muka jaddada mata. Allah ya jiƙan Malam nasan yaso yaga wannan rana amma Allah bai nufa ba. Hamida na yafe miki duk wani ɓacin rai da kika sakani Allah ya sakawa aurenki albarka.

Cewar Mama Hajjo cikin fidda kuka mai sauti, nan take kukan Hamida ya ƙaru matan cikin ɗakin suma suka shiga matsar kwallar tunawa da marigayi baba Jafaru, daga bisani Goggo Larai ta miƙe ta kama hannun Hamida suka fita zuwa ɗakin kishiyoyin Mama.

*Rahma Ce, ina magana da uwargida, Amarya dama 'yan mata, saƙon labarin ya shafi kowa hatta magidanta maza da samari, na kawo muku sabuwar tafiya da fatan zaku bini a hankali dan jin me wannan labarin ya ƙunsa. In Sha Allah zaku ƙaru ta fuskoki da dama.*