KUNDINA

06

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*;
    
*NAFISASASAAL*



06

Na kai minti goma a zaune, sannan Aunty Amarya ta shigo.

Ba tace min komai ba, ta wuce ɗakin barcinta.

Ƙaton ɓakin leda ta fito da shi, cikin taushin muryarta kamar kullum ta ce;

 "ga wannan, Allah Ya sa ki koma makaranta a sa'a Fatima"

Kafin na fara kwararo mata godiya, ta tashi ta bar ni da sakakken baki.

Duk da haka ban fasa cewa; "na gode, Allah Ya ƙara buɗi" ba.

Jikina na rawa na ɗauki ledan. Gudun kar mu haɗu da wani ya kaiwa Hajiya Babba gulmar fitowata daga Sashen sai na bi ta baya, ta inda babu wanda zai ganni, na shige Sashena.


*HAJIYA BABBA*;

Fatima tana fita Alhaji ya kalleta cikin faɗa sosai ya ce;

"Wallahi Saratu, ba ki da hali kuma ba ki san girmanki ba. Da kike mata gorin ta kori Mahaifiyarta, ai ba ita ta kori Mahaifiyarta ba, kece kika korar mata uwa, da mugun kaidinki.

 Su dai ƴaƴa kowa yana da su, kuma fatan da ki ka yiwa na wani shi zai faru da na ki. 
Wallahi Hanifah ta fiki hankali da nutsuwa, shekarunki na banza ne Saratu. Dan Allah tashi ki fice min daga Parlo, saura kuma na ji wani abun ya biyo, sai na mugun saɓa miki sama da yanda bakya tunani, babbar kwabo kawai"

Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, haka Hajiya Babba ta miƙe, babu abinda ya fi ɓata mata rai, irin yabon da yayiwa kishiyarta Hanifah a gabanta.

Indai kuwa zagin Fatima ne yanzu ta fara, sai dai ya yi duk abinda zai yi.

Da wannan tunani da isa Sashenta, ranta a ƙuntatace.


*FATIMA*

Ina isa Sashena na saki ajiyar zuciya haɗe da murmushi.

Gudun kar wani daga sashen Hajiya Babba yayimin shigowar bazata sai da na saka mukulli na kulle sashen.

Hannuna har rawa wajen fito da abinda yake cikin ledar da Aunty Amarya ta ba ni.

Dogayen Riguna ne marasa nauyi masu kyan gaske har kala biyar. Ga turare, shower gel da lotion masu kyau. Sai bandir ɗin dubu ɗaya guda ɗaya.

Kasa riƙe jin daɗina nayi na saki kukan farin ciki, na janyo wayar da na ajjiye a gefena na lalubo number Mama na danna mata kira.

Sai da ya fara ringing zuciyata ta fara bugawa, tsoro ya shigeni, sai dai ban katse ba. 

Kamar baza'a ɗaga ba.

 Sai da ya kusa katsewa na jiyo nutsatsiyar muryarta ta ce;

"Assalamu alaikum"

Maimakon na amsa mata sai na fashe da kuka.

Ba tace min komai ba, kuma ba ta katse kiran ba. 

Tsoron kar na cigaba da kuka ta katse kiran bayan tsahon lokacin da ta ɗauka ba ta ɗaga kirana na ce;

"Ina wuni Maama, Mama nayi kewarki, ki yafemin, kinga na roƙi Baba zai mayar da ni Makaranta har ya karɓi takarduna, yanzu Aunty Amarya ma tayimin kyautar Kaya, har da su  turare da kyautar kuɗi"

Jin shiru ba'a cemin komai ba yasa na dakata haɗe da sakin kuka ina ƙara cewa;

"Mama kina jina? Wallahi nayi miki alƙawarin ba zan sake maimata kuskurena da na yi a baya ba, Baba ma nayi masa alƙawari, kuma dagaske na ke Mama"

Duk da haka bata ce min komai ba, kuma bata katse kiran ba. Kuka mai ɗan sauti na fashe da shi,  ina nanata kalmar;

"Mama kiyi haƙuri, ki yimin magana na ji muryarki"

Ɗif ta katse kiran.

Kaina na dafe saboda wani irin sarawa da ya yi.


Ina cikin wannan yanayin wayar da na ƙanƙame a hannuna bayan katse kiranta ya fara ringing.

Sunanta na gani, garin rawar hannun na ɗaga naje na danna katsewa, ban yi yunƙurin kira ba, gudun karta ƙara kira ta kasa samuna.

Cikin ikon Allah sai gashi ta ƙara kira.

Sai da na saita kaina na ɗaga, amma bance komai ba, burina kawai naji muryarta.

"Fatima" ta faɗa a tausashe da alamar kuka a muryarta.

Kasa amsawa nayi sai kaina da na ɗaga kamar tana ganina.

"Kina jina?" Ta ƙara faɗa a tausashe.

A wannan karon a hankali na ce;  "ina jinki Mama"

A jiyar zuciya ta sauke ta ce;

"Ki nutsu ki yi bitar kuskurenki da kanki, zaki ƙara sanin illar da kika yiwa rayuwarki, har ki gyara a gaba, domin baya ya riga ya wuce. 
Ba alƙawarin da zaki yi mana ba ne zai sa ki kare mutunciki, gane irin kuskuren da kika aikatawa rayuwarki shi zai sa ki gyara. 

Aure lokaci ne, idan lokacinki ya yi ko da bakya fita ƙofar gida, har cikin gidanku Allah zai shigo miki da mijin aurenki. Na yafe miki Fatima, Allah Ya bada sa'a Ya sanaya albarka a cikin neman iliminki, ki kula da kanki.

Ki gaishemin da Auntynku, ki ce ina yi mata godiya."

Daga haka ta sake katse wayar, ba tare da ta bari  na ce komai ba.

Wayar na bi da kallo, zuciyata tayi sanyi ƙalau. 

Da suna tare ita da Baba, ko suna waya da sai na ce; shi ya faɗamata ta gayamin, irin kalmar da ya faɗamin ranar da na je masa da batun komawa ta makaranta.

Jikina a sanyaye na kwashe kayan da Aunty Amarya ta bani, kowanne na adanashi a inda ya da ce.

Haka nayi wunin wannan ranar ina saƙe-saƙen kan yanda al'amura zasu kasancemin idan na koma Makaranta.

Ban je ƙarbar abinci sashen Hajiya Babba sai dare, ban shiga parlonta gaisheta ba, saboda nasan a cike take da ni.

Haka na dawo Sashena naci abinda ya sawwaƙa. Ina yin sallar Isha'i na kwanta barci.

Haka kwanaki suka fara shuɗewa, kullum idan na je gaishe da Baba, sai ya ce na kwantar da hankalina ya na sane da ni.

Tsakanina da Hajiya Babba hantara ne, da baƙaƙen maganganu kamar ta nayi da sa'arta.


Cikin ikon Allah ranar ina zaune, Baba ya turo aka kirani, ya yi min maganar zana Jam satin da zai zagayo. 

Kamar anmin albishir da gidan aljanna haka nayi ta washe baki ina godiya.

************************************

Da satin zana Jarabawarmu ya zagayo, Baba  ne da kansa ya kai ni, ya ce idan mun gama na kirashi zai turo a ɗaukeni.

Cikin sa'a da yaƙinin samun nasara na gama zana jarabawa, raina fari ƙal, ina jina kamar sabuwar mutum.

Bayan na fito na kira Baba, ban jima a tsaye ba, Driver Hajiya Babba ya ƙaraso.

Daga gaisuwa ban ƙara ce masa komai ba, duk yanda ya kai ga son jin wani abu daga bakina ban kulashi ba. Saboda na hannun daman Hajiya Babba ne.

Bayan mun iso gida, ban ce masa komai ba, na shige Sashena.

Ina shiga Sashena ko wanka ban yi ba, na turawa Mama saƙon na zana Jarabawar Jam ta tayani addu'a Allah Ya bani sa'a.

Nan take reply ɗinta addu'arta ya shigomin.

 Na maimaita karanta saƙonta yafi sau biyar, ina jin daɗin irin addu'ar da ta yimin, ina murmushi.

Da ƙwarin gwiwar jin daɗin saƙon samun nasarar da Mama ta turomin na miƙe na shiga wanka.

Bayan na fito, ɗaya daga cikin kayan da Aunty Amarya ta bani na, nayi kwalliya da shi.

Na ɗauki dubu ashirin daga cikin kuɗin da ta bani na bar gidan.

Abinci mai rai da motsin da raina yake so, na hau adaidaita sahu na siyo

Ina kan hanyar dawowa yawuna yana tsinkewa, saboda  ƙamshin abincin yake shigarmin hanci.

Ta hanyar da babu wanda zai ganni, balle a kaiwa Hajiya Babba gulma, na shige Sashena, ina yiwa kaina dariya.


A haka nayi ta gudanar da rayuwarta yau da daɗi gobe babu.

 Kullum ina ƙunshe a ɗaki, daga zuwa gaishe da Baba, sai karɓo abinci a sashen Hajiya Babba.


Bayan wani lokaci Jarabawar Jam ɗinmu ya fito, kuma na samu makin da ake so.

Daga Ni har Baba bakinmu a washe.

Baba bai yi ƙasa a gwiwa ba, har sai da na samu gurbin karatu a BUK.

A daren washe garin da zan fara zuwa makaranta, tsit nayi a zaune ina tunani, tare da hasaso irin farin cikin da na ga Baba ya na yi, kamar ni kaɗaice ƴarsa da ta fara samun gurbin karatu a Jami'a.

A take maganar Mama ya faɗomin da take cewa;

"Ki nutsu ki yi bitar kuskurenki da kanki, zaki ƙara sanin illar da kika yiwa rayuwarki, har ki gyara a gaba"

A hankali na miƙe na ɗauko littafin da na yiwa take da *KUNDINA* kamar waccen lokacin shafi-shafi na dinga karantawa ina haddacewa, har na zo kan shafin da tarihin rayuwata ya fara.

Wani kuskure ne a cikin *KUNDINA* da zamemin tabon da bazan manta ba?.✍🏻