SARTSE A ZUCI...!

SARTSE A ZUCI....! Chapter 8

by @ayshadansabo

*SARTSE A ZUCI...!* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book*

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 8*

Lokacin da suka iso Zaria suka zarce ƙayataccen tanfatsetsen gidan Daddy dake GRA gani sukai gabaki ɗaya kyawun gidan a fili yafi a hoto tsaruwa,daga Yaya Zayd har Yaya Sulaiman sun yaba da tsarin gidan da kuma irin dukiyar da Daddy ya narkar wajen mallakar wannan aljannnar duniyar.Babu inda yafi birgesu a gidan irin ɓangaren Lounge Garden da kuma na swimming pool dake cikin gidan domin daga Yaya Zayd har Yaya Sule akwaisu da son yin ninƙaya a cikin ruwa.Babu inda Momy bata zaga dasu a ciki da wajen gidan sun gani ba,hatta ɓangaren Anty Mamah itace ta fara yi musu jagoran zuwa ta gabatar ma Anty Mamah dasu a matsayin zaratan manyan Yaran Alhaji Taheer da bai haɗa ƙaunarsu data kowa ba.Ita Kanta Anty Mamah bata taɓa tunanin cewa Yaya Zayd da Yaya Sulaiman ba daga jikin Momy suka fito ba,domin koda Daddy ya bata labarin yawan Yaransa bai taɓa sanar da ita cewa bashi ya haifi Zayd da Sulaiman ba.Sai da suka samu kwanaki biyu da dawowa ne tasan hakan,shima ji tayi suna hira akan wasu kuɗin gadonsu da aka juya aka samu manyan riba a sama shine Daddy ke jaddada musu cewa su yaiwata sanya Iyayensu a cikin addu'a.Bayan barinsu falon Daddyn ne da yake tana tare da shi sai take tambayarsa dama bashi ya haifesu ba? Shine ya sanar da ita cewa ɗan Uwansa Marigayi Alhaji Abdallah shine ya haifa masa su.Sosai tayi mamaki ta kuma gasgata amana da irin ƙaunar dake tsakanin Asiya da Momy,nan take taji Momy ta sake birgeta domin samun mace irinta mai riƙon alƙawari da maida ɗan wani nata sai an tona a cikin wannan zamanin.Musamman daya kansance cewa ita Momy Allah bai bata Yara Maza ba ga Uban tarin dukiya da Daddy ya tara a yanzu,wanda dole su Yaya Zayd ɗin ne za su hau kan dukiyar wajen tayashi juyata.Tabbas da wata ce iya hakan kaɗai zai iya sanyawa ta mance baya ta fara nuna kishi a kansu,sai gashi ita babu wannan a cikin zuciyarta domin da dukkanin zuciyarta take ƙaunarsu kuma ƙauna na tsakani da Allah.Anty Mamah ta sake gasgata kyawun zuciya da rashin ƙyashi irin na Momy ne a lokacin data fara tallata mata business ɗinta na saida rigunan Yara tana ɗaura mata a status ɗinta business partners ɗin Momy da kuma sauran customer's ɗinta suka fara rubibin kayanta,itama sai Anty Mamah ta shiga tallata mata turarukan wuta kuma aka fara odarsu ana rububinsu domin duk wanda ya saya sai ya janyo wasu.A haka suka taimaki kansu suka sake bunƙasa business ɗinsu tare da samun sabbin customers ta jikin junansu ba tare da ƙyashi ko hassada ba,koda wasa Anty Mamah bata yi gigin baro shagonta na Kano ta dawo dashi Zaria ba domin ta kafu a can ɗin sosai.Rashin haihuwar Yara maza bai taɓa zuwa kan Momy ba bare har ya dameta,domin kullum ji take tamkar daga jikinta Yaya Zayd da Yaya Sulaiman suka fito.Haka Iyayenta da suka kasance masu ilimi da aiki dashi basu taɓa nuna mata cewa rashin haihuwar Yara maza wata gazawa bace,shiyasa ko kaɗan babu wannan tunanin a cikin zuciyarta.Kwanakinsu Yaya Zayd uku da isowa ƙasar sukai wa garin Kaduna tsinke domin zuwa suyi tozali da ƴan ƙannensu Amal da Hameedah,Yaya Zayd duk ya ƙosa ya saka luv ɗinsa a cikin idanunsa ya kuma ga wani kalar class da gogewa ta sake samu a rayuwa.Ko kaɗan basu sanar dasu cewa a ranar da suka je za su isa ba domin sun shirya yin suprising ɗinsu ne,don haka ranar Hameedah ta fito daga exam kenan ta koma hostel tana zaune sai ga kira.Tayi mamakin ganin sabuwar lambar 9ja domin dukkaninsu sun aje SIM card ɗinsu na UK sun maida na 9ja,don haka saida tayi picking call ɗin kawai taji muryar Yaya Zayd yana sanar da ita cewa gasu a cikin school ɗinsu waje kaza.Hameedah ta fasa ihu tana kallon su Amal da ƙawayenta Zulaiha da Meenal ta sanar da Amal cewa gasu Yaya Zayd nan sun kawo musu ziyarar bazata,Amal ta miƙe zumbur cike da farin cikin cewa za ta ga Yaya Sulaiman ta zari mayafin doguwar jallabiyar dake jikinta saƙar ƙasar Oman ta yane kanta dashi.Tayi masifar kyau cikin doguwar rigar da kalarsa ya kasance coffee brown,farin beauty face ɗinta babu komi a samansa sai kwallin data saka a idanunta wanda ya sake fiddo asalin kyawu da hasken idanun.A tare suka fito daga hostel ɗinsu ita da Hameedah wacce itama ta saka rantsatstsiyar black Abaya daya haske farar fatarta,tayi kyau fuskarta sai glowing take.Direct inda su Yaya Zayd ɗin suka ce suna jiransu suka nufa,kuma tun daga nesa zaratan samarin suka sake yaba girma da class ɗin da ƙannen nasu suka ƙaro.Yaya Zayd ya kasa ɗauke idanunsa a kansu su duka yana mamakin kauɗi da yanga da Amal ta ƙaro,yayi mamakin yadda ya kasa ɗauke idanunsa akan Amal da irin feeling ɗin da ya ji ya ratsa har kwanyarsa.Da ƙyar ya iya ɗauke ganin akan Amal ya mayar kan Yaya Hameedah,yana sake hango sanyinta da nutsuwarta daya zama nature ɗinta komi nata babu haniya a cikinsa.Rungume juna su duka sukai suna welcoming juna time ɗin dasu Amal ɗin suka ƙarisa zuwa garesu,Yaya Sulaiman ya sake Amal da tayi hugging ɗinsa tana sanar dashi irin missing ɗinsa datai.Komi ya faru akan idanun Zayd Abdallah da yaji zuciyarsa tayi zafin da irin hugging juna da sukai tsakanin Amal da Yaya Sulen,sam bai ga aibin nasa kalar rungumar da yayi ma Hameedah,wanda da ƙyar ya iya sake Yaya Hameedah daga jikinsa yana jin wani azababben feeling a kanta na kewaye jininsa.Suka koma mota ya buɗe mata front ta shiga yayin da shi kuma Yaya Sulaiman Amal ta jashi can nesa kaɗan da motarsu wajen wata bishiya da aka aje fararen kujeru a wajen suka zauna,hirar yaushe rabo ya ɓalle a tsakaninsu kafin Yaya Sulaiman ya fara tsokanar Amal da cewa waye surukin nasu?Amal dariya kawai tayi masa itama tana tambayarsa zuwa yanzu wace kalar black beauty gal ce ta sace musu zuciyarsa? Ya bata labarin cewa tabbas sun fara soyayya da wata Nadeeya yar garin Gombe da suka haɗu acan UK ɗin.Ya sanar da ita cewa a yanzu tana shekarar ƙarshe ne tana karantar Economics,Amal ta taya shi murna ta kuma sanyashi ya nuna mata pic's ɗin Nadeey ba tare da ɓata lokaci ba.Kuma kamar yadda yaci burin cewa shi black beauty yake burin mallaka itama Nadeeya black beauty ce sosai,kuma da alamu akwaita da nutsuwa da kamewa domin yanayin shigar da tayi ya bayyana hakan kai tsaye.Ranar gabaki ɗaya sai wajen magriba suka baro Kaduna,domin fita sukai yawon shaƙatawa Yaya Zayd sunata zuba luv ɗinsu shi da Hameedah.Ita dai Amal kallonsu kawai take tana taɓe baki domin gani tayi ya ƙaro wulaƙanci wajen miskilanci da tsare gida shi a dole ga babba,ko gaisuwarta a tsume ya amsa kuma ko yace yayi missing ɗinta.Da suka ajesu za su juya ne Amal ta duƙa tana sanarwa Yaya Sulaiman cewa ya isar mata da saƙon gaisuwarta wajen Anty Mamah da Jamcy,ya taɓe baki yana tambayarta wace ce kuma Jamcy? Ta sanar dashi wace ce ita tana mamakin ya akai basu haɗu da ita a gidan ba sai kuma ta tuna cewa ita Jamcy ƴar zaman ɗaki ce bata cika fitowa ko falo ba inba da dare bane.Su kuma tasan ma ba zuwa side ɗin Anty Mamah za su riƙa yi ba don ta gama gane cewa daga mutumin nata Yaya Sulaiman har Yaya Zayd ɗin babu wanda ke yin Amaryar Daddy su a dole kishi suke taya Momy da gaske.Haka dai sukai sallama dasu kowanne cikinsu ya dire ma Fav ɗinsa tarin tsarabar da yayo dominta,gogan Yaya Zayd wani ƙaramin kyakykyawar luggage ya direwa Hameedah mai ɗauke da tsarabarta a ciki.Shi ko Yaya Sulaiman wani madaidaicin bag ne shaƙe da kayan ciye-ciye na tsadaddun chocolate ya direwa Amal,domin yasan tafi kauri a wannan ɓangaren sai kuma turaruka masu sanyi da suke cikin wani ƙaramin jaka daban.Sukai sallama dasu cike da ƙaunar juna Yaya Zayd na sanar da Hameedah cewa nan da 3 day's zai koma ya ɗauketa domin a ranar za ta kammala exam ɗinta,ita kuma Amal sai next week za su ƙare domin ba tare suka fara ba.Kamar kuma yadda ya faɗi ɗin after 3 day's ɗin ya koma ya ɗauketa zuwa Zaria,suka wuce direct ɓangaren Momy suna tafe suna hirar soyayyar da har kunya Hameedah ke ji idan ya zaro mata wani zancen domin gani take tamkar ba shine miskilin Yayannan nasu ba.Momy ta taresu cikin ƙauna da soyayya tana jin tarin annushuwa a cikin zuciyarta idan tana tuna cewa nan da wani lokaci kaɗan Hameedah za ta zama mallakin Yaya Zayd ɗin,domin a daren jiya suka fara magana ita da Daddy cewa da zaran sun kammala bautar ƙasa kawai za a saka lokaci a ɗaura aure su tare a gidansa dake Kaduna sai ya tada ƴan hayan dake gidan tunda yana fata kafin Yaya Zayd ɗin su samu aiki za su fara kula da dukiyar gadonsu shi da ɗan Uwansa.Tunda Hameedah ta dawo daga school sau biyu kawai ta je ɓangaren Anty Mamah suka gaisa,amma suna haɗuwa a ɓangaren Daddy da safe su gaisa.Sam basa haɗuwa da Jameelah wacce kewa Hameedah kallon miskila ce ita,Jameelah tana yawan cema Anty Mamah Hameedah nada jin kanta ita ko Amal son mutane gareta.Ranar da Amal ta kammala nata exam ɗin Nuhu driver yaje ya ɗakkota domin Yaya Sulaiman da Daddy sun tafi Abuja a ranar,kuma za su samu kwanaki biyu kafin su dawo.Tunda Amal ta dawo gidan ta tare a inda tafi wayo yanzu wato ɓangaren Anty Mamah,ranar dasu Daddy suka dawo sam basu ji isowarsu ba suna ɓangaren Anty Mamah sun ƙule a cikin ɗakin da Jameelah ke zama suna hirar saurayin da Jameelah tayi.Sai da Hameedah ta kira wayar Amal ta sanar da ita cewa Yaya Sulaiman na nemanta sannan tasan cewa sun dawo,lokacin data isa ɓangaren Momy ta taddasu su duka ita dasu Yaya Zayd a cikin main parlour suna zantawa.Kallo ɗaya Yaya Zayd yayi mata ya ɗauke kansa bayan ya dalla mata harara,sosai take bashi haushi yadda take shigewa Anty Mamah ita kaɗai ce bata taya Momy kishi.Sannan tun bayan dawowarsu ƙasar ya fahimci Amal ta ƙaro wulaƙanci na iyayi da ƙwalisa,ga tsiwarta dake tsaya masa a zuci da ya fahimci shi ma yana nan sai abinda ya ƙaru ma.Yaya Sulaiman ne ya sanya ta girka masa party jallof da salad domin yace da yunwa suka shigo,ita kuma Yaya Hameedah Yaya Zayd cewa yayi ta shirya ta rakashi restaurant yaci abinci domin bazai iya jira har a girka wani abinci ba tunda tuwo Daddy ya saka Momy girka masa domin ita ke dashi a ranar,su kuma basa cin tuwo sam.Amal ta kallesu ta taɓe baki time ɗin da Hameedah ta wuce zuwa room ɗinsu domin shiryawa su fita,time ɗin da suka fice Amal na ɓangaren kitchen ɗin Momy tana shiryawa Yaya Sulaiman abincin daya buƙata.Sai dai tana aikin ne zuciyarta na jin haushin yadda Yaya Zayd ɗin ke neman mayar da Hameedah jelarsa duk inda zai sanya ƙafa sai ya wani jajibeta,su kuma su Momy basa taɓa hanasu domin sun ɗauki yarda da soyayyar duniya sun ɗaura a kansa sam baya laifi a wajensu.Hakan kuma ba ƙaramin ƙona zuciyarta yake ba,domin ita sam soyayyar da sukewa juna ba birgeta yake ba.Duka-duka hutun sati biyu sukai suka tattara suka koma school,Hameedah suka shiga final year yayinda Amal ta shiga level 3.Yaya Zayd da Yaya Sulaiman suka fara shirin tafiya camp domin suna saka ran list ɗin da zai fito second batch ya kasance da sunansu a ciki,hakan ko ya kasance domin a second batch aka kafe sunayensu da sunan garin da aka cillasu.Yaya Zayd aka tura shi jihar Ekiti yayinda Yaya Sulaiman akai posting ɗinsa zuwa Kano,suka shirya suka wuce cike da kewar Momy da za su yi shi kuma Yaya Zayd cike da kewar wife ɗinsa Hameedah kamar yadda ya fara kiranta da matarsa kai kace har an riga an ɗaura auren ne.Koda suka gama camping babu wanda ya nemi canji domin Daddy yace kowanne yayi zamansa a garin da aka turashi tunda su Maza ne ba mata ba bare a nema musu canji,don haka Yaya Zayd yayi zamansa a jihar Ekiti hankalinsa kwance shi kuma Yaya Sulaiman yayi zamansa a Kano.Koda yaushe Hameedah suna maƙale da Yaya Zayd a waya suna soyewarsu,duk wasu ƙawayenta na hostel da course mate ɗinta sun san labarin Yaya Zayd a bakin Hameedah domin kowa ya shaidi irin zazzafar soyayyar da take masa.Amal Taheer tunda suka shiga level 3 ta sake zage damtse domin tana da burin Daddy da Yaya Sulaiman suyi alfahari da ita,so take ta fito da first class don haka bata da lokacin kowa sai karatu.Sosai Amal take yin samari a ciki da wajen school amma basu isheta kallo ba,sam bata ƙaunar batun soyayya shiyasa ta tsani wani sabon lacturer ɗinsu mai suna Dr.Kabeer Asgar domin shi kaɗai ne matsalarta a yanzu daya liƙe mata yana ƙaunarta da gaske.Kullum sai ya kirata fin sau biyar a rana tunda ya samu nasarar amsar lambarta a wajen bestynta Zulaiha Naseer,ta ɗan fara samun sauƙinsa ne a lokacin da dabara ya faɗo mata suka haɗa baki da Yaya Hameedah suka sanar dashi cewa Daddy yayi musu miji dukkaninsu ana jiran su ƙare school ne kawai a saka musu rana.Da yake social Ustaz ne yana da fahimtar addini sosai sai ta samu sauƙin nacin kiran da yake mata,amma ya kasa haƙura gabaki ɗaya yakan kirata a ƙalla sau biyu a rana safe da dare kafin ta kwanta bacci.Watarana Amal sun fita cin shawarma a ranar Sunday ita da friend's ɗinta Zulaiha da Meenal da kuma Yaya Hameedah,Amal ta haɗu da Aman Shehu Kurfi wanda ya ciri tuta a cikin ƴan maza.Suna ƙoƙarin shiga ƙayataccen wajen sayen Shawarma dasu burger shi kuma yana fitowa daga cikin wajen hannunsa riƙe da manyan ledoji,da yake Amal itace a farko shiyasa a kanta ya fara sauke idanunsa kuma a lokaci guda ta tafi da dukkanin nutsuwarsa.Amal a ranar duk son kwalliyarta ma batai ba tana sanye ne da simple bubu na material da yayi mata mugun kyau,daga saman kanta zuwa ƙirjinta tayi rolling veil daya zauna sosai ya kuma fito da kyawun cute beauty face ɗinta da babu kwalliya a samanta daga kwalli sai man leɓe mai taushi data goga.Kallo ɗaya Amal tayi masa ta ɗauke kanta tana saurin raɓashi ta shige ciki su Yaya Hameedah suka rufa mata baya,babu wanda yabi takan gayen daya sanƙare a tsaye yana kallonsu har suka gama shigewa cikin wajen.Cikin sauri yayi kiran wani ma'aikacin wajen da suka saba dashi sosai ya bashi umurnin cewa duk abinda waɗannan ƴan matan da suka shiga yanzu za su saya shine zai biya kuɗin,don haka ya bashi card ɗinsa yace ya zama a kusa da zaran sun kammala ya biya kuɗin ya kawo masa card ɗinsa zai jira a mota.Daga haka ya nufi wajen ƙayatacciyar Ash motarsa ya buɗe driver seat yayi zaune bayan ya zube ledojin hannunsa a front seat,kyakykyawar fuskar Amal Taheer da kuma structure ɗin jikinta kawai ke yawo a cikin brain ɗinsa da ƙwayar idanunsa.Har wani lumshe idanunsa ya dinga yi yana sake buɗesu a ƙofar fitowa wajen domin bashi da burin daya wuce sake ɗaura idanunsa akan kyakykyawar surar da tayi wuff da zuciyarsa farat ɗaya,don haka lokacin dasu Amal suka kammala sayayyarsu suka fito kowacce hannunta riƙe da ledoji akan idanunsa suka fito.Rufa musu baya yayi lokacin da suka fice domin zuwa bakin titi su tari abin hawa,ya faka motarsa nesa kaɗan da inda suke tsaye yana sake ƙarewa Amal Taheer kallo daga nesa.Lokacin da suka tare abin hawa suka hau ne ya rufawa mai napep ɗin baya,sannu a hankali yake biye dasu ba tare da sun san cewa ana biye dasu ba.Mai napep ɗin daya sauke su Amal na fakawa motar AS Kurfi ta faka daga bayansa kaɗan,hakan yasa su Zulaiha na fitowa AS Kurfi ya fice ya taresu da sallama.Babu wacce ta tsaya ta saurareshi sai Zulaiha sarkin sauƙin kai,koda yayi mata kwatancin Amal yake son lambarta ta zuba masa idanu a lokacin tana kallon tsantsar haɗuwarsa da ajinsa.Tamkar ba za ta bashi lambar ba sai kuma ta bashi bayan tayi masa gargaɗi cewa kada ya taɓa sanar da Amal cewa wajenta ya samu,sukai sallama yana zuba mata godiya ita kuma ta rufawa su Amal baya tana tunanin ƙaryar da za ta yi musu idan sun tambayeta dalilin tsayawa ta sauri guy ɗin.Koda su Meenal ke tambayarta waye ta tsaya magana dashi sai ce musu tayi tambayarta yayi yana neman wata new student,ita ko Amal koda wasa ma bata ɓata bakinta wajen tambaya ba domin shawarmarta kawai ta tasa a gaba tana ci...........✍🏻