MASARAUTAR KAIZUR 45
by @nusybee143
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 45
Shiru Amjad ya yi yana bin Ummu Huzaifa da kallo zuciyarsa na suya,ummu Huzaifa ta cigaba da faɗin
"Ya dace ka san cewa ya fi ka dabara,ba faɗa da hayaniya za ka zauna kana yi don an kashe mana yara ba,wata hanyar ɗaukar fansar za ka nemo,akwai dabaru iri-iri, musamman ma yanzu da ya bar masarautar,na san ko iya haka aka tsaya ka yi masa illa,itama yarinyar ka ɓata mata rai,hakan ya yi,sai ka kuma nemo wata hanyar,amma yanzu tsafi ya kyautu a haƙura da shi hakanan"
Shiru Amjad ya yi ba tare da ya sake magana ba, kafin a hankali ya ce"za mu ɓullo da dabaru,sai mun ga bayan wannan azzalumin Sarkin in sha Allah"
Ummu Huzaifa ta ce "in sha Allah abu Huzaifa"
*DAULAR KAIZUR*
"Sahal!
Muhammad Sahal!!"
Fuska a ɗaure ya ɗago yana kallonta,bata sake magana ba ta dawo kusa da shi ta zauna, sannan ta ce"wai menene matsalar ne?
Kana yawan zama kana tunani?gaba ɗaya ka sake ramewa daga lokacin da ka zo zuwa yau,kwana uku kacal
Ko yanayin wajen nan ne baya yi maka daɗi?haka ne ko ɗana?"
Ƙasa ya yi da kanshi yana girgiza kai,a hankali ya ce"Ummeey don Allah ki daina gaya min wannan sunan!"
Kallonsa ta yi, ta ce"wanne sunan?"
Ya ce"sunan da kike gaya min!"
Bin shi ta yi da kallo na ƴan daƙiku, kafin ta ce"to menene dalilin da ya sa ba ka so?"
Kai tsaye ya ce"bana son tuna wanda ya saka sunan ma,kuma bana son sunan,akwai bambanci mai girma tsakaninsa da sunan da nake amfani da shi a yanzu, Nasrullah"
Munaya ta gyara zama tana kallonshi ta ce"na gane,ka fi son sunan da iyayen rikonka suka saka maka kenan?"
Girgiza kai ya yi,ya ce"iyayen riƙo na sunan da suka saka min ba sunan Musulunci bane,kuma tuntuni ma na daina amfani da shi
Wannan sunan masoyiya ta ce ta saka min shi"
"Budurwar ka?"ta tambaya da mamaki a shimfiɗe akan fuskarta
Kanshi tsaye ya jinjina kai ba tare da ya kalle ta ba
"Yanzu kana nufin ka fi son sunan da budurwa ta saka maka akan wanda mahaifinka ya saka maka?"Nasrullah ya jinjina kai ba tare da ya yi magana ba
Munaya ta jinjina kai ta ce "lallai ma kuwa!
Ko da yake an ce ka rayu a daular kafirai,daga baya ne ka amshi musulunci,na ga alamun har yanzu musuluncin bai gama ratsa ka yadda ya dace ba,baka gama sanin wanene mahaifi a Musulunci ba"
"Ummeey da a ce musulunci bai gama ratsa ni ba da yanzu ba'a maganar wannan sarkin naku a doron ƙasa,da yanzu ya zama tarihi,don da tuni na daɗe da kashe shi"
Da tsananin mamaki fiye da na baya Munaya take kallonsa,bai ankara ba ya ji ta sauke masa mari, sannan cikin ɓacin rai ta fara faɗa "ka san wanene mahaifinka kuwa?
Ko da ace ba shi ya haife ka ba ka samu zarrar da za ka dube ni ka ce za ka iya kashe shi?
Yana farin ciki da alfahari da dawowarka amma kai kana faɗin maganar banza akanshi?
To ina yi maka gargaɗi da Babbar murya, ka san wanene uba a wajenka,ka girmama shi, sannan idan ka sake fadar magana makamanciyar wannan zan saɓa maka Sahal "
"Ki gafarce ni Ummeey,idan magana ta ta yi miki zafi
A gabanki aka ba mu labarin irin rayukan da ya kashe wadanda ba su yi masa laifi mai yawa ba,sam ba su cancanci hukuncin kisa ba, sannan a gabanki aka ba mu labarin cewa an kawo ki ne don ki haifi mai gadon kaizur,ni kuma an haife ni ne don na gaji kaizur
Ba ya sonmu, bai damu da mu ba,na gaji da zaman garin nan, wallahi Ummeey don ke kaɗai nake zaune a nan babu yadda zan yi ne"ya ƙarasa magana cikin ƙunar zuciya
Tun lokacin da sarki Mu'iz ya hana su barin Masarauta,a maimakon su koma cikin Masarautar sai suka gwammace su samu waje, Nasrullah ya haɗa musu bukka,ya kan fita daga gidan ya je ya yi farauta ya kawo musu abinci, duk wata gaisuwa da fadawa da dakaru suke yi masa ko kallon banza ba su ishe shi ba,idan kuwa rawar kai ya kai su tambayar za su ɗaukar masa kaya yana iya kai duka ma
Munaya ta girgiza kai cikin karayar zuciya, ta ce"Sahal!
Ba ka san sarauta bane?kuma ka manta ni baiwa ce?"
Shiru ya yi kawai ba tare da ya yi magana ba,ta janyo shi kusa da ita sosai,bai yi musu ba ya matso,ya ɗaga kai yana kallonta,a hankali murmushi mai sanyi ya ƙwace mata, ta shafi fuskarshi,ya lumshe idanu yana sauraren ta,a hankali ta ce"ba na manta sanda na haife ka,haka nake ta kallon fuskar ka, wadda har zuwa yanzu yanayin girma ne kawai ya sauya akanta,amma kana nan a ɗana, kyakykyawa, wanda nake jinshi a cikin zuciya ta, wanda na zaɓa fiye da rayuwata
Ina alfahari da kai ɗana,kuma ina fata ka zamo nagartacce"murmushi ya yi sosai yana sake kwantar da kanshi a gefen kafaɗarta ta dama,lallai ya yarda da cewa mahaifiya ita ce rayuwar ɗanta
Duk da cewa ba wani jin daɗin inda suke zaune suke yi ba,amma suna cikin matuƙar farin ciki, kasancewar su a tare da juna
A tarihin rayuwar Nasrullah, ko na ce Sahal,babu wata uwa da ta taɓa maye masa gurbin tashi uwar,ko yaya ma ya ji ta a matsayin uwa a gare shi,saɓanin uba, Murad ya ɗauke shi a matsayin ɗa,ga Sarkin yaƙi Ra'uf, mutum na farko a tsawon rayuwarsa da ya bayyana masa rauninsa,shi kuma ya lallashe shi ya ƙara masa ƙarfin gwiwa,ya ja shi a jiki don ya yi masa maganin damuwarsa, wanda ya nuna masa soyayya,ya Kula da shi,a hankali murmushi mai sauti ya ƙwace masa, Munaya ta ɗago shi daga jikinta tana kallon idanunshi,akwai alamun rauni da damuwa a bayan murmushin da yake yi,a hankali ta ce"Muhammad Sahal!
Nice ko?"ya dube ta ya ce"me kika yi min Ummeey?"
Ta ce"na yi maka faɗa mana"kwanciya ya yi sosai kanshi a kan cinyarta, Ummeey ta kama wasa da gashin kansa,ya lumshe idanunshi yana sauraren bugun zuciyarsa,a hankali ya ce"Ummeey ni fa a rayuwa ta babu wanda ya taɓa yi min faɗa irin naki,sai Sarkin yaƙi Ra'uf, lokacin da nake rayuwa a Baruda azabtarwa kawai ita ce tsawatarwar da ake yi min,kin ga har yanzu jikina akwai tabbuna waɗanda suka kwashe shekaru har yanzu ba su ɓace ba"
Munaya ta mayar da hawayenta sannan ta ce"idan na fahimta kana tuna waccan azabtarwar da aka yi maka kana ɗora alhakin hakan akan mahaifin ka ko?"
Sahal ya ce"Ummeey ni fa musulmi ne,na san ƙaddara mai kyau da marar kyau
An horar da ni an azabtar da ni a Baruda,amma a dalilin hakan na zama mayaƙi mai ƙwarewa,hakan ya zamar min alkhairi
An ci mu da yaƙi,an kashe min masoyiya ta, wadda ta zama ita ce sanadin dukkan farin ciki na,amma Allah ya musanya min da waje mafi alkhairi,na samu ninkin abin da na rasa a baya,na samu masoyiya mafi alkhairin ta baya,na samu uban da da ace tun farko hannunsa na faɗa da ban shiga halin da nake ciki ba,amma alhamdulillahi,komai ya yi min yadda ya kamata,ban yi baƙin ciki ba,na rasa wadda nake so saboda rashin asali,shima ban yi baƙin ciki ba,idan rabo na ce Allah ya nuna min ranar da zan mallake ta"
"Cikakken jarumi kamar ɗana dai ya wuce ya karaya saboda mace"Munaya ta faɗa cikin son ganin ta ba shi ƙwarin gwiwa,duk da cewa ya ba ta tausayi sosai
Murmushi ya yi mai sauti,ya lumshe idanu ya buɗe,a hankali ya ce"ita ce ƙwarin gwiwa ta Ummeey,da gaske bana son na rasa ta,amma idan na rasa ta na san haka Allah ya so, musamman ma yanzu da na same ki a lokacin da ban yi tsammani ba Ummeey,ina alfahari da hakan,na godewa Allah "
Munaya ta yi murmushi ta ce"ka same mu dai, tunda mahaifinka yana raye shima" ɗauke kai ya yi yana ɗaure fuska, daidai lokacin suka ji sallama a bakin bukkar tasu
Munaya ce kawai ta amsa,shi kam gyara kwanciyarshi ya yi a jikin mahaifiyar shi,yana ɗauke kai,suka suka rissina a gaban su, ɗaya daga cikin su ne ya ce"ran yariman kaizur ya daɗe,mai martaba ya ce a yi masa kiranka "
Shiru babu niyyar zai amsa ma, Munaya da ta fara tsorata da lamarin ɗan nata ta dube shi ta ce"Sahal abbynka yana kira"
"Ba zan je ba!"ya amsa kai tsaye
"Ba za kaje ba Sahal?ba za ka je ba?
Mahaifinka ya ce yana kiranka ka ce ba za kaje ba?
To wallahi ko ka tafi ko ni na tashi na bar ka,na gwammace na koma ɗakin duhun akan na cigaba da zama ina kallonka kana yiwa mahaifinka rashin ɗa'a
Mantawa kake yi har yanzu ni baiwar mahaifinka ce? saboda kai ya bar ni nake yin abin da na ga dama?
Ka tashi ka je kiran da ake yi maka!!"babu musu ya miƙe jiki a mace, fuska a ɗaure ya fita,dakarun suka biyo bayansa, Munaya ta bi shi da kallo tana fatan wannan karon a samu daidaito tsakanin ɗa da uban
Sahal kuwa yana fita maimakon wajen mahaifinsa sai ya wuce can gefen sashen mahaifin nashi ya zauna yana ɗaure fuska,da dakarun suka fara damunsa da magiya ma sai ya rufe su da duka,tilas suka ƙyale shi
Sai da ya ga dama sannan ya miƙe ya koma bukkar tasu, Munaya ta bi shi da kallon tuhuma,bai ce mata komai ba ya samu waje ya kwanta akan dardumar da ya saƙa musu da hannunsa,kuma suke kwana a kai
*DAULAR TAYAAR*
Yau ce ranar da Yarima Zohran zai fara zuwa don ganin gimbiya Hayat,ita dai gimbiya Hayat ji take yi kamar wadda aka rufe mata ƙofofin walwala da farin cikin ta, ta kasa manta Nasrullah ɗinta,a duk lokacin da ta tuno shi ta kan tafi lambunta,ta zauna a jikin bishiyar da yake yawan zama,ta jingina,ta yi kuka sosai,tana tuna labarin shi da ya ba ta lokacin da yana Baruda,ta so a ce ta inganta rayuwar shi,ta ba shi farin ciki,amma hakan bai yiwu ba, saboda ƙaddara ta riga fata,a yanzu babbar damuwarta ita ce bata san inda Nasrullah ɗinta yake ba,yana lafiya?yana cin abinci?yana da damuwa?yana cikin farin ciki?
Kai babu yadda za'a yi ya kasance cikin farin ciki bayan ba sa tare,take hawaye suka zubo mata sosai,kuka har da shashsheƙa
Jikinta a sanyaye take shiryawa,ji ta yi dama mutuwa ta yi, da ta huta da ganin wannan baƙar ranar,ranar da zata tunkari wani namiji da sunan wanda zata aura,ba Nasrullah ɗinta ba
Huda da take taya ta shiryawa itama dai haka take ji,kusan ma a ce ta fi Hayat jin zafin wannan haɗin,haushi sosai take ji ga duk namijin da ta ji ya ko yaba kyan Hayat ballantana ma har ya tunkare ta da soyayya,ji take yi Nasrullah tamkar ɗan'uwa na jini ne a gare ta
Bayan ta kammala shirya Hayat samun waje ta yi ta zauna tana kallon ta,don ji take yi ba zata iya raka Hayat wajen wani namijin ba Nasrullah ba, ita ma Hayat ɗin bata damu ba,ta miƙe jiki a mace ta fice daga ɗakin,sauran kuyanginta da suke tsaye a bakin ƙofarta suka raka ta har masaukin bakin sarki Iyaad,inda Yarima Zohran yake zaune yana jiran fitowarta
Da sallama ta shiga ɗakin,kanta a ƙasa, Yarima Zohran da yake zaune a kan tsadaddiyar lallausar dardumar da aka malale ɗakin da ita,ya ɗago yana ƙare mata kallo ba tare da ya amsa sallamar ba,itama bata damu ba,ta ƙarasa ciki,ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa
Zaman shiru suka yi na wani ɗan lokaci, kafin yarima Zohran ya katse shirun, cikin muryar izza da nuna iko ya furta
"Ba ki iya gaida mutane bane? musamman waɗanda suka fi ki komai a rayuwa?"
Kallonshi gimbiya Hayat ta yi da mamakin wannan maganar, cikin isa yarima Zohran ya ce"eh!
Na san kin san cewa ina gaba da ke a komai,ko yayanki Nashwaar da yake magajin wannan masarautar kafin ya bar duniya biyayya yake yi wa magana ta
Na san masarautar ku ita ce mafi girma ta huɗu a nahiyar nan,to ya kamata ki san masarautar Kiswa ita ce ta biyu
Sannan ya kamata ki fara daraja ni tun a yanzu,a matsayina na mijin da za ki aura,don kiswa ba ma ɗaukar rainin matanmu, musamman waɗanda suke ji da kansu kamar su ɗin wata tsiya ce, irinki,ina fatan kin gane,kuma za ki kiyaye?"
#Nusy_bee
***