TUHUMA!

Chapter 1

by @mamananalbarkace777

⚖️TUHUMAH.⚖️


🥰 MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️

*Bismillahirrahmanirrahim.*
*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, Allah ina roƙon Ka ka sa yadda na fara rubuta labarin nan lafiya na kammala shi  cikin aminci da ƙoshin lafiya.*

            
           PAGE 1️⃣

Cikin hanzari yake tafiya da kamar zai tashi sama, kyakykyawan matashin saurayine, wanda a ƙalla zai kai shekara ashirin da takwas zuwa da tara. Sanye yake cikin riga da wando na makanike, a kafaɗar shi rataye da wata ƴar jaka duk ta ɓaci da baƙin mai, da alama daga aiki ya taso.

 Sai da na masa kallon tsaf na gano baiwar zallar kyau da cikakkiyar haiba da Ubangiji ya masa. Fatar shi baƙa ce sai dai ba baƙi irin sosai ɗin nan ba, baƙi ne mai kyau irin sheƙin nan.
Kyakykyawar zagayayyiyar fuskar shi ɗauke take da manyan idanuwa  dara-dara, yayin da launin idanun suka kasance farare tas ƙwayar cikin su kuma baƙa siɗik. Yana da zara-zaran gashin ido yadda kuka san na mace, sai kwantacciyar girar shi wadda take a cike har haɗewa ta yi da ƴar uwar ta. Yana da dogon hanci Masha Allah Ƙasan hancin ɗauke yake da ɗan madaidaicin bakin shi wanda kalar laɓɓan suka kasance masu ɗan duhu.
Yana da yalwar sumar kai duk da ya yi aski irin saisayen nan, amma kallo ɗaya za ka wa kan shi ka gane yana da cikar suma sakamakon yadda gashin kan nashi yake a kwance tamkar na Fulani.

Ƙarar horn ɗin da aka danna ne yasa ya ƙara saurin tafiyar shi, Ganin motar tasha gaban shi hakan yasa ya tsaya tare da sa hannu ya dafe goshin shi, ya zubawa motar ido ya jan tsaki yana jin ran shi babu daɗi.

Buɗe murfin motar aka yi wata kyakkyawar mashiyar budurwa ta fito,  a ƙalla zata kai shekara ashirin, fatar ta fara ce irin farin nan mai ɗaukar hankali, sanye take cikin doguwar rigar abaya baƙa, daga gaban rigar an mata kwalliyar golden color, Sam ba ta da jiki irin siririyar nan ce, sai dai tana ɗan cika daga ƙasa.

Yana ganin ta fito ya ja tsaki tare da fara tafiya dan barin wajen, tana ganin haka da  sauri ta sha gaban shi, ta narke fuska tare da haɗa hannayen ta duka biyu alamar roƙo ta ce
"Dan girman Allah Ya Anwar ka tsaya ka saurareni."

Haɗe fuska ya yi babu alamar wasa yace "Bani hanya na wuce." Ganin babu wasa a fuskar shi, hakan yasa ta matsawa ya wuce.

Da sauri ta bishi a baya murya na rawa tace "Ka tsaya mu yi magana dan Allah."

"Banda sauran magana dake Hafsat." Shima ya faɗi hakan, yana daɗa saurin tafiyar shi.

Ganin za su shiga cikin mutane, sai ta yi saurin shan gaban shi ta narke fuska, tare da haɗe hannayen ta biyu alamar roƙo, hakan yasa ya dakata daga tafiyar da yake, ya ɗago ya watsa mata idanun sa dake da wani irin kwarjini cikin dakakkiyar murya yace
"Hafsat ki bani hanya na wuce."
Duk da yanayin nashi ya ɗan tsorata ta, domin ba ta taɓa ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amma sai ta dake ta ƙi bashi hanya. Sai ma ƙara matsowa gaban shi da ta yi ta marairaice ta ce
"Dan Allah ka yi haƙuri Ya Anwar, ka zo ka shiga mota na sauke ka gida, kaga fa mutane har sun fara kallon mu."
Ta ƙarasa maganar muryar ta na rawa kamar za ta yi kuka.

Juyawa ya yi, ya kalli gefen su sai yaga su ɗin ake kallo da gaske, sai ya juyo ya kafe 
Kyakkyawar fuskar da kallo kamar yana nazarin wani abu.

"Ya Anwar na yarda in munje gida ka hukunta ni, amma dan Allah kar ka hukunta ni ta wannan hanyar."

 Ɗaga mata hannu ya yi cikin ɗan sassauta fushin nashi ya yi ƙasa da murya yana kallon bakin titi yace
"Hafsat ba zan shiga motar ki ba, kuma hakan ba yana nufin hukuncin ki ba kenan, ki wuce ki yi tafiyar ki dan Allah, duk wata magana na gama ta tuni, nace ki fita a rayuwata ko ana  dole ne.?"
Ya ƙarasa maganar muryar shi na fita da ɗan ƙarfi, da alamun gajiyawa sosai a tare da shi.

Gaba ɗaya jikin Hafsat ya yi  wani irin sanyi, har ya wuce ta gaban ta, bata san lokacin da ya wuce ba.  Juyawa tayi tare da zubawa bayan shi ido, a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro akan kumatun ta.
Magana ta fara da kanta a fili
"Me yasa Ya Anwar ya canja min lokaci guda? Na shiga ukuna ni Hafsat."

Bata ankara ba taji ana danna ma ta horn da tashin hayaniyar mutane, sai lokacin hankalin ta ya dawo jikin ta, ta kalli inda ta aje motar taga ta tsaya ne a tsakiyar hanya, cikin hanzari ta ƙarasa wajen motar ta, cikin ladabi ta kalli mutanen dake jiran ta ɗauke motar su wuce tace "Dan Allah ku yi haƙuri."

"Ba komai." Ita ce kalmar mutumin daya ɗan leƙo daga cikin motar shi ya faɗa.
Wani matashin saurayi dake kan mashin ne ya taso mata cikin faɗa yace "Kin ga Dallah Malama ki shiga ki matsar mana da gwangwanin ki a hanya mu wuce, kin wani tsaya kina mana iyayi da bamu haƙurin munafurci, komai ku ƴaƴan masu kuɗin nan sai kun nunawa talaka kun fishi."

Bata saurari hayaniyar shi ba, ta shiga motar tana jin zuciyar ta duk babu daɗi, tana tafiya tana tunanin abinda ya faru, bata san lokacin da hawaye ya fara zubo mata ba.

Ji ta yi ba zata iya tuƙin ba, dan haka ta gangara da motar bakin hanya ta kife kanta a jikin sitiyarin motar, nan wani ƙaƙƙarfan kuka ya kubce mata, ta daɗe a haka bata ɗago ba, ganin kukan ba mafita bace ita da kanta ta lallashi kanta  ta yi shiru.

Sai dai ba ta jin za ta iya zuwa inda tayi niya, dan haka ta karya kan motar ta ta dan komawa gida, tana tafiya tana duba hanya kamar mai neman wani abu, a haka har ta isa unguwar su.

Unguwa ce irin ta manyan masu kuɗi, wasu irin manyan gidaje ne zagaye da unguwar, sai dai wasu sun fi wasu tsaruwa da kyau.
Kai tsaye ta nufi wani tamfatsetsen gida wanda gaba ɗaya yafi sauran girma da haɗuwa, kallo ɗaya zaka wa gidan kasan lallai mai shi ba ƙaramar dukiya ya tara ba.

Danna horn ta yi, nan da nan mai gadin gidan ya wangame Ƙofar, tana shirin danna hancin motar ciki ta hango wani adaidai ya shigo unguwar ta madubin motar ta. 

Fasa shiga ta yi ta jawo motar baya, mai gadi na gaishe ta ko amsawa ba ta yi ba, cikin hanzari ta fito ta tsaya jikin motar idanun ta akan adaidatan, sai ga Anwar ya fito yana gyara zaman jakar kayan aikin shi dake kafaɗar shi, ya zura hannu a aljihun wandon shi tare da zaro kuɗi ya miƙawa me adaidaitan, yana bashi chanji  ya  nufi wani ɗan ƙaramin gida dake jikin gidan su Hafsat.

In ba ka lura sosai ba, ba za ka san akwai gida a wajen ba, sakamakon yadda ginin wannan babban gidan ya cinye gaban gidan baki ɗaya,  ko katangar shi ba'a gani sosai, sai ƴar ƙofar da zata nuna maka alamar akwai gida a wajen.

Tunda Anwar ya sauka a mashin ya lura da Hafsat tsaye, hakan yasa ya haɗe fuskar shi kamar  bai gan ta ba, kai tsaye ya nufi gidan.

Ganin abin da ya yi na share ta, sai ta ji babu daɗi a ranta baki ɗaya, ita canjawar ta shi  ba ƙaramin  mamaki ya bata ba, dan ba haka ya saba mu'amalantar ta ba.

Yana shirin tura Ƙyauren ya ji Muryar ta "Ya Anwar sannu da zuwa."

Juyowa ya yi ya kalle ta sai ya ji ta ɗan bashi tausayi, gyaɗa mata kai ya yi kawai, ya tura ƙofar zai shiga.

"Am Ya.." maganar tace ta yanke ganin irin kallon da ya watsa mata,  ya ja tsaki ya tura ƙofar ya shige ya barta tsaye tana jin wani irin zafi a zuciyar ta.

Ya daɗe a tsaye tana kallon ƙofar da ya shiga, jiki a sanyaye ta juya ta nufi motar ta ta shigar da ita cikin gidan, da ƙyar ta amsa gaisuwar da Baba mai gadi ke mata, kai tsaye ta nufi Ainahin ƙofar da zata kaita cikin gudan.

A tsakar gida ya tarda mahaifiyar shi zaune a ƴar rumfar dake ƙofar ɗakin ta, kan cinyar ta faranti ne ɗauke da wake tana tsincewa, kallo ɗaya zaka wa matar ka hango zallar kamannin da take da Anwar, sai dai ita fatar ta fara ce, kuma bata da jiki sosai.

 Tana ganin shi ta saki murmishi tana faɗin "A'a mai babban suna an dawo kenan?."

Ƙoƙarin maye fuskar shi ya yi da murmishi yace "Na dawo Inna, ya gida ya ranar nan?." Ya ƙarasa faɗin hakan tare da zama kusa da ita kan tabarmar yana faɗin "Wash Allah Inna na gaji da yawa yau."

Kallon shi ta yi cike da tausayin ɗan nata tace "Yau ma a ƙafa ka dawo kenan?."

Girgiza mata kai ya yi yace "A'a Inna yau ba'a ƙafa na dawo ba, kin san kafin Baba ya fita ya bani Ɗari uku yace na karya, to cikin ikon Allah yau na samu wani ɗan gyara na taɓa, Allah yasa ogan mu yace na riƙe duka, to awarar ɗari biyu na siya pure water na hamsin, Kinga sauran hamsin ga dubu ɗayan aikin, kin ga sun kama dubu ɗaya da hamsin kenan, sai nayi dubara na ɗan rage tafiya a ƙafa zuwa gidan mai, daga nan na samu mai mashin na hau ya ƙaraso dani a ɗari biyu." Yasa hannu a aljihun sa ya fiddo da naira ɗari takwas da hamsin ɗin da ta rage ya miƙawa Mahaifiyar tashi yace "Ungo sauran canjin  Inna, naga shinkafa za ki mana sai ki ƙara ki sai mana salad."

Murmushi Inna tayi, ta kalli hannun shi da yake miƙa mata kuɗin ta girgiza kai tace "Haba Anwar, kai da baka ci komai, kuma ka yi wahala ga tafiya aiki gobe, ka riƙe za su maka amfani in salad ɗin ka ke so  ina da wani canji sai a siya."

Miƙa mata ya ƙara yi, fuskar shi ɗauke da murmushi yace "Allah Inna ki amsa babu abinda zan siya yanzu."

Ganin ya dage akan sai ta amsa hakan yasa ta miƙa hannu ta amsa, Naira ɗari ta zare ta miƙa masa sauran tace "Allah yasa albarka, wannan ma ya isa."
Da "Amen." Ya amsa, yana jin daɗin addu'ar ta gare shi.

Nan ta tashi tace "Bari na zubo maka sauran ɗumamen tuwon,  kamar nasan ba zaka dawo da yunwa  na ajiye maka."

Dariya ya ɗan yi yace "Innata kenan, Allah dai ya ƙara Miki lafiya da tsawon kwana mai amfani.

Amsawa ta yi da "Amen ɗan albarka." Ta shiga wani ɗan ƙaramin kitchen, ta fito hannun ta ɗauke da kwanon tuwon ta ajiye a gaban shi, ta koma ta zauna ta cigaba da tsintar waken.

Wanke hannun shi ya yi 
ya fara ci, yana kallon mahaifiyar tashi wani daɗi na ratsa zuciyar shi, a duk lokacin da ya kasance da iyayen na shi ya kan tsinci kanshi cikin farin ciki, sakamakon yadda suke nuna masa kulawa da ƙauna, kullum burin su suga ya samu farin ciki, shi yasa ya ke addu'a da fatan watarana Allah ya azurta shi, shima ya faranta musu kamar yadda suke mi shi.

Yana gama cin tuwon, ya wanke hannun shi ya matsa kusa da Inna, yasa hannu a farantin waken dan ya taya ta tsincewa.
 
Kallon shi ta yi tace "Ba wanka ya kamata ka fara ba?."

Girgiza kai ya yi yace "Inna bari mu gama sannan."
Gyaɗa kai ta yi, dan ta san ko tace ya bari ba bari zai yi ba, haka Anwar ya ke, baya taɓa kallon kan shi a matsayin namiji in dai zai ga Innar shi na aiki, zagewa yake ya ke ya taya ta  iya ƙarfin sa, babu kalar aikin da bai iya ba na gida.

Suna tsintar waken suna taɓa hira fuskar su cike da farin ciki, baki ɗaya ya ma manta abinda ya faru tsakanin sa da Hafsat.

-----

   *HAFSAT.*

Ganin ta shiga ƙaramin farlo bata ta Mom ɗin ta ba, kai tsaye ta nufi babban farlo tana tafiya a kamar zata faɗi.

Bakin ta ɗauke da sallama ta shiga tare da jefa ƙaramar jakar ta a kan kujera, tayi wurgi da ɗankwalin abayar tare da zaunawa daɓar a ƙasa tasa hannu ta dafe kanta.

Matar dake tsaye a wajen Dining table tana jera abinci, ta ɗago ta kalle ta tace "Baby lafiya ki ka shigo ki ka zauna anan?."

Ɗagowa ta yi ta kalli matar, fara ce ita ma sosai tana da jiki,  basa  kama da Hafsat  sai dai in ka kalle ta sosai za kaga kama ta jini, sanye take da doguwar rigar atamfa ta caɓa ado kamar wadda ke shirin zuwa biki, wuyan ta sanye ya ke da sarƙa ga wanda ya san gold yana gani zai gane sarƙar gold ce, haka hannayen ta suma sun sha awarwaron gold sai baza ƙamshi take.

Ganin Hafsat ta yi shiru tana kallon ta, hakan yasa ta ajiye filet ɗin hannun ta, ta tako ta ƙaraso wajen Hafsat ɗin ta tsugunna gaban ta tare da dafa kafaɗar ta tace "Wai Baby me ke damun ki ne? Ko dai wani ne ya ɓata Miki rai a makarantar?."

Girgiza kai Hafsat ta yi ta kalli matar idanun ta cike da hawaye tace "Babu komai Mom kaina ne kawai yake min ciwo." Ta ƙarasa maganar tare da dafe kan nata.

Cikin nazari matar ke kallon ta tace "Anya kuwa Hafsat?." 
Narke fuska ta yi tare da gyaɗa kai kamar za ta yi kuka.

Taɓe baki Mom ɗin ta yi tace " Akwai wani abu dai da ya faru, dan ban san ki da yiwa ciwon kai kuka ba."

Rau-rau ta yi da ido tace "Mom ki yarda dani, kaina ne ke ciwo fa." Ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.

Kama hannun ta tayi ta miƙar da ita tsaye tace "Ai sai ki wuce mu je ki rage kayan jikin ki, ki yi wanka ki zo ki ci abinci ki sha magani ki huta."

Ba dan taso ba tabi mahaifiyar tata, wani haɗaɗɗen bedroom suka shiga,  Ya Allah bedroom ɗin ya tsaru iya tsaruwa komai na cikin sa pink da fari ne, ga wani ni'imtaccen ƙamshi dake tashi, ko mai a tsare gwanin burgewa.

Kai tsaye ta wuce da ita toilet, faɗar haɗuwar toilet ɗin ma ɓata baki ne, ruwan wanka ta haɗa mata da kanta ta, sannan ta saki hannun ta ta kalle tace "Ki yi wanka sai ki fito kici abincin ina jiran ki?."
Tana gama faɗin hakan ta fito tare da jawo mata ƙofar.

 Wadrobe ɗin Hafsat ta buɗe, ta zaɓo mata ƙananan kaya marasa nauyi ta ajiye a gefen gadon, sannan ta fita daga ɗakin ta je ta cigaba da gudanar da sauran ayyukan ta.

Ta daɗe a toilet ɗin tana zuba ruwa a jikin ta, a hankali kalmomin da Anwar ya faɗa mata su ke dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta kamar yanzu yake faɗa mata su, da ƙyar ta yaƙi zuciyar ta tayi wankan tare da ɗauro towel ta fito.

Shiryawa tayi cikin kayan da ta tarda Mom ta fiddo mata, dan  ta riga data saba in dai ta shiga wanka Mom ɗin ta tana nan to ita zata zaɓar mata  kayan da zata saka, sai dai in ta tafi aiki ko kuma tana ɓangaren Dady.

Madadin ta fita kamar yadda Mom tace, sai ta haye kan luntsumemen gadon ta wanda yaji shimfid'u na alfarma, ta ƙudundune a cikin lallausan bargon ta tare da faɗawa duniyar tunanina.

Sai da ya kai lomar abincin da ya ɗebo a cokali, ya kalli ɗayar kujerar dake gefe, ya juya ya kalli matar ta shi tare da ɗage girar shi ɗaya alamar tambaya?.

Girgiza masa kai ta yi tare da nuna masa ƙofar bedroom ɗin Hafsat.
Haɗiye abincin daya zuba a bakin sa ya yi yace "Wai kina nufin ta dawo taƙi fitowa?." 

Sai da ta ɓalle murfin ruwan  gorar ruwan dake gaban ta, ta shiga tsiyayawa a kofi sannan tace "Wataƙil ta gama wankan, ina tunanin halin nata ne ya motsa na shegen zurfin ciki, dan ta min sallama akan zata je School tana fita babu jimawa ta dawo, har hawaye naga tana yi na mata tambayar duniyar nan taƙi bani amsa, ƙarshe tace kanta ke ciwo."

Dakatawa ya yi da cin abincin ya ajiye cokalin hannun shi, nan da nan yanayin fuskar shi ya canja, ran shi a ɓace yace "Yanzu Zainab dan tsabar rashin kulawa irin ta ki, ace yarinya ta dawo tana kuka tace kanta na ciwo, har ta kasa zuwa makaranta, ki kasa tsayawa ki ji me ye matsalar ta har ma kina faɗa min halin ta ne ya motsa?." Ya ƙarasa faɗar hakan cikin ɗan ɗaga murya.

Kallon shi take ganin yadda ya dage yana faɗa, daga cewa ta dawo tana hawaye, sai ta girgiza kai tace "Ya ka ke so na yi da ita Alhaji? A Iya tunanina Hafsat ba yarinya bace da zan ta lallaɓa ta.

Wani irin zabura ya yi ya miƙe, tare da jan dogon tsaki  ya nufi hanyar ɗakin Hafsat.

Ita ma Mom miƙewa ta yi tana jin takaicin halin mijin nata, ganin yadda ya ruɗe daga ji ance Hafsat na ciwon kai, duk da ta saba da halin shi na nuna tsantsar soyayyar shi ga Hafsat ɗin, amma wani lokacin in ya yi wani abu yana bata haushi sosai, a gaban kowa baya ɓoye yadda ya ke ƙaunar Hafsat,  wani lokacin in ya aikata wani abin sai ta godewa Allah da ta kasance ita ce mahaifiyar Hafsat,  da ace ba ita ta haifi Hafsat ba, tsaf zai iya cewa tana zaluntar ta ko watara ya sake ta sanadin Hafsat ɗin.

Bin bayan shi bedroom ɗin ta yi, zaune ta tarda shi a bakin gadon Hafsat ɗin yana lallashin ta akan ta tashi zaune taƙi, sai ma ƙara ƙudundunewa da take cikin bargo, miƙa hannu Dadyn yayi cikin lallashi yace "Babyn Dadynta taso mu ji me ye matsalar waye ya taɓa min ke?."

Da ƙyar Hafsat ta yunƙura ta tashi tana yatsina fuska,  cikin shagwaɓa ta matsa kusa da Dadyn nata tare da kwantar da kanta a kafaɗar shi ta kyaɓe baki tace "Dady kaina ke min ciwo."

Hannu yasa yana ɗan shafa kanta alamar lallashi yace "Ki daure ki tashi ki fito kici abinci, zan kira Dr Sapwan yanzu zai zo ya duba min ke."

Maƙale kafaɗa ta yi cike da shagwaɓa tace "Ni a'a Dady ba sai ya zo ba, nasan zan samu sauƙi ka ji."

Kallon ta ya yi cikin lallashi yace "Baby da kin bari ya zo sai ya duba min ke."

"Um um Dady ka barshi." Ta faɗi hakan tare da zame jikin ta ta miƙe tsaye tana tangaɗi kamar zata faɗi tace"Ai ciwon kan ma ya yi sauƙi kaga na tashi, mu je zan ci abincin."

Da sauri ta ya riƙo ta yana faɗin "Bi a hankali kar ki faɗi mana."

Mom da ta zama ƴar kallo ganin Hafsat ta tashi, hakan yasa ta juya ta nufi ƙofar fita  tana faɗin "Ke dai ki ka sani, yarinya sai shegen iyayin tsiya."

Dady dake riƙe da hannun Hafsat, jin abinda da Mom ta faɗa yasa ya hasala ya ɗan ɗaga Muryar shi dan ta ji yace "Ke kam Zainab ba ki ji daɗin halin ki ba wallahi, yarinya na fama da ciwo baki tausaya mata ba kina neman takura mata."

Banza Mom tayi da shi, ta ƙarasa ta zauna kan kujerar ta ta jawo flet ɗin abincin ta ta hau ci, tana kallon Dady da Hafsat ta gefen ido, sai faman lallaɓa Hafsat ya ke akan taci abincin, har ɗiba ya ke yana bata a baki tana amsa da ƙyar yana miƙa mata ruwa tana sha kamar wata ƴar ya ye.


🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️

***