🧑‍🍼 RABO...❣️

16

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode seventeent

   Cikin farin ciki Omar ya koma gida tun kan ya shiga wanka ya shaida ma Lisa ta kaima sa abincin sa dakin Ammi bayan ya kammala komai ya wuce part din ta yana cin abinci yana tunani akan plans dinsa dayake tsara wa kamar wanda aka tsikara ya mike yaje gurin wardrobe dinta yasoma bincike a ciki yana kara shirya kayan ciki yana jawo wani doguwan abayan ta yaji faduwan abu kasa se bebi takan shiba seda ya gama binciken sa tukunna harya rufe wardrobe din yaga dan mitsilin kit din daya fado kyan da yayi masane yaja hankalin sa harya bude shi, fuskan sa taff da mamaki ya karasa karanta invitation din da letter da aka kawo wa Ammi tashi shiru yadan yi na wani lokaci yana tunani, se ya maida ta ya rufe ya cigaba da binciken da yakeyi seda ya duba drawer din mirror dinta yaci karo da keys din daddy dinsa dayake nema sauke ajiyan zuciya kawai yay ya mike ya dauki dan kit din ya fito sauri yaketa yi harya isa dakin sa ya dauko akwatun daddy din nashi yana saka mukullin nata ta bude cikin azarbabi ya daga murfin yay cin karo da kyakkyawan littafin da aka ajiye ciki seda ya kare masa kallo tukunna  yasa hannu biyu ya dauko shi Koba a fada ba kasan abu me mahimmanci ne cikin wan nan littafin, zaman dirshan yay a gurin yasoma budewa shafi yana karanta wa_

                  ABUJA

Zaune suke a parlour Maya da wata sabuwar makociya ta datayi me kirki tana yawan shigowa Maya  asha shafta don kuwa 'yar drama ce Farida ta iya zama da mutane sosai, Maya ganin kusan halin su iri daya ne dana Farida shiyasa take son ta sosai cikin gajeren lokaci suka shaku matuka har salma najin ta kamar 'yar uwar ta ta jini, har gidan ta take zuwa itama abinda Maya batayi wa mutan unguwa ita kadai take rayuwar ta saboda dagawa amma sega Farida tazo cikin dan lokaci sun saba dukda itace da fari take yawan yinin mata a gida kasance war mijin ta se dare yake dawowa, to duk wani wanda ze zauna da Maya seya fahimci irin son da takewa autar ta baby da irin tabarar datake yi da sangar ta fitina iri iri sabanin nawal datake a nutse komi nata shiyasa Farida mutuniyar tace nawal_ 

   Omar Kano na zaune yana karatu sallah kawai ke tadashi daya dawo ze dora da ga inda ya tsaya harseda ya raba dare tukunna tausayin mahaifin nashi ya gama kamashi da Ammi duka tarihin rayuwar iyayen nashi yana ciki Daddy dinsa ya rubuta shi har kawo karshen rubutun sa na cikar burin sa Ammi ta soshi a zuciyan ta ta furta masa kalmar so, kuma bega hakan a rubuce ba yasan Ammi bata cika masa burin nashi ba, ya kuma kara tabbatar da lallai so masifa ne! Sosai yake jin babu dadi cikin zuciyan sa cikin wani irin yanayi yace " Ammi meyasa masoyin ki zeyi miki haka? Duka saboda shi kika wahala haka tabbas bazan kyale mutumin nan bah dole zuwa Abuja ya kamani sena bi miki hakkin ki Ammi in Sha ALLAH sena dawo miki da martabar ki"

  Bayan kwana biyu dasuka gabata ya gama duka wani bincike dayake akan Omar Abuja sam baya bari Esmaeel yasan abinda yake yi ko tafiyan dazeyi a yau babu wanda yasani se aminin nashi Farid dazasu tafi tare ta jirgi da guards dinsa biyu, wanda ya tura suna musa aiki kuwa yasa sun rigada sun tanada musu komai hatta hotel room din daze sauka an tanaje shi 2 da 'yan mintuna kuwa jirgin su ya sauka, se basu wuce hotel dinba suka wuce company Omar Abuja hakan yasashi yin mamaki sosai ganin bakon nashi dayay, dakin tattauna wa na mussam man suka zauna yana ta kallon Omar kano donya ganeshi, 

   " Nayi mamaki dajin labarin kafa" 

Omar Kano ya masa maganar yana kallon sa, shima cikin kallon sa yake na rashin fahimta yace " na aikata wani abu ne a labarin nawa dakaji?" 

  " Sosai kuwa, wan nan dalilin ne ya kawo ni gurin ka domin jin gamsas sar amsa" shiru ya masa nadan lokaci tukunna yace " to ina sauraren ka" 

  " Har idan wan nan soyayyar taku gaskiya ce meyasa zakayi wa mahaifiya ta haka? Kaci mata zarafi gaban kowa nata meyasa zakayi wan nan butulcin kaikuwa? Har gida ashe ka tura mata da invitation tazo domin ka karshe kayi mata wan nan  sakayyar meyasa zaka cutar min da ita haka dayawa?bayan duka irin kaunar da take maka harda sakamin sunan ka!" 

  Hawaye sosai Omar ya fara yana juya kai nan take yana yinsa ya sauya haryana dafe kansa daya ke sara masa kamar yay kuka yace " i don't know wlh sam banajin dadin rayuwa ta yanzu, bana iya tunani akan maman ka kullum cikin mafarkin ta nake sedai da zarar na farka ina kuma manta komai ne hakika nasan Tabbas banida lpy naji asibiti har sau babu adadi ana cemin jini nane ya hau, abin ya isheni ya dameni kullum mutane na se anzo min da vidio din nan ana tambaya ta taya haka ya kasance harna gaji don bansan amsar dazan bawa mutane, kamar yadda kaima banida amsar baka akan tambayar ka" 

  " Shin ina maganar abokin ka ta tsaya kun sameshi ko ana kan bincike har yanzu? Idan kun gaza yin nasara zan hada da nawa ma aikatan anemo shi, nayi rantsuwa akan duk wanda ke da sa hannu a abin nan bazan bar shiba" 

  " Wani abokin nawa kake maganar ne?" 

  Zuwa yanzu mamaki ya hana Omar kano magana kallon sa kawai yakeyi na dan lokaci san nan yace " Abokin ka dakace yayi wan nan vidio din" 

   " Omar duka wani abu Dana furta a gidan ku kalaman matata ne Maya, itace ta sakani badon zuciya ta na kauna ba nayi wan nan magan ganun babu yadda zan iya da masifan Maya ayanzu lamuran ta na neman fin karfi na, Esmaeel yayi fama dani harya gaji numbers dina ma yanzu yayi blocking dinsu saboda naki gaya masa wanda yayi wan nan vidio din kuma ni ban saniba banida amsar dazan bawa koni kaina bare ku" 

   Mamaki ya ishe Omar Kano ayanzu kuma yaji abinda yakeso tabbas Maya ta cika azzaluma shi kansa mijin nata bata bariba don kada ya dauki mataki, aikuwa Maya zakiyi nadama, katse masa tunani Omar Abuja yay da cewa " kaima zaka tafi da zafina a zuciyan ka Koh? Banida yadda zanyi ni kaina abin yana min ciwo" ya karashe maganar yana dafe kansa da a yanzu yakejin kamar yana rinjayen sa ya masa nauyi " So matar ka kenan tasan komai idan hakane dan gane da wan nan abin daya faru?" 

  " Zata yiwu ta sani din Maya tanada kishi Sosai tanada zafin kishi" 

" Sam banga kai abin ya dameka bama, bayan a yanzu mahaifia ta tana tsakanin mutuwa da rayuwa koyaushe Allah ze iyayin ikon sa akan ta, batasan me rayuwar duniyar nan take cewa ba" 

  Salati Omar Abuja ya fara yana danne saitin zuciyan sa daga karshe ma maganar ya gagare shi seda kyar ya iya furta "Meya sameta?" Daga haka ya tafi ya sulale kasa sumamme, Omar Kano ya harde kafa kawai yana kallon ikon Allah kafin kuma ya mike yaje ya samu sakataren sa ya shaida masa ya kira wo Dr dinsa yazo ya dubashi a sirrin ce kada ya bari kowa yasani, cikin hanzari kuwa ya kwala wa Dr waya, shi kuma ya koma ciki yasoma shafa masa ruwa har Dr din ya iso be farfa doba, sedai suka kamashi sukai maida dakin hutun sa ya fito ya basu guri, tunani yake kala kala Omar har Dr din ya fito ya masa sallama ya tafi, seda ya kara kusan 5 minutes tukunna ya shiga dakin ya tsaya yana masa kallon Head to toe sam yarasa mutum min nan meze nuna wa daddy harda Ammi take masa irin wan nan kauna, gani yay kamar idonsa na masa gizo dayaga bakin sa na motsawa karasawa yayi yaje ya kara kunnen sa saitin bakin sa ga mamakin sa yaji Zainab yake ambato ashe harda ware yatsun hannun sa kamar me shirin rike wani abu, tabe baki Omar Kano yay ya mike yana cewa " kai soyayya wahala ce wlh ina zan iya wan nan wahalar" ficewa yay abinsa ya shaida ma sakataran nashi idan ya farka ya shaida masa ze dawo, 

    Suna tafe yana bawa Farid duka labarin abinda ya faru wanda yasa yay mamaki sosai kafin yace wani abune ya katse shi da cewa " Farid komai yazo karshe fah! Nama Joseph sako nasanar masa aikin daga yau ya kare duk wani bayani da suka gama hadawa su kawo min shi yau, just kasa ido kaga yadda zamu kare da matar nan kwakkwaran hujja kawai nake tsumayi yanzu, shikuwa in Sha ALLAH sena nema masa me magani kafin na bar garin nan yana wahala dayawa"

  " ALLAH ya bamu sa ah " shine kawai abinda Farid yace suka cigaba da tafiya har hotel din saboda gajiya basu nemi abinci ba daga wanka suka kwanta duk da magrib na kara towa_

  Rurin da wayar Farid ta farane ya farkar da su a nannauyen baccin da ya dauke su wayar na saitin Omar yana dauko ta yaga babe hakan yasa shi sakin mugun tsaki ya cilla masa wayar ya shige bathroom, har seda ya fito ne Farid ya aje wayar da yake ya dauro alwala sukayi sallan magrib din tare don time dinta ya riga ya wuce, suna idar wa Farid yafita nemomusu abin sawa a bakin salati dukda ga securities bebi takan suba, seda sukayi nak ne ya koma kan sofa Omar yana wani lumshe eyes dinsa sosai yakejin kasala baccin magrib nan da yayi zuciyan sa a cunkushe yace 

  " Farid kira Joseph muji what time zasuzo ne"  

  Dariya Farid yay gami da cewa " mutumi na yadai? Kaketa lafema sofa haka" shiru ya masa Omar donya fahimta iskan ci Farid keson yi masa, yalai kuwa seya koma kusa dashi yana cewa " Haba big man yanzu meye amfanin zaman kadai ci? Duk da kanada mata ko budurwa ayda hakan be faruba, to kai kullum cikin hadewa 'yan mata  fuska kake kai kullum kayita zama empty kaida sifili a yanzu banga marabar kuba indai akan matane" 

  Slowly ya bude idanun sa yana watsa wa Farid harara yana cewa " wai kai ancema kowa ma mayen mata ne irin ka? Konace ma wani abu ke damuna, kullum zancen ka mata mata! Haba do ALLAH dan karami dani kana irin wan nan maganar tayama zan hadama kaina tension" 

  " Lallai iskancin kafa kara yawa yake Omar! You mean kayi kan kan ta da soyayya kome? Nakasa fahimta" 

" Haba Farid meyasa kafiya yawan surutu ne? Kuma mara amfani taya zaka hadani da kanka kana 23years ni kuma 20 nifa wataran iskancin ka girma ta yakeyi tayama zaka hadani dakai, kaje can kayi kaida kaga zaka iya" galala Farid yake kallon sa da manyan idanun sa harya kare zancen sa tukunna sam be sauke hannun sa ako inaba Farid se kan madam joy din Omar yana cewa " let me see" waro idanun sa waje yay jin abinda Farid ke shirin yi masa  gashi dama sedan boxes a tare dashi kawai ya birkita ya dire akan sofa din ya koma kan bed, Farid sosai yake dariya yana nuna shi, yana cewa " dan rainin wayau daka bari naga inda yarintar taka take ai, ko aure mukayi maka wlh tsaf seka shiga..... pillow din daya bugo masa ne a fuska yasashi yin shiru yana cigaba da dariya harda kwanta wa kan sofa din, seda yay me isarsa tukunna ya dago yana cigaba da kallon sa yace " Wlh zanta Addu'ah Allah hadaka da rigimam miyar matar da zakuna cakusa wa don kai ka auri mace me hakuri Omar cutar ta zakayi" 

   Murmushi ne kawai ya subuce wa Omar yana kara jinjina iskancin Farid, magana ze kumayi ya katse shi da cewa  " kiramin Joseph " 

   Karfe 8 da wani abu duka suka hallara a parlour harda makociyan Maya, Omar ita ya fara yiwa magana ma yace " madam Farida ina fata dai kinyi nasara kamar ko yaushe?" Lallau san murmushi tasaki gami da cewa " OGA umaru munekeda nasara kam in Sha ALLAH don nariga na sami abinda mukeda bukata, mikewa kawai tayi da laptop dinta ta aje kan senter table yadda kowa zega abin zata yi ta kunna vidio din datayi wa Maya nan danan muryan nata kuwa yacika dakin saboda shewar datayi tana cewa  " Haba Farida ina ganin ki kamar wayay ya, to ki zauna miji yana daga miki hankali kullum, ki kalli yadda kika rame fah kinsa damuwan da namiji a ranki" 

  Cikin kuka Farida tace " to ya kikeso nayi Maya? Lamarin lateef yanzu haryasoma girma ta na gaji gaskiya tattara wa zanyi na koma garin mu bakin ciki seya kashe ni kullum cikin kuka nake saboda irin rawar jikin dayake yi akan ta, ashe ma wai tsohuwar budurwar sace mijin ya saketa aure kuma yace babu fashi harya kai kudin auren ma, wlh duka na tsani komai Maya tausayin rayuwa ta nakeyi ganin sakayyar da lateef ke shirin yimin" 

Ba karamin tausayi tabawa Maya ba ganin yadda taketa kuka da sharce majina, hannun ta tariko cike da tausayin aminiyar tata tace " kwantar da hankalin ki Farida nasan irin zafin da kikeji yanzu domin kuwa nima ban juma da shiga irin matsalan nan naki ba ni mijina ma har dukana yay saboda budurwar sa"    " HASBINALLAH WA NI'IMAL WAKIL!! Maya ashe kema kinji irin abinda nakeji kema kin shiga wan nan halin! Don girman Allah ki temaka min ya zanyi ne Nima? Ya kikayi da wan nan tashin hankali?" Murmushi kawai Maya ta saki na mugun ta taciga ba da cewa "  amma dana tashi tsaye nayi maganin abin a yanzu mijina be isa yayi maganar koda wata mahaluki ya agaba naba ko ance yayi baze iyaba ko a inane ma kuwa se abinda nace, ita mijin ta mutuwa ma yayi budurwar tashi takeson dawowa kansa har gida naje na mata kashedi takiji ina gaya miki da birthday dinsa taron da mukayi ya tura mata da invitation duk besan kar nake kallon saba nasaka ana bibiyar sa duk inda yake, nayi sa ah kuwa shegiyan matar nan tazo garin nan yaje harda kama mata hotel don neman gindin zama! Ke sekinga matar ma kamar aljana don kyau hankali nah in yayi dubu ya tashi!" 

   " INNA LILLAHI!! Maya ya kikaji kekuwa! A hotel fa kikace!" 

   " Tsaya mana Farida ina kaiki, ke kuma, ai dana fisu iskancin kawata na tura gurin ta Zainab din, harda abincin da muka shirya la fiyay ye muka saka masa maganin tada sha awa har basan adadin maganin bah har juice din seda nasaka aka kaiwa mayya dake inji mijina akace tass ta lasheshi ta cinye, da da autata yaso yakoma na hana kada taje tai mugun gamo ilai kuwa almurar yana zuwa tasoma kai masa hari harda kwabe kaya tana masa magiya taji azaba!! Cikin dariyar mugun ta Maya harda buga kafa " in banda Allah yasa mijina nada tsoron Allah da tuni ta rinjaye shi da tsinan nan jikin nan nata Allah ya temaketa yay waya aka kawo masa allurai ya narka mata ya samo ya taho gida, kawayata na dakin tanata musu vidio da hutuna basu saniba, aka watsa hotunan a duniya har gidan surakan ta seda aka kai musu vidio din nan nata jama a anata zuwa yimin jaje ana tsine mata harta mutu bazata manta wan nan ba kuma nayi warning din ta bazata kara gegar mijina ba kota bibiye shi a banza donna gama shanye abuna nini kadai dagani seshi hanka lina a kwance yake yanzu, don haka kema zan temake ki Saboda amintar dake tsakanin mu ina sonki Farida shiyasa bana shakkar gaya miki duka Wani sirri nah don haka dena kuka ni nan zan miki maganin damuwan ki" 

   Hannun ta Farida ta riko cikin jin dadi take zabgawa maya godiya cikin zuciyan ta kuwa tsinkewa mata kawai take tana kara sallama wa wan nan bakin hali nata, da haka tayi mata sallama ta bargidan,  sosai Omar kano yake hawaye donya jike tissue din dake hannu sa idanun sa yay jajur tausayin mahaifiyar tasa na kara bimasa jiki haka Farid shima, sam gaba dayan su makircin Maya ya basu mamaki bayan vidio din ya kare shiru dakin sa dauka na wasu lokuta san Omar din yace

   " Madam Farida kinyi min abinda bazan taba mantawa dashi ba a rayuwa ta ina gode miki da wan nan kwakkwaran sheda da kika kawo min in Sha ALLAH mutum ci Ammi ze dawo a idanun jama a koba duka, yadda kika temakeni haka nima zan miki kyauta taban mamaki" seda ya sallami wanda yake matsayin me gadin gidan na farida wato Joseph da wanda yake matsayin mijin Farida duka jami an sirri ne, bayan fitar sune yake cewa Farida " Maya matar aure ce kuma ba yarinya ba ina tunanin hanyar dazan bi na nuna mata nata kuskuren kaf family dinmu seta zaga ta kaskan tar da kanta ta fadi abinda tayi duk da ga wan nan video din hakan be wada ceniba, ga tsuhuwar soyayyar data lalata wadda suka juma suna ginata kan tafarkin gaskiya dole bazan bar matar nan taji dadin rayuwa ba koda kuwa zan iya rasa raina ne sena dauki fansa" dogon numfashi Farida taja kana tace 

   " OGA Omar wan nan ay ba abin tada kai tsaye bane kan wan nan dan karamin aikin, saboda raina aikin danayi ko sunana ban boyewa Maya ba don tana ganin ita din me wayau ce, duk da zakaji shwara ta wani kala, amma itace hanya mafi sauki dazesa idanun Maya ya raina fata tayi duka abinda kake da bukata, kamar yadda tayi amfani da irin son da mahaifiyar ka kewa mijin ta ta yaudare ta haka kaima zakayi amfani da wadda tafi kauna sama da komai a duniyar nan ka dauki fansar ka....✍️