🧑‍🍼 RABO...❣️

17

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode eighteent

  Kallon cigaba inajin ki Omar yake mata hakan yasa ta cigaba da magana tana cewa " Maya abinda yake mafi soyuwa a rayuwar ta shine autar ta zainab" wani irin dumm Omar yaji heart dinsa na dokawa cigaba da magana tayi " muddin ka rabata da wan nan yarinyar idanun ta zasu raina fata haka zalika dole ta kwantar dakai tayi maka duka abinda kake da bukata, wan nan hanyar itace nake gani mafi masa laha idan akace za a dauke mijin ta shiba yaro bane bincike seyafi tsauri akansa yana da hankali da tunani kuma sabanin baby datake yarinya duka 12 years take yanzu ajeta bazeyi wahala ba akan mahaifin ta" 

   Shiru Omar yay yana zurfafa tunani sedai ya tsinkaya muryan Farid yana cewa " Ay wan nan itace mafita madam Farida yarinya 12years ay bazatayi wahalan sarra fuwaba ko za ayi shekara nawa kuwa za ayi  zamu iya Adana ta abu daya dazakiyi yanzu duka wani information nata zaki bamu  yarinyar da wani time ake iya samun su a waje?" Murmushi kawai Farida tayi tace " abinka da Auta 'yar gata duk time din zaka ganta a waje to tana tare da Dad din ta ko mummy ta hanya daya ne datake free gareku shine time din school din su, shine kawai driver ke kaisu school ita da sister dinta" 

   " Good! Abinda nakeso naji kenan dama ay in Sha ALLAH ayki kamar anyi an gama shine " or ready dama Farida tagama hada duka bayanan daya kamata akan baby wan nan dalilin ne yasa bata wani tsaya musu bayani ba ta basu shi ta musu sallama ta koma gidan ta da suka kama mata itama don nata aikin be kareba kam har yanzu, kallon su Omar kawai yake harta fita yana kissima abubuwa dayawa a ransa yana kumajin wani tsananin tsanar Maya a ransa da autar tata da akace tana so, dafashi Farid yay yace calm yourself down big man in Sha ALLAH komai zeyi dai dai"

   " How? Farid taya kake ganin komai zeyi dai dai? Har abada matar nan ta gama cutar da mahaifiya ta komeye zan mata a duniyar nan baze kai rabin wanda tayi mana ba ta riga ta gama zubar mana da mutumci" numfasa wa Farid yay kana yace " kayi gaskiya tabbas! To amma kasani tabbas matar nan zata dan dani menene bakin ciki Madam Farida tayi gaskiya zatayi nadama zakuma ta shiga kunci Linkin wanda ta samu haka fargaba da tsoro kullum zasu kewaye mata rayuwa zata raina kanta dole" 

  Seda ya nisa tukunna Omar yadan cije lips din sa yace" Allah ya shigo da autar tata hannu na, zatayi nadama tafi dubu setayi kuka har hawayen ta ya kare seta shiga kuncin da Ammi bata shige shiba zatasan ta dauko wa kanta rigimar daya fi karfi ta " atare suka gama karance bayanan baby da Farida ta basu saboda abin dariyar dake cikin sa Omar harda murmusawa hadi da abin takaici ga kwadayi koda suka ga sunan makarantar tasu nan take Omar ya bada aiki akanta cikin guards din sa sunjima sosai suna tattauna wa akan lamarin kafin su kwanta tsaf suka gama searching komai akan school din yadda dokokin su yake_

     Bayan kwana biyu Omar Kano yagama tsara plans dinsu shida Farid da madam Farida, bangaren Maya kuwa zaune suke a parlour din ta itada sadiya tanata kokarin yin kira cikin wayan ta harta gaji tayi tsaki tana cewa " kai wan nan jaraba Farida ina kika shiga? Tun Shekaran jiya da dare nake kiran number din ta a kashe gashi basa gidan nidai tsoro na Allah  kasa  ba wan nan azzalumin mijin nata ya saketa ba, to amma kuma ta tafi bata fadamin bah"

  Tsaki sadiya taja gami da cewa " toke wai meye naki na wan nan damuwan ne? Naga dai itace za a temaka toba seki kyale taba idan ta fasa canda matsalan ta ni inbanda kin dage ma banga dalilin daze sani hulda da itaba" 

  " Wai sadiya meyasa bakya jituwa ne da Farida? Ni na kasa gane muku wlh mata me saukin kai ga kirki amma batai miki bah haba sadiya! Koda yake komai yazo karshe in Sha ALLAH zan san yadda nayi na daidai tsakanin ku" tabe baki sadiya tayi kana tace " Naga alama wan nan Farida nan gaba seta fini matsayi a gurin ki, a iya sanina duk wanda yake takura autar ki bakya kaunar sa kenan har abada, amma ita segashi abin mamaki ita har cimata mutum ci take a gaban ki kuma kina kara yabon ta haka" murmushi kawai Maya tayi tace " DUK wani abu da Farida kewa Baby matsayin wasa nake daukar sa don sanin kanki ne kinsan tanada barkwanci "

  " Lallai Maya kinyi nisa, to nidai zancen ya isheni haka, yunwa nakeji yau me ma aikatan gidan naki suka girka ne?" Dariya kawai maya tayi tace" Ay yanzu babu girki a gidan nan sedai su masu aikin nasu banda mu umarnin Baby ne tace duka basu iya girki bah  zamuje restaurant muyi nak semu dawo gida yanzu ma nasan sun kusa dawowa school mutafi" jinjina kai kawai sadiya tayi dataji abin ya girma meta ta mike kawai ta nufi kitchen din tana kara tsinewa Baby a zuciyan ta tana karajin tsanar ta over don iskancin da baby take kam itama yasoma kaita karshe,

     Omar Abuja kuwa lamarin sa se du a i, ciwon kai ya sawo shi a gaba dalili kuwa yadda yake tursasa zuciyan sa akan tunanin Zainab, yauma Omar kano zuwan bazata yayi masa, ya sauke sa a dakin hutawan sa don yana bukatar hutun tausayi sosai ya bawa Omar ganin yadda yaketa juya kai duk saboda Ammi shi yashiga wan nan halin, numfasawa yayi tukunna yace " har yanzu kana fama da ciwon kan nan kenan?" 

" Omar lamari na a yanzu ni kaina yana bani mamaki, harna gaji da ganin doctors akan lalurana" 

" Ay irin wan nan matsalan naka bana doctors bane, time din da daddy na yayi irin shi maganin Hausa yayi gurin wani malamin abokin sa dake nan garin ma, nida shi muke zuwa ansar maganin kuma Alhmdlh munyi nasara meze hana kaima yanzu ka jaraba "

   " Ada nafara wan nan tunanin harna fara magana da mahaifin na, so tunda kazo da wan nan maganar fyn se kamin baya ninsa kawai dama aiyuka sunyi mana yawa yanzu a company din nan bani da wani time wlh gara da Allah yasa yana garin nan ma" 

   Yan school kuwa baby Allah Allah take a tashe su su koma gida kuma a shiga gari saboda ba islamiyya takaici ne ya kamata kuwa bayan an tashe su driver bezoba takaici ya isheta  Fanan tasawa kuka gashi har an soma watsewa tanata rarrashin ta tamaki sauraren ta ita kawai taje ta nemo musu mota su tafi gida bayadda ta iya da baby jikin ta a sanyaye ta kamo mata hannu suka fito daga cikin school din tace suje titi suhau mota su tafi gida amma sam ta turje cikin muryan kuka tace " wlh yaya bazan biki titi a rana ba haka kije ki taho da motan ina jiran ki ni haske min ido takema bazan iya shiga ba" 

  " Please sister ki daure kinji mutafi babu nisafa zamu fita titi please" make mata kafada Baby tayi tana pouting din bakin ta, " it's okay zoki hau bayana na Goya ki tunda ranar ce bakya so ki kwanta a bayana ki rufe eyes dinki har mukai titin " hartayi kamar ta aminta ta kuma yamutse mata fuska tace " Yaya i can't ranar da zafi fah dayawa sedai in ciki zaki maidani" ta karashe maganar kamar zata fashe da kuka haka itama cikin marai rai cewa tace " i beg you sis bana son na tafi na barki a nan ne, sedai in school zaki koma toh idan nazo na miki magana" seda baby ta juya ne ta hangi school din nasu tasoma dire dire tana cewa " ni wlh bazan koma ba kalli har an rufe gate din ma kowa ya tafi dana san haka ze mana ana tashi motan school zamu bi mu tafiyan mu kuma sena gayawa daddy ya koreshi tunda yamin haka " ta karashe maganar cikin fushi ganin abin na kanwar ta bana kare bane yasata cewa " to yanzu dai kada kije ko ina bari naje nayi sauri na taro 🚕 mu tafi gida time na kara tafiya " daga mata kai kawai baby din tayi ta tafi tanata waigen kanwar tata harta gitta ta gefen motan Farid wadda take didim da tinted yana zaune a ciki duk abinda ya faru akan idanun sa wanda ya shagala da kallon  ta  harya mance meyazo yima seda yaga gitta warta tukunna ya dawo nutsuwar sa yana cigaba da kallon bayan ta ta mirror yadda take tafiya cikin nutsa wanta me daukar hankali murmushi mugun ta ya saki a fili ya furta " yarinya tsautsayi ne yasaki kin bin yayar ki ta wani bangare kuma kin temake ta ba rabon taga yadda za a rabaku akan idanun ta" ragowan guards din su dake bakin titi yayma waya kawai yace aikin nasu ma ya canza kome zezo da sauki su tafi kawai Ahankali ya karasa tafiya inda baby ke tsaye tanata wasa da zofen azurfa dake hannun ta yaji dadi matuka da ba a bakin school din tasu take tsaye ba duk da fuskan sa dauke take da facemask sallamar data jine yasata dagowa tana kallon sa duk da yasa facemask hakan be hanata gane yana mata murmushi ba " Am sorry daddy's little lover! Driver ya bata miki rai Koh" cikin taushin murya da rarrashi yake mata maganar batace kalaba illah kallon sa kawai datakeyi cigaba yay da cewa 

   " Dad ne ya turo ni na kaiku gida, Sabida driver bashida lpy yace na kula masa da auta sosai, yace ku 2 ne ina sister din taki take?" Tura baki gaba tayi tace " da wayace karka zo da wuri harta tafi taro mana taxi kuma sena gayawa daddy ka shanya mu a rana" sosai yay murmushi Farid na samun nasara ya kara ran gwadar da kansa yana cewa " Eyyah to sorry, ya zamuyi da sister din taki yanzu?" Tabe baki tayi itama tace " kajira ta dawo semu tafi " dan waro idanun sa Farid yay yace " a ah gaskiya ki shiga mota muje titin mu dauke ta baiwar Allah zatayi ta shan rana " shiru tadan masa tana kallon sa se kuma ta murguda baki tace " eh din ka jira ta dawo yadda kasa mu jiranka kaima seka jirata " azuci Farid yace kallai yarinyar nan kardai baki da kunya! Aikuwa dakin sha wahala" gyara tsayuwa sa yayi yace " okay mu jirata harta dawo din kuma ki sani tunda muka bata time a nan bazan tsaya nasai miki ice cream din da Dad yace na siya miki bah " tunda taji an ambaci ice cream ta me goya schoolbag dinta tana cewa " muta fi naji mu dauke ta kai kama isa Dad yace ka siyan Ice cream kaki " shidai Farid guntse dariyar sa yayi ya juya ya bude mata bayan motan ta shiga ya rufe yaje mazaunin driver shima ya shiga abinsa zuciyan sa kal da farin ciki ga dariyar ta dake cinsa ita adole shi driver din ta koh ta wani hakin ce abaya akwai jin kai yana murmushi me sauti kasa kasa ya dauko wani wani kwalba ya bude murfin ta tukunna yace " Baby fara shan wan nan ice cream din kafin mutafi akan hanya na kara muku keda sister din taki" 

  Cikin zagwadi baby tayo gaba dafda kujeran sa sedai taji yama haban ta wani irin azabab ben riko tana shirin kwalla kara ne taji yana tuttule mata abinda ke cikin kwalbar nan danan kuwa tayo waje da idanu kuru kuru jin abin na tafiya har cikin ta seda ya gama tsiyaye mata abin cikin kwalbar tass san nan ya saketa bekara bi takan taba yaba motar sa wuta harseda yabar layin tukunna ya juya yaga ta soma tafiya luuu zata kifa kan kujeran dariyar dayake dannewa ne kawai ya fara  yana cewa 

  " Yaro man kaza....✍️