19
by @nanabmb
🧑🍼RABO!!❣️
*NA*
NANA BMB
Episode twenty
Mikewa Farid yay ya nufo ta wanda hakan ne yasa ta sakin kukan da take danne wa ya fito cikin tsoro tasoma ja baya tana dada yage Baki tana kiran mummy ganin yana shirin cin matane taxura a guje suka shiga zagaye a parlour din yakas cin mata gurin gudu ne kafar ta ta bige ta da gefen kujera ba shiri ta auka kanta kafin ta mike ne yayo mata rumfa ze fara rarrashin ta ta kwaye baki zata sandara uban ihu yayi azamar dora hannun sa a bakin nata yana cewa " Baby ki nutsu mana niba mugu bane kinji ko ki nutsu ki saurare ni" saurin daga masa kai tayi duka ilahirin jikin ta na tsuma saboda tsoro yana dauke hannun sa kam da saki wani kara tana kwalama mummy kira da Dad duka hannu biyu yasa ya toshe kunnen sa saboda ihun har tsakiyan brain dinsa ya shiga ba shiri ya kuma kai hannu ze toshe mata bakin yaji wani kafirin cizo wanda yasa shi sakin kara batare daya sani bah mikewa kawai yay daga rankwafa war dayay yana yarfe hannun sa don tabbas ya cizu ba karya 😂 hakoran na baby ba abin raina wa bane gasu kananu amma sunsan takalan mugun ta, ganin ta diro a kujeran ne zata kara tayar masa da hankali yay azamar tarar numfashin ta yana cewa " is ok stop crying mummy ko to bari na kira miki ita" kallon rainin hankali tasoma masa wanda yasashi kuma hade rai shima yace " idan kika kuma shouting anan bazan kira taba don haka ki nutsu" murya kamar zatayi kuka tace " meyasa ka kawo ni nan ina su mummy din suke mezanyi anan kuma?" Cikin muryan kuka take tambayar sa saboda gaba daya a firgice take dashi, seda ya gama nazar tatta cikin kallon ta dayake yi yace " su mummy suna gida itace ma tasa na kawoki nan so in kika kwantar da hankalin ki ma dakan ta zatazo ta dauke ki ku tafi gida"
" Liar!! Kai makarya cine bazan taba yadda dakai bah mugu kawai! Ka maidani gida inba habaka nayita maka ihu!" Tana maganar tana zubar hawaye duka fuskan tayi jage jage da hawaye da majina" zama kawai yayi cikin duba hannun sa dayake yine yace " kije kiyi wanka kizo kici abinci sena kira mummy din taki ki tambaye ta dakan ki ta baki amsa" cikin takaici tace " bazan yi wankan bah ina ruwan ka dani kawai ni ka kiramin mummy!" Tana maganar tana matsar kwallah seda ya kalle ta nadan lokaci tana tsaye kikam tukunna yace " to nima bazan kira tanba kiyita tsaiwa anan" mikewa yay ya ciro ice cream din dasuka siyo mata ya aje kan dining table ya dora kafafun sa akan dining din yana kadasu cikin rashin mutum ci yace " kuma wan nan ice cream din nan gani nan bari yarinya indai bakiyi wankan ba bazaki shashiba kuma bazan kira tanba"
Jikin tane yayi sanyi mussam man robobin ice cream din data gani karaso wa tayi kusa dashi cikin muryan kuka tace " promise me please zaka kira min mummy idan nayi wanka kuma zansha ice cream din" cikin murmushi Farid ya daga mata kai itama jin jina masa kan tayi tace " to nuna min bathroom din" ba musu kuwa ya kaita har bakin bayin wankan ze juya tayi maza ta riko shi har yanzu hawaye na zuba a idanun ta hakan yasashi mamaki ita hawaye da alamu shiyafi yawa a jikin ta kallo daya zaka mata kasan akwai tsoro a tare da ita har yanzu murya na rawa tace
" Ayni ban iya wankan ba mummy ce take min!"
Tose ki fara koya daga yau ay, ko kuwa a tunanin ki ni zanyi miki wankan ne?"
" Allah bazan iya wankan ni kadai ba!" Ta karashe maganar tana sakin wani marayan kuka dariya kawai yay yace " wlh yarinya dama kika samu sedai kizabi daya kuwa ko kiyi wanka koki fasa shan ice cream din can kam" tunkan ya rufe baki ta auka bayin yana murmushi ya koma parlour ya zauna yana cigaba da kallon TV har seda yama manta me tashiga yine yajiyo motsin ta yana dago wa yaga ta dauro towel har yana jan kasa saboda yayi mata yawa kallo daya zaka mata kasan anci mutum cin soup da man shafa wa gimtse murmushin dayake shirin yi yay yace " meye kuma zaki wani fito da towel sejan kasa yake zaki bata mana towels ina kayan naki yake dazaki fito a haka?"
" To ay kayan sun jike!" Ta fada a shagwabe tana tura baki gaba, shima kuma haushin ne ya kamashi cikin jaraba yace " wani kayan zaki saka yanzu da kika kama kika jika wa 'yan can kawai daga wanka zaki kama ki jika kaya ya kikeso nayi dake kenan yanzu a wan nan daren zan fito siyo miki kayane tunda ajeni kikai!" Betako kumabi takan saba saboda yunwar dake kwakular mata ciki taje ta dauka ice cream batare da bata time ba tafara sha yana kallon ta yana antaya mata harara ko ajikin ta kuma seda tayi nisa ashan abun tane tace " dazaka kawoni nan din ita mummy din bata baka da kaya naba? Har kanamin hayagaga Allah sena gayawa Dad yasa an maka duka tunda kake sani kuka" tana maganar cikin zallan yarintar ta, tsaki ya buga san nan ya mike yaje bedroom din ya buda wardrobe ya samo mata wani dan gajeran wando da riga duk kayan itace kadai zata iyama jikin ta duk da inner ce rigar saman wuyan nata a matse yake gata me santsi watsa mata su yay kan bed ya koma parlour din seda ta gama shanye roban ice cream biyu ta mike harda gyatsa ta zauna gefensa cikin shan toka tace
"kira min mummy"
Cikin tsare gida shima yace " jeki kisa kaya tukunna sekizo na kirata, suna kan bed kayan na dauko miki" ba musu ta mike ta shige ciki ganin kayan ne ya kara hassala ta Farid be ankara seji yay ta watso masa kayan a jiki tana cewa " Allah ya sawaka nasaka kayan maza a jiki nah kallin su burum burum zakace min na saka Allah ya kyauta" seda ya karewa kayan kallo ne ya dago yaga ta zauna ta cukule baki tana kallon TV watso mata kayan yay shima cikin bacin rai yace " to karki saka kinji! Karki kuskura ki kuma cewa ma na kira miki mummy tunda bakyajin magana!"
Kuka tasa masa tana cewa " to taya zan iyasa kayan maza a jiki nah ay bazan iya bama" ko inda take be kara kallon ba ganin hakan ne yasata soma gun guni ga mamakin Farid se gani yay tana shirin sutale towel din a gaban sa yay saurin kara kar katar da kansa yana kallon wayan sa kasa kasa yace " gaskiyar Madam Farida dai da tace baki da tunani" bayan tasaka wandon ne tasoma kiciniyar saka rigar seda ta saka hannun rigar ne ta kasa zura wuyan takaici ya tuke ta kamar tai kuka tace " to ka karasa samin rigar mana ni bazan iya bah!" Wayan sama yasoma latsa wa ya mata banza ta kuma magana ya share ta kawai seta zaga ta site din da fuskan nasa take tana mika masa hannun ta data zura musu rigar dafe goshin sa yayi yana cewa " Haba baby meyasa bakida hankali wai!" Tana dire dire ta Cilla masa rigar kawai tasaka kuka ta koma ta kwanta akan kujera tana kuka me ban tausayi tana kiran mummyn ta, ahankali yasoma juya kai yana kallon site din datake kamar wanda zega abin tsoro, yaga ta kwanta rubda ciki tanata kuka girgiza kai kawai yay ya dauka rigar ya tsaya akan ta yace " sorry taso nasa miki rigar tana mikewa ya rintse idanun sa tukunna ya saka mata wuyan rigan seji yay tana dariya seda ya gama saka mata rigar ne ya bude idanun sa yana kallon ta tana nunashi tace " saboda zaka saka min riga shine kake rufe idon ka!" Tana maganar tana dariya kallon yadda rigar ta dan kamata yayi "Banason nagano wa kaina ne" cikin rashin fahimta tace " mezaka gani?" Tabe baki yay yace meko zan gani anan da wani shafaffen kirjin ki" kallon kirjin nata tayi tana tabe bakin nata itama tace" To da me kake so kirjin nawa yayi?"
" Kinga taso kici abinci ki kwanta dare nayi" cikin tabe baki tace " banacin abinci fa da dare nariga Nasha ice cream, kuma banajin bacci homework dina kawai zanyi bayan na gama waya da mummy" seda ya koma gefe ya zauna koda yay kira yasaka wayan nashi speaker number din daya kira akace a kashe take cikin basar wa yace" Tom number din mummy a kashe tayi bacci bakiga time bane yanzu kowa yariga yayi bacci se gobe kwayi magana" harya kare magana baby tana galla masa harara tasoma gunguni da kasa kasa tana zabga masa hararan kasan ido again cikin shan toka don kada tanemi kara daga masa hankali akan mummy din yace " Ke! Ni kike zagi!!" Ya fada a tsawace har seda 'yan cikin ta suka juya kamar zata fashe da kuka tace to ina schoolbag dita homework zanyi" harga Allah ta bashi tausayi amma ya basar yace " in kinyi homework kiyi me dashi?"
" Oho maka! Nidai babu wanda ya isa ya hanani zuwa school gobe ehe!!" Tana murguda baki tana maganar baki kamar ze tabo bango yadda take turashi gaba yi yay kamar be jitaba ya cigaba da kallon TV seda ta gama kunkunin tane taje ta dauko chocolates din dake cikin ledan Ice cream din tanasha tana kallon TV din itama gaba daya seda hankalin ta ya dauku ne ya juya yana kallon ta chocolate kawai take sha abinta ga gashin ta data jika anyi mata two babies ya sauko har bayan ta jelen tufkar da akayi gashi ta jike kan kawai ya tabe bakin sa a zuci yana cewa " kalli gashin ta sekace na babbar mace wata 'yar mitsili da ita" lallausan murmushi ya saki Saboda tuno da Fanan dayay yana kallon baby din still yake tunani dama shida Fanan din ne suke a tare yanzu daya nuna mata zallan abubuwan da zuciyan sa takeji game da ita ba wan nan 'yar kucilar mara kunyar ba, ita kuwa ko a jikin ta harda canza channels na cartoon aka harde kafa ana kallo, gyara kwanciyan sa yayi kawai ya lumshe idanu yana tunanin Fanan sedai ya tsinkayi muryan ta tana cewa
" Toni a ina zan kwanta? Bana bacci ni kadai kuma bazan kwanta a kan kujera bah" batare da ya bude idanun saba yace " don't worry ki gama kallon muje dakin zanyi gadin ki har gari ya waye" ita kanta tasan magana ya gaya mata ta tabe bakin ta ta kuma dukufa kan TV shikuwa saboda gajiyan tafiya yana cikin tunanin Fanan bacci yay gaba dashi wanda bashi ya farka ba se wajan 3 na dare yaga TV nata aiki ita kadai baby tayi bacci juyi daya ne zatayi ma ta fado kasa kashe kayan kallon yay ya maida ta bedroom din ya lullube ta seda ya tofa mata Addu'ah ne yakoma parlour din shima yay tashi Addu'ah din ya kwanta.
ASUBA TA GARI ✍️